An Kama Wani Matashi Da Ya Kware Wajen Sayen Man Fetur Don Sayarwa 'Yan Ta'adda A Zamfara

Yace sun saka ido ga reshi inda sai yau ne suka samu nasarar kama shi, da galan galan har guda goma sha takwas da kuma Babur din da yake amfani da shi wajen sayen man a gidajen mai dake Gusau babban birnin jihar ta Zamfara. Dauran wanda har wayau shine mai ba gwamna shawara ta fannin tsaro ya kara da cewa, wannan nasarar bata rasa nasaba ga irin addu'oin da mutane keyi na rokon Allah ya tona asirin duk wanda keda hannu ko ya taimaka wajen hana jihar Zamfara zaman lafiya.

An Kama Wani Matashi Da Ya Kware Wajen Sayen Man Fetur Don Sayarwa 'Yan Ta'adda A Zamfara

An Kama Wani Matashi Da Ya Kware Wajen Sayen Man Fetur Don Sayarwa 'Yan Ta'adda A Zamfara

 

Daga Aminu Abdullahi Gusau

 

A yau ne dubun wani matashi mai suna Zayyanu Abubakar da dake  kauyen Bingi a cikin karamar hukumar mulkin Anka ta cika.

 
 
Yace sun saka ido ga reshi inda sai yau ne suka samu nasarar kama shi, da galan galan har guda goma sha takwas da kuma Babur din da yake amfani da shi wajen sayen man a gidajen mai dake Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.
 
Dauran wanda har wayau shine mai ba gwamna shawara ta fannin tsaro ya kara da cewa, wannan nasarar bata rasa nasaba ga irin addu'oin da mutane keyi na rokon Allah ya tona asirin duk wanda keda hannu ko ya taimaka wajen hana jihar Zamfara zaman lafiya.
 
A don haka yaja kunnen jama'a da su guji taima kawa yan ta:adda domin duk wanda aka kama to ya kuka da kansa.
 
Da yake amsa tambaya ga yan jarida, wanda ake tuhuma Zayyanu Abubakar ya amsa laifin sa, sai dai ya musunta cewa yana kai man fetur din  ga yan ta'adda.
 
"Gaskiyar magana ni na sayi wannan man kuma nakan yi amfani da Babur din dake gabana na sayi mai  na naira dari biyar naje na zube a galan, kuma nakan samu wasu yan kabu kabu in basu kudi su shiga da nasu Babura a gidan mai su sawo man, ni kuma in basu ladar naira dari daya.
 
"Idan na je da man nakan sayar wa mutanen garin mu, kuma wallahi ban taba sayar da mai ga wani dan ta'adda ba, babban dalilin yin hakan shine ina son inga cewa na taimaka wa mutanen garin namu, saboda muna fuskantar matsalar man fetur.
 
'Ina da aure kuma ga yara ga yan gudun hijira a gida na, naga babu wata hanyar da zan samu kudin da zan saya masu abinci, amma duk da haka nayi ladamar yin wannan sana'ar da fatar ku yan jarida zaku fadawa jama'a dai dai abun da na fada maku" inji Zayyanu.