Shaguna 100 sun ƙone a karo na uku gobara na tashi a kasuwar Kara

Shaguna 100 sun ƙone a karo na uku gobara na tashi a kasuwar Kara

Gobara a karo na uku  ta kone sama da shaguna 100 a kasuwar kara dake cikin birni jihar Sakkwato.
Wutar Gobarar da tashi da safiyar  Assabar 6:30 an samu nasarar kashe wutar da karfe 3:30 na rana bayan shafe awa 9 tana ci.
Wani da yake da shago a ciki, an sakaya sunansa domin baya son shugabannin kungiya su ga laifinsa kan magana da manema labarai ya ce "Wutar ta shafe awa 9 tana ci, ta kone shaguna sama da 100 kama daga layin masu sayar da abinci da ya hada da gero da dawa da masara da shinkafa, sai layin masu Kyame da layin makera da masu maganin gargajiya.
"A kiyashi an yi hasara kudi za su kai miliyan 500 a wannan wutar domin dukkan shagunan dake layin dana fada maka sun kone masallaci ne kawai bai kone ba," a cewarsa.
Ya yi kira ga Gwamnati ta cire batun siyasa a kwamitocin da take kafawa a duba dalilin wutar da kuma daukar mataki cikin gaggawa bai kamata gwamnati ta zuba ido mutane suna hasara don son zuciyar wasu mutane ba.
Ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na uku da wutar ke ta shi a kasa da shekara daya kuma duk ta tashi sai ta ci shaguna da yawa bayan jaje ba abin da gwamnati ke yi akwai bukatar sake wannan tunani don ceto dukiyar mutane da ake hasara.
Alhaji Aminu Danhili tsohon shugaban kungiyar 'yan sakai a kasuwar kara yana cikin wadanda gobarar ta konewa shago ya ce hasara an yi ta sosai sai dai a gode Allah, zuwa yanzu ba wanda ya san yawan hasarar da aka  yi.
"Ana hasashen dalilin tashin gobarar wasu ne suka kone shara daga ne abin ya wuce hannunsu ta shiga shagunanmu, jami'an kashe gobara sun yi kokari sosai ganin an shawo kan wutar, sai da muna kira ga Gwamnati ta tallafa mana ganin hasarar da muka yi," a cewar Alhaji Aminu Danhili.