Rikicin PDP ya dawo sabo Secondus bai aminta da ya sauka a Okotoba ba

Rikicin PDP ya dawo sabo Secondus bai aminta da ya sauka a Okotoba ba

Rikicin PDP ya dawo sabo Secondus bai aminta da ya sauka a Okotoba ba

Fargaba na kara mamaye zukatan mabiya jam'iyar PDP a kasar Nijeriya in da rikicin da ya dabaibayi jam'iyar ya koma sabo a lokacin da ake tunkarar babban taron kasa, shugaban jam'iyar Uche Secondus ba zai bar ofis a watan Okotoba ba.
Majiyoyin da suka sanar da jaridar daily trust sun ce Secondus ya tsaya kai da fata sai ya kammala wa'adinsa ya ce zai bar kujerarsa ne kadai in an yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima.
Uche an zabe shi a Disamban shekarar 2017 wa'adin shekara hudu da zai kare Disamba  2021.
Masu ruwa da tsaki da gwamnonin PDP suka zauna sati biyu da suka wuce aka rage wa'adin mulkin shugaban da wata biyu zai sauka a watan Okotoba saboda a yayyafawa wutar rikicin da ta taso ruwa.

Majiyar ta ce Secondus bai aminta da ya bar ofis a watan Okotoba ba.
Ya ce ya nemi shawarar wasu manya a jam'iyar PDP sun ce ya tabbata ya kammala wa'adin mulkinsa.
Duk da haka ana saran shugabannin gudanarwar jam'iyar su yi zama a gobe Talata domin sanya ranar taron shugabannin zartarwar kasa gaba daya.