WATA UNGUWA: Fita Ta 18
WATA UNGUWA: Fita Ta 18
Page 18
BABI NA SHA TAKWAS
_NISAN KIWO_
"Hajiya ga motocin garin." Ɗan union ɗin ya faɗa yana nuna mata motocin dake lodi da yatsansa.
Ya kalli karen motar ya ce "kondusta ga fasinja a saka ta a motar Balgori don Allah."
"Ok ta shiga wannan motar saura mutum ɗaya ta tashi." Karen motar ya faɗa.
Maheerah ta shige motar kai tsaye ta zauna tana ci gaba da sake sake a ranta.
Ɗan union ɗin ya ci gaba da tsayuwa a gurin da alama yana jiran ta sallame shi, sai dai ba alamar zata ɗago ta kalle shi bare ya saka ran ta ba shi wani abu.
Girgiza kai ya yi cikin tausayawa a ransa ya ce 'Da alama wannan budurwa tana cikin kalubalen rayuwa.'
Kondusta ya fara tattara kuɗin matafiya har ya zo kan Maheerah ya ce "Hajiya kawo baki."
Sai da ya maimaita zancen kafin ta ji ta ɗago da jajayen idanunta ta zuba masa su. "Nawa ne kuɗin?"
"Dubu huɗu."
"Habah dai malam dubu huɗu ya yi yawa." Ta marairaice.
"Su ne kuɗin saboda tsadar mai, idan baki da su iya iya sauka daga motar."
Sai a lokacin ta tuna da jakar makarantar dake rataye a kafaɗarta dama abin da ya ɗarsa mata tunanin barin gari. Don haka ta sauke jakar.
Dubu huɗu ta ƙirgo ta bashi sannan ta cilla duniyar tunani.
"Mahee Baby ga wannan kuɗin dubu 20 ne ki ajiye mana su a wajenki, na yin kodumo ne a watannan, kin sani dole zamu shayu sosai."
Maganar Ja'afar ta safiyar yau ta dinga dawo mata a kunne tamkar yanzu yake furtata.
Murmushi mai ciwo ta yi ta ce a ranta 'Kuɗinka ne zasu min jagora zuwa inda zan yi shirin tarwatsa rayuwarka. Shi kuma Babana zai ga ribar sallama jini wa duniya na yi maku wannan alƙawarin.'
A daidai lokacin motar ta shiga direban ya cilla hancin motarsa ya fice daga tashar, sai fatan a sauka lafiya.
******"*"*****
Zumbur ya mike tsaye bayan shafe tsayin daƙiƙu yana mayad da numfashi tamkar wanda ya yi tseren gudu. Cikin hanzari ya fice daga ɗakin yana dube-dube.
Duddoo dai bai ce masa uffan ba sai binsa yake da ido. Can bayan daƙiƙa biyar sai ga shi ya dawo ɗakin ya tsaya tare da ɗora hannu ɗaya a kai yana hargiza gashinsa.
"Me ya faru ne Jafsee?"
Iska ya fesar daga bakinsa sannan ya ce "Wannan macijiyar ta gudar mini da kuɗi."
Ɗan murmushi Duddoo ya yi sannan ya ce "Har nawa ne kuɗin?"
"Dubu ashirin ne fa, gaskiya ta jiƙa min aiki." Ya faɗa yana jan tsaki tamkar jikan jaɓa, sannan ya ce "Da na san inda ta je ba shakka da na bita na karɓo kuɗina amma ba komai gobe ma rana ce."
****. ******
Ana cewa dare mahutar bawa, domin a lokacin ne ruhuka kan sami nutsuwar hutawa. Duk da ƙwarewar bacci da shahararsa a bangaren sata a ranar bai yi gigin satar Irfan ba. Domin kuwa yadda ya ga safiya haka ya ga dare. Ya ɓata muhimman sa'o'in shi na hutawa gurin tunanin mafita a matsalar da ta Kunno masa kai a rayuwa.
Washegari tun da sassafe ya fice daga gidan ko ƙaryata bai yi ba. Ko da hajiyarsa ta zo kiransa su ci abinci sai ta tarad da sashensa a rufe.
Sosai ta yi mamaki don haka ta je ta sanar da alhajinsa ba bata lokaci suka kira shi a waya.
"Wai Ina kaje ne da safe haka Irfan?" Alhajinsa ya tambaya.
"Am! Alhaji ina wurin aiki ne, da akwai wani aikin da ban kammala ba jiya shi ta sa na yi sakko yau." Ya faɗa a hargitse sannan ya datse kiran gudun kada Babansa ya kuma jefo masa wata tambayar da zai kasa amsawa.
Bayan fitarsa gida bai zame ko'ina ba sai gidansu Mahee don yana son ya samu Baba ko Sadiƙu a gida don duk da bai tabbacin Baban zai saurare shi.
Yana zuwa ya ja ya tsaya a ƙofar gidan tamkar ɗan dokar da aka bawa aikin kama mai laifi. Sadiƙu ne ya fara fitowa daga gidan riƙe da buta yana shirin wanke fuskarsa, da alama tashinsa kenan daga barci.
"A'ah! Irfan kai ne tun da sassafe haka?" Ya faɗa cike da mamaki duk da bai kamata ya yi mamakin ba. Domin a dai yadda Irfan ke matuƙar son Maheerah zai iya yin abin da yafi haka a kanta.
"Ni ne ina kwana yayanmu?" Murmushin yaƙe Sadiƙu ya yi.
"Lafiya ƙalau malam Irfan, meke tafe da kai? Ina ce jiya na maka bayanin komai bai kamata ka dawo nan ba."
"Ka dai gutsira min bayani, amma baka ba ni cikakkiyar hujjar da ta saka Baba ya korar min mata ba." Ya faɗa a sanyaye.
Janyo hannunsa Sadiƙu ya yi suka shige zauren gidan, ya tura ƙofar ɗakinsa dake zauren suka shiga sannan ya sake hannunsa.
"Yawwa zauna nan mu yi magana a sirrance." Sadiƙu ya faɗa yana nuna masa gefen katifarsa.
"Wane irin laifi Mahee ta aikata wa Baba har ya kore ta daga cikin rayuwar ahalinsa?" Irfan ya tambaya tare da kafe Sadiƙu da manyan idanuwansa.
Sadiƙu ya yi da ajiyar zuciya Hmmm sannan ya ce "Ranar wanka ba a boyon cibi, duk yadda na so da son rufe maka gaskiya watarana zata bayyana ne, har gara ka ji da bakina. Mahee jinina ce amma ta yi abin da ko dabbar dake rayuwa a gidanmu bata yi ba." Ya ɗan tsagaita yana karantar yanayin Irfan.
"Har yanzu ban ji laifin da ta yi ba ai."
"Me kake ci na baka na zuba? Yanzu zan kaika filin sukuwar, inda zaka hau dokin da zai tabbatar maka da abin da kake son ji."
Irfan bai sake cewa komai ba ya dai yi masa ƙuri da ido, tamkar ya ga baƙuwar halitta.
Sadiƙu ya ci gaba "Mahee ta ɓata kanta ne da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, daga ƙarshe ta biye wa wancan lalataccen yaron na unguwar Dagarma shi ne ya ɗora ta a wannan turbar kuma ya lalata mata rayuwa daga nagartacciyar yarinya zuwa mazinaciya."
Tun da Sadiƙu ya fara magana Irfan ya yi suman zaune tuni ya daskare a gurin, kalmar Sadiƙu ta ƙarshe akan Maheensa ita tafi cakar masa zuciya 'Mazinaciya? Wal iyazu billah.'
Cikin barin baki ya ce "Habah! Yayanmu na yi tunanin idan kowa zai kama raɗa ko jita-jitar magulmata kai ba zaka kama ba. Shi kuma Baba kawai sai ya yanke hukunci ba tare da bincike ba?"
Murmushi mai ciwo Sadiƙu ya yi kafin ya girgiza kai ya ce "Ka yi tunanin wani ne ya faɗa mana?
"Eh mana, nasan bai wuce sharrin mahassada."
"To ba wani ba ne ya faɗa dubunta ce ta cika, an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa, ranar da asirinta ya tonu da kaina na bi ta a baya bayan ta fita da shirin makaranta. A nan na gane wa idanuna abin da har gobe ya kasa gogewa a maɗaukar hoton idanuna."
Irfan ya jijjiga matuƙa lokacin da yake sauraren wannan labarin da ya kasance mafi muni da ya taɓa ratsa masarafar sautinsa. Ya dafe saitin ƙirjinsa tsawon daƙiƙu bai ce komai ba kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ya ce "Yayanmu yanzu ina kake tunanin zan same ta?"
"Na yi fatar ace na sani Irfan, da na riga ka zuwa, na yi nadamar bayyanar da wannan sirrin ga mahaifanmu. Da na san haka zata faru da na binne wannan sirrin a raina sannan na samowa ƙanwata mafita." Ya faɗa yayin da yake ƙoƙarin shanye ruwan hawayen da ya taru a idonsa.
"Ka ban address ɗin mayaudarin saurayin nata, mai yiwuwa zan samu wata fitilar da zata haska min inda zan sami matata.
Ya miƙe, ya karɓi address ɗin sannan ya fice.
Sadiƙu ya girgiza kai yana jinjina irin girman soyayyar da Irfan ke yi wa Maheerah, duk da wannan ɓarnar da ta aikata har yanzu baya ganin laifinta kuma bai janye ƙudirinsa na aurenta ba.
***** ***** ******
Zaune take a cikin mota yayin da motar ke ta cin hanya ta zuba tagumi da dukkan hannayenta guda biyu, hawaye ne ke tsere a kumatunta. Bata damu da share su ba, sosai ta zurfafa a kogin tunanin rayuwar da zata fuskanta bayan rabuwarta da ahalinta.
"Baiwar Allah meke damunki?" Wata siririyar murya ta ratsa masarafar jinta.
Ta dago tare da share hawayenta ta ce "Ba fa.........
Ummu Inteesar