Babban Buri:Fita Ta Biyu
Kwantar da kansa ya yi a saman kafaɗarta sannan ya lunshe idanuwansa murya can ciki ya ce "I miss You 'yaar tsohuwa"
بسم الله الرحمن الرحيم
FITOWA TA BIYU.
~~~~A haka muka jima muna fira da Hajiya Inna sai daga bisani na miƙe na yi mata sallama kan zanje na yi sallah na dawo.
Ƙarfe 2pm dai dai muka ji tsayuwar motocin gidan sai kuma hayaniyar 'yan gidan da muka ji ta yawaita, dani har su Yahanazu rige-rigen isa ga tagar kitchine muke yi domin bawa idanuwanmu haƙƙinsu.
Ganin wadansu Turawa muka yi sun doso hanyar shiga babban Parlourn gidan su biyar yayin da gayyar gidan suka rufo masu baya ko wannen su ka kalli fuskansa za ka fahimci yana cikin farin ciki da annushuwa.
Mamaki ne ya kamani ganin mutum biyar saɓanin yadda Hajiya Inna ta gayamin su shida ne, har lokacin ina bakin ƙofar tagar tsaye ina tunanin ina ɗayan yake ne.
Motar dake parke a filin tsakar gidan wace tunda mutan gidan suka dawo naga sun shigo tare ba wanda ya fito daga cikin ta sai direba koshi yana fitowa ya mayar da murfin motar ya kulle ne naga an wangale ƙofar baya , idanuwa na zuba domin na ba su nasu haƙƙi, ai kuwa saiga wadansu kyawawan takalmi sun bayyana yayin da ƙafar cikinsu take ta faman walwali da ɗaukan ido.
An yi 5minutes da fito da ƙafafuwan kana sai ga gangar jikinsa ta bayyana a fili.
A jiyar zuciya na sauke da ƙarfi ganin namiji mai cikar halitta ya bayyana a fili, kaina na ɗaga zuwa ga fuskarsa domin ganin waye wannan, saukar idanuwana a kan fuskarsa ya yi dai-dai da bugawar da zuciyata ta yi har sau uku, ba shiri na ɗauke idanuwana a kansa.
Jin dundun da a ka sakarmin a baya ne ya hankalto dani duniyar dana lula.
Yahanazu ce a kai na take faɗan "Khadeejah ki je Hajiya Inna na kiranki tana part ɗinta, tun ɗazu nake kwala maki kira bansan tunanin me kike yi ba da bakiji ni ba.
Sosa gefen fuskata na yi sannan na kalleta na sakar mata harara nace "shi ne za ki ƙaryamin baya da wannan basamuden hannun naki?".
"Eh mana, idan na yi magana baki jini ba ai kinji duka a baya."
"Bashi kika ɗaukarwa kanki" na faɗa haɗi da ratsa gefenta na fice daga kitchin ɗin.
Part ɗin Hajiya Inna na nufa ina tafe ina tunanin wannan waye, can kuwa na yi wa kaina faɗan mi ya dame ni da shi da zan damar da kaina da zancensa.
Sallama na yi kana na ƙame a guri ɗaya a ƙofar ɗakin ina jiran a bani izinin shiga.
Kusan minti biyar naji shuru na sake wata sallamar ammah shuru kake ji, kutsa kaina na yi cikin ɗakin inamai tunanin ina Hajiya Inna ta shiga kuma wace ko da yaushe tana zaune a Parlourn.
Birki naja nayi tsaye ganin mutum a hakimce saman kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya sai faman sarrafa waya yake yi wacce ake yayi a zamanin nan namu, ko takalmi ba'a cire ba daga jikin ƙafafuwan, sadar da idanuwana na yi zuwa ga mallakin fuskan, ba shiri naja da baya da niyar komawa gunda na fito ganin wanda ban taɓa sa ran gani ba, sai dai muryar Hajiya Inna ce ta yimin cikas "Hadeejatu ina zuwa kuma?".
Gaba ɗaya yawun bakina ƙamewa suka yi na rasa da wanne baki zan bata amsa, sai idanuwa da na sakar mata.
Ganin na yi taja birki tana rabon idanuwa a cikin parlourn tana faɗan "ni dai idan hancina ba ƙarya zai fara ba ƙamshin turaren shalele na nake ji."
Sai lokacin naga ya ɗago dara daran idanuwansa ya zubawa Hajiya Inna su yana mai girgiza ƙafarsa dake saman ɗaya kana cikin sanyayyiyar muryarsa mai kama da wanda ke yin raɗa ya buɗe baki da ƙyar ya ce" Tsohuwa me ran ƙarfe" lokaci ɗaya na fara neman numfashi na amman sai bara zanar ɗauke wa yake yi, a haƙiƙanin gaskiya ko cikin mata samun mai zaƙin murya da yin magana cikin salama da taushi da wuya ne balle cikin maza.
Kabbara Hajiya Inna ta yi cike da farin cikin da ban taɓa ganinta a cikinsa ba ta nufe sa tana murmusawa haɗi da taɓi da hannayenta tana faɗan "ga shalelena ga shalelena, maraba maraba maraba da shalelena, "yaushe ka shigo baka neme ni ba?" ta faɗa tana mai zama kusa da shi sai faman murmusa take yi.
Kwantar da kansa ya yi a saman kafaɗarta sannan ya lunshe idanuwansa murya can ciki ya ce "I miss You 'yar tsohuwa"
Shafa kwantanccen gashin kansa ta fara yi yayinda shi kuwa ya wani lunshe idanuwansa haɗi da ƙara kwantar da kansa a kafaɗarta.
Ɗan leƙa fuskarsa ta yi sannan ta ce dashi "tashi ka je ka watsa ruwa kazo ga lafiyayyen abincinnan mai rai da lafiya na tanadar maka da kaina na shiga kitchin na girka maka shi.
Miƙewa ya yi daga jikinta ya nufi wani ɗaki dake gefen na Hajiya Inna wanda tun lokacin da nake shigowa part ɗinta ban taɓa ganin kowa ya shiga cikinsa ba.
Kallo take yi wurinda nake a tsaye har lokacin ina faman rabon idanuwa ta ce "Zo nan Hadijatu yi haƙuri na barki tsaye ganin shalelena ne da na yi kinsan an daɗe ba'a haɗu ba."
Ɗan murmusawa na yi wanda bansan lokacin da ya suɓucemin ba, sannan na nufi wurinda take zaune na zauna a ƙasa iname wasa da 'yan yatsun hannuna.
Dafa kafaɗata ta yi ta ce dani "Dan Allah ki shiga kitchin ɗina ki haɗawa shalelena abinci a cikin plate ki ɗan yi masa yadda naga ana yi na zamaninnan ɗan wake ne gashi can da zafinsa ki haɗa masa da kwai da tumatir da dai sauran abubuwan da naga kuna sawa a kai ki kai masa a ɗakinsa , kinsan Allah Ya yi sa da son abincin gargajiya har dai ɗan wake da awara, zan je sashen wadancan tsagerun na wanke su domin naga mutunci ya yi masu ƙaramci, wai harni wadannan yaran za su yi tafiya mai nisa su dawo amman a rasa wanda uwarsa za ta turosa ya gaida ni, zan je naji dalilin hakan."
Ni dai bance da ita komai ba har lokacin kaina na ƙasa , sai dana ga ficewarta cikin ɗakin na mike a sanyaye na nufi gunda kitchin ɗinta yake.
Ɗan waken dana isko na jera a cikin plate me faɗi sai da ya cika cikin tsari me kyau da burgewa sannan na yanka masa kwai da tumatir da da yajin dana gani a ajiye, na nemo plate na rufe gaba ɗaya , sannan na buɗe freezer dake ajiye a cikin kitchin ɗin ina dudduba me yaka mata na haɗa masa dashi domin ya jika maƙoshinsa , ku jini da karanbani, na faɗa a dai dai lokacin da nake ɗaura gorar kunun ayan da nagani a ciki da swan a saman tire, ko wannensu fira bibbiyu na haɗa masa.
Daukar tiren nayi na doshi ɗakin da nake sa ran yana ciki nayi, sallama nayi har sau biyu amman shuru banji motsin komai ba, hakan ya sanya ni tura kambun bakina ɗauke da wata sallamar , lumshe idanuwana nayi lokacin da daddaɗan ƙamshin turare ya yi wa hancina lale marhabin.
Buɗe su nayi , na jingina jikina da ginin ɗakin inamai ƙarewa haɗaɗɗen Parlourn kallo.
Komai na ɗakin purple and white colour ne, kama daga kujerun ɗakin har izuwa kan labulayyan dake malale jikin ko wacce ƙofa, yadda aka tsara ɗakin abin burgewa ne ga duk mahaluƙin daya ci karo dashi, sai wani daddaɗan ƙamshin turaren dake tashi a ciki.
Jin hannuna ya fara sanyayewa ne yasan yani nufar gunda naga ɗan ƙaramin center table dake ajiye a tsakiyar ɗakin kana na ajiye tiren na tsaya ƙara ƙarewa ɗakin kallo.
Gajiya nayi da tsayin na doshi hanyar ficewa daga ɗakin ina tafe ina wai waiye kamar karna fice nake ji.
Kitchin na koma na ɗauko haɗin ɗan wake na ƙara dosar hanyar ɗakin.
Harna ajiye plate ɗin na tsaya ƙara ƙarewa ɗakin kallo, jin wani sanyayyen ƙamshi na dunfaro ni ya sanyani ƙara lumshe idanuwana iname ƙara buɗe ƙofar hancina domin na bashi nasa haƙƙe.
Wajen 3minutes idanuwana suna kulle sai can nayi azamar buɗe su ai kuwa basu sauka a ko ina ba sai akan wanda banyi zato ba.....
Za mu cigaba a Gobe............
*ƳAR MUTAN BUBARE!.
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU} MARUBUCIYAR MATAR ABDALLAH.
Maryamah