Majalisar Dattawa Za ta Sasanta  Rigimar Nijeriya Da Dubai

Majalisar Dattawa Za ta Sasanta  Rigimar  Nijeriya Da Dubai
Ahmad Lawan
Daga Babangida Bisallah, Minna.
Majalisar dattawa ta kudurin aniyar shiga tsakani don warware takun sakar diflomasiya tsakanin Najeriya da kasar hadaddiyar daular larabawa (United Arab Emirates), Dubai. 
Majalisar ta dauki matsayin ne bayan da ta tattauna matsalar kamar yadda shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe ya gabatar mata a zamanta na ranar Talata.
Ezrel Tabiowo, Mai taimaka ma shugaban majalisar dattawa akan aikin jarida ya bayyanawa manema labarai hakan bayan zaman majalisar talatar makon nan a Abuja.
Ya ce abin da ya haifar da matsalar, a watan Fabrairu na 2021 ne gwamnatin tarayya ta dakatar da kamafanin safarar jiragen sama na Emirates mallakar kasar UAE daga gudanar da sabon gwajin cutar Korona baya ga wadda fasinjojin suka yi kafin tashin su daga filayen jiragen samar Abuja da Legas.
Yace akan haka ne kamfanin zirga-zirgan jiragen sama na Emirates ya dakatar da zuwa Nijeriya. 
Yace amma bayan wani zaman sasantawa tsakanin kasashen biyu, zirga-zirgar ta dawo duk da cewa kamafanin na Emirates ya cigaba da yi ma fasinjoji gwajin na Korona kafin su tashi daga Najeriya, abin da ya fusata gwamnatin tarayya ta tsaida kamfanin daga tashi ko sauka a Najeriya. 
Kan haka, majalisar ta umurci kwamitocin ta na harkokin kasashen waje, tsaro da kuma shige da fice da su tattauna da ma'aikatar harkokin waje ta tarayya da hukumar leken asiri ta kasa don samo hanyar warware matsalar.