ZOBEN WUTA: Labarin Mai Ban Mamaki da Tausayi

ZOBEN WUTA: Labarin Mai Ban Mamaki da Tausayi

ZOBEN WUTA


   By
Jiddah S Mapi


Chapter 4


                      ~Jirginsu yana landing suka fito a tare, Abeed ya ciro bakin space yasa a idonshi, kyau ya kara sosai akan wanda yayi da farko, Deen ke rike da trolley ɗinsu, motoci manya manya masu tsananin kyau duka baƙaƙe suka jeru tun daga bakin kofa har zuwa cikin airport ɗin, wani me baƙin kaya da bindiga a hanunshi da bakin glass, ya cire bakin glass ɗin da ɗan gudu yazo inda suke tsaye kusa da jirgin, durkusawa yayi alaman respect sannan ya karɓi trolley ɗin dake hanun deen, zubawa motan dake gaba ido sukayi su duka biyu suna jiran ganin wacce zata fito, duk a zatonsu Ammi ce hakan yasa kowa ya shirya domin yimata oyoyo, kyakkyawar matashiya me kama da larabawa ce ta fito daga motan, sanye take da farin kaya net ɗinkin a buɗe yake sosai, tana kama dasu sosai ba kaɗan ba saide sun fita fari, domin su har yellow yellow suka zama, mayafi siriri ne a hanunta yayinda tasa hulan net a kanta fari, ba zata wuce shekara 17 ba, jikinta kamar madara, cikin jin daɗi ta ɗan ɗaga rigan duk da high shoe ne a kafarta rigan ya mata tsayi, faɗawa tayi jikin Abeed tace "welcome back ya Deen"
cikin rashin fara'anshi yace "thanks"
zameta yayi a jikinshi domin yaji haushi da ba ammi bace tazo ɗaukansu"
kallonshi tayi sannan ta kalli na gefenshi da sauri ta faɗa jikin Deen tace "welcome back ya Deen"
cikin sakin fuska yace "zee-zee ya kike? ina Ammi?"
tace "Ammi na gida"
ya rike hanunta yace "okay let's go and meet her, munyi missing nata sosai"
kallon uban motocin da sukazo ɗaukansu yayi, a ranshi yayi tsaki yace "duk wannan motocin sabida mutum biyu? abu mota ɗaya ma ya isa"
buɗe musu marfin motan akayi, an tsaida kowa da shiga airport har sai sun fita kafin kowa zai iya shiga, jera motocin sukayi akan titin suna tafiya, kowa saida ya tsaya da tuki akan titin saida duk suka wuce da motocin kafin aka saki hanya.
Federal lowcost unguwan manyan masu mukamai da kuma kuɗi shine unguwan da suka nufa, faɗan irin manya manyan gidajen da suke unguwan ɓata lokaci ne, a kofan wani get me yalƙi kamar da ruwan gold akayi suka tsaya, tun daga bakin titin daya kama hanyan gidan abin kallo ne bale kofan gidan, a haka ma ba'a shiga cikin gidan ba, buɗe makeken get ɗin da yake sheƙi kamar kaga fuskanka a jiki akayi, cusa hancin motocin akayi har zuwa cikin gidan, duk yawan motocin saida suka shiga gidan, gida ne me girma sosai, kofofin glass ne a jiki ko ina abin kallo ne a gidan, buɗe musu kofan akayi suka fito tare, kyakkyawar yarinyar ta tsaya a tsakiyansu suka jera suna tafiya, Deen ne ya rike hanunta shi kuma Abeed hankalinshi akan waya, ciki suka shiga har zuwa falon alfarma dake gidan
"you are welcome my twins"
Ammi ce tayi magana, Masha Allah, wannan halittan dole ta haifo kyawawa, duk da ta manyanta hakan bai hana kyawunta bayyana ba, inda ake maganan kyawawa wannan matar ta kai harta dawo, tsadadden bakin leshi ne yake wanda yaji stones yake sheƙi a jikin tsadadden skin nata, duk da ta ɗaura ɗankwali hakan bai hana gashinta zuba har gadon bayanta ba, manyan idanunta duk sune abinda ƴaƴanta suka fi yin gadonshi, sexy eye's take ɗauke dashi idanu masu kalan na mage, cikin idon maimakon baƙi brown ne ga wani sarƙan da kana gani kasan na gold ne a wuyanta, hanunta ɗauke da zobe da warwaro na gold, matar nan karshe ce a wajen ado, ganin sun ɓata rai su duka sunki yimata magana ta kalli wanda yake rike da hanun zee-zee ta rungumeshi tace "Deen kada kuyi fushi dani na tuna da mahaifinku shiyasa na zauna a gida bazan iya zuwa airport na dawo daku ba"
jikinsu yayi sanyi, deen cikin sanyin muryanshi yace "Ammi ya akayi kika ganeni yau? bacin anko mukayi nida Abeed?"
murmushi tayi bayan ta sake shi tace "sabida nasan Deen ne kaɗai zai iya rike hanun kanwarshi su shigo tare"
rungume Abeed tayi tace "kada kuyi fushi dani kaji Abeed ɗina?"
ya turo baki yace "to Ammi ina jin yunwa"
a shagwaɓe yake magana, Ammi tace "to ai na aje muku abinci me daɗi"
hanunsu ta kama tana tsakiyansu suka jera zuwa dining, manyan manyan warmer's ne farare akan dining ɗin, tace "da kaina zanyi serving ƴaƴana"
duk suna kallonta Deen yace "thank you Ammi"
shiru tayi, ta juyar da kai ta yadda ba zasu ganta ba ta share hawaye, deen ya ganta amma yayi kamar bai gani ba, yace "Ammi tare dake zamuci ko?"
gyaɗa kai tayi 
yace "yawwa sabida munyi missing naki sosai, har Beed ya fara rashin lafiya"
kallon Beed tayi tace "da gaske?"
girgiza kai yayi "ni lafiyana kalau"
"wallahi Ammi karya ne sai kinga yadda ya dawo ranan kamar wanda yayi s..."
da sauri ya bige bakinshi dan wani lokaci Deen yanada suɓutan baki, kallonsu tayi su duka sannan taci gaba da serving nasu dan ta ɗago me yake shirin faɗa, wani lokacin dukansu basuda kunya basa tuna ita ɗin mamansu ce, itace ta haifesu, zee-zee tace "yaya kamar wanda yayi sesame kake son cewa? to ya fara wasan yara kenan?"
daka mata tsawa Abeed yayi ganin tana so ta janyo asirinshi ya tonu, tsit tayi bata kara koda motsi me kyau ba, Ammi ma shiru tayi ta fara cin abincin tana mamaki, Abeed ne ya fara tashi yana goge bakinshi da tissue yace "thank you Allah, thank you Ammi am full"
zai tafi tace "Beed?"
saida gabanshi ya faɗi dan yasan idan ta kirashi haka to akwai magana, yace "na'am"
idonta akan plate ɗin da take cin abinci tace "kaji tsoron Allah"
ya kai 5mins yana kallonta bata ɗago ba kuma bata daina cin abinci ba, deen ma yana kallonta, da kyar ya harhaɗa magana yace "Ammi me kuma nayi?"
tace "ba sai mutum yayi komai ba ake tuna mishi yaji tsoron Allah, ko nayi laifi ne dan na faɗi haka?"
yace "A,a bakiyi laifi ba"
ya kara minti biyu a wajen ya kasa yin komai, da kyar yaja kafa ya tafi, ɗakinsu da yake kamar a kasar turai ya shiga, akan gado ya faɗa ya janyo pillow me taushi ya rungume, lumshe ido yayi yana tuna maganan Ammi, juyi yayi akan gadon ya kwanta rub da ciki ya rufe ido
"kaji tsoron Allah"
wannan kalman yana da matukar tsayawa a rai duk wanda aka gaya mishi sai yaji wani abu a ranshi, koda bakayi komai ba bale ace ka aikata wani abin, a haka har deen ya shigo ɗakin bakinshi ɗauke da sallama, bai amsa ba kuma bai tashi ba, cire kayan jikinshi yayi yasa na zaman gida domin shan iska, kallon Beed yayi bai saba haka ba idan sun dawo, canja kaya yake ya ɗau mota ya fita, shine ba zai dawo ba sai dare lokacin bacci, daga nan idan yayi bacci kuma sai gobe da safe ya shirya domin zuwa aiki, amma wannan karon ya zama shiru, hawa gadon yayi yaja blanket shima bai mishi magana ba ya rufe ido, a hankali ya tashi ya cire kayan ya barsu a inda ya cire, riga armless yasa da wando three quarter, takalmi palms na zaman gida yasa sannan ya fita daga ɗakin, direct ɗakin ammi ya nufa, a bakin kofa ya tsaya yana knocking, babu amsa sai yayi expecting tana kasa ne, juyawa yayi zai tafi yaji shesheƙan kuka, a hankali ya tura kofan ya shiga, hankalinta da gangan jikinta duk ta mayar kan babban hoton da akayi enlargement ɗinshi, akasa a cikin glass, hawaye take yi tana shafa hoton, saide da alama bataso kowa yasan tana kukan, domin sai toshe baki take, kwalliyan dake fuskanta duk ya ɓaci, babban mutum ne sanye da babban riga da kuma hula wanda da gani kasan me tsada ne, yana  dariya ya ɗaga hannu alaman gaisuwa akayi mishi hoton, yana da matukar kyau kuma yana kama dasu Abeed domin kana ganinsu zaka san sun haɗa jini, da hakorin makka maƙale a hakorinshi hakan ya kara mishi kyau sosai saide shi baƙi ne saɓanin su farare, atake Abeed ya fara zufa duk da sanyin dake cikin ɗakin na tiles da Ac, idanunshi suka rikiɗe suka koma jajur kamar gawarshin wuta, jijiyoyin kanshi suka, baisan time ɗin daya karasa ciki ya fizge hoton ba, a firgice ta tashi tana share hawayen da sauri ta kalleshi tana kakalo murmushi tace "Abeed yaushe kazo?"
cikin wani irin murya da yake nuna tsananin fushin da yake ciki yace "ina zaki san na shigo kina nan kina kallon hoton wannan tsinannen mutumin"
cikin kuka tace "Abeed shi ɗin fa mahaifinka ne...."
da wani irin tsawan da yasa upstair da suke kai ya girgiza, yace "karki kara alakantani dashi, wannan ba babana bane"
gyaɗa kai tayi a tsorace ta matso wajenshi jikinta har yana rawa tace "to Abeed ba babanka bane bani hoton kaji ɗan albarka....??"
toshe kunnuwanta tayi lokacin da taji karan buga hoton da yayi da kasa, nan take glass ɗin dake jikin hoton ya tarwatse, baya tayi tana kallon Abeed da yake huci kamar zaki, idonshi akan hoton yasa kafa ya taka, take kafanshi ya tsage ya fara jini, da gudu tazo zata rike kafanshi da yake shirin kara taka glass ɗin yace "stay away from me!!!"
bata san time ɗin data ɓuya a bayan labule ba, kallon ashanan dake saman plate dake kusa da mirror yayi, da alama maganin sauro take kunnawa dashi, zuwa yayi ya ɗauko, idanunta a waje tace "Abeed me zakayi da Ashana...?"
kafin ta karasa maganan ya kyasta yasa akan hoton, kallon yadda kafanshi ke fidda jini yana ɓata tiles ɗin tayi a mugun firgice, ashanan ya kuma kyastawa yasa a jikin labulen ɗakin da suke da matukar tsayi da kyau, wuta ne ya fara ci a ɗakin cikin ihu tace "Deen!!! Deen!!! Deen!!! wuta, kazo wuta"
ganin zata fita a ɗakin yayi sauri ya fara rufe kofan, janyeshi ta fara a jikin kofan tana cewa "ka bari, Abeed ka bari"
ture ta yayi, ji kake tim ta faɗi kasa kusa da labulen da yake tsananin ci da wuta, rufe kofan yayi yana jin Deen yana kiran sunanshi da cewa ya buɗe kofan, makullin yasa a aljihun wandon jikinshi sannan ya jingina da jikin kofan, zee-zee da Deen har jini hanunsu yake wajen bubbuga kofan, saide babu ko alaman buɗewa a jikin kofan, deen cikin karayan zuciya yace "Abeed ka buɗe, Abeed ba zan iya rasaka ba, dan Allah ka buɗe"
jin bai buɗe ba, ya kalli zee-zee wacce ta haukace wajen buga kofan tana kiran sunan Ammi, zafin wutan yasa ammi ta fara tari tana kakkare fuskanta, duk da bai taɓa ta ba amma ufti da zafi yasa ta fara fita hayyacinta, yana tsaye yana kallonta shima yana jin tsananin zafi amma wutar da zuciyanshi take yi tafi wannan zafi, a hankali Deen yace "zee-zee kice mishi na ɗau wuƙa zan kashe kaina"
cikin kuka tace "to"
ɗaga murya tayi tace "ya Beed? ka buɗe ya Deen ya yiwa kanshi illa da wuƙa"
baisan time ɗin daya ciro makulli a aljihu ya fara buɗe kofan a rikice ba, kasa buɗewa yayi tsaban tsananin firgicin daya shiga, Ammi data fara ganin duhu duhu tana ganin haka taja da kyar taje bakin kofan, hanunta ta ɗaura akan nashi ta fara kokarin buɗe kofan, ganin baya buɗuwa yace "Ammi ki buɗemu deen zai mutu"
zee-zee kara ɗaga murya tayi tace "ya Deen zai mutu Ammi"
cikin kuka yace "Ammi? Deen ba zai mutu ya barni ba ko? zamu rayu tare dashi? saide na mutu na barshi ko Ammi na?"
cikin azaba ta gyaɗa mishi kai, fuskanta ya riko da tafukan hanunshi tana kallonshi shima yana kallonta yace "Ammi ki amsa min ba zai mutu ba ko?"
da kyar tace "eh"
murmushi yayi wanda ya bayyana tsananin kyawunshi, da kyar ta buɗe kofan, zee-zee tana ganinsu ta janyo Ammi, a daidai lokacin numfashin Ammi ya tsaya cak, idanunta suka rufe bakinta kuma ya buɗe, zee-zee ta waro manyan idanunta cikin tsananin tashin hankali tace "Ammiiiiiiiiiii"
Deen dake rungume da Abeed ya zaunar dashi a gefe yaje da gudu, yana tashin Ammi, bata buɗe ido ba, zee-zee dake zaune a kasa daram kan Ammi akan cinyarta, a hankali ta zame kan ammi ta kwantar da ita kasa, wajen Abeed taje idanunta a bushe tace "ka kashe ta?"
bai mata magana ba sai tashi da yayi yana shirin tafiya, hanunshi ta rike da karfi tace "ka kashe ta?"
fizge hanunshi yayi zai tafi ta tsaya a gabanshi tace "ka kasheta?"
juyawa yayi zai canja hanya yaji ta rike hanunshi, a fusace ya juyo zai mareta ta rike hanunshi cikin zafin nama, duka ta fara kaiwa kirjinshi tana kuka tace "bazan yafe maka ba, I hate you ya Abeed I hate you so much"
yana tsaye yana jinta tana duka kirjinshi harta gaji dan kanta, sai kuma ta faɗa kirjinshi ta fashe da kuka ta rungumeshi, a hankali yasa hanu yana shafa shafa bayanta da almanan lallashi, deen sai safa da marwa yake ga Ammi daya kwantar akan sofan, hanunshi rike da waya da alama ya kira doctor, jin ana knocking yaje da gudu ya buɗe kofan, doctor ne ya shigo da kayan aikinshi, deen yace "ta zauna cikin wuta shine ta suma"
da sauri ya karasa ya fara duddubata, allura ya fara yimata sannan yace "karka damu ufti na wutan ne yasa ta jikkata amma garin ya haka ya faru?"
kanshi kasa yace "gobara ne ya tashi a ɗakinta kafin muzo kuma yayi nisa"
yace "Allah sarki Allah ya bata lafiya"
Ameen, drip yasa mata kana yace "ka zauna kusa da ita zata iya farkawa a firgice domin wutan"
gyaɗa kai yayi, atake security's suka kashe wutan ɗakin, bayan doctor ya tafi suka zauna shiru, deen kusa da Ammi ya zuba mata ido, itama zee-zee tana kusa da deen, shi kuma Abeed yana tsaye a gefe ya jingina bayanshi da bango ya ɗaga kanshi sama, sun jima a haka kafin Ammi ta farfaɗo, kamar yadda Doctor ya faɗa haka ta tashi a firgice da kyar deen ya kwantar da ita kafin ta gane inda take, ganin komai ya lafa zee-zee tana murmushi haɗe da kuka tana kallon Ammi, a hankali ya juya zai tafi, deen yace "karka sake kaje kasha giya"
shiru yayi yabar wajen, Deen zaune yake kusa da Ammi amma hankalinshi akan Abeed da yake ɗaki, ya kalli zee-zee da tayi tagumi yace "zoki zauna kusa da ita"
zuwa tayi ta zauna a inda ya tashi, cikin natsuwa yake tafiya harya isa kofan ɗakinsu, tura kofan yayi ya shiga, hamdala yayi da bai ganshi kwance yana shan giya ba, faɗawa yayi kan sofa yayi shiru yana jiran fitowanshi daga toilet, kamar da wasa ya kai awa ɗaya a wajen baiga alaman fitowa ba, zuwa yayi wajen toilet ɗin ya fara knocking, ganin bai buɗe ba ya tura kofan ya shiga, toshe hanci yayi jin warin alcohol daya buga mishi hanci, ga kuma Abeed dake kwance a kasan tile yana bacci, gefenshi kwalaben giya masu tsada da yake siya ya ɓoye ba tareda deen ya sani ba, facemask ya ɗauko ya rufe fuskanshi kafin yazo ya ɗaga Abeed, cikin maye ya buɗe ido yace "Deen ka barni mana bacci fa nake bansha komai ba, tunda baka so ai na daina sha"
bai mishi magana ba ya cire mishi rigan jikinshi da kuma three quarter ya barshi boxer kawai, janshi yayi zuwa cikin bedroom ya kwantar dashi akan gado, cikin muryan maye da idanunshi wanda suka koma ciki ciki yace "deen kar kayi fushi dani kaji? you are my blood"
rufashi yayi da duvet kana ya tashi ya koma cikin toilet ɗin yana jinshi yana cewa "deen idan kayi fushi dani ba zanji daɗin rayuwa ba, na dena shan giya fa tunda jimawa, duk abinda baka so na daina"
shiga toilet ɗin yayi ya fara wanke rigan da wandon duka ya shanya a ciki, wanke toilet ɗin yayi gaba ɗaya ya fesa air freshener, atake warin giyan ya tafi sai kamshi, fita yayi ya kashe mishi wutan ɗakin ya tura kofan falo ya koma wajen Ammi wacce take cewa a cire mata drip zatayi fitsari, da kyar ya lallasheta ta hakura da fitsarin saida drip ɗin ya kare har bayan mangrib, duk yawan masu aikin gidan zee-zee da Deen ne sukayi girkin dare, sun jera komai akan dining har zuwa lokacin Ammi da Abeed suna bacci, shi giyan ne ya sashi bacci ita kuma allura da drip, sai bayan Isha ya fara murza ido, a hankali ya tashi yana salati tareda yin hamma, ya manta duk wani abinda ya faru ya kalli jikinshi yaga babu kaya sai boxer, da sauri ya kalli agogo yaga karfe 8 na dare, dafe kai yayi a hankali komai daya faru ya fara dawo mishi, cikin sanyin jiki da gajiya ya tashi akan gadon ya shiga toilet, wanka yayi me kyau yana kallon kayan da Deen ya wanke mishi, fitowa yayi yana ɗaure da towel bai damu ya shafa mai ba kawai yasa jallabiya coffee, duk sallan da ake binshi saida ya idar, deen ya shigo domin ya duba shi, ganin yana zaune akan sallaya yana addu'a ya juya ya koma, saida ya gama addu'a ya tashi ya fita, duka suna kan dining suna cin abinci saide fuskansu babu walwala, a hankali ya zauna kujeran dake facing na deen, saide Deen bai kalleshi Bama abincinsa kawai yake ci, itama zee-zee abinci take ci bata ko kalleshi ba, shima bai damu ba ya fara zuba nashi, ci ya fara wajen yayi shiru sai karan haɗuwan spoon da plate kawai akeji, Ammi wacce ta idar da salla da kyar ta tashi, already tayi wanka kafin tayi sallan, night cream nata me kamshi ta shafa sannan ta buɗe wardrobe ta ciro riga silk baƙi, da net net a jikin hanun da kuma wuyan, kasancewar tana jin zafi har yanzu ta buɗe kanta tareda cire ribbon ɗin data kame tulin gashinta  dashi, gashin ne ya zubo zuwa gadon bayanta, flat shoe tasa sannan ta fita daga ɗakin domin yunwa take ji sosai kamar taci babu, so take ko tea ta haɗa tasha ko zataji sauƙi, da sauri ta koma da baya lokacin data gansu duka a zaune suna dinner, komawa tayi yace "Ammi"
tsayawa tayi domin bata san waye ya kirata cikinsu ba, daga deen har zee zee suka kalleshi, yace "Ammi kizo muci abinci tare"
sai yanzu ta fahimci Abeed ne domin kwai ta gani akan abincinshi, a hankali ta karasa ta zauna, abincin dake gabanshi ya fara bata, taunawa take a hankali tana kallonshi, yace "na baki ruwa?"
gyaɗa kai tayi, ya tsiyaya ruwa a glass cup ya kai bakinta, sha tayi tace "na gode Abeed"
bai amsa mata ba yaci gaba da bata harta koshi.