ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 36

ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 36

ANA BARIN HALAL....: 

*Page 36*

*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559

*********
Ina shigowa kuwa na haɗu da yaya Ahmad wanda fitowan shi kenan daga ɗakin ummie, kallo na yayi yana murmushi yace,   "barrister ya tafi kenan?"  murmushi nayi na ɗaga kaina sama alaman ehh,  murmushin ya sakeyi yace,  "A.G mutumin kirki ne ayshaa, ki so shi xakiji daɗin zama ɗa shi, dattijo ne sosai, kuma bayida hayani, idan Allah yasa yazama mijinki zakiji daɗin zama da shi",   murmishi kawai nayi ina zama akan ɗaya daga kujerun parlon, muna haka ummie ta fito hannun ta ɗauke da filet, da sauri na miƙe na karɓa na wuce kitchen,  sallama sukayi da shi ya wuce gidan shi.
Ina fitowa naga ummi bata parlon, wucewa nayi har ɗakinta na sameta suna shirin kwanciya ita da hafsy, don ɗakinmu sai da baƙi sosai a gidan muke kwana, ɗakin ummie hafsy ke kwana ni kuma ɗakin hajiya ummah,  sai da safe na mata, sannan na wuce side ɗin hajiya ummah, bayan ummie ta biyoni domin rufe musu ƙofa.
  Wuraren 10:00 na dare kuwa sai ga ƙiran shi ɗan halak, dama na shiga ɗakin hajiya umma ɗaya  wanda muka mai da shi namu, a zuciyata nake maganan shi akan yaƙi ƙira, hala ma ya ƙira wancan ɗayan ne, tsaki naja bayan na kashe wutan ɗakin na hau zan fara addu'a, kawai sai ga wayan shi ya shigo, ido na zubawa wayan yayita neman agajin ɗauka ban kula shi ba, yana katsewa wani ƙiran ya sake shigowa, shima har ya kusa yankewa tukun nasaka hannu na ɗauka.

Ajiyan zuciya ya sauƙe mai ɗan sauti, shiru mukayi dukkan mu babu wanda yayi magana, amma kowa yana sauraran sautin bugun zuciyar ɗan'uwan shi,  mun ɗauki sama da mintuna goma babu wanda yayi koda tari ne, har nayi niyyan  kashe wayan, amma kuma kaman wanda yake duba sai naji muryan shi a ɗan shaƙe yayi magana,   "beauty na dawo gida, mummy ta ɗan tsayar da ni muna hira",  ajiyan zuciya na ɗan sauƙe a hankali, sannan nace,  "bakayi wayan ba kenan"? Shiru yayi kaman mai tunani, don shi gaskiya a gefen shi ya manta da maganan wata da yayi bayan Eeahan shi, chan kuma abun ya faɗo mishi a rai yace,  "ni na isa na ƙira wata bayan na miki alƙawarin ke zan ƙira? Heedayah ma tana gaishe ni nayi kaman ban san tana wurin ba, ganin haka itama tayi ta kanta".
Dariya ne ya suɓuce mun,  "ni fa bance maka har da sisters ɗinka kada ka kula ba",  na faɗa ina riƙe dariya na, don yanayin yadda yayi maganan ya sakani dariya,   "ok tou nagane, banda su heedayah, tou ƙirgamun wanda baki son na dinga kula su beautyn A.G".
 Gyara kwanciya na nayi nace,  "wannan yarinyar da friend ɗinta",  ina jin shi yace, "one",
Murmushi nayi nace ko wacce mace idan ba ƴan gidanku ba ko kuma tsufaffi, har ƴan office ɗinku",  ina gama faɗa na saka hannu na toshe bakina, "insha Allahu zan kiyaye beauty, sai dai ina neman alfarma guda ɗaya a wurinki", ya faɗa da mugun nutsuwa a muryan shi, ban amsa mishi ba naji yafara mun bayani,   "Eesha ni mai tsare kaina ne sosai, kuma zan ƙara fiye da yadda nake a baya, ni lawyer ne dole wasu matan zasu neme ni akan damuwan su, insha Allahu na miki alƙawari daga abunda ya haɗani da su babu wani abu da zai biyu baya, sannan Ina da family both side, mummy da daddy nah, kuma akwai mata,  insha Allahu zan tsaya dai dai da yadda shari'a ya umurce mu dayi,  wata mace insha Allahu bazata ga dariya na ko murmushi naba idan bake ba, sai dai a bisa kuskure, zan tsare  miki kaina yadda bakiyi zato ba, amma kema bana son ki kula ko wanni saurayi please."
 Wani irin nutsuwa ne yazo mun a zuciyata, wanda bansan meye dalili ba,  "ni ae bana kula samari, ni basu ma burgeni,"  na faɗa ƙasa-ƙasa da murya,   "amma dai ni ina burge ki ko"? Naji muryan shi yana tambaya na, runtse ido na nayi, sannan nace,  "ni tausayinka kawai nakeji".
 "Alhamdulillah" naji ya faɗa, sannan kuma naji yace,   "Eesha kin gama mun komai a rayuwata, duk macen da take tausayinka tou ba ƙaramin so zata maka ba, Allah na gode maka",  ya faɗa da ɗan ɗaga muryah.
Zaro ido nayi ina rufe bakina da hannu ɗaya,  "nifa ciwon kanne yake sani tausayi bawai sonka.....",  sai kuma nakasa ƙarasawa, saboda yau ɗaya kawai naji ina jin kunyan nace bana son shi, haka dai mukayi ta hira wanda bansan ma 12:00 am yayi ba, sai da naji yace nayi haƙuri ya jani muna hira har 12, sallama mukayi kowa ya kashe wayan shi.


********
Washe gari yazo amma a parlon hajiya ummah muka zauna, sallama ya mun akan gobe zai wuce Abuja, don tanan zai tashi, yau banji yana jana da hira ba kawai shiru yayi ya ƙura mun ido, har narasa yadda zanyi da kallonshi, duk ɗago kaima kuma sai ya ɗaga mun giran shi sama, haka dai har 9:00 tayi sai yace nayiwa hajiya umma magana suyi sallama zai tafi gida, tashi nayi naje ɗakin na mata magana, sallama sukayi tana ta saka mishi albarka, da alƙawarurruka  Kaman itace mai auren shi,  bunch na 500 ya ajiye mata ya fice, tana ta zabga mishi addu'a, nidai nabi bayan shi, muna fita yace muje yayiwa ummie sallama, haka naja tsummukaran ƙafana jiki a sanyayae na raka shi har parlonta, suna tare da hafsy da yayah Ahmad, hannu ya miƙawa yayah suka gaisa, sannan ya gaishe da ummie, nidai gefen hafsy naje na zauna kaina a ƙasa,  hira suka ɗan taɓa kaɗan, sannan yayiwa ummie sallama akan gobe zasu wuce tare da yayah Ahmad, flight na ƙarfe 9:00am zasu bi, hafsy ya ƙira sukayi waje, chan sai gata ta dawo, hannunta riƙe da envelop an saka 100k wa ummie,  sannan tace mun naje yana jirana a waje, ni dai tashi nayi na fice, ina jin ummie nayiwa hafsy faɗan meyasa ta karɓo, ita kuma tana cewa, ko da wa ita yabayar karɓewa zatayi wallahi, tana faɗa tana dariya abunta, haka dai na wuce nayi waje.

A jikin motan na tsaya hannu na riƙe da murfin motan,  shi kuma yana zaune a driver sit, ƙafan shi ɗaya a waje ɗaya a ciki, hannun shi akan stearing motan, dukka ida nun she a zube a kaina, munyi shiru babu wanda ya tanka a cikin mu, chan dai nayi ƙarfin hali nace,  "kana ta hidima dasu ummie da hajiya ummah, an gode Allah ya ƙara buɗi",  baice uffan ba sai ido dai da yaci gaba da zuba mun su,  ɗago kaina nayi muka haɗa ido da shi,  "Beauty zakiyi mssn ɗina"? kawai naji ya faɗa ido a lumlumshe, Girgiza kai nayi alaman a'a, da sauri ya daga kanshi yace,  "shiyasa nakeso nayiwa yarinyar nan tambayan gaskiya, idan ta amsa mun kawai zanyi haƙuri na amsheta".
 "tambayan me zaka mata"? Na tambaye shi,   "ko da gaske tana sona, idan har da gaske ne zan bawa kaina haƙuri kawai ayi da ita",  ya faɗa yana wani ya mutsa fuska,  sama na ɗaga kaina kawai ia kallon taurari, batare da na sauƙe kaina ba nace,   "idan ta amsa maka kuma zaka sota? Bayan kache mun bazaka sake kula wata mace ba"?  Kallona na mayar kanshi jin yace,   "tou ae kene beauty, ni so nake kawai a soni, ke kuma kin nuƙe kin ƙi ki soni",   ya faɗa idon shi na kaina, idona cikin nashi ina jin yadda zuciyata take wani irin mugun harbawa,  a hankali na ɗauke kaina saboda yadda nake jin wani irin yanayi idan muna kallon juna, baki na tura gaba nace,  "tou ni dai bama son kayi magana da ita, bana son ma ka koma school ɗin",    "tou please Eeshaa ki soni",  ya faɗa kanshi tsaye, shiru nayi ina tunani, chan kuma sai nace,   "shine zai saka bazaka so wata ba" ido na akan shi,  lumshe ido yayi ya ɗan ɗaga mun kai alaman ehh,  "tou zanyi tunani, amma..... Sai kuma nayi shiru ganin Yayah Ahmad ya fito, ƙurawa Yayah Ahmad ido nayi, _Sai da ya Kusa isowa inda muke sai nayiwa A.G sallama na wuce, anan suka ɗan tsaya kaɗan, sai kuma naji tashin motan kowan su.

Washe gari suka wuce Abuja, zuwa dare kuma jirgin su A.G ya ɗaga, kafin ya wuce ya ƙirani munyi waya, washe garin  ranan tafiyan shi kuma ya ƙirani wuraren ƙarfe shida na asuba akan sun isa lpy,  daga wannan ranan kullum sau biyu a rana sai munyi waya da shi, wataran ma sau uku zuwa huɗu, amma bamu wani dogon hira da shi,  M.G kuma shiru banji ko sau ɗaya ya ƙirano a waya ba, nima haka sai na share shi.

*********
Kwanci tashi asaran mai rai haka dai rayuwa ta  lula damu har december, har satin bikin raliya, wanda har zuwa lokacin mamie bata san da maganan aure na ba, ana sauran 2weeks auren raliya kuma Aunty j ta haihu, itama ɗa namiji aka samu, wanda yaci sunan Yayah Auwal, wato *MUHAMMAD AUWAL*  amma suna ƙiran shi da Affan,  a zuwan mu sunane nasan M.G yana ƙasan yana Abuja abun shi, domin ranan sunan ma hafsy tace mun sun haɗu da shi, yace ta gaishe ni suna saurine zasu fita da yayah, nidai naji haushi, saboda meyasa M.G ya wani ƙaurace mun, babu waya babu ziyara, gaskiya Alƙawari baice haka ba,  haka dai nima na share batun shi, mun dawo kuma bikin raliya.

Mudai babu ruwan mu da wani rawan kan bikin, yayun mi dai duk sunzo daga Abuja, kuma har da Aunty B da Areef,  maijego kawai aka bari da wata ƴar'uwar ta, Adda ma tazo, Auntƴ ma'u ma tazo, gida dai ya cika da dangi sosai, ranan da za'ayi walima, da safe hadiza suka zo da ƴan'uwa na chan, zuwan tane ma ta jani muka shiga side ɗin mamie,  anan naga habiba, tayi wani irin ƙiba, ga cikin ya fito sosai, tana zaune a ƙasa tana shan kankana, gaisawa sukayi da hadiza, ni kuma ta kalleni fuskan ta ɗauke da fara'a, murmushi na mata, itama ta maida mun da gaggawa, sannan naga ta kalli gefen da mamin ta take zaune, ganin bata ganinta sai ta mum alaman nazo nasha kankanan, murmushi nayi na mata alamamn na gode tasha kawai,  haka dai tayita ƙureni da idon ta,  har muka gama muka fita fatar bakin mu bai furtawa juna komai ba,  tausayin ta cike da zuciyata.
A haraban gidan mu akayi haɗaɗɗen walima, wanda yafi na habiba ƙayatuwa, amaryah tasha kyau sosai, tayi shiganta mai kyau,  sit ɗaya muka zauna da ni da hadiza da maryam, domin tazo mana,  hafsy da ummita suna chan cikin friends, don raliya bata tsoron mamie irin habiba, ita da taga bikinta ya matso kusa sai ta jawo hafsy ajiki suka cigaba da sha'anin su, duk ɗaga kna da zanyi sai mun haɗa ido da habiba, kuma sai ta mun murmushi, nia sai na mayar mata, har magrib tukun aka watse, washe gari aka ɗaura aure, akayi wuni,  bayan la'asaar aka kai amaryah ɗakinta, naji ance bayan 1week zasu koma kaduna da mijin, don achan yake da zama, mudai washe gari muka bi Adda da Aunty ma'u muka ga gidan amaryah, gida yayi kyau sosai, don da muka fito naji Adda da Aunty ma'u suma hiran wannan karon mamie ta samu yadda ta keso, don Abba ya sakar mata kuɗi sosai bakaman na habiba, shiyasa tayi bushashanta son ranta.

Rayuwa tana ta jan mu da gudu har muƙa shiga watan Febuary, wanda yana daidai da saura 2month A.G ya gama ya dawo, alokacin idan kin kalli habiba sai ta baki tausayi, duk haskenta ya ƙaru tayi bauu ga kumburi da ƙafafunta da jikinta gaba ɗaya sukayi, wata ranan laraba ta tashi da wani azababben naƙuda, mamie har side ɗin ummie ta shigo ranan a ruɗe ta gaya mata, haka aka ɗunguma akayi asibiti da ita,  *RIMI CLINIC* Mamie da iyalenta suke zuwa, saboda haka chan suka nufa, bayan ummie ta umurce mu da mu ɗaura abinci nida hafsy,  babu nutsuwa a tare dani muka shiga kitchen ɗaura abincin,  chan wayan A.G ya shigo, a tsatstsaye na ɗauka na mishi bayanin aiki nakeyi, a cikin muryana ya fahimci akwai matsalah, tambaya nayi me yake faruwa, nan na gaya mishi habiba ce zata haihu, kuma tana shan wahala, rarrashi na yayi da kalamai masu daɗi, inda har yake ce mun saura mu, nida shi, yasan shikan duk ranan da zan haihu sai an mishi  Alluran bacci, dariya nayi na mishi sallama.
Wuraren 12:00 mun gama haɗa komai, hattah flask da akace mu sake cika guda biyu mun cika, driver ne ya ɗauke mu tare da mahma muka bi bayan su, isan mu kuma babu wuya akace Abba ma ya taso daga Abuja yana hanya shi da yayah Auwal, har ɗakin da take muka shiga muka duba ta, nidai sai da nayi hawaye irin wahalan da naga tana sha, mahma da ummie suna riƙe da ita akan tasha ruwan ɗumi, ita kuma mamie tana tsaye daga bakin ƙofa, idan anjima kaɗan kuma ta fita tayi kiran waya, abu dai har wurin magrib babu haihuwa, ana haka Abba suka iso, bayan ya dubata ne suka shige office ɗin Dr don suji ko yayah ake ciki, nan Dr yace idan ta cika zuwa 8:00 bata haihu ba zasu mata C.S,  haka su Abba suka wuce mosque sukayi sallah, har sai da sukayi ishaa tukun suka shigo, mu dai muna tsaye cirko -cirko a bakon ɗakin, shigan Abba bai daɗe ba naga mamah ta leƙo ta Ƙirani, jikina yana rawa nabi bayanta.

Muna shiga na kalli habiba rungume ajikin Abba tana kuka duk ta galabaita,  "Abba na roƙeka ka umurci mamie ta bani izinin magana da ƴar'uwata kafin na bar duniya, Abba ina son magana da Ayshaa kafin na mutu, Abba mutuwa zanyi",  ta faɗa tana ƙara kukan da takeyi, Abba ne ya dube ni sannan yace,  "Ni nabaki daman kiyi magana da ƴar'uwarki, ae da nasan duk tsawon lokacin nan ta hanaki zumunci da ƴar'uwarki wallahi da na ɗauki mataki, kuma yanzu ma bai ɓaci ba zan ɗauka akan kowa, da wanda ta hana da wanda sun san an hana basu gaya mun ba, Allah dai ya sauƙe lafiya habiba nah".

Kallon mamie tayi cike da rauni tace, "mamie ki gafarce ni na mata magana"? Ɗaga mata kai tayi tana share hawayen ta, hannu habiba ta miƙo mun, ni kuwa ban ɓata lokaci ba na ƙarasa jikinta, rungumeta nayi hawaye na zuba a ido na,  "sisto na kiyafe mun duk abunda ya faro, wallahi ɓa'a son raina nake ƙin kula ki ba umurni nake bi don na rabauta, amma kullu kina raina, ki yafebmun aure miki Aliyu da nayi sisto",  hannu na nasaka na rufe bakinta hawaye na yana zuba babu kakkautawa, itama hannu ta saka ta riƙe nawa dana Abba tace,   "Abba kazama shaidah duk abunda na haifa na bawa sisto duniya da lahira, idan mace ce a saka sunan sisto, idan kuma namiji ne sunan ka nake so Abba, ina kwaɗayin su yi rayuwa da halaye irin na ko, duk duniya babu abun da nake so irin kai da sisto na",  sannan ta dawo da kanta kaina tace,  "kicewa Aliyu na yafe mishi duk abunda ya mun duniya da lahira, kuma ku haɗu ku riƙe mun abunda zan haifa idan mai rai ne", azaban ciwo ne yasaka ta ɗan yunƙura kaman zata sauƙo, nan kuma likita ya shiga yace mu ɗan fita daga waje zai dubata.

Muna waje ina rungume ajikin Abba inata kuka yana rarrashina, gefe ɗaya kuma mamie ce ta sunkuya tana ta share hawaye ummi na bata baki, ita dai hafsy sunyi tagumi ita da mama da yayah auwal da hajiya ummu suna zaune a ɗan gefe kaɗan.

Muna nan har wurin 1hr likita bai fito ba, chan kuwa muka jiyo kukan jariri, wani zabura nayi zanyi ciki Abba ya riƙoni, ita ma mamie tashi tayi tsaye, sai Ummie ta hana ta shiga, duk jikima rawa yakeyi narasa murna nakeji ko kuma me nake ji, muna haka har bayan mintuna kusan ashirin sai ga nurse ɗaya ta fito hannun ta riƙe dababy a farin showel, da sauri na nufeta hannu na miƙa ita ma sai ta saka mun babyn fuskanta da fara'a, da sauri na buɗe ina kallon fuskan babyn mai tsananin kama da su jamilah, sai dai farine sosai kaman ƴan gidan mu, murmushi da fitan hawaye ne a fuskana, ina jin nurse ɗin tace an samu ɗa namiji, godiya wa ubangiji duk aka fara, Abba yana tambayan mai haihuwan fah, nan naji tace Dr yana duba ta, na daɗe ina kallon fuskan yaron ina jin wani irin ƙaunar shi a zuciyata, hannu Abba ya saka ya karɓi yaron, babu yadda na iya na miƙa mishi, addu'a ya mishi sosai, sannan ya miƙawa yayah Auwal yana zolayan su da nikan bazaku bani ƴar budurwa bane kam na cika ta huɗu? Kowa sai ya sulluɓu ƙaton saurayi munana, dariya su mamah sukayi suna mu ae haka yafi mana, ayita haiho mana mazaje, ita dai mamie dariyan yaƙe ne a fuskanta, amma duk hankalinta yana ga ɗakin da habiba take, yaron yana rie a hannun ummie Dr ya buɗe ɗakin da habiba take ya fito,  Abba ya miƙa mishi hanni suka sake gaisuwa, Abba yana tambayan shi yaya jikin ita mai haihuwan?  Share zufan goshin shi yayi sannan yace wa  Abba,  "Munyi iya ƙoƙarin mu mubata kariya ta haihu lpy, amma tana haihuwa wanda yafi mu sonta ya amshi abunshi, sai dai nace kuyi haƙuri wanda yafi mu son habiba ya amshi abun shi",  nidai abu biyu kawai naji bayan magana shi, shine naji muryan mamie da ƙarfi tace,  "Ƙarya kakeyi likita, habiba bana bata mutu ba",  sannan naji muryan hajiya umma tana "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wannan wani irin mummunan labari ne"?  Daga nan ban san me ake ciki ba, sai farkawa nayi na ganni a ɗakin ummi na akwance, gefe ɗaya kuma yayah Auwal ne yayi tagumi hafsy na gefen shi tana ta share hawaye, da hanzari na miƙe zaune nace,  "Yayah mummunan mafarki nayi, ina ummie nah"? Riƙo ni yayi da yaga ina ƙoƙarin zurawa waje a guje, Yace  "ina xakije Ayshaa"?
Da sauri nace "zanje parlor ne ummie ta rakani na duba yayah habiba take, mafarkinta nayi wai ta haihu......", sai kuma naji tsoron Ƙarasa faɗin sauran, hafsy ne naji ta fashe da kuka ta taso ta rungume ni,  "Adda ba mafarki bane da gaske kin rasa ƴar'uwar ki yau",  kallonta nayi baki a buɗe nace,   "kuma kinga ta haihu? Yaron namiji mai kama da su jamilah"? Ɗaga mun kai tayi tace,  "Adda ae har kin ɗauki yaron ma kafin a faɗa mana rasuwan".
  Juyawa nayi na kalli yayah auwal, muryana yana rawa nace, "yayah rakani na ganta",  hannu na ya riƙo muka fita har side ɗin mamie, muna shiga a parlor na hango mamah da  sai hajiya umma a zaune a saman kujera, sai wasu daga cikin ƴan uwan Mamie a parlon, ga mahaifiyar mijin raliya da wasu daga maƙotan mu, daga ɗaki kuma ina jin sautin kukan mamie da ake ta bata haƙuri,  ido na na mayar wurin dinn<ng ɗin mamie da aka matsar da kujerun aka kwantar da habiba a ƙasa, ga wasu ƴan'uwan mamie da suke zaune a gefen gawantan, juyawa nayi na kalli yayah Auwal bakina yana rawa ina nuna gawan habiba nace,  "Habiba ce wannan yayah"? Ɗaga kai yayi alaman itace,   "bakaga ana sanyi ba ne yayah aka kwantar da ita a ƙasa"?  Hawaye na bin fuskana, bai amsa mun ba sai ya juya ya fice a parlon, ɗakin mamie na shige na tsaya a bakin ƙofan ina bin su da kallo, idon ummi yana kaina ni kuma ina raba ido na, chan na hango babyn a kwance akan gado,  kallon mamie nayi da take ta kuka naji na ƙira sunan ta da ƙarfin da bansan murya na yana da shi ba,   "mamie kinga abunda kikayi ko? Ashe ƴar'uwata bazata daɗe ba, bazamu goyi yaran mu tare ba? Kin raba mu, bayan tace mun duk ranan da ɗaya ya haihu zamu kwana muna kallon babyn  mu saka suna mai daɗi, muyi wa junan mu takwara, mu so ƴaƴan, zata so nawa kaman nata, zan so nata kaman nawa, amma kin raba mu, ashe ma Allah a kusa zai raba tsakanin mu, kukan me kikeyi? Nice nan kuka ya same ni",  na faɗa ina buga kƙirjina, da gudu mamie ta taso ta rungume ni tace, "dukkanmu kuka ya same mu Aysha",  runtse ido nayi saboda kukan da naji babyn yana yi, juyawa nayi na fita zuwa parlor, direct wurin gawan habiba na nufa.

Allah ya jiƙan habiba ƴar uwarki hajiya Ayshaa, don nasan yau sai ciwon ya dawo miki sabo, Allah ya jiƙan ƴan uwan mu baki ɗaya, Allah ya raya abunda habiba ta haifa, Allah ya ƙara muku haƙuri da juriya,  makaranta littafin ANA BARIN HALAL.....  Ina roƙawa habiba gafaran da masu ganin laifinta tun farkon book ɗin kuyi haƙuri, kowani ɗan Adam ajizi ne,  amata uzuri rabon haihuwa yaron nan ne ya kaita auren Aliyu.

Don Allah idan anga errors ayi haƙuri, banyi editing bane ina sauri


*AUNTY NICE*