Babban Buri:Fita Ta Ashirin Da Biyar

Sai lokacin na kula da Fateema dake hakimce gaban mota sai fira sukeyi abinsu da'ita da abokin Ya Haidar. Jin motar ta tsaya ne yasa nasan mun kawo wurin. Fitowa muka yi muka fara tafiya ya yinda abokanan Fateema dana Ya Haidar suka take mana baya. Muna shiga cikin ɗakin taron kiɗi ya canja salo sosai ake waƙemu a cikin waƙar wacce ba ƙaramin daɗi ta yi ba. Sai guraren 11:30pm aka tashi daga taron , waƴanda zasu yi rakiyar amarya suka yi gaba waƴanda zasu koma gida suma suka kama hanyar su. Ba a mota ɗaya muka koma ba wannan karon dani da Gwaggo matar malam da wata ƙanwar Baba dake Wurno ne a cikin motar.

Babban Buri:Fita Ta Ashirin Da Biyar
BABBAN BURI
 
 
 
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
 
 
 
 
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.
 
 
 
 
 
 
 
FITOWA TA ASHIRIN DA BIYAR
 
 
 Yau takama Laraba kuma yaune za'ayi wankin amarya, sosai ƴan uwa na nesa dana kusa suka samu zuwa, duk inda ka duba zaka tsinkayo al'umma zaune suna sha'anin su.
 
 
Ƙarfe 4pm an kammala ƙawata harabar gidanmu da kayan ƙyale ƙyale iri iri , wurin ya ɗauki ƙyalli gwanin sha'awa.
 
Haka aka fito dani nasha atamfa me kwaleliyar jaah.
Turmi ɗaya ne aka raba gida uku, ɗaya na ɗaura ɗaya aka ɗauramin akai ɗaya kuwa na yi lulmuɓi dashi a kayimin kwalliya irinta zamanin da, gashi nasha ƙunshi jaah na fito gwanin sha'awa dani kamar ka sace ni ka gudu.
 
Ƙawayen Fateema ne biye dani a baya suma sunyi shigarsu gwanin sha'awa.
Yayinda a tsakiyar fili kuwa kiɗin kwarya ne ke tashi mutane sai taka rawa suke yi.
 
A can tsakiyar fili na tsinkayo ANTY HAUWA MAMAN USWAD da ANTY FATEEMA SUNUSI RABI'U UMMU AFFAN da ANTY MAIJIDDA MAI KUƊI da ƴan group ɗin BABBAN BURI, gaba ɗayan su sai taka rawa suke yi cikin salon burgewa.
 
A haka aka watse taron lafiyar Allah, duk wacce zata wuce da tata jikka mai ɗauke da pink flower a jikinta tare da suna na dana Ya Haidar.
 
Da daddare ma haka akayi ta kiɗin ƙwarya sai wuraren 11pm kana suka sarara.
 
Baccin gajiya na yi Sosai dan ma Allah yasa gobe bama yin komai sai gurin gyaran kai da zanje nida Fateema koshi sai bayan la'asar.
 
 
★★★★★★
 
*Rana bata ƙarya........*
 
Yau da misalin ƙarfe 12pm dubban mutane suka sheda auren Aliyu Aminu Suleman Wurno da amaryarsa Nana khadeejah Aliyu Suleman Wurno, akan sadaki dubu ɗari.
 
Sosai aka gudanar da wasanni bayan ɗaurin auren kana daga bisani aka wuce wurin walima.
 
Ƙarfe 2pm aka shigo da ango gida bayan andawo daga wankin sa a gidan limamin masallacin unguwarmu, sosai ya yi kyau cikin farin yadi yasha babbar riga da rawani.
 
Ƴan uwa sukayi ta zuba masa kuɗi da turamen atamfa haɗi da turare.
 
A lokacinne aka fito dani nima cikin shigata ta farin yadi nasha kwalliya sai ƙyallin amarci nake yi, akayi ta zuba mana photuna idan ka ganmu kamar ka sace mu ka gudu.
 
 
Bayan sallar magarib Baba ya tara mu a ɗakin Hajiya Inna ya yi mana faɗa sosai haɗi da sanar dako wannenmu haƙƙin ɗan uwansa daya rataya a kansa.
 
Itama Hajiya Inna haka ta yi mana faɗa sosai tana yi tana sharce hawaye.
 
Daganan aka sallame mu, nikam gurin shirin zuwa dinner na tafi, lokaci ɗaya kuwa aka tsantsaramin kwalliya taji da faɗi idan ka ganni ba zaka taɓa cewa nice Khadeejah ba.
 
9pm motocin ɗaukan amarya suka fara tafiya da ƴanmsta gurin dinner , lokacin da akace motar ango tazo a lokacinne kuka yazomin na rirriƙe Mama ina faɗan "ba inda zanje nikam a gaya masa na hwasa auren, daga ni har A'isha kuka mukeyi wanda ya ƙaryawa Mama gwiwa itama lokaci ɗaya kuka ya suɓuce mata.
 
Nan mukayi ta kuka saida Baba yazo ya ɓanɓareni jikin Mama ya fito dani daga sashenta ya shigar dani cikin motar dake parke a tsakar gidan kana ya juya ya yi tafiyarsa yana sharce ƙwallar data zubo masa.
 
Kaina na ɗaura a saman gwiwata inaci gaba da kuka maicin rai.
Jin mutum kawai na yi ya rungumo ni jikinsa, ban zata yana cikin motar ba sai da naji ya rungumo ni.
 
Ƙara lafewa na yi cikin jikinsa ina mai sauke ajiyar zuciya.
 
Sharce min fuskata ya hauyi sai da ya gyaramin fuskar tawa sannan ya ƙyeleni yana me tausata da kalamai masu sanyaya rai.
 
Sai lokacin na kula da Fateema dake hakimce gaban mota sai fira sukeyi abinsu da'ita da abokin Ya Haidar.
 
Jin motar ta tsaya ne yasa nasan mun kawo wurin.
Fitowa muka yi muka fara tafiya ya yinda abokanan Fateema dana Ya Haidar suka take mana baya.
 
Muna shiga cikin ɗakin taron kiɗi ya canja salo sosai ake waƙemu a cikin waƙar wacce ba ƙaramin daɗi ta yi ba.
 
Sai guraren 11:30pm aka tashi daga taron , waƴanda zasu yi rakiyar amarya suka yi gaba waƴanda zasu koma gida suma suka kama hanyar su.
 
Ba a mota ɗaya muka koma ba wannan karon dani da Gwaggo matar malam da wata ƙanwar Baba dake Wurno ne a cikin motar.
 
Kai tsaye gidana suka zarce dani daga gurin dinner.
 
Sosai aka dinga faɗamin addu'ain da zan shiga dasu cikin gidan lokacin da zan shiga , bakina ɗauke da bisimillah na sanya ƙafar dama a cikin gidan , iname rufe idanuwana ina karanto addu'oin da Gwaggo ke raɗamin cikin kunne.
 
A saman gado na aka ajiyeni lulluɓe da ɗan mayafin dana yi amfani dashi a gurin dinner.
 
A bakin mutane na dinga jin suna santin ɗakin nawa da yaba irin dukiyar da aka narkarmin, domin kuwa kaina na ƙasa.
 
Sai 12am suka watse aka barni daga ni sai halina ko Fateema bata tsaya ba , tabi bayan ƴan uwana suka tafi suka barni ni kaɗai.
 
Toilet na shige na watso ruwa sannan nazo na sanya atamfar da Fateema ta ajiyemin.
 
Sallar isha'i na gabatar sannan na haye gado nayi zamana haɗi da sanya mayafi na rufe fuskata.
 
Ban jima da zama ba Ya Haidar ya shigo ɗakin hannunsa riƙe da leda, kai tsaye saman mirror ya ajiye ledar sannan ya dawo kusa dani ya zauna yana mai sanya hannunsa ya yaye lulluɓin da na yi.
 
Kallona ya dinga yi yana me ƙara godiya ga Allah daya mallaka masa ni.
 
Umurtata ya yi dana yo alwala a banɗaki cikin rawar Muryar dana rasa dalilin sauyawarta na ce dashi"inada alwala".
 
Banɗaki ya shiga yayo alwala sannan ya fito ya jamu sallah raka'a biyu sannan ya jaa mana doguwar addu'a.
 
Fita ya yi ya dawo hannunsa riƙe da plate da wuƙa ya janyo ledar daya shigo da'ita .
 
Kaza ce gasashiya sai turirin zafi take fitarwa haɗi da ƙamshin daɗi.
 
Sosai naci na ƙoshi sannan na kora da madara.
 
Miƙewa na yi nayo brush sannan na dawo na ɗane gado haɗi da lulluɓe jiki na da bargo.
 
 
★★★★★★
 
Kiran sallar farko a saman kunne na akayi ta, na tafi miƙewa naji ƙafafuwana a riƙe , hawayene suka silalomin daga kan kuncina banma samu zarafin ɗauke suba.
 
Ji nayi anyi sama dani ko ban faɗa ba nasan Ya Haidar ne, rufe idanuwana na yi iname cusa kaina a cikin ƙirjinsa.
 
Sosai na samu kulawa a garesa, lokaci ɗaya na wartsa ke.
 
Sosai na jinjina wa Baba da Ya Haidar domin ganin uwar dukiyar da suka narke min.
 
Yinin ranar naga tattali haɗi da tarai raya a gurin mijina , nasan ba dan komai hakan ta kasance ba saidan samuna da yayi a cikakkiyar mace na tabbata dana yi watsi da mutumci na tun a waje tabbas da wannan ranar saina fuskanci cin zarafi da wulaƙancin a gurin mijina, na yi wa Allah godiya daya nufeni da kawowa mijina daraja ta ta ƴa mace.
 
Tabbas yanzu duk buruk kana Allah ya cikamin su saura ɗaya tal kuma shine *BABBAN BURI* da nake dashi a rayuwata na inbawa ƴar uwata ilimi mai yawan gaske wanda zata yi alfahari da hakan a ko ina da ƙarfin jikina.
 
 
★★★★★★
 
Bayan wata ɗaya.
 
Yau watan su Baba Bello biyar a gidan yari, kuma a yaune aka zartas masu da hukuncin su na kisa ta hanyar rataya.
 
Tau sai dai muce Ubangiji Allah ya sa muyi ƙarshe mai kyau........
 
Za mu cigaba Gobe........
 
ƳAR MUTAN BUBARE CE