Hukuncin Kotun Ƙoli: PDP Ta Hango Nasara a Sokoto

Hukuncin Kotun Ƙoli: PDP Ta Hango Nasara a Sokoto

 

Kotun kolin Najeriya ta kammala sauraron shari'a kan zaben gwamnan jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yamma, kamar yadda The Nation ta rahoto. 

A zaman ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, 2024, kotun mai daraja ta ɗaya a kasar nan ta tanadi hukuncinta a ƙarar da aka nemi tsige Gwamna Ahmad Aliyu na APC. 
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta na gwamna, Sa'idu Umar ne suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli, inda suka kalubalanci nasarar Gwamna Ahmad Aliyu. 
Kwamitin alƙalai biyar na kotun karkashin jagorancin mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun, a zaman  Laraba, ta ɗage sauraron ƙarar domin yanke hukuncin ƙarshe. 
Mai shari'ar ta ɗauki wannan matakin ne bayan sauraron kowane ɓangare da ƙarar ta shafa, inda ta ce za a sanar da ranar yanke hukunci nan ba da jimawa ba. 
Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Aliyu a zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023. 
Umar da PDP sun yi zargin cewa Aliyu da mataimakinsa, Idris Gobir, ba su cancanci tsayawa takarar gwamna ba a zaben da ya gabata.
Sun kuma yi zargin cewa ba kawai tafka kura-kurai kaɗai aka yi a zaɓen ba, gaɓa ɗaya zaben an gudanar da shi ba bisa ka’ida da tanadin dokar zabe ta 2022 ba. 
Amma duk da haka kotun ɗaukaka ƙara ta yi fatali da ƙarar bisa rashin cancanta. Daga nan masu ƙarar suka garzaya kotun ƙoli, Channels tv ta ruwaito.