WATA UNGUWA: Fita Ta Tara

Hafsar ta fito tana zumɓura baki alamar ba ta son aiken, dai-dai ƙofar fita ta ci karo da 'yar Garbe kanuri shi ma mazaunin gidan hayar ne, ba ta yi wata-wata ba ta mintsini yarinyar ta fice da gudu tana dariya. A wajen ma kafin ta yi nisa ta tarar da wata yarinya za ta je markaɗe ta saka hannu ta ture robar ta zuba a guje tana dariya. Nan ta bar yarinyar na kuka tana faɗar "Allah zai saka mun, kuma wallahi sai ma na je innarku ta biya ni, ba dai kuna siyar da kayan miya ba?."

WATA UNGUWA: Fita Ta Tara

p9

 

BABI NA TARA

 

Tsaye take a ƙofar banɗaki sai jijjiga ƙafa take tana kaɗa jiki da alama a matse take sosai amma tana jiran na ciki ya fito ne.

Can bayan kamar mintuna biyu ta fara magana a ƙagauce "Habah Iyan Hazze! Don Allah ka yi sauri ka huto in har ba burinka ka ga marata ya yi bindiga ba ne."

Daga cikin banɗakin Iyan ta ƙyaro zance "Gaskiya kina da damuwa Jilde, yanzu uzurin nawa zan datse don kawai ki shigo?"

 

"Wannan dai siga haƙƙi ne ko hanzin cikinka za ka kasayar ya ci a ce ka gama. Wallahi nan da minti ɗaya in ba ka huto ba sigowa zan yi." Jilde ta faɗa a kufule, cikin hausarta irin ta su ta Fulani.

Cikin gatse Iyan Hajje ta ce "Don Allah shigo abinki Jilde, ai dukkanmu mata ne kowa bisa ga uzurinsa."

Abin da Iyan ba ta sani ba Jilde bafulatana ba ta san gatse ba, ga shi a matse take kawai sai faɗawa ta yi ciki faram-faram ta yi uzurin da ya kai ta, ba tare da ta kalli sashen da Iyan take ba. Kusan a tare suka fito, Iya na ta mamakin Jilde duk shekarunta a ce ba ta san gatse ba?

Ko da yake a zahiri ba wai ta damu da yanda Jilden ta tarar da ita ciki ba ne, domin ita a nata ƙaramin tunanin hakan ba komai ba ne tun da yake dukkansu mata ne, kuma ma abu ga gidan haya shi ya sa ba ta yi mata magana akan hakan ba.

Tana fitowa ta nufi ƙofar ɗakinta inda ta kasa sana'arta ta kayan miya, yara maza biyu da mace ɗaya ta tarar suna jiranta a gun tana ƙarasowa ɗayan yaron ya ce "Iya a ba ni tumatur da salak na hamsin."

Ba ta tamka shi ba ta ɗaga hannu tare da zaro wata cukurkuɗaɗɗiyar leda a saman rufin rumfar ta saka masa kayan a ciki sannan ta miƙa masa tare da karɓar kuɗin.

Ɗayan yaron ma haka ta sallame shi har a lokacin 'yar macen nan ba ta ce komai ba.

"Sarauniyar miskilanci me za a ba ki?" Iya ta tambaya.

Da ƙyar ta iya buɗe baki ta yi magana kamar mai ciwon baki "Attarugu da yakuwa, sai albasa da Kabewa duka na ɗari biyu."

Karɓar kuɗin ta yi ta saka mata sannan ta bar gidan, ita kuwa Iya ta nufi ɗakinta tana faɗar "Ke! ke!! Hafsa, ban ce ki je gidan Baba mai ice ki siyo mun kai ɗaya ba ne? Me kike jira ga shi an kusa azahar ba mu ɗora komai ba."

Hafsar ta fito tana zumɓura baki alamar ba ta son aiken, dai-dai ƙofar fita ta ci karo da 'yar Garbe kanuri shi ma mazaunin gidan hayar ne, ba ta yi wata-wata ba ta mintsini yarinyar ta fice da gudu tana dariya. A wajen ma kafin ta yi nisa ta tarar da wata yarinya za ta je markaɗe ta saka hannu ta ture robar ta zuba a guje tana dariya.

Nan ta bar yarinyar na kuka tana faɗar "Allah zai saka mun, kuma wallahi sai ma na je innarku ta biya ni, ba dai kuna siyar da kayan miya ba?."

Daga can cikin gidan kuwa Fa'ee ce ta kammala wankinta, ta zo za ta yi shanya sai ta tarar da kayan Shamsiyya a kan igiyar, ba ta cewa kowa ƙala ba, ta saka hannu ta ture tufafin Shamsiyyar a gefe alhali tana sane da cewa ba su gama bushewa ba, kawai ta hau shanya nata tana hura hanci irin ga isasshiyar nan.

Fitowar Shamsiyya daga ɗaki kenan idonta ya faɗa kan wannan ɗanyen aikin da Fa'ee ke yi mata.

Ba ba ta lokaci ta yi kukan kura tana zuwa ta saka hannu ta janyo kayan Fa'ee ta watsar da su a tsakiyar gidan.

Ga ma gidan ko'ina magudanar ruwan ƙazanta ne, kashin Kaji da na Dabbobi ba abin da babu na nau'in ƙazanta a tsakar gidan.

Kowacce ta tashi iyakaci ta share ɗakinta da iya ƙofar ɗakinta don kada a more ta.

Fa'ee na ganin haka ita ma ta wancakalar da kayan Shamsiyya ƙasa ta tattaka a cikin ruwan kwatamin da suka yi ɗan ƙwarya-ƙwaryan kuddudufi a wurin tana faɗar "An faɗa miki an fi ni iya rigima ne? Masifa da bala'i ko wanne nau'i kike ji gidan danjar kika tarar yarinya."

Ita ma ta yo kanta a zafafe tana cewa "Ba ke kika fara tsokana ta ba? Da wane dalili za ki janye min kaya ko igiyar ta gadon tsohonki ce?"

"Allah ya sa ba ni kaɗai ba ce balle a mun gori, ke ma dai gidan ba na ubanki ba ne, gidan haya gidan ka zo na zo, kowa da ƙaddarar da ta janyo shi zuwa nan." Cewar Fa'ee a kufule.

A haka suka ci gaba da cacar baki tamkar kaji har abun ya kai su da gwada ƙwanji domin har dambe sai da suka yi.

Da fari ba wanda ya yi yunƙurin dakatar da su duk da cewa kuwa gida ne na jama'a, gida mai ɗauke da ɗakunan sama da goma, ai ba a ce an rasa mai tsawatarwa ba. Sai yanzu da suka ka ga ana neman yin 'haihuwar guzuma 'ya kwance uwa kwance' sa'annan iyayen 'yan'matan suka raba hargitsin kowa ta ja 'yarta suka yi sashensu.

Washegarin ranar da misalin ƙarfe bakwai na safiya Mahee ta fito daga gidansu tana ciccin magani, kallo ɗaya za ka mata ka tabbatar yanayin fitar dole ne ya kamata domin hatta baccin dake idonta bai ƙaurace ba, sai lumsashe ido take tamkar wacce ta sha abun maye.

Duk da cewa tsakanin gidansu da gidan Bargaja akwai tazara domin kusan tafiyar mintuna goma ce ko fin haka a ƙafa, hakan bai hana mata maida hankali ga nufar inda aka aike ta ba, domin ta kwana da sanin duk gidan da za ta je da safen nan yana da wahala ta samu kayan miya in har ba 11am ta yi ba, su kaɗai ne ake iya samun ragowar na jiya a gunsu.

Ko da ta isa gidan fiye da rabin ƙofofin ɗakunan gidan a rufe suke, kasancewar har zuwa lokacin ana cikin yanayi sanyi ne.

Ƙofar iya na ɗaya daga cikin ƙofofin da ke rufe, don haka ta ja ta tsaya cak tana tunanin mafita.

Fa'ee ce ta turo ƙyauren ƙofarsu ta fito, sai ta ci karo da Maheerah a tsaye "A'ah! Mahee ce da safen nan?" Ta faɗa da murmushi a fuskarta tana matsowa wurinta.

Ita ma martanin murmushin ta mayar mata kafin ta ce "Wallahi kuwa kin ganni wai na zo siyen attarugu da albasa kuma na ga Iya bata tashi ba."

"Ah! Bari na tayar miki da ita, yanzu haka ma ina ji ta tashi ƙofar ce kawai ba su buɗe ba." Ta faɗa tare da ƙarasawa ta fara ƙwanƙwasa ƙyauren ƙofar da ya kasance na langa-langa.

"Ga ni nan fitowa waye?" Iya ta Tambaya daga ciki.

"Fa'ee ce, za a siyi kayan miya ne." Ta ba ta amsa. Cikin hanzari Iya ta miƙe da kuzari ta nufo ƙofar ɗakin tare da buɗewa yayin da Fa'ee ta wuce zuwa sabgar gabanta.

Sandarewa Mahee ta yi kamar an dasa ta a gun tsabar mamaki da ya kamata.

Ba komai ya ba ta mamaki ba, kamar ganin iya na hankaɗo yagaggen labulen ta fito, sai ga ƴaƴanta manyan budare sun fito daga ciki tare da wani ƙaramin yaro. Ba ta gama mamaki ba ta ga wani matashin saurayi da a ƙiyasi zai kai shekara 16 ya fito daga ciki shi ma.

"Me za a ba ki?" Iya ta dawo da ita daga tafkin mamakin da ta faɗa.

"Attarugu da albasa na Saba'in." Ta faɗa ba tare da ta janye dubanta daga ƙofar ba.

"Farida duba mun leda baƙa ƙarama a cikin ɗakin nan." Cewar Iya yayin da take ƙoƙarin kasa kayan miyar.

Wacce aka ambaci sunanta ta hankaɗe labulen da ya yi wa ɗakin sutura tare da shiga ciki, kuma ta bar shi a ɗage don ta ga haske.

A nan fa Mahee ta ƙara cika da tsananin mamaki ganin yanda ɗakin yake cunkushe da kaya gami da mutane. Ɗakin falle ɗaya ne an saka gadaje biyu a ciki, filin da ya rage bai wuce na kwanciyar mutum biyu ba.

A kan ɗayan gadon kwandunan tumatur da sauran kayan miya ne daga gefe sun mamaye rabin gadon, rabin filin gadon kuwa wasu yara ne kwance a kai sun lulluɓe sai shaƙar baccinsu su ke hankalinsu kwance tamkar tsumma a randa.

A kan ɗayan gadon kuwa tsummokara ne ga su nan birjik da wasu madaidaitan akwatin ƙarfe ƙwaya uku a kai. Daga gefe ɗaya na gadon, mijin Iya ne a kwance.

Daga can tsakankanin gadajen biyu wasu manyan bakkuna(Ghana must go) ne cike da tsummokara, ƙasan ɗakin kuwa ko albarkacin ledar ƙasa bai samu ba, ƙura ce duk ta bice wuri, har in ka taka ana iya ganin zanen ƙafarka ya bayyana kamar ba siminti a gun.

Mahee dai na nan tsaye mamaki ya gama kashe ta, ta jiyo muryar 'yar daga ciki "Iya ban ga ledar ba fa."

Babansu ne ya taso yana faɗar "Anyah! Ki duba kan gadon nan da kyau, inda take ajiye tarkacen sana'arta." Daga haka yayo waje.

Zuwa can sai ga ta da ledar da ta nemo da ƙyar ta miƙawa Iya.

Iya ta kwashe kashin kayan da ta yi ta zubawa Mahee a leda tare da karɓar kuɗinta.

Haka Mahee ta ja ƙafafunta ta fice daga gidan tana mamakin irin wannan rayuwa, yanzu duk yawan mutanen nan a ce a cikin ɗakin nan ɗaya suka kwana? Kusan rai takwas fa. Wannan da a lokacin zafi ne Allah ne kaɗai zai kare su daga cutar sanƙarau. Mutanen gidan sam ba su da ilimin addini balle su san yadda ya kamata su tsara rayuwa kan tafarki madaidaici, kowa da bikin zuciyarsa.

A ranta take faɗar 'inda ranka ka sha kallo.'

Da Mahee ta san me zai faru a gidan bayan ficewar ta da awa biyu da wataƙila ta dawo don kashe kwarkwatar ido. Duk da ita ba renonsu Iya mai bakin Aku ba ce amma za ta so gani.

Domin kuwa wani zazzafan rikici ne ya ɓarke tsakanin maman Fa'ee da mijin Atika, wanda har ta kai su ga gwabzawa.

Sai ji kake tim-tim tau-tau ana kai naushi da tiƙa ba ƙaƙƙautawa yayin da Fa'ee ta shigarwa mamanta faɗan, Atika kuma ta shigarwa mijinta. Ga Atikar wata irin rusheshiya ce, da bazarta ne mijin ke rawa, shi ya sa yake takaro rigima ba li-ba-la don kawai ya san tana tare masa.

Yanzu ma abinda ya faru kenan ko da Atika ta ƙyalla ido ta ga a na ta makar tsamurarren mijinta sai ta shigo faɗan da ƙarfinta.

Tana zuwa ba ta yi wata-wata ba ta janyo maman Fa'ee ta nanata da ƙasa tare da hawa ruwan cikinta ta taushe ta tana kai mata bugu ta ko'ina.

A take idon maman Fa'ee ya raina fata, don kuwa duk masifarta da zafin namanta yau ta tabbatar da ta taro August. Tuni idanunta suka fito tulu-tulu kamar na Mujiya. Numfashinta ne ya fara gagararta sai yunƙurin kubce mata yake ta na fizgo shi da ƙyar, ji take kamar kayan cikinta za su yi waje.

Fa'ee kuwa ganin ana shirin aika mahaifiyarta ƙiyama ta shiga neman abun duka, duk da ta san ba ta da ƙarfi

n da za ta tari Atika amma ta yanke a ranta cewa ba shakka yau sai dai a yi mutuwar kasko, amma ba za ta juri kallo ba.