Gwamoni Sun Kira Taron Gaggawa bayan an ba Hamata Iska a Taron PDP 

Gwamoni Sun Kira Taron Gaggawa bayan an ba Hamata Iska a Taron PDP 

 

Jam’iyyar adawa ta PDP na ci gaba da fama da rikice-rikice tun bayan zaɓen 2023, lamarin da ya jawo hankulan gwamnoninta da sauran shugabanni. 

A ranar Laraba, yayin taron kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT) da aka gudanar a Abuja, an samu hargitsi bayan magoya bayan Sanata Samuel Anyanwu sun farmaki Sunday Ude-Okoye. 
Punch ta wallafa cewa lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu jiga-jigan jam’iyyar suka nuna rashin jin daɗinsu da yadda abubuwa ke faruwa a PDP. 
A ƙoƙarin shawo kan matsalolin da suka addabi jam’iyyar, gwamnonin PDP sun shirya taron gaggawa da za a gudanar a ranar Juma’a a Asaba, jihar Delta. 
An ruwaito cewa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ne zai jagoranci taron kuma zai tattauna batutuwa kamar: Buƙatar gudanar da taron kwamitin gudanarwa na ƙasa (NEC) 
Shirin gudanar da tarukan mazabu da jihohi 
Rikicin da ya shafi Sakatare na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu 
Rahoton shugaba Umar Damagum kan halin da jam’iyyar ke ciki Matsalar shugabanci da ke ci gaba da ruruwa a PDP 
A cewar wani jigo a jam’iyyar, akwai matsaloli da ke buƙatar a warware su cikin gaggawa kafin PDP ta rasa nagartarta a idon al’umma. 
Shugaban jam’iyyar na rikon kwarya, Umar Damagum, ya bayyana cewa shugabannin PDP ne ke ruruta rikicin da ke neman tarwatsa jam’iyyar. 
"Wasu shugabanninmu da ya kamata su haɗa kan jam’iyya, su ne ke haddasa rikici da ƙirƙirar rabuwar kai." 
Ya kuma yi gargadi da cewa, idan har PDP ta cigaba da tafiya a haka, za ta ci gaba da fuskantar matsaloli a gaba.