Hankalin Magidanci Ya Tashi Bayan Da Amaryarsa Ta Yi Mutuwar Kai Tsaye A Dakin Kishiyarta

Hankalin Magidanci Ya Tashi Bayan Da Amaryarsa Ta Yi Mutuwar Kai Tsaye A Dakin Kishiyarta

 Iyalan Malam Musa, mazauna Zaria a jihar Kaduna, sun fada tsananin tashin hankali da alhini sakamakon rasuwar kai tsaye  da amaryarsa mai suna Gambo ta yi a dakin kishiyarta.

Bayanai sun tabbatar da cewa, Gambo ta ziyarci kishiyoyinta biyu dake gida daya a sanyin safiyar Juma'a data gabata.

Duk da ba wata jituwa ke tsakaninsu da kishiyoyin ba, sun zauna suna taba hira inda suke jiran dawowar mijinsu wanda yayi balaguro.

An kawo wa Gambo abinci amma tace ba za ta ci ba saboda ta kira mijinsu a waya tace masa tana bukatar cin gurasa, wacce yayi alkawarin taho mata da ita idan zai shigo gidan.

Bayan isowar Malam Musa ne ya tarar da wannan lamarin inda ya gigice tare da fita hayyacinsa.  

An yi wa Gambo jana'iza kamar yadda addinin Islama ya tanadar tare da kai ta gidanta na gaskiya. Bayanai daga bakin mijin Gambo da 'yan uwanta na kusa sun tabbatar da cewa tana fama da ciwon zuciya, lamarin da yasa ake  tsammanin cewa zuciyar ce tayi ajalinta waton ta samu bugun zuciya kenan.