MAMAYA:Labarain Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta Bakwai 

MAMAYA:Labarain Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta Bakwai 

 

 *Shafi na Bakwai*

 

 

'Baiwar Allah , bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin gidan, sai dai turus tayi tsakar gidan tana ƙare ma Innarsu kallo yanda ta ga ta wani kwasa da gudu ta faɗa ɗakinta.

 

Ta jima tana tunanin Inna tana fama da matsala, domin tana yawan kamata da abubuwan ban mamaki da tambayoyi da yawa amma sam bata bata damar da zata binciki damuwarta .

 

 

Kai tsaye ɗakin Innarsu ta nufa bakinta ɗauke da tarin tambayoyi da zatai ma Innar tasu yau dai.

 

 

Sai dai me !

Tana shiga ta iske Innar su sai sheƙa barci take hadda jan numfashi irin na waɗanda barci yayi ma shegen daɗin nan.

 

 

Kanta ya sake ɗaurewa da ganin hakan , ba yanda za'ai daga shigowar Inna cikin ɗakinta ace har tayi irin wannan barcin.

 

 

Juyawa tayi cikin sanyin jiki ta nufi nasu ɗakin, zuciyarta na bata shawarwari da dama ga me da halin mahaifiyar tasu .

 

Cikin ƙanƙanin lokaci ta cire kayanta ta watsa ruwa, ta je ta ɗauko nata abincin sai ta iske abincin a zube gun gashi tamkar yarane sukai wasa kanshi , ga alama kowane kwano sai da akai wasan zubawa da juyewa a cikinsa .

 

Gyara komi tayi zuwa muhallin da ya kamata , sai dai zuciyarta ta gaza aminta da abincin nan , bakinta alaikum ta ɗaukesa duka ta juye cikin masan su .

 

Bata tsaya ɓata lokaci ba ta kunna wuta ta ɗora wani girkin.

 

Ɗakin Innar ta sake komawa domin tana jin tausayin Innar can ƙasan zuciyarta ainun .

 

 

Still barci take yi tamkar matatta wannan lokacin dan babu jan numfashin ɗazun kuma .

 

 

A hankali ta isa gaban Innar ta fara karanto ayoyin Alqur'ani mai girma cikin kunnuwan Innar .

 

Ya Salam !

 

 

"Ashe daman kallon mahaukaciya kike mun duk abin nan ?

 

"Ai kuwa bari Ubanki ya dawo kasuwa yau sai ya rabani da ke cikin gidan nan wallahi ,,

 

 

Tsabar tsoro ya bayyana a fuskar Bilkisun ganin yanda fuskar Innar ta koma yau .(duk tayi kumburi ga alamar yakushi nan a fuskar tamkar wadda tayi dambe da mazuru )

 

 

Sai da takai sumuni sannan ta dubi Innar hankali tashe tace " Miya sameku Inna haka a fuska ?

 

 

Ba ƙaramin daɗin ganin raunin fuskarta da Bilkisun tayi ba ta ji, ko banza yarinyar akwai ta tausayi da kulawa , bayan hakan da tuni anyi uwar watsi a gidan komi zai faru ya faru .

 

 

"Inna miya faru daku ne haka dan Allah ?

 

 

Cikin alamar jin jiki Innar ta dubeta tace ,

 

"Jiyane cikin dare na fito zanyi fitsari sai na zame na faɗi ,,

 

Kallon Innar takeyi da alama ta dai ji maganar ammafa ba dan ta yarda ba.

 

"Inna ya kamata ku dinga neman tsari daga dukkan tsautsai da masifu , saboda duk wanda ya saba da yawaita tasbihi ga Ubangiji da wuya kiga yana fadawa cikin masifu ,,

 

Bata ankaraba sai jin saukar duka tayi ɗum !

 

"Ni zaki tasa gaba kiyimun wa'azi dan uwaki ?

 

"Da kika ganni nan kamar a banzace to sai da nayi saukar hizifi ɗaya da rabi sau ukku ,,

 

Ita dai Bilkisu sadda kanta ƙasa tayi , ta san cewa yau ta tsokano faɗan Innar tasu .

 

 

Tunowa da girkinta yasa ta ba Innar haƙuri ta nufi gun girkinta .

 

Tsab ta gama girkin nata , tana jiyo tashin muryan faɗan Innar tasu na fitowa daga cikin ɗakinta.

 

 

Ta zubama kowa nashi ta ɗauki na innar tasu ta nufi ɗakinta da nata .

 

 

Tana buɗe abincin ta fara taɓa hannuwa .

 

"Yau Ni Huraira naga ta kaina , yanzu ƴarnan dan Ubanki sake wani girkin kikayi ?

 

"Oh Ni Huraira !

Ka haifi yaro baka haifi halinsa ba ,,

 

Ita dai Bilkisu ta dage sai haƙuri take bata kanta a ƙasa .

 

 

Suna cikin haka ne Babansu ya shigo gidan.

 

Girgiza kansa yayi kafin ya dubi Bilkisun ya tambaye ta .

 

"Ɗiyar albarka mike faruwa ke da Innar taku ?

Kafin Bilkisu tayi magana har Innar ta zabura ya tashi zaune tace "Nasan daman ita kaɗai zaka tambaya ban da Huraira sarkin faɗa da mita ai,,

 

Dariyar murmushi yayi , ya miƙa ma Bilkisu ledar dake riƙe ga hannunsa.

 

"Saƙonki inji yaron nan Nasiru,,

 

Ai sai Inna ta i da birkice wa ,

 "Allah akan yaron nan sai mun saɓa da kowa nan gidan, yaron ko kunya bai da ita ga ƴar banzar zuciya sai shegen faɗin rai da  ban tsoro na banza da ya iya ,,

 

Daga Mal. Ahmad ɗin har Bilkisun kallonta kawai suke yi dan abin nata yaso yayi yawa yau .

 

Miye na sanyo Nasir cikin tsogumi da mitar da ta saba yau?

 

"Inna kiyi haƙuri gashi kiga ko miye dan Allah ,,

 

"Yo Allah na tuba ai dole a ban na fara buɗewa naga tsiyar dake cikin saƙon,,

 

 

Ita dai Bilkisu ganin ta manta da laifin da tayi mata yasa ta saɓe ta bar ɗakin tana hamdala .

 

 

 

 

Sai da ta gama komi ta shirya yau islamiyya zata je domin Baba ya shaida mata babu abin da malam Aminu (Ɗan bahago)zai mata ko ta je makarantar.

 

Babu abin da batayi ba na gyaran gidan dana ƙannenta san nan ta fice zuwa makarantar .

 

 

Ba ƙaramin daɗi taji ba da ta ga anata shawagi waje alamar bata makaraba kenan yau ,

 

Kai tsaye ajinsu ta nufa dan tasan Shema'u ta jima da zuwa yanzu , (saboda Shema'u bata makara nan take sallar la'asar dan karma ta makara)

 

Tayi mamaki kwarai da bata hango Shema'u ba a gun zamansu dan haka  ranta ya bata Shema'u bata lafiya duk yanda akai dan sun rabu ɗazun a makarantar boko tana shaida mata yau idan sun tashi islamiyya zasuje gidansu Hauwa'u Sani (kawarsu ce ) su dubo mamarta bata da lafiya .

 

Dan haka ta juya ta nufi gidansu Shema'u duk da cewa akwai ɗan nisa da makarantar tasu .

 

Kasancewar sauri take ba ƙaƙƙautawa yasa nan da nan ta isa gidansu Shema'un .

 

Bayan sun gaisa da Mama ne take shaida mata ai Shema'u tace "yau ta gidansu ita Bilkisun zata biya mata su wuce tare islamiyyar .

 

Hakan yasa ta gane sun sha banban a hanya kenan.

 

Itama saita juya cikin sauri ya koma islamiyyar , sai time ɗin ta ankara da wautar da tayi na sake fitowa daga cikin islamiyyar duk da cewa ta san da wuya in zasu haɗu da mal. Aminu yau ,

ance yayi tafiya .

 

 

 

Bata samu kwanciyar hankali ba sai da ta ganta filin islamiyyar ba kowa duk an shige aji ana karatu.

 

Nasu ajin ta nufa cikin kwanciyar hankali dan tana jiyo sautin surutu ƙasa_ƙasa alamar babu malami ajin nasu .

 

 

Mal. Aminu (ɗan bahago) zaune yana tunanin yanda kwata_kwata bai son yaji lokacin zuwa islamiyya yayi, domin duk yanda yake jinsa cikin farin ciki yana zuwa bakin makarantar zai tsinci kansa cikin wani yanayi wanda bai san yanda zai misaltashiba .

yasha matsama kanshi da tambayar mike damunsa a cikin kwana kin nan .

 

 

Tafiya garesa zuwa Kaduna amma kawai ya samu kansa cikin makarantar islamiyyar ba tare da yasan abin da zaiyi cikinta ba.

 

Bilkisu nata sauri domin ta shige ajinsu sai kawai taci karo da Mal. Aminu ranshi a ɓace ga wata ƙatuwar bulala riƙe a hannunsa ya tunkarota kai tsaye .

 

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un !

 

'Shine abin da Bilkisu ta ambata kenan taja tayi tsaye a gun da take .

 

Tun kafin ya ida kawowa gareta fuskarsa ta sauya zuwa fuskar ban tsoro ,

 

Tsugunnawa gun tayi jikinta na kyarma , hankalinta a matuƙar tashe .

 

 

Bai jira komi ba ya fara dukanta ba tare da sauraran wani uzuri daga gareta ba , haka bai ji tausayin kukan da take yi ba .

 

Sai da ya tabbatar da jikinta ya gama gaya mata sannan ya zubar da bulalai yayi tafiyarsa ya barta a gun tana kuka.

 

Shema'u tun daga nesa ta hango abin da ke faruwa take kuka , ta rasa abin da ke faruwa kwanakin nan da ƙawar ta ta Bilkisu , tana yawan shiga cikin matsala da damuwa gun malamai biyun nan Sir Muntasir da Mal. Aminu sun matsa mata sun takura mata a rayuwar makaranta .

 

Haka dai ta isa da gudunta ,miƙar da ita sukai suka rungume juna suna ci gaba da kuka suka nufi ajinsu .

 

 

Nasir kwance ɗakinsa yana tunanin Bilkisu , yarinyar tayi daidai da wadda yake muradin samu matsayin matar aure .

 

Sai dai yana son bincike kan yarinyar sosai dan ya lura Inna ba ƙaramar wahala take ba yarinyar ba, duk ta ƙare ba ita ce ta haifeta ba idan ya kin tata daidai.

 

Fuskar mutumin ke masa gizo a idanunsa, a fili yace " Ga alama kaine matsalata dan na hango soyayyar Bilkisu a ƙwayar idanunka , sai dai ka makara iyakarka malami nikam masoyi nake gareta .

 

 

Tofa waye ke son Bilkisu kuma ?

 

Badai Sir Muntasir ba?

 

 Taku Haupha ce.