Karshen Zamani:Yanda Ɗa Ya ƙona Mahaifiyarsa Har lahira A Neja

Karshen Zamani:Yanda Ɗa Ya ƙona Mahaifiyarsa Har lahira A Neja

 

Mazauna unguwar Darusalam dake Minna, Jihar Neja sun tashi cikin kaɗuwa da firgici bayan da wani matashi, Steven Jiya, ya bankawa mahaifiyarsa, Comfort Jiya wuta ta babbake har lahira. 

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Steven, wanda ɗan ƙwaya ne, ya dawo daga garin Suleja   bayan ya shiga gida ne, sai kawai ta raya masa cewa ya ƙona mahaifiyarsa.

 
Jaridar ta ce a lokacin Comfort, wacce tsohuwar Shugabar makarantar sakandire ce, tana tsaka da girki a kicin, sai kawai wannan tambaɗaɗɗen ɗa ya zazzaga mata fetur ya kuma cinna mata wuta a gidanta da ke unguwar Darusalam ya kuma tsere.
 
Nan fa ta fito a waje tana ihu a kawo mata ɗauki, inda kan ka ce kwabo, wutar ta ƙone mata ilahirin jikinta.
 
Wata majiya a dangin marigayiyar ta ce an garzaya da ita asibiti inda don jinya. Sai dai kuma, da misalin ƙarfe 3  na yammacin jiya Juma'a, marigayiya Comfort ta ce ga garin ku nan.
 
Wata majiyar ta ƙara da cewa dama can Steven fitinanne ne kuma ya yi yunƙurin hallaka uwar tun a baya.
 
Jaridar ta ce ta tuntuɓi rundunar ƴan sanda ta Naija amma haƙar ta ba ta cimma ruwa ba.
 
Sai dai kuma, in ji jaridar, tuni dai ƴan sandan Caji-ofis na Minna su ka samu nasarar damƙe Steven kuma har an kai shi babbar kotun Minna inda zai girbe abin da ya shuka.