MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutun Da Aljan, Fita Ta Ta Goma
Bata gama rufe bakinta ba taji anyi wata tsawa mai tafe da haske kamar walƙiya, hakan yasa ta komi ya koma muhallinsa ta ganta tsaye kofar ɗakinsu , bata jira komi ba tai wuf ta koma cikin ɗakin tana hamdala ga Allah. Can cikin barci Huraira ke jin ana motsi a tsakar gidan anata kaiwa da komowa karshe taji ana zuba ruwa ana kamar karatu ƙasa-ƙasa, wuf ta miƙe zaune ko shakka babu uwar kilbibin can ce ke mata karakaina tsakar gida cikin dare zata je ta fara karatun Alkur'ani mai hana mutane barci ko , Bata bata lokaci ba ta nufi tsakar gidan ɗauke da fitilarta mai haske .
*Shafi na Goma*
"Bilkisu ya akai kwana biyu baki buɗe wayarba sai yau ? Kin san yanda na shiga cikin damuwa da tashin hankali na rashin jin halin da kike ciki ainun, kaɗan ya hana ina dawo gida inga halin da kike ciki ,,
Tunda ya fara magana ta ke jin tamkar yafi kowa iya jero kalaman natsuwa da hankali .
Hakan yasa ta ji jikinta yayi wani sanyi ƙalau dan har cikin gaɓɓai take jin amon muryarsa .
"Bilkisu kina jina ina magana amma kikai shiru kika ƙyale ni ko ?
Kamar yana gabanta haka ta sunne kanta ƙasa alamar jin kunya.
Yana sane da ta ji kunyar maganarsa abin da ke ƙara birgesa da ita kenan kunyarta na ƙara masa ƙaimi gun sonta ainun.
Cike da natsuwa da kwanciyar hankali suka dinga firan su wanda ita ba komi take iya bashi amsa ba sai dai tayi murmushi ko dariya.
A fusace ya faɗa ɗakin bakinsa ɗauke da sallama.
Huraira dake kwance kan gadonta duk ta bi tayi wuri-wuri domin sai taga kamar hannun aljanun ne zai sake ɗaukarta, dan haka take ta mui-mui da baki ala dole ita addu'a take yi.
Tana ganin malam ta saki ajiyar zuciya tana jin yanzu babu aljanin da ya isa yazo gareta ga Malam ya shigo, dan haka miƙe tsaye bakinta ɗauke da yaƙe tace...
"Yauwa Malam zo nan ka zauna muyi labari kwana biyu sam baka samun damar zaunawa kana labari da ni"
Tsaki ya ja ya dubeta rai a ɓace yace.......
"Huraira shin ina kike zuwa idan na tafi kasuwa ?
Zaro idanuwa waje tayi tana jin wata tambayar rainin azziki da Malam ke mata kai tsaye .
Abin ka da mafaɗaciya sai ta fara halin nata ai .
"Yo Malam ai ba yau nasan da man ɗaukar susun ma'ahu kaimun a cikin gidan nan ba, tsabar kaga na kawo idanu na zuba cikin gidan nan yanzu yasa kake neman kaini ƙarshe to wallahi ahir ɗin mutum ban da kawai ni ɗin jarumar mace ce Allah ya baka ma ai da baka iske ko gawa taba yanda yaƙi ya kacame tsakanina da Aljanu can cikin dawa "
Iyakar ɓacin rai da hassala zuciyar Malam ta gama ɓaci da hassala amma sai ya ɗaure karo na biyu ya sake jefa mata tambayar ina taje yau ?
Ai sai takaici yasa Huraira fashewa da kuka iyakar karfinta abin da yasa yaran ƙanana zuwa ɗakin Innar tasu .
Malam na ganin ta saka kukan rainin hankalin nata da ta saba yi duk sanda tai wani iya shegen sai ya girgiza kansa ya ja hannun yaran ya nufi ɗakinsa da su yana tur da halin mahaifiyarsu Huraira.
Duk budirinmu da ake ɗakin Innar tasu ita sam bata san anayi ba domin Nasir ya kashe ta da irin soyayyar sa mai sawa ka manta kowa da komi ka daina sauraran karatun kowa sai na shi
Sun jima suna wayar sannan sukai bankwana ta miƙe tsaye ta yi shirin barci ta haye gadon su zuciyarta cike da ainufin farin ciki da kewar muryan Nasir ɗin .
Can tsakiyar dare Bilkisu taji muryan Innar tasu na kwaɗa mata kira kamar tana cikin tashin hankali yanayin amon muryarta.
Cikin sauri ta miƙe zumbur ta nufi ɗakin Innar tasu jikinta har rawa yake dan azabar fargaban abin da ke faruwa da Innar cikin daren nan .
Sai dai tana fitowa daga cikin ɗakin nasu ta ga baya ɗaya gidan nasu ya juye ya koma kamar wata ƙatuwar asibitin mahaukata da tsaffi masu kalan Aljanu suna kwance wasu na zaune wasu kuma an masu allura wasu kuma ƙarin ruwa ne manne a jikin su .
Kowa har kai gabansa yake babu wanda ya damu da wani balle ya tanka masa, haka ta fara wuce su tana ganin kamanninsu kala daban-daban abin tsoro kuma .
Tana cikin tafiya taci karo da wani abu ƙasa, dubawar da zata yine tai ido huɗu da Innar tasu kwance ƙasa sai birgima take ita kaɗai babu kowa gunta ga fuskarta duk ta yamutse tayi wani kwab-kwab da ita kamar zata zube ƙasa.
Cikin ɗaga murya ta ce "Sannu Innarmu me ya kawoki nan ? Baki lafiya kema ? Inane nan ɗin?
Ita dai Inna tunda Bilkisu ta kamota sai ta yi tsit ta rufe idanuwanta kamar wadda barci ya kwashe mai nauyi .
Bilkisu baiwar Allah sai ta fara yunƙurin tada ta su koma gida dan ita tasan ba cikin gidansu suke ba.
Tana cikin kiran sunan Innar taga ta kife kasa fuskarta na kallan ƙasa bayanta ne ke kallon sama, cikin tausayin Innar ta kamota da nufin ta joyuta baya daga kwanciyar rubda cikin da tayi .
Tana kamota sai taji ta sulbe kamar wata sululu da ƙyal ta samu ta jiyota, ai kuwa tai saurin sakinta domin gaba ɗaya babu komi sai ramin fuskar da ramin ƴan cikinta babu komi gun .
Sai dai tayi-tayi ta saketa amma abin ya gagara duk da cewa itace ta riƙe Innar tasu amma kuma ta sake ta sakinne ya ƙi yiyuwa .wata irin dariya taji ana gaggaɓa mata mai neman kashe dodon kunnuwa, wadda ta rasa daga inda dariyar take fitowa ma kwata-kwata.
Ɗagowa tayi ta kalli sauran tsoffin dake kwance gun, sai ta gansu sunata wata irin birgima suna juyi wani jan ruwa mai kama da koko na fita daga jikinsu , gaba ɗaya sai suka mirgina suka dunƙule waje guda suka cure suka zama wani dunƙulen abu yayi wuf ya faɗa cikin ramin jikin Innar tasu, faruwar haka ke da wuya taga fuskar Innar tasu na canzawa lokaci zuwa lokaci .
Ji tayi bakinta ya fara karanto addu'ar neman tsari daga abin tsoro wato ....
"Hasbinallahu wani'imalwakim,,
Bata gama rufe bakinta ba taji anyi wata tsawa mai tafe da haske kamar walƙiya, hakan yasa ta komi ya koma muhallinsa ta ganta tsaye kofar ɗakinsu , bata jira komi ba tai wuf ta koma cikin ɗakin tana hamdala ga Allah.
Can cikin barci Huraira ke jin ana motsi a tsakar gidan anata kaiwa da komowa karshe taji ana zuba ruwa ana kamar karatu ƙasa-ƙasa, wuf ta miƙe zaune ko shakka babu uwar kilbibin can ce ke mata karakaina tsakar gida cikin dare zata je ta fara karatun Alkur'ani mai hana mutane barci ko ,
Bata bata lokaci ba ta nufi tsakar gidan ɗauke da fitilarta mai haske .
Tana fitowa ta hango ta tsugunne wajen magudadarsu ta juya baya , cike da faɗa ta sunkuci butar dake aje cike da ruwa ta je ta juye su jikinta tana cewa....
"Allah kin gama hanani barci da karatun gulmarki ƴan nan "
Ita dai bata jiyuba bata kuma motsaba , hakan yasa Huraira kwaɗa mata kira ta dalleta da fitilar hannunta .
Wayyo Malam!
Komi Inna ta gani take kiran Malam?
Taku ce Haupha!!!!
managarciya