Matsin rayuwa: Ƴan APC sama da miliyan 26 sun yi barazanar ficewa daga jam'iyyar domin kafa ta su 

Matsin rayuwa: Ƴan APC sama da miliyan 26 sun yi barazanar ficewa daga jam'iyyar domin kafa ta su 

Kungiyar 'Team New Nigeria' (TNN) ta fara shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar APC don kafa sabuwar jam’iyyar siyasa da za ta ceto Najeriya daga talauci, yunwa, rashin tsaro da lalacewa.

Jaridar THE TELEGRAPH ta rawaito cewa ƙungiyar ta bayyana cewa tana da mambobi masu rijista har miliyan 26,382,000 daga sassan ƙasar nan, waɗanda su ka amince su gina sabuwar Najeriya ba tare da rashin shugabanci mai kyau, son kai, da jami’an gwamnati masu cin hanci da rashawa ba.

Shugaban  kungiyar, Modibbo Yakubun Farakwai, ne ya bayyana haka yayin kaddamar da kwamitin haɗin kan ƙungiyar na jihar Kano a hukumance a Kano a yau Litinin.

“Mun fahimci cewa mutanenmu suna matuƙar buƙatar sauyi, amma ba kawai sauyin gwamnati suke nema ba. Suna neman jam’iyyar siyasa da za ta kawo sababbin fuska domin maye gurbin tsofaffin shugabanni. 'Yan Najeriya suna son ganin sauyi a al’adar gudanar da mulki da ingancinsa. Suna son ganin gaske a tsarin yadda gwamnati ke aiki a duk matakai.

“Ina so in yi amfani da wannan dama in gaya muku cewa da goyon bayan ku, TNN za ta samar ba kawai wata gwamnati madadin ba, har ma da wata al’adar mulki madadin, wacce aka tushen ta a kan ƙa’idar dimokuradiyya,” in ji shi.