HAƊIN ALLAH:Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Tara 

HAƊIN ALLAH:Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Tara 
HAƊIN ALLAH:Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Tara 
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 
 
 
  Page 9
 
 
Cikin ikon Allah muna zuwa gidansa, matarsa tai tsalle ta dire tace, "Wallahi ba zan riƙe maka yarinya ba, komi zai faru ya faru, haka kawai ka kai yarinya Lagos ban san uwar data koyo ba, da rana tsaka ka kawo min ita wai na haɗa ta da Yarona? To wallahi ban haɗawa kai duk abin da kaga dama ina jiranka."  Da farko ya biye mata suna ta cacar baki abin ba daɗin kallo balle saurare. Faɗa take sosai iyakar ƙarfinta ba zata riƙe mai yarinya ba sai dai ya sake ta kan hakan ta amince. 
Ko da ya fahimci da gaske ba riƙe nin zatai ba, sai yace mu tafi gun Mamarsa, ya kaini gunta, muna zuwa itama tace tunda can da nake yarinya ƙarama bai bar mata ba sai yanzu da taƙi kaɗan sai aure zai kwaso yarinya ya kawo mata? To ba za ta amsa ba yasan inda zai kai yarinyarsa tun wuri kafin dare ya yi ma shi... Sallamar wata dattijuwa ce ta tsaida faɗan da take, anan na fahimci ashe ita ma Kakata ce ta wajen Uwa, bayan sun gaisa ta dubi Babana tace, "Gunka na zo, don Allah ka rufa min asiri ka sa a saki Hajjo da yaronta kafin sauran yaranta su ji abin da ke faruwa domin idan taƙamar tsiya kake a cikin yaranta akwai kwamandan Sojoji, tana da yara masu kakin soja da mopal don haka ita fitina kwance take mai tada ta kuma kanshi take ƙarewa." Mamar Babana tace "To wacece Hajjo kuma miye haɗinsa da ita?" Sai kawai kuka ya ƙwace min, sai da nace ma Hajjo ta barni gunta ban san ganin kowa sai Mamana itama ba yanzu ba, amma ta matsa sai da ta kawo ni, to ga irin tukuicin da akai mata ai nan. Yana cika yana batsewa yace, "Su ne suka sace min yarinya ashe gunta na ganta don haka nace a rufe min ita sai naji dalilin sace min yarinya da su kai."   Su duka suka ɗauki Salati suna nanatawa Kakata ta miƙe tsaye ta kakkaɓe zaninta tace, "To ni dai na fita tunda na gayama gaskiya tunda baka ji kuma gaka ga zuri'ar Hajjo nan kai ne a ƙasa wallahi don tana da masu ƙwato mata haƙƙinta, irin masu fushi da fushin .... Bata ida maganar ba aka ji ana ƙwaɗa sallama ƙofar gida, ko da jin sallamar sai Babana ya kalli Mamarsa ya miƙe ya fice kamar mu duka aka kira muka bi shi bayansa, muna fita muka ga motar sojoji ƙofar gidan ga Hajjo cikin ƙaramar mota da Salim ga alama ranta a ɓace yake, wani soja ya ware hannu zai ƙwaɗa wa Babana mari Hajjo tai hanzarin hana shi tace da muryar faɗa, "Ka ban mamaki kuma ban taɓa tunanin rashin arziƙi da rashin darajar naka ya kai har haka ba sai yau. Ina son ka sani ni na wuce kasa a wulaƙanta ni a gun ƴan sanda da ace mu ma ƙananan mutane ne kamar kai Yau da sai na sa an tafi da kai Kano an koya ma ladabi da sanin girman manya an baka tarbiyya Yaro, amma ka ci darajar yaran dake tsakaninmu da kai bayansu da ka gane Barno Gabas take Yaro, ta. Yayarta ta isa inda take tana bata haƙuri ni kuma na nufi gunta ina kukan zan bita, Uncle Salim ya jawo ni zai sani motar Hajjo tace, "Ko bayan raina ban ce ka riƙe Jiddah ba Salim tunda ubanta bai da mutunci don haka ka bar mai ɗiyarsa ya jiƙata ya shanye ta."  Ina ji ina gani Hajjo da Uncle Salim suka tafi suka barni ina kuka ina komai ba wanda ya tausaya min, Babana ya dubi Mamar mahaifiyata ce, "Don Allah Inna ku je da ita zan zo tunda ba wanda zai iya riƙe min ita nan."   Tabbas dangin Uwa daban ne, bata musa ba, haka ta kama hannuna muka wuce ina waigen mahaifina da mahaifiyarsa data kasa riƙe ni.
Tabbas zamana gun Inna na ji daɗi tamkar ina gaban Hajjo komai ana min kuma ina lokaci-lokaci ina gano mahaifiyata, sai a lokacin na goge zargin rashin son da nake tunanin tana min na fahimce ta tana da kawaici da kau da kai sosai akan sha'anin rayuwa bata da yawan magana haka bata cika kulani ba saboda ina ɗiyar fari gunta. Sai a lokacin naga ƙanina shima ya girma Masha Allah ba laifi, ina sonsa don wani  lokacin da shi nake tafiya gida. 
Kwanci tashi aka sakani makarantar boko data islamiyya ina zuwa ban rasa ci ba ban rasa sha ba, sai dai tun daga ranar da Babana ya bada ni yace zai zo bai zo ba haka bai taɓa aiko da komai ba yace a ban ko sallah ta zo bai min ɗinki Inna ke min komai. 
Watarana na je gidan Mamana na iske ta tana goge hawaye na tambayeta lafiya tai shiru sai da mijinta ya shigo yake bata haƙuri anan na fahimci mahaifina ne ya zo ya amshe ɗansa wai zai kai shi makarantar allo. Ni kuma kukan na saka domin nasan yadda wahalar almajirci take, bai kamata ba ace ya kai yaronsa almajirci ba, haka dole muka dangana ni da mahaifiyata muka haƙura da batun ƙanina.
 
Duk garin ban da ƙawa sai wata Safiyya ita ma daga kitso da take min muka haɗu shike nan jininmu ya haɗu da ita, ina matuƙar tausayawa rayuwarta domin tsoho take aure tana yarinya duk da ba fahimtar yadda zaman aure yake nai ba ni dai ina jin tausayin Safiyya don haka komi aka dafa gidanmu sai na kai mata kasancewar mijinta kuɗin abinci yake bata bai kawo ɗanyen abinci yace ta dafa, to Ni kuma sai na dinga kawo mata safe da rana wani lokacin har dare ina cewa ta dinga adana kuɗin tana siyen sabulun wanki da wanka, duk da suma idan naga Inna cikin kuɗi ina matsa mata taban in siyo ma Safiyya sabulu tai wanki, to hakan yasa duk ƙarshen wata idan yaran Inna sun kawo mata sabulu da kayan abinci nake matsa mata tana ban ina kaiwa Safiyya. Mutane da dama sun sha kawo zugar cewa Inna ta raba ni da Safiyya wayau kawai take min, sai Inna tace ba ruwanta tasan ba mai iya shiga tsakanina da Safiyya don haka sai kowa ya yi shiru. 
 
Watarana na dawo makaranta naga Inna da Mamarmu da sauran Yayyenta a gidanmu duk cikin damuwa ba mai fara'a sai naga idon Inna kamar kuka take ma, nan da nan hankalina ya tashi na shiga tambayar abin da ke faruwa.
Yayan Mamana yace "Jiddah ki yi haƙuri komai yake faruwa dake da sanin Ubangiji, kuma insha Allah ba za ki taɓe ba, ki ƙara haƙuri kan wanda ki kai a baya, insha Allah za ki yi farin ciki kuma kowa sai ya yi alfahari dake a rayuwa. Jiddah Mahaifiyar mahaifinki ta zo Yau tace angama komai gobe za su aurar dake don haka ki koma gidansu a Yau don gobe ɗakin mijinki za ki kwana, saboda sun gaji da zamanki a nan kuma su basu bada yaransu agolanci tunda an samu mai sonki za su aurar dake ko mahaifinki bai san da auren ba tunda ya tafi yawonsa na Dawa."  Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un!!! Ita ce kalmar data fito daga bakina, sai kuma nace "Kawu wane irin aure kuma? Ni wa na sani ma da zan aura?" Sai kawai sauran matan suka saka kuka ina ganin Mamana na share hawaye ta miƙe ta ɗauki hijabinta ta fice bata ce min komai ba. Haka ina ji ina gani Inna ta kwaɓa lalle tai min duka ƙafa tai min ga hannuwa ta jiƙa magani kala-kala ta ban tace na shanye, wani kuma tace idan lallan ya kama nayi wanka. Ƙarshe dai da dare Inna ta haɗa min kayana Ni da ita da Safiyya muka doshi gidansu mahaifina, kowa zuciyarsa ba daɗi.
Muna zuwa muka iske dangi cike da gidan ana ta hidimar buki da gaske, wanda ba wanda yasan Amarya sai a lokacin akai ta nuna ni ga dangina ana cewa nice amarya. Inna ta baroni ina kuka tana kuka tace gobe iyayenki za su zo ayi komai da su ki yi haƙuri Jiddah haka taki rayuwar take ke kuma watarana sai labari." Ni da Safiya har dare ya tsala kowa na harkar gabansa ba a ce ga inda zamu kwanta ba don haka muka raɓa gefen wata tabarma muka kwanta har safe. Tunda safe sai ga dangin Mamana sun zo da iyayen kaya bayin Allah duk da basu da shi amma sai da suka kawo duk wani abu da Uwa ke yi sun kawo min. Kayan kawai aka amsa aka watsar da su nan tsakar gida kamar dai yadda aka watsar da ni amarya da ƙawata Safiya kalaci ma Yayar Mamata ta bada kuɗi aka siyo mana mu kai, har zuwa rana duk muna tsakar gida ni da dangin Mamata cikin ikon Allah sai ga abinci daga gidan Inna an kawo wanda shi ne wanda dangina suka ci na mahaifiyata duk da ana ta cin abincin amma ba wanda yace gana amarya ko na iyayenta. Sai zuwa la'asar aka ban sabbin kaya aka ce nayi wanka na saka lokacin za a ɗaura aure, sai a lokacin naji ance an ɗaura aurena da Ƙamaraddeni wanda ake kira da Dini kan sadaki Naira dubu talatin cif.
Da dare aka ɗauki amarya ina tare da ƙawata da Yayar Mamata duk da sai da aka so yin faɗa gun kai amarya an yi komai dangin Mamana basu tanka ba sai gun kai amarya suka ce dole a je da ko mutum guda ne a cikinsu.
 
Wannan shi ne asalin aurena da Deni, buki da kwana biyu Mamana ta kawo min cincin da dubulan har da alkaki, don an ce ita zatai min ba su ba. Buki da kwana huɗu aka kawo min kayan lefe na daga gidansu Babana wanda ana tafiya na kira Safiya nace ta zo ta zaɓi duk abin da take so a cikin lefen. Bayan ta zaɓa na rufe na aje.
Zamana da Deni kadaran-kadahan ban da wayon da zan musa masa ko yi masa ba daidai ba, komi yace ban kaucewa don haka ko da yaushe yake kaini gidansu ko gidanmu yace na yini sai dare zai zo mu tafi gida. Ba yadda Mamana batai ba amma sam ta ƙi daina kaini gidan tace na dinga zama ɗakina amma yace ai shi ke kai ni duk inda na je don haka ba laifi bane ba, kawai buƙatarsa idan zan fita ko makwabta ne na ba da ajiyar makullin gidan a aje ma shi. Wata biyar da aurena Allah Ya yiwa Inna rasuwa, tabbas naji rasuwarta sosai domin ita kaɗai ce ta riƙe ni babu tsana babu hantara balle tsangwama har muka rabu. 
Damuwa ta farko dana fara cin karo da ita sace kayan lefe na duka aka kwashe atamfofin aka tsince min kayan kicin irinsu kuloli da sauran tarkace, ban damu ba nace Allah Ya kyauta gaba haka ma Mamana tace itama. Ban jima ba na samu ciki, sai dai irin mai wahala ne ko da yaushe cikin amai nake ga ciwo kala-kala ina fama, hakan yasa ban fashin zuwa gun awo duk ranar Talata nake zuwa da cikina ya tsufa amma da farko bayan sati huɗu nake zuwa awon.
 
Har zuwa yanzu Safiyya ita kaɗaice ƙawata abokiyar shawara ta, kullum na fita na dawo sai na iske hijabinta ko gyalenta ko takalmanta ta aje ta ɗauki nawa a tunanina biyowa take idan zata wuce take aje wa tana ɗaukar nawa. Ban taɓa kawo ma raina cewar Safiyya cin amanata take da mijina ba sam. Sai ga shi jiya da idanuna na kamata tana cin amanata a cikin gidana ta manta yadda na ɗauke ta da matsayi na fifita ta akan sauran ƙawayena na makaranta na maidata ƴar'uwata ta jini mahaifiyarta kallon mahaifiyata nake mata, ashe ban sani ba zan wayi gari nayi mugun gani tsakaninta da mijina... "Jiddah don Allah ki daina wannan tunanin ba abin da zai saki sai matuƙar damuwa, ki barshi da Allah tabbas zai saka maki domin ya zalunce ki, ita ma zata ga sakayya ai yanzu tun a duniya ake fara ganin sakayya." Maganar Gaje ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin dana afka don haka na share hawayena nace mata zan tafi gida na gaji da zama gidan nan tunda dai gari ya waye rana ta fito. Itama tace tafiya za tai duk da ba yadda ba tai da Ni ba na ci abinci ko na sha koko na ƙiya ba, domin babu abin da zan iya ci ko sha yanzu Ni.
 
Bayan na dawo gida sai abin ya zame min biyu kawai naji ina kewar ƙawata Alawiyya ko tana ina yanzu? Ko itama an mata auren dolen ne? Ko tana can tana karatunta? Ƙarshe nayi mata addu'ar Allah Yasa tana cikin aminci a duk inda take.
 
Sai can yamma Deeni ya shigo gidan ko sallama daman bata dame shi ba sai sa'a yake yin sallama, kai tsaye ƙuryar ɗaki ya wuce ko kallo ban ishe shi ba, ya ɗan jima sai kuma ya fito ya sake ficewa ba tare da ya kalli inda nake tule ba da uban cikina ba, wasu hawaye masu zafin gaske suka zubo min, wace irin rayuwa ce ke tunkara ta? Miye laifina a zaman aurena? Deeni bai taɓa nemana na juya mai baya ba, haka Deeni bai taɓa sakani abu na tsaya ɓata lokaci ba, komai ina yi daidai ƙarfina sau tari ma ina ƙure kaina amma ban nuna damuwa, kawai burina na zauna lafiya da mijina, so nake na samu gatan da na rasa daga iyayena, so nake na samu ƴancin dana rasa daga iyayena. Tunda akai aurena ban saka Babana a idona ba, haka babu wanda ya zo daga wajensa daga ni sai dangin mahaifiyata kawai nake rayuwata, ina jin ciwon yadda nake rayuwa tamkar marainiya tamkar ban da Uba amma ya zan yi? Wannan yasa nake da burin zaman aurena ya zama shi ne farin cikina mijina ya zama mai share min hawayena mijina ya zama silar dariya a fuskata ko da yaushe, amma taya kenan? Tun asalima daman kallon marar wayau na kula yake min, domin abubuwa da dama idan ya yi min kallonsa kawai nake na kauda kaina ba don ban san cuta ta ya yi ba ko ƙuntata min ba, a'a sai don zaman lafiya kawai nake so mu yi, sannan ban da kowa sai shi, shi ne kawai gatana sai mahaifiyata da sauran danginta to su kuma kowa ta kanshi yake babu mai ƙarfi a cikinsu, dama ban saka dangin mahaifina domin su ɗin basu san da zamana ba, ko gidan naje ban jin daɗin yadda ake nuna min halin ko in kula gabana ake fifita yaran ƙanin Babanmu da Yayyensa hakan na mun ciwo don haka na daina zuwa nake rayuwata cike da tausayin kaina. 
Yanzu ya zan yi kenan? Tabbas Ina gab da faɗawa cikin tashin hankali wanda yafi na baya ga dukkan alama... Sallamar yaron makwabtan Mamarmu ya dawo dani daga tunanin da nake.
"Ance a gaya maki Allah Ya yiwa mijin Mamarku rasuwa yanzu." 
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Kasa kuka nayi shike nan, tawa ta sake samuna, yanzu Mamana zata shiga cikin ƙunci na gaske kenan tunda mijinta mutum ne mai tsoron Allah yana bakin ƙoƙarinsa kanta har da Ni, ya sha zuwa guna mu gaisa ya ban kuɗaɗe ya sha kawo min kayan abinci. Allah Sarki ni Jiddah na sake rasa wata damar kenan.
 
Bayan yaron ya tafi na leƙa don ganin ko zan ga Deeni na gaya mai amma ban ganshi ba, ga shi ina son tafiya kafin a kai shi gidansa na gaskiya, hakan yasa kukana ƙara yawaita naita zagaye gidan tamkar ina ɗawafi amma ban samu mafita ba, domin dai nasan babu kyau mace ta fita gidan mijinta bai sani ba. 
Na fi awa uku a cikin tashin hankali sai ga shi ya shigo kunnensa maƙale da abin jin kiɗa har rausayar da kansa yake alamar kidan da yake sha yana mai daɗi.
Bayan ya shiga ɗaki na bishi duk da kukana ya kasa tsayawa nace mai, "An aiko daga can gidanmu mijin Mamarmu ya rasu ɗazun daman jiranka nake ka zo sai na tafi." Wani banzan kallo ya watsa min ya taɓe bakinsa ya ɗaga kafaɗa ya wuce ni tsugunne ina tsiyayar da ƙwalla. Jikina sanyi ƙalau na tashi na zari hijabina na rufe gidan na tafi gidan gaisuwar ina cike da tunani kala-kala a zuciyata. Lokacin da naje har an rufo shi an dawo, da ƙyar na gaisa da mutane na shige ƙuryar ɗakin Mamana na kwanta na cigaba da rera kukana.
 
Ana gama sallar magrib Mamana ta shigo inda nake ta taɓa jikina taji zafi rau, tace, "Ki tashi ki tafi gida kar dare ya yi sosai kinga bake kaɗai bace ba, kuma ba a san ana kai wa dare kin ji?"
Allah Sarki Mamana ban san tana ina zan kama ba ko da naje gidan dama kin barni na kwana a nan. Haka zuciyata ke gayamin domin ni lamarin Deeni ya wuce sanina ma yanzu abin nashi gaba ya yi madadin ya ban haƙuri sai ma ya fito da sabon hali mai wuyar gaske.
Ganin ban da mafita na tashi da ƙyar na shirya zan tafi Mama ta aika aka siyo min fura da nono tace na dama nasha kafin na kwanta.
Tun daga nesa na hango Deeni tsaye ƙofar gidan fuska a ɗaure ya tsira min ido tun daga nesa yana ƙare min kallo. 
Gabana ya faɗi cikina ya yamutse kawai naji ban iya ɗaga ko da ƙafata guda don haka na tsugunne a gun cikin mawuyacin hali.
 
Shi kuma Deeni ganin haka sai ya ɗauka wani sabon rainin hankali ne ta zo da shi daga kawai ta iske shi yana har kar gabansa uban miye na ta ɗauki damuwa ta ɗora ma kanta har ma take wani kukan munafurci zata gane kurenta don ba zai bari ta raina shi ba, ai ba da kuɗin ubanta yake neman matan ba, idan tace zata kawo mai rainin hankali ita ce a ruwa ba shi ba.
 
Don haka a fusace ya nufi inda take tsugunne rai ɓace.
 
 
Mu haɗe a page na gaba don jin yadda rayuwar auren Jiddah ta koma.
Taku a kullum Haupha!!!!