Daga Babangida Bisallah, Minna
Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello yayi tir da Allah waddai kan harin da aka kaiwa masallata a kauyen Ba'are ta karamar hukumar Mashegu da yayi sanadin rasa rayukan jama'a akalla 16.
Bayanin na kunshe ne a wata takardar manema labarai, da sakatariyar yada labaran gwamnan, Mary Noel Berje ta fitar a safiyar juma'ar nan.
Sakatariyar ta cigaba da cewar, gwamna Sani Bello ya bayyana cewar ya za a yi wasu gungun jama'a ko daidaiku su rika kai hare-hare a wajen Ibadah har su rika kashe rayukan jama'ar da ba a san adadin su ba, a lokacin da suke Ibadah.
Gwamnan ya jajantawa iyalan mamatan, ya cigaba da cewar zai cigaba da daukar matakai kan ayyukan 'yan ta'adda a wasu sassan jihar.
"Abin takaici ne a ce wasu mutane ba sa tausayin rayukan jama'a da mutunta wajajen Ibadah har su rika kashe mutane a masallatai a lokacin da suke sallah.
"Tunani na ya tafi akan iyalan mamatan kan halin da za su tsinci kansu, ina rokon Allah ya jikan mamatan ya kai su gidan aljannar Firdausi, su kuma wadanda suka samu raunuka ya ba su sauki", a cewar shi.
Rahotanni dai sun tabbatar da kai hari ga mutanen kauyen Ba'are a cikin karamar hukumar Mashegu a larabar makon nan a lokacin da suke sallar asuba wanda yayi sanadin mutane goma sha shida, yayin da kwamishinan 'yan sandar jihar, CP Monday Bala Kurya ya ce binciken ya tabbatar da mutuwar mutane tara, yayin da dama suka tsira da raunuka.
In ba a manta ba, ko a kwanakin baya an kai irin wannan harin a garin Mazakuka ta karamar hukumar Mashegun da yayi sanadin rasa rayukan jama'a da dama a lokacin da suke sallar asubahin.