ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 26
ANA BARIN HALAL...
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 26
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
**********
Murmushi nayi na maida wayan a silent, ɗago kai nayi sai muka haɗa ido da yayah muhammad, ganin irin kallon
tuhuman dayake mun, bansan lokacin dana fara dariya ba ina rantse mishi ba fa wani bane daban
Yayah M.G ne fah na faɗa ina yi hanyar barin parlon, dariya suka kwashe da shi su biyu, ina jin muryan shi yana cewa yayah Ahmad kaji mun yarinya da tsarguwa, tou idan tayi wari zamuji ae, nidai ban ƙarasa jin sauran abun da suke cewa ba nayi gaba, sai dai ima jin dariyan yayah Ahmad, ina shiga parlon ban saurari su Aunty J ba na wuce ɗaki, rufo ƙofan nayi na nemi wuri na zauna, kaman jira yake call ɗinshi ya sake shigo mun, cikin nutsuwa na ɗauka ina mishi sallama, "sisto nayi fushi, nayi fushi da ke, munyi waya da ke fa jiya, amma ko kice mun zaki shigo Abujah, adalci kenan?"
Rufe fuskana nayi kaman yana kallo na ina dariya nace, "nifa na ɗauka yayah Ahmad ya gaya maka"? "sauƙe tou don dai kam bai gaya mun ba, kuma bashi ne ya kamata ya gaya mun ba, kece ya kamata naji daga wurinki, yanzu sai da A.G yagaya ya tukun na san kinzo, hala har muyita waya baza kice mun kinzo ba, don kada ɗan marayan Allah yazo ya ganki".
Cike da mamaki nace, "shi kuma yayah A.G ɗin yayah akayi yasan nazo"? Dariya ya kwashe da shi yace "wurin yayanki yaji kin san shi da bin dindigi yasan komai da yake faruwa a ƙasan, yakan riga sanin wani abun ma misali kaman wannan", ya ƙarasa faɗi yana murmushi, ajiyan zuciya na sauƙe, ni dai mamakin abun kawai nakeyi, "tou shi ina ruwan shi da sanin me nake ciki? Na ɗauka ma ya manta dani ae zuwa yanzu"? "kina ƙanwar aminin shi ne zakice ina ruwan shi da sanin me kike ciki? Tou ae yanzu ko shi barrister ba lallai bane yabi ƙwaƙwafin rayuwar ki irin A.G, kinsan shi fa yana da mugun kiyayewa akan abunda yasa a gaba, yanzu hala ma result ɗinki ma ya riga ki sani" ya faɗa yana dariya na.
Nidai share maganan nayi na cigaba da gaishe shi, "sai kin koma sch tukun zaki bar Abuja ko"? Najiyo muryan shi yana mun tamabaya, "ehh insha Allahu" na bashi amsa.
Kafin ki tafi insha Allahu zan shigo, domin yanzu akwai wani aiki dana tafi yi a Benin, kafin komawanki insha Allahu zan dawo", daga nan muka ci gaba da hiran mu yadda kullum muka saba, har muka gama hiran bamu sake sako sunan A.G a ciki ba, bayan mun gama wayan ne na fito zuwa parlor, anan na samu yayah Ahmad ya shigo, ashe ita kuma Aunty B har ma ta tafi gidan ta, ban wani ja lokaci ba nayi musu sallama na koma ɗaki, domin ummie tana yawan tunatar damu, idan munje gidan yayun mu muna rage zama a wuri idan suna tare da matan su, idan an taɓa hira kaɗan mu basu waje.
Kullum idan na tashi da asuba, ima idar da sallah nayi azkhar zan gyara gidan gaba ɗaya, kuma har side ɗin Aunty B nake zuwa na gyara, domin ummie ta horar da mu aiki, duk da sanyi na zakiyi mamakin yadda nake aiki, amma idan an haɗa ni da hafsy ne tou babu mai ganin saurin nawa, sai dai banbancin ƙyalƙyale wuri, gidajen nasu babu wani datti, sharewa nakeyi nayi mopping sai na kunna turaren wuta a kowanni sashi, domim tun dare nake wanke-wanke, kuma tunda naje bamu ɗaura abinci a side ɗin yayah Ahmad, wannan Aunty B ta ɗauke, sai dai idan tayi ta saka na kowanne side, ina gama gyara ko ina nake zuwa na kwanta tare da Areefh a side ɗinsu, sai Aunty b ta gama haɗa breakfast nake fitowa na mishi wanka nima nayi, don gaskiya bana tayata aikin breakfast, saboda ko dankali zata soya tun dare nake fere mata, ranan da zatayi masa ma ni na kwaɓa mata shi da wuraren ƙarfe huɗu na asuba, so bayan na musu ayyukan su sai na ɗan kwanta na huta, amma abincin rana tare mukeyi, don gaskiya ba kasafai nake barinta da aiki ba, na dare ma tare mukeyi, don ma bamu cika yin abinci da rana ba, saboda su yayah basu nan, magrib suke dawowa sai kawai ayi abinci ɗaya, zaman mu gwanin ban sha'awa, kullum muna tare da juna, gashi akwai ƙauna mai girman gaske tsakanin mu da matan yayun mu, don gaskiya ummie a tsaye ta ke da Addu'an haɗin kan iyalanta, kuma Alhmdllh Allah ya amsa mata.
*********
Rayuwa kullum ciki take burirrika, amma kwanakin mu kuma kullum ƙarewa suke, a haka hutun mu ya ƙare, dama 3weeks aka bamu, a haka har na shiga sati na huɗu, wanda lokacin nafara shirin komawa gida, zo kiga yadda hankalin Aunty j gaba ɗaya ya tashi, nidai har wani tausayi take bani, haka yayah Ahmad yayi ta rarrashinta akan idan ya maida ni zai taho da hafsy, insha Allahu ita ma zataji dadin zama da ita, babu yadda ta iya saboda ni karatu nake.
Ana saura kwana 2 na koma sai ga M.G ya dawo daga tafiyan da yayi, tun ana gobe zai dawo ya gaya mun na mishi special girki, saboda haka ranan Aunty B ta tayani muka mishi abinci kala biyu, sannan mukayi snacks kala wurin uku, muna gamawa na kwashe su zuwa side ɗin yayah Ahmad na jera akan dinning, sannan na wuce naje nayi wanka na shiryah cikin wata baƙar abayata mai kyau, Aunty Asma'u ce ta kawo mun ita bana da taje aikin hajji.
Wuraren ƙarfe uku suka shigo gidan shida yayah Ahmad, leƙowa nayi muka gaisa hannu na riƙe da na Areefh, ɗaga dukkan giran shi yayi yana kallona cike da mamaki, " barrister yayah naga kaman Ayshaa ta ƙara girma da tsawo? Anƴa zamu barta tagama school bamu aurar da ita ba"? Ya ƙarasa faɗi yana dariya, juyawa nayi da sauri na koma cikin ɗaki nima ina dariyan, gaskiya na daɗe banga yayah M.G ba, sai naga ya wani ƙara haske da kyau, gashi komai yayi kyau yake mishi, yanzu ɗaga giran da yayi sai yayi mun bala'in kyau a fuska, ina jin su suna ta hira da yayah Ahmad suna cin abinci, suna kan dinning ɗin har aka ƙira sallan la'asaar, daga nan suka wuce zuwa masallaci, bayan sun dawo ma suka cigaba da hiran su har zuwa wani lokacin, sai chan daga baya yayah ya ƙirani maje parlon, ima shigowa kuwa ya sake ƙura mun ido, fuskan shi ɗauke da murmishin shi mai kyaun nan, "ki zo ku gaisa da M.G, bari mu ɗan fita da yayah muhammad, bazamu daɗe ba zamu dawo", hannu na riƙe da gefen gyalen abayata ina kallon yayah har ya fita, bayan sunyi sallama M.G sai ya ƙura mun ido, har ajikina nake jin kallon da yake jifah da shi yayi mun yawa, saboda haka sai naja kujera na zauna, ƙasa-ƙasa na sake gaishe shi, kuma ban yadda dana sake yadda mun haɗa ido ba, shiru wurin ya ɗanyi na wani lokaci, kaman bazai ce komai ba, har na sake ɗago kaina amma sai charaf idon mu suka sake haɗu, da sauri na mayar da kaina ƙasa ina wani zazzare ido irin na rashin gaskiya.
Murmushi yayi sannan yace "ƴan mata ina labari"? Ɗagowa nayi na kalle shi, domin kalmar da ya jefe ni da shi wai *ƳAN MATA* ya taɓoni, kasancewar bai taɓa ƙirana da hakan ba, giran shi ya sake ɗaga mun fuskan shi ɗauke da murmushi, kafin ya samu zarran sake jefo mun wani maganan, sai ga wayar shi tana kawu wuta, alamar tana neman agaji, ina kallon shi fuska cike da murmushi ya ɗauka, "mummy barka da yau yyh bauchi"? Sannan jimawa kaɗan na sake ji yace, "insha Allahu zan shigo very soon mummy nah,"
Bayan yayi shiru na wani lokaci yana sauraran me wayan sai kuma naji yace "ganin nan ma wurin ayshaan mummy" babu daɗewa ya miƙo mun wayan ƙasa -ƙasa yana cemun. "mummyn muce na wurin A.G.
Cike da jin kunya na amshi wayan na shiga gaisheta, "Doughter nah yayah kike? Hope dai babu wata damuwa ko? Kuna gaisawa da A.G dai ko?" cike da jin kunyar ta na amsa mata gaisuwan, sauran kuma naji nakasa sakewa nace komai, sai murmushi kawai nake tayi kaman ina gaban ta, fatan alkhairi ta mun sosai da addu'a, sannan na miƙawa yayah M.G wayan cike da jin kunyar matar, sallama sukayi ya kashe wayan, ƙura mun ido yayi fuskan shi ɗauke da murmushi, "itace mummyn mu ƙwalli ɗaya da muke ji da ita nida A.G, itace mahaifiyar A.G dana fara baki labari wato Aunty Rashida, macece mai ilimin gaske da kirki, akwai shaƙuwa sosai tsakanina da ita, tana sona sosai kaman ita ta haifeni, abun mamaki kuma hiran da zamuyi da ita bazaki taɓa ganin A.G sunayi ba, wani lokacin idan tayi magana taga bai ce komai ba sai ta hau shi da faɗa, "ni dai idan baxaka ringa amsa mun magana ba a daina zama kusa dani, haba mutum yana naniƙe da kai amma kuma bazai yi magana da kai ba yadda ranka zaiyi daɗi", sai dai ni kiga muna hira da ita sosai, amma kuma idan kinga irin son da take mishi zakiyi mamaki, don idan ciwon shi ya tashi ta dinga kuka kenan, tana masifar son shi sosai".
Murmushi nayi ina sauraron shi, "kin san duk abun da ya shafi A G tana so, ballantana da taga ya damu da ke bakiga yadda take mugun sonki ba,", ɗago kaina nayi cike da mamaki nace "ya damu dani ko kuma dai ya damu da jin haushi na, har labari na yake bawa mummyn? Dama ya riƙe sunana ne?"
Dariya yayi yace, "ae duk abunda ko ni ko barrister ya damu da shi tou A.G ma ya damu da shi hala ma har yafi damuwa da shi, kin san tsakanin shi da barrister akwai wata ƙauna mai ƙarfin gaske, don tunda ga kaina bai sake sakewa da ƙaunar wani ba sai barr."
Murmushi nayi ina jijjiga kai alamar ina tare da shi, wayan shi a karo na biyu ta fara kukan neman agajin a ɗauke ta, murmushin fuskan shi ne ya wadata lokaci ɗaya, sannan kuma ya ɗauki wayan yana ƙara wadata murmushin, "A.G friend, kaman kasan yanzu hiran ka nakeyi", shiru yayi yana sauraran wayan, nidai ido na yana kanshi, can sai naga ya kwashe da dariya yana, "wallahi nida Ayshaa, yanzu ma na haɗa su suka gaisa da mummy",
Kallo ni yayi sai naga ya miƙo mun wayan, kasa karɓa nayi kaman yadda ɗazu na karɓi na mummy, "karɓa mana A.G ne a layin", babu yadda na iya haka na saka hannu na karɓa, da ƙyar na kai wayan kunne na, shiru dukkan mu mukayi, ina ganin M.G kuwa ya wani ƙura mun ido yana smilling.
Nima smilling ɗin nayi nace bari na haƙura da typing ɗin nan, sai kuma gobe idan mai kowa mai komai ya kaimu,
Ina ƙara jaddada muku wannan book fah true life story ne biyu cikin ukun shi, kashi ɗaya zai zama gyara labarin kawai akayi da shi, karfa azo wurin sanin mahaifin amaryah *KHADIJATUL KUBRAH (MAMAH)* aga ba yadda aka so ba rai ya ɓaci, haka tsarin rayuwa da ƙaddaran *HAJIYA AYSHAA U.U ƁALEWA* yazo.
*WASILA KAFI* DIS PAGE IS FOR YOU, kullum baki gajjiyawa da jinjina mini, na gode Allah ya bar zumunci.
*AUNTY NICE*
managarciya