Tambuwal zai riƙa baiwa 'yan banga alawus duk wata 

Tambuwal zai riƙa baiwa 'yan banga alawus duk wata 
 
https://managarciya.com/tambuwal-zai-riƙa-baiwa-yan-banga-alawus-duk-wata
Gwamnan Sakkwato  Aminu Waziri Tambuwal ya ba da gudunumwar motocin sintiri guda 143 da baburan hawa guda  550 a cikin watanni 15 domin karfafa aikinsu.
Motoci 10 kirar Hilux da babura 500 da ya bayar ga 'yan sa kai a ranar Litinin data gabata suna cikin ababen hawa da ya rabawa jami'an tsaro domin karfafa su a yakar mahara da masu garkuwa da sauran abubuwan bata gari musamman a yankin Sakkwato ta gabas a jihar Sakkwato.
https://managarciya.com/tambuwal-zai-riƙa-baiwa-yan-banga-alawus-duk-wata
In za a iya tunawa a 3 ga watan Yunin 2020 Tambuwal ya bayar da gudunmuwar motoci 98 ga jami'an tsaro bayan kwana 26 ya bayar da mashin Boxer guda 50 ga sojoji dake aiki a jiha.
Bayan watanni takwas Tambuwal ya baiwa 'yan sanda motoci 15 daga cikin 25 da aka sawo domin samar da tsaro. 
Tambuwal a lokacin da yake baiwa 'yan sa kai da ake kira 'yan banga a Sakkwato motocin aiki ya ce wannan yunkuri an yi shi ne domin taimakawa kungiyar ta rika aikinta na sintiri da samar da bayanan sirri da za su rika aiki da jami'an tsaron jiha. 
https://managarciya.com/tambuwal-zai-riƙa-baiwa-yan-banga-alawus-duk-wata
Gwamnan ya ce sun samar wa ƙungiyar unifom da kudin alawus a duk wata da sauran abubuwan da za su taimaki aikinsu.
Tambuwal ya godewa shugabannin kungiyar banga kan sadaukarwarsu da jajircewa da hadin kan da suke baiwa jami'an tsaro a jiha, ya roke su duk aikin da za su yi karkashin kulawar jami'an tsaro kar su samar da kungiya mai daukar miyagun makamai gwamnati ba ta aminta da hakan ba.
Ya yi kira mutane a jihar su shiga kungiyar banga don samar da cigaba ya godewa shugabannin addini da gargajiya kan hadin kan da suke baiwa jami'an tsaro.
Kwamishinan 'yan sanda  a jihar Kamaluddeen Okunola Kolawale ya nuna farincikinsa ga wannan tallafi na Gwamna domin yana cikin tsarin abin da shugaban 'yan sanda na kasa ke so  na bunkasa 'yan sandan farin kaya. 
https://managarciya.com/tambuwal-zai-riƙa-baiwa-yan-banga-alawus-duk-wata
Ya ba da tabbacin 'yan sanda za su aiki tare da 'yan bangar a jihar Sakkwato.