HAƊIN ALLAH: Labarun Soyayya Da Cin Amana Mai Muni, Fita 29

HAƊIN ALLAH: Labarun Soyayya Da Cin Amana Mai Muni, Fita 29

HAƊIN ALLAH

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 

       


           Page 29

 *Ban san da wane baki ba zan gode ma masoyana ba, masu kirana da masu turomin saƙo sai dai ince Allah Ya bar ƙauna da zumunci ina godiya kan alherinku gare ni sosai* 

Suna cikin tafiya, sai Barista Alawiyya ta hango wata baƙar mota na binsu a baya, murmushi tai kawai ta saki kan motarta, maimakon ta koma gidan da suka kwana sai ta ɗauki hanyar gidan gonar  Babanta dake hanyar Zariya cikin ɗan dajin dake tsakanin Kaduna da Zariya yake, ashe shima Daddy yaga motar don haka duk inda Alawiyya tai ita yake bi, ya yi mamakin abin da yasa ta kaisu gidan dake cikin jaji amma sai ya bari su isa sai ya tambaye ta.

Sai kuma ya ga wata jar mota irin waccan baƙar na bin bayan waccan baƙar motar, hakan yasa ya kasa jurewa ya kira wayar Alawiyya.

"Alawiyya ta ya za ki kaimu dawa bayan kina ganin mota har biyu na bibiyarmu? Kamar fa kin yi wauta a lamarin nan, saboda kin ga Hausawa na cewa Sarkin yawa yafi Sarkin ƙarfi mota har biyu wa yasan abin dake cikin su?"

Sai da ta furzar da numfashi sannan tace cikin muryar ko'in kula, "Kar ka damu Daddy mota guda tawa ce, gudar ce nake buƙatar ta zama tawa ita ma, domin na jima ina mafarkin samunta sai Yau na ganta." Ta kashe wayar tana wani murmushi. 
Dr. Faisal ya ƙara gyara zama ya haɗiye miyan bakinsa da ƙyar ya ce a ransa, "Anya kuwa wannan Alawiyya ce wadda na sani? Wadda mutane suke kira shegiya ɗiyar shegiya tashin Lagos? Anya kuwa ita ce wadda wajen kwana ya gagara shekarun baya da suka wuce? Tabbas idan ita ce to an sauya mata halaye kaso tamanin da tara na halayenta sun fece." Ya sake kallonta abin mamaki waƙa ta kunna ta shiga girgiza kanta tana bin waƙar ko alama babu sauran ɓacin rai a kan fuskarta.

Kasancewar gidan ba kowa cikinsa, tunda babu wani abin amfani ciki yasa sai da ta fito da kanta ta buɗe gidan, ta ja gate ɗin gidan ya buɗe Daddy ya shige a lokacin ne baƙar motar ta juya da gudun tsiya tabar gun, ita ma jar motar ta mara mata baya.

Suna shiga cikin gidan kai tsaye kowa ya kama ɗakinsa, amma sai Alawiyya ta dawo falo ta zauna ta kunna waƙa a wayarta, ta kama rubuce-rubuce. Hakan yasa su ma su Daddy suka fito falon don duk jininsu akan akaifa yake, sun ga motoci na bin bayansu amma kuma tace wai guda motarta ce, gudar kuma neman ta take daman har a mafarki tabbas Alawiyya dabance ko da yaushe ƙara tumbatsa take gun ba da mamaki kan lamurranta.

Cikin hikima ta dinga jansu da labari kan shari'ar da ta taɓa yi irin wannan da hanyoyin da ta dinga bi har ta samu nasara. Sai suka samu kansu da daina jin tsoro suka ji tamkar ma an yi shari'ar an samu nasara, don haka Daddy yafi murna ya dinga saka mata albarka yana ƙarawa.

Sai da taga hankalinsu ya kwanta sannan ta shige ɗaki sai gata ta fito cikin baƙaƙen kaya riga da wando hatta fuskarta ba a iya gani, su kansu don a gabansu ta fito da ba za su iya gane ta ba, hatta hannuwanta baƙar Safa ce, ta rufe kanta da baƙar hula irin mai rufe hanci ƙwayar idanunta kuma ta saka baƙin gilashi ta daɗe.

Cikin ɗan sauri tace, "Daddy idan na fita da awa guda za a kawo maku mota ku shiga za a maida ku gidana na cikin gari, amma idan mai motar ya zo to nice zan kira ku, kada ku buɗe ƙofa duk bugun da za ai mata ku jira kirana, zan je wani aiki ne na dawo sai mun haɗe gida."

Dukkansu kasa magana su kai, musamman Daddy da bai saba ganinta a wannan shigar ba, sai kace namijin Film ɗin indiya ko American films. Ganin sun kasa mata magana yasa tai murmushi ta fice ta ja ƙofar ta baya ta rufe, cikin wani ɗan ɗaki ta shige sai gata ta fito da sabon mashin ta haye ta fice, duk abin da take su Daddy na tsaye gun tagar daƙin suna kallonta, ba wanda bai mamakin ganin ta fiddo mashin ba cikinsu.

Kamar an cilla ta haka ta harba mashin ɗin cikin daji ta kama gudun gaske tana duba location a wata ƴar ƙaramar na'ura dake hannunta. Daidai wata siririyar hanya ta tsaya ta samu waje ta ɓoye mashin ɗinta ta fito da ƙaramar bindiga daga ƙugunta sai kuma ta fito da wayarta ta kira Daddy tace su bi mai motar dake jiransu ƙofar gidan, ta maida wayar ta nufi wata ƙaramar hanya bayan ta gyara riƙon bindigarta sosai.

Tayi tafiya sosai kafin ta isa wani ƙaton gida dake cikin dokar dajin shi kaɗai ne ba wani gida a dajin baki ɗaya idan ba shi ba. Ƙarar kiɗa ce ke tashi a cikin gidan tamkar gidan casu. Kasancewar ƙofar gidan a kulle take yasa ta daka tsalle ta haye katangar gidan ta dira, a hankali ta dinga sanɗo har ta isa ƙofar falon dake buɗe amma kuma akwai wasu ɗakunan sai dai su a rufe suke kamar ba kowa gidan, sai da ta leƙa falon ta taga ta ga ba kowa cikin falon sannan ta afka cikin ƙwarewa ta shiga ɗakin dake cikin falon, ba kowa amma ga disko na tashi kamar ya tada gidan, cikin mintuna kaɗan ta fahimci wanda ta zo nema bai gidan sai budurwarsa dake toilet na wanka. Murmushi tai don hakan ma ya yi mata daɗi.

Waje ta samu ta zauna bayan ta rufe ƙofar ɗakin, ta jima sannan ta ji alamar buɗe ƙofar toilet ɗin, ko kanta bata ɗaga ba, balle ta nuna alamar damuwa ko jin tsoron kar wadda ta fito ta ganta.
Jennifer da ta fito daga wanka tana sauri ta shirya kafin masoyinta ya zo, ya gaya mata akwai aikin da zai fita na sati don haka yake son su je yawo na Yau kawai don ya ji daɗin aikinsa, ta ga mutum kwance kan gadonta ga alama ma barci yake, sai abin ya bata tsoro ta nufi wayarta da hanzari amma kamar a mafarki taji an buge mata hannu wayar ta faɗi ƙasa bata samu damar riƙe wayar ba don azabar dukan da akai mata.

Tun da Dauda ya kawo ta gidan nan bata taɓa ganin wani ya shigo ba, idan ba yaransa ba, sai kuwa irin mutanen da yake kawowa ya aje su kuma a tsorace suke don azabar da yake gana masu shi da yaransa wasu mutuwa suke wasu kuwa dama don ya kashe su kawai yake kawo su, sai kuma manyan ƴan siyasar dake zuwa kawo mai aiki, amma Yau ga wani shafaffe da mai ya kawo kansa har gidan mutuwa... Kaya ya miƙa mata ta amsa cike da mamakin ƙarfin halin mutumin, amma data tuna masoyinta Oga Dauda na tafe sai murmushin mugunta ya kubce mata, ta amshi kayan ta saka.
Alawiyya ta fito da ankwa ta saka mata kenan ta ji dirin mota, ko shakka babu tasan ta Oga Dauda ce, ita kuma Jennifer tana jin dirin motar masoyinta sai ta wage baki da nufin yin ihu, ta manta ƙarar discon data kunna ba zai bari ko ƙarar harbin bindiga a ji ba.

Cikin sauri Alawiyya ta fisge ta kamar wata ƙaramar yarinya haka ta jata suka fice daga ɗakin ta buɗe na kusa da shi suka shige, a lokacin da yaran Oga Dauda suka shigo ɗauke da bindigu suna ihun bin waƙar dake tashi cikin gidan.

Suna shiga ɗakin Alawiyya ta ga mutune su uku ɗaure da igiya duk dattawa kuma maza, suna ganinsu suka nuna alamar razana, amma ganin yadda aka wurgar da Jennifer matar gidan sai suka waro idanuwa waje suna kallonta da mamaki ƙarara kan fuskarsu.

Ɗif ƙarar kiɗan ta tsaya, sai kuma su ka ji ihun yaran na ƙwaɗa kiran sunan "Madam where are you?" Cikin sauri Alawiyya ta toshe mata baki, ganin zata bata matsala yasa ta kama bayan kunnenta ta murza kawai sai Jennifer ta faɗi a sume ba numfashi.

Cikin raɗa Alawiyya ta dube su tace,  "Ku me kuke a nan?"

Suka kalli juna suka ƙara kamar masu mamaki sai guda ya ce, "Sunana Alh. Hassan garkuwa su kai da Ni Yau sati guda, sai iyalina sun kawo masu Miliyan goma za su sake Ni."  Cikin mintuna ta fahimci damuwar don haka ta nuna masu I'D card ɗin ta, tace "Ku ban mintuna biyar na gama da su na dawo."

Bata jira komai ba ta kwance masu ɗaurin, ta buɗe ƙofar ta fice ta maida ƙofar ta rufe, hakan ya yi daidai da fitowar yaran Oga Dauda uku tsakar gidan, cikin sauri suka zare makamansu suka nufi Alawiyya da nufin yi mata kwaɓ ɗaya.

Ba ƙaramin mamaki su kai ba, ganin yadda mutumin ya ƙware gun kare duka da maida martani cikin lokaci , ba su ankara ba, har ya buge biyu da mummunan raunuka shi kau har zuwa yanzu ko sau ɗaya ba wanda ya samu ya isa gare shi, sai shi ne kawai ke ta dukansu ta ko'ina tamkar ba shi kaɗai bane su kuma su uku ne ba.

Sauran biyun su ma suka shigo suka sake komawa su uku, amma a banza don haka suka ɗauko bindiga don wuƙa bata kama shi suka harba, sai dai ƙarar alburishin kawai suka ji ya faɗi ƙasa ba wani alamar jini alamar ita ma bai ji kenan. Sai suka karaya cikin sauƙi Alawiyya ta buge su ta ɗaure ta watsa ɗakin, ta fito da wayarta tace, "Maza a kawo mota babba cikin sauri."

Bincike ta koma ta cigaba da yi cikin ɗakunan gidan, duk abin da take so ta ɗauka, sai ga motar da ta kira ta zo , cikin gaggawa suka kwashe duk mutanen dake gidan suka fice daga gidan, ita kuma ta ɗauki mashin ɗinta ta bi bayansu.


Basu jima da tafiya ba sai ga Oga Dauda ya zo, tun a bakin ƙofar gidan ya fuskanci akwai matsala.
Cikin sauri ya shiga yana waige-waige ya fito da bindigarsa ya riƙe yana tsammanin ko da yaushe ana iya kawo mai hari, sai dai har ya shiga cikin ɗakin ba kowa bai ga alamar kowa ba, ya buɗe ɗakin da yake ajiye mutane ya ga wayam ba kowa ya fasa ihu yana dukan bango. Firgigit ya yi kamar wanda ya dawo daga duniyar tunani, "Ina masoyiya take?" Da gudu ya koma ɗakinta bata nan cikin sauri ya fito da wayarsa ya fara kiran ta, ta jima tana ringing sannan aka ɗauka, cikin kaɗuwa ya ce, "Masoyiya me ke faruwa ne? Kina ina? Waye ya shigo mana gida?"

Wata dariya ya ji wadda ya kasa gane inda yasan muryar, sannan aka ce, "Kai ɗin baka da zarra balle nasara haka zalika dai baka da ƙwarin gwiwar yin jayayya da Ni, waye kai a duniyar tantiranci? Wane kambu ka amsa na karramawar kai ɗin shaiɗani ne? Wa yasan da zamanka a duniyar Ibilisai?"

Zufa ta yanko mai, kamar muryar mace kamar muryar namiji wai me ke faruwa da shi ne? Babu wanda yasan gidansa na dajin nan amma an shigo an yi mai ɓarna an tafi da masoyiyarsa har ana masa barazana?" Cike da takaici yake magana a wannan karon, "Ba wani dogon bayani nake nema ba, kamar yadda ba zan lamunci ƙaramin abu ya samu masoyiyata ba, kawai so nake naji waye kai? Wace takun saƙa ce a tsakanina da kai da har ka zo gidana na sirri kai min haka? Ina so ka sani ba zan taɓa yafe maka ba, kamar yadda ba zan ɗauki wannan tozarcin da kai min ba na shigowa har gidana ka tafi da rabin raina ba... "Sauran yaranka guda biyar ma suna wajena ai Dauda." Aka ƙara mai bayani daga can ɓangaren.
Jagwab ya zauna ya dafe kansa, ya kasa ko da cewa ƙala daga can ya ji ance bari na baka masoyiyar taka ka ji muryarta ba mamaki ka fi aminta da cewa wannan karon ka shiga inda bai kamata ba ka shiga, ka jefa kanka inda baka iya fitowa, ma'ana kana jayayya da inda ba a yinta kana hauka a inda hankali ke aiki." Cikin kuka Jennifer ke cewa, "Don Allah masoyi kai masu abin da suke so su ƙyale Ni wallahi sun iya mugunta don Allah ka cece Ni ka cece jaririnka dake cikin cikina masoyi."
Wani uban ihu ya saka yana cewa, "Don Allah mun zama iyaye masoyiya? Da gaske na kusa zama uba nima?"

"Babu tabbas ɗin hakan idan ba bin doka ta kai ba, ka sani a yanzu baki ɗaya a hannuna kake don haka ka natsu ka ji me zan gaya ma, ina son ka gayamin ina yaran Alh. Aliyu suke?" 

Kamar mai maganar na gabansa haka ya zaro idanuwa, "Yaran gidan Alh.Aliyu ! Tabbas akwai matsala domin an riga an ba da su ga dodon tsafi ba mamaki ma sun gama da shafin yaran tunda jiya aka amshe su." Maganar zuciyarsa kenan. Daga cikin wayar aka sake cewa"Kana iya yin duk abin da za kai na tsawon kwanakin da za ai ana Shari'a amma ina so ka sani duk ranar da ka sake kirana kai min burga tabbas sai na nuna maka wacece Barista Alawiyya a zahirin gaske." Kit ta kashe wayar.

Dama haka Barista Alawiyya take? Daman da wannan ce yake waya? Tabbas zai nuna mata namiji yafi mace nesa ba kusa ba, sai yasa ta yi gudun ceton ranta bayan ya hambaɗe mata duk wani jigo da gata nata.

Ta masu karatu ya zata kaya kenan?

Taku a kullum Haupha!!!