DA AURE NAH: Labarin Cin Amana Mai Muni, Fita Ta Biyar

DA AURE NAH: Labarin Cin Amana Mai Muni, Fita Ta Biyar
DA AURE NAH
                  
*NA*
          *HAUWA'U SALISU**
 Page 5
Juya takardai naitayi a hannuna na gaxa budeta sai nayi kamar xan bude sai naji wata matsiyar karaya saina fasa Karshe dai na hankada katifata na jefata na kwanta nai lub 
Baqaramin daurewa nayi ba danaji kiran da  Mama kemunba na tattaro duk wata jarumta nasaka nafita gun mamarKallo daya taimun tafara jeromin tambayoyi dama baki lafiya kikai shiru 
AutaBan hanaki xama da ciwo ba ba tare da kinsanar mun ba 
Yaushe xaki daina wannan sokoncinne wai to bari yayanku yashigo yakaiki chemist adubaki Nidai da ido nabita Dan nasan ko munje bai isa yagano ciwonaba inba fada masa nayi ba 
Magana nake maki Auta mike damunki ne kaina kemun ciwo mama nasha magani a makaranta To kici abinci ki je ki kwanta Allah ya sawaqe dako naso in aikeki gidansu Hajiya Abida ki kaimun kudin Adashina  idan ba gixo kunne na kemunba gidansu Habeeb kenan wajen mamansu kenan ai koda gaske ban lafiya ba abunda xai hanani rarrafawa kodan naga Habeeb Dan haka nai gaggawan janyo hijab dina dake kan tagar Mama nace kawo na miqa mata ai kusane mama cikin sa a kuwa ta miqomin kudin na karba na fita 
Tun daga kofar gidanmu nake hangen kofar gidansu Habeeb naga koxan gansa inda yasaba xama amma babushi ba alamarsa Sosai naji ba dadi a raina harnaji daman ban anso saqonba na kwanta jinyar xuciyata a haka har nashige gidan nai sallama Qanwarsa Fatima ta ansamun natambayeta mamarsu tace tana ciki na jira taimata magana Haka na xauna inata raba idanu ina qarema gidan kallo na gadai dakin mamarsu da sashen Babansu sai wani bangare danake tunanin ko shine bangarensu Habeeb Dan yana da Yayansa guda Daya Suleman duk da niban sanshiba wai soja ne yana can gun aikinsa Inacan inata tunani naji Muryan Mamarsu namun maraba banda abunki Huwailat basaiki shiga daga cikiba in itabatai hankalin cemaki kishigaba Murmusawa nayi bakomi Hajiya dama mamane taban sako nakawo namika mata kudin ta ansa ta kirga tace kigaidamun ita sosai nace xataji sai anjima
Nafito xuciyata fal takaici banko kallon gabana naji nayi karo da mutum gaba daya naji na afka masa munyi baya munfada ma bango ina kwance kan kirjinsa yasaka duka hannayensa biyu yaxagaye mun kugu dasu 
Matsanan ciyar kunya tahana nadago fuskana naga waye wannan sannan miyasaka ya qisakina koya tureni nafadi dan nicena fito ban kallon gabana natafi duniyar tunanin Mutumin da keson Qawata baniba 
Sharr hawaye suka xubo fuskana abunda yaxaja dagomin Fuska dayayi waxan gani Habeeb ne Ashe yakalleni sosai ya girgixa kai yasaka hannu yasharemun hawayena kidinga kallon gabanki idan kina tafiya Yajanyeni daga jikinsa ya shige cikin gidan  Ya salam so cutane jinai tamkar karda yadaina mun magana Ashe haka yakeda murya mai sanyi tab Zainab ta cuceni cikin damuwa na taka na fita daga gidan xuciya cunkushe da abubuwa da dama Allah ya taimakeni ba kowa tsakar gidan na shige dakina nadasa sabon kuka tamkar wadda akaima shegen duka har na tsawon lokaci kana na dangana najawo later nan nakasa budewa na maidataWasa wasa nashiga damuwa ko a makaranta inna hadudasu Hafsat ba kalan tambayan daba samun amsar da yace banda lafiya Zainab kuwa jinake tamkar na yanke duk wata alaqa da ita Dan itace taimun Katanga da Habeeb aganina dabata xan iya janyo hankalinsa guna yanxufa Dan haka nake mata shaqe shaqe danma yar iskai ko a jikinta take nunamin bata damuba da duk abinda nake mata Kamar yau nafito da niyyar xuwa gidansu Hafsat kawai na hango Habeeb dawata yarinya sunata dariya cikin tsananin kaduwa na qara matsawa inga wace mai sa arce haka tasamu Habeeb yaketa nishadi tare da ita abaxata naga Zainab ce Kawata tashin hankali da gaske Habeeb da Zainab soyayya suke yaxama dole nayi bankwana da sonka Habeeb nabarma Zainab kai koda hakan xaisaka narasa farin cikina
 Cikin dauriya na qarasa nasakarma Zainab yake Dan ba murmushi bane nace yan mata daga ina tai dariya tace gunki xani sai nahadu da Yallabai ancemun jiya yaje gida bannan ina gidansu Aunty salma time din Share maganai nayi Dan batada amfani guna nikam gidansu Hafsat xani ina fada ina barin wajen tare da mamakin Habeeb ko kallo ban ishe shi ba 
Sanin batsayawa xanba yasa Zainab biyoni harda Dan gudunta ina juyawa naga Habeeb bayanta kawai yake kallo murmushi kwance a fuskansa 
Cikin dakewa nace kefa banxace kuna magana xaki tafi kibarsa 
Dariya tayi aiyace xaixo anjima gida ya
sameni ninai daman ban mata maganaba Ahakadai muka qarasa gidansu Hafsat ita kadai keta xubarta nikam ciwon kaima labarin kesani wai Habeeb mutumin kirki ne yana da hankali ga natsuwa kai nashigesu ni Huwailat Acanma haka sukaita labarinsu bana fahimta har muka fito kowa ya kama gabansa nikam na yi danasanin fitowata yafi dubu a ranai Jarabawanmu ta fito ta J S C E naci boarding school dake hanyar abuja wato madallah baqamin murna nayi ba 
Sai dai su yah Abba sunce ba wannan maganar nasa kuka na kama kafar mama Dan Allah kinga yanxu na girma aji hudu xanifa bakamar wancan karan daxani daya ba Baba dake gefe yace kiyi shiru indai makarantar kwanace kinje kingama Auta
Dadi naji sosai Dan kobanxa xan daina ganin Habeeb da Zainab Dan haka baki alaikum naita shirye shiryen tafiyana banfadama kowa a cikin kawayena ba 
Ranar daxan tafi na je kofar gidansu Habeeb Dan masa kallon bankwana kallon karshe inafatan sanda xan dawo na manta dashi a rayuwata kwata kwata Yana zaune yanata karanta wata later yana murmushi nasan ta zainab cema yake karantawa ina hangosa ya dauko Biro shima yafara rubuta wata Cikin xubar hawaye nabar gun nakoma gida na iske yah Abba najirana mutafi Saboda abunda nagani yasa nafashe da kuka sosai na rumgume Mama ina kuka na gaske Dan xuciyata ciwo take mun sosai da qal mama ta lallasheni na bi yah Abba muka tafi Har makaranta yakaini yaban kudi yaimun bankwana yatafi gida 
Hostel dinda aka kaini nabi da kallo kamar yanda yan hostel din suka Bini da kallo  Allah sarki Zainab da Hafsat kuyi hakuri na karya alqawarinmu nabarku natafi wata makarantar Dan samun lafiya ga xuciyata dataki Zainab 
Sai Hawaye Sharr baxata naji sunsa ihu new new tab harma kin daina da haka muka fara muma nan inji wata dake kusa dani kallonsu kawai nayi na lafe kan katifa ta 
A haka dai naci gaba da rayuwa a makarantar ba laifi inaganewa sannan nayi sabbin qawaye Asmau da Aisha sai dai bantaba mantawa da tunanin Habeeb ba a kowace rana saina tuna dashi sosai Samarun zariya bayan tafiyar Huwailat makaranta 
Yau sati  biyu kenan baiga ta wuceba bayan yaga ankoma makaranta yasan kuma bata wasa da karatunta ko makara batayi to mike faruwane da ita karfa ace dammm gabansa ya fadi hakan baxai faruba insha Allah Nasan Allah xai mallakamun ita taxama uwa ga yarana mata gareni suruka ga Hajiyanmu kawai yasaki murmushi xai bincika yaji abunda yake hanata fitowa da xuwa makaranta yauba sai gobeba insha AllahAranai qagara yayi dare yayi yaje gidansu  Zainab danjin abunda yake buqata shiyasan wadannan kwanakin Sam baida walwala sannan baida kuxari damuwa na shinfide a xuciyarsa wadda harta fara bayyana kanta ba shakka ba qaramin so yake mataba yarinyai nan Dare nayi yaje gidansu Zainab akafada masa batanan taje Hutu garinsu Mamanta rai bace yadawo gida yarasa abunda ke masa dadi Washe gari yana xaune yana Dan kullum din yaga Hafsat tafito daga gidansu Huwailat kamar hawayema take indai idansa ba gixo yake masaba cikin karfin hali yanufeta yajefa mata tambayar ina qawaiki kwana da yawa bana ganinta Rushewa da kuka Hafsat tayi tasake riqe wata later gam dake hannunta tana girgixa kanta Xufa ta yanko masa ta ko ina shin miya faru ne Hafsat ina Huwailat din bata lafiya ne kinyi shiru ki ban amsa. 
Takarda ta miqa masa tayi tafiyarta idan ya kula ma kamar hararansa take Hafsat din bai
bi takaiba burinsa yaga meke cikin takardai dayasaka Hafsat kuka To masu karatu miye a cikin takar dai Shin Huwailat ta manta da Habeeb kuwa Zainab da gaske soyayya ce suke da Habeeb Miya saka Hafsat kuka a gidansu Huwailat. 
Ku biyo ni Haupha dan jin amsarku.....