Hanyoyin mallakar miji ga matan Hausawa

Mata sun kasu kashi-kashi a wannan ɓangaren wasu sukan mallake mijinsu ta hanyar da ta dace ba tare da sun kaucewa Shari'a ba. Yayinda wasu matan suke mallake mijin ta hanyar kaucewa.

Hanyoyin mallakar miji ga matan Hausawa
Hanyoyin mallakar miji ga matan Hausawa

RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL SOKOTO.

Jama'a barkanmu da yau, barkanmu da sake saduwa a wannan filin.

Yau kuma muna tafe da hanyoyin mallakar miji.

Mata sun kasu kashi-kashi a wannan ɓangaren wasu sukan mallake mijinsu ta hanyar da ta dace ba tare da sun kaucewa Shari'a ba.
Yayinda wasu matan suke mallake mijin ta hanyar kaucewa.

Muna tafe da bayanan duka hanyoyin.

*Hanyoyin mallakar miji ta hanyar da ta dace*

A nan kafin na ce komai zan fara da wannan takaitaccen bayani, idan kina son ki mallake mijinki ta tafarkin da ya dace dole sai kin kasance masa mace tagari.
Akwai sifofin mace tagari wanda idan har kika siffantu da waɗannan siffofin ba shakka zaki zama sarauniya a gurin mai gidanki, hakanan zaki mallake shi cikin sauƙi.

Dama shi Namiji tamkar raƙumi ne idan kin iya sarrafa shi, idan kika ja akalarsa zai karkata duk inda kike so.

Ga kaɗan daga cikin hanyoyin mallakar miji a saukake;

* Ki kasance mai biyayya ga umurnin mijinki matuƙar bai sabawa shari'ar Muslunci ba.

*Ki kasance mai girmama iyayen miji da danginsa, domin biyayyar zata ƙara miki matsayi da farinjini a gun mijin da danginsa. Ka da ki manta cewa duk wanda ya so uwa dole ya so ƴaƴanta.

* Ki kasance mai tsafta domin tsafta tana daga cikin imani.
* Ki kasance gwanar iya kwalliya da kwarkwasa.

*Ki kasance mace mai iya kıssa da kissisina. Domin ita wannan kissar tana ɗaya daga cikin abubuwan da zasu mallaka miki zuciyar mijin har mutane su yi tunanin ko kin kauce hanya ne gurin mallakar.

* Ki nisanci ƙazanta domin ita ƙazanta takan iya zama linzamin canza akalar zuciyar mai gidanki daga kaunar da yake miki ya fara jin haushinki sannu a hankali sai ki ga kamar ya fara tsanarki.

*Daga ƙarshe ina mai ƙara jadadda miki ki kasance mai killace sirrin mijinki, ki kiyaye masa dukiyarsa sa'annan ki zamo mai yawan ibada da addu'o'i, domin addu'a takobin mummini ce ita take yiwa musulmi garkuwa daga dukkanin bala'i ko wata damuwa da ta tunkaro shi.


Hmmm! Yar uwa ki gwada yin amfani da waɗannan hanyoyin domin sai an gwada akan san na ƙwarai, haka da gwajin ne Jirgin sama ya tashi.

Mace tagari Sirrin maigidanta.