Kotu ta buƙaci a cigaba da tsare Yahaya Bello a hannun EFCC ta kuma dage shari'ar

Kotu ta buƙaci a cigaba da tsare Yahaya Bello a hannun EFCC ta kuma dage shari'ar

Mai shari’a Maryanne Anenih na babbar kotun birnin tarayya Abuja a ranar Larabar da ta gabata ya bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a hannun hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC.

Alkalin ya kuma dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 10 ga watan Disamba, 2024 domin yanke hukunci kan neman belinsa.

Bello da wasu mutane biyu, Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu, suna fuskantar tuhume-tuhume 16 da EFCC ta gabatar musu.

An zarge wadanda ake tuhumar da hada baki, cin amana da kuma mallakar kadarori ba bisa ka’ida ba.

Daga Abbakar Aleeyu Anache