Bagudu ya aika sunayen Shugaba da mambobin hukumar zabe ga majalisar dokokin jiha

Bagudu ya aika sunayen Shugaba da mambobin hukumar zabe ga majalisar dokokin jiha
Bagudu ya aika sunayen Shugaba da mambobin hukumar zabe ga majalisar dokokin jiha
 
 Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu a ranar Talata ya aikawa majalisar dokokin jihar sunayen shugaba da mambobinsa da yake son a tantance a kuma tabbatar domin su jagoranci hukumar zabe mallakar jiha.
 
A takardar da ya  tura wadda mai baiwa gwamna shawara kan yada labarai Yahaya Sarki ya rabawa manema labarai a birnin Kebbi  ya ce sunayen sun hada da  Aliyu Muhammad Mera a matsayin shugaba, sai Ahmed Amadu Nasani, Mustapha Usman Ka'oje, Honarabul  Aliyu Ahmed Adamu da Honarabul  Sa'idu Moh'd Dankolo, dukansu mambobi ne a hukumar zaben.
Bagudu ya ce zabar mutanen yana kunshe ne a cikin daftarin doka sashe na 198 da kundin tsarin mulki wanda aka yiwa gyaran fuka a 1999.
Bagudu ya ce ya nada mutanen ne domin su taimaka masa ga hakkin da doka ta daura masa.