Kotu ta hukunta mutane 100 a Zamfara kan saɓawa dokar taƙaita zirga-zirga

Kotu ta hukunta mutane 100  a Zamfara  kan saɓawa dokar taƙaita zirga-zirga

Dokar tsakaita zirga zirga a Zamfara kotun tafi da gidanka ta kama da hukumta mutun 100.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Biyowa bayan dokar da gwamnatin jihar zamfara ta saka na tsakaita zirga zirga da daga karfe shidda na safe zuwa karfe goma na dare, da kuma hana daukar mutun fiye da daya ga masu baburan hawa, da kuma hana sayar da man fetur ga jarkoki,

Kotun tafi da gidan ka da aka kafa domin hukun ta masu kunnen kashi tace kawo yanzu ta samu nasarar kamawa da hukum ta mutun dari, masu laifuka daban daban.

Barista Abdurrashid Haruna, sakataren wannan kotun ta tafi da gidan ka ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa dake Gusau babban birnin jihar.

Yace tun lokacin da gwamna Bello Muhammed Matawalle ya sanya wa dokar hannu kuma ya kaddamar da kwamitin tsaro suka ban zama wajen kama duk wanda yaki bin wannan dokar, kuma shi yasa suka samu nasarar kama mutanen da suka karya dokar har su dari.

A ta bakin sa sun bi hanyoyi da dama domin su samu nasarar wannan aikin, inda har yace sun kama motoci kwara biyu dauke da abun ci, kuma sun kama Shanu guda biyar mallakar wani sojan Najeriya kuma sun kwace shanun.

Barista ya bayyana cewa, bayan babban kwamiti, sun kirkiro wasu kananan kwamitota domin samun saukin guda nar da ayukkan su.

"Kunga muna da kwamitin dake kula da yanda ake sayar da man fetur,da wanda ke kula da zirga zirga, da mai kula da harka yada labarai, da mai kula da tabbatar da anbi umurnin rufe kasuwan nin mako mako dake fadin jihar da dai sauran su.

" Domin dai asamu saukin matsalar tsaron da ya addabi wannan jihar munyi kokarin rufe wasu kananan kasuwan ni da muke tuhumar yan ta'addan na sayen kayan masarufi, kamar kasuwar garejin mai laina, da lalan da kasuwar yar hanya, da tashar gambo dake mayanchi, tashar lambar Bakura da kuma koloni dake Talatar Mafara".Inji shi.