Sanata Wamakko Ya Ba Da Tallafin Miliyan 10 Ga Mutanen Da Sojoji Suka Kubutar a Sokoto

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ba da tallafin miliyan 10 ga mutanen da sojoji suka kubutar hannu ‘yan bindiga bayan da suka yi garkuwa da su da nufin sai an ba su kudin fansa kafin su sake su, in da sojoji suka yi nasarar kubutar da su a ranar Jumu'a da Assabar da ta gabata.
Sanata Wamakko ya bayar da dubu 100 ga kowanen mutum daya maza da mata cikin mutum 66 da aka ceto hannun ‘yan bindigar a dajin Gundumi, ya kuma bayar da dama a yi abin da yakamata ga sauran kudin da zai rage a miliyan 10.
Sanata ya nuna gamsuwarsa ga kokarin gwamnatin jiha karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto da ta bayar da nata tallafin dubu 100 ga kowane mutum da abinci shinkafa da gero da masara, haka ma jagorancin jiha na tafiya kan turbar da ya dace, an baiwa marada kunya.
Sanata Wamakko wanda tsohon Gwamnan Sakkwato ne ya jinjinawa sojojin Nijeriya musamman wadan da suka yi hobbasar ceto mutanen nan cikin nasara ya yi fatar a kara kaimi waurin kubutar da sauran mutanen da ke hannun ‘yan bindigar tare da yin addu’ar kariyar ubangiji ga sake faruwar hakan.
Sanata Wamakko a lokacin da yake faranta rayuwar mutanen, ya sanar Gwamnatin jiha tana saman turbar da mutanen Sakkwato ke bukata musamman yanda take aiwatar da abubuwan cigaba da za su taimaki talaka a jiha.
managarciya