HAƊIN ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Shida 

An jima sannan motar ta tashi muka kama hanya, mu dai bamu san inda motar ta nufa ba,mun dai shiga mota kawai da zummar mu bar Lagos ta kowane irin runtsi.  Alawiyya ta haɗe kai da gwiwa tana kuka, ko ban tambaya ba nasan tunanin Mamarta take da Inna Kande, to ya zamu yi ? Haka Allah Ya nufa za a haifemu a watsar muita wahala cikin garuruwa har mai ɗauka ta ɗauka.

HAƊIN ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Shida 
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 
 
 
 
 
            Page 6
 
 
 
 
Tafiya muke mai haɗe da gudu, donma garin bai rabuwa da mutane komin dare yasa mu kai ta wuce mutane wasu na shaiɗana wasu kuwa sana'ar loda kaya a mota suke, kowa dai da abin da yake ba ruwan wani da wani. Alawiyya ta dubeni ta nuna min motar da ake loda mashina tace "Mu je ciki mu ɓoya ba mamaki ma su je garinku kinga mun huta da yawo."  Nayi shiru ina hangen rashin dacewar zuwanmu garinmu wajen wa za mu je to? Wake sona? Ban da mai so kaf garin namu don haka nima ban son su duk yadda muke na yafe su kamar yadda suka yafe Ni. Alawiyya kawai na sani a shafin rayuwata don haka ita ce kaɗai jinina ƴar'uwata wadda duk rintsi zan rayu da ita. Ko da Alawiyya taga ban aminta da maganarta ba, sai tace "To ai nasan inda ake lodin motocin Kano, Kaduna, da Bauchi ki zo mu je can mana sai mu hau ai dai ba garinku a ciki ko?"  Ni fa a yanzu ko asalin sunan garinmu ban sani ba, don haka nace mata, "Me zai hana mu je garin da ba wanda muka sani ko ya sanmu mu ci-gaba da rayuwa? Na kwaso kuɗin Iyami masu yawan gaske don mu samu rayuwa mai amfani kinga sai mu kama haya duk inda za mu je ba ruwanmu da kowa mu cigaba da saida abinci tunda duk mun iya ko ya kika gani?"  Alawiyya ta amince da shawarar dana kawo musamman data ga tarin kuɗin dana wafto na Iyami, muna zuwa muka kutsa motar ana ta rubibi, ba kan kujera muka zauna ba, kan katakon maleji muka zauna muna kallon mutanen cikin motar duk maza ne ba mata ko ɗaya.
 
An jima sannan motar ta tashi muka kama hanya, mu dai bamu san inda motar ta nufa ba,mun dai shiga mota kawai da zummar mu bar Lagos ta kowane irin runtsi.  Alawiyya ta haɗe kai da gwiwa tana kuka, ko ban tambaya ba nasan tunanin Mamarta take da Inna Kande, to ya zamu yi ? Haka Allah Ya nufa za a haifemu a watsar muita wahala cikin garuruwa har mai ɗauka ta ɗauka.
 
Sai da mu kai tafiyar kwana uku sannan mu ka ji ana cewa an iso Kano kowa ya shirya. Murna fal kan fuskarmu domin muna jin yadda ake maganar Kano, babban gari ne mai cike da abubuwa masu yawa, ko da muka sauka muka biya kuɗin mota sai muka danna kai kawai cikin gari sai idan mun ji yunwa mu sai abinci da ruwa, abin mamaki abincinsu da sauƙi sosai ba kamar na Lagos ba. Mun sha yawo sosai bamu samu inda zamu zauna ba, kowa uzurinsa kawai yake, don haka da dare ya yi muka shige wani masallaci muka kwanta, asubar fari Ladan ya ganmu ya tada mu yace kar ya sake ganinmu a cikin masallacin nan, idan ya sake ganinmu sai kashinmu ya bushe.
 
Haka muka dinga gararanba muna neman gun kwana, arziƙinmu ɗaya kuɗaɗen basu ƙare ba, don haka bamu da yunwa ko alama sai rashin wanka da gun kwana, to daman wankan ai ba ko da yaushe muke da ƴancin yinsa ba, don haka bamu damu ba sosai. 
Watarana muna yawon zageyen da muka saba muka ga wani gida babba mutane sunata shiga ba mai hana su don haka sai muma muka afka cikin gidan nan, muna shiga muka ga mutane zaune wasu kuma a can saman dakali sunata rawa ana masu liƙi , wasu na ihu. Sun jima suna yi sai kuma muka ga sun sauka an kashe kiɗan wani mutum ya hau yana sanarwar, "Don Allah ku natsu yanzu wasan zai fara."    Kawai mutane suka saka ihu abin gwanin ban tsoro, don haka nayi wuf nace ma Alawiyya ta tashi mu tafi, amma sai naga tayi murmushi ta ja hannuna ta mayar da ni mazaunina tace, "Wai ke baki fahimci me za ai ba ne? Gidan wasan kwaikwayo ne fa muka zo, Wallahi ni daman suna matuƙar birgeni don haka ba inda za mu je sai sun gama wasan."   Ko da naji cewar ƴan wasan kwaikwayo ne sai na zauna farin ciki fal raina domin suna matuƙar birgeni sosai nake son su, da ganinsu ba su da damuwa irin tamu ko da yaushe fes da su a cikin Film, ashe zamu haɗu? Allah abin godiya nafi farin ciki da haɗuwa dasu fiye da haɗuwa da mahaifina ma Ni. 
Gabanmu ƴan wasan kwaikwayo sukai wasa abin da ya dinga tsuma zuciyata kenan naji cewar dama na girma da babu abin da zai hanani yin wasan kwaikwayo nima ba shakka da sai na shiga harkar. Mu dai muna zaune muna kallon wasan kwaikwayo mutane duk sun fice sai tsiraru amma mu ko a jikinmu domin ba mu ƙi a kwana gunba tunda ba mu da wajen kwana, rara gefe muke kawai duk inda muka samu mu kwana da asuba kafin a kama mu muke barin wajen. Sai da aka gama wasan tas sannan muka fice ashe dare ya yi sosai a lokacin ga duhu ga hadari ya taso sosai, kawai muka rungume juna muka fashe da kukan baƙin ciki da takaici, tabbas duk lokacin da nake a yanayin nakan ji tsanar iyayena fiye da yadda nake jin tsanar rasa gata a zuciyata.  "Kai lafiya kuka zo nan cikin daren nan kuka haɗe kai kuna kuka?". Muryar wani mutum muka ji a kanmu, tare muka kalle shi, nan take muka gane shi, yana cikin waɗanda ke tattara kuɗaɗen gidan wasan kwaikwayo da muka fito yanzu. 
"Mutane ne ku ko aljanu? Don babu yara kamar ku da iyayensu zasu barsu haka kara zube a sake ba  ko da shegu ne." Jin abin da yace yasa muka ƙara fashewa da kuka, ai gaskiya ya faɗa gwara shegu da mu, domin duk inda suke yanzu suna kwance cikin gidaje haka cikin ɗaki amma mu fa... Gamu tsakiyar titi cikin dare garin da babu dangin Iya babu na Baba muna tumɓele kamar awakin sakarai. 
Fahimtar cewa mutane ne mu yasa ya ɗan yi jim kana ya sake cewa, "Baku da wajen kwana ne? Ku zo mu je dare ya yi da safe mun yi maganar abin da ke faruwa yanzu zaman ku a nan haɗari ne domin akwai muggan ƙauraye da ɓarayi... Kafin ya ida zancensa har mun kusa inda yake ya shige gaba muka bi shi baya ba tare da mun yi wani dogon nazari ko tunani ba.
 
 
              LAGOS
 
 
 
Iyami gari na wayewa ta fito tsakar gida bata ga Jiddah ba balle Alawiyya sai tai tunanin sun tafi makaranta don haka taita kimtsa kayansu tana cewa zata ga yadda Alawiyya da Jiddah za su rabu a Yau, ko mutuwa suke suna dawowa ba zata tafi da Alawiyya ba, haka ba zata bar Jiddah ba, ta gama tsara yadda zata maida Jiddah addininta hatta suna ta zaɓa mata mai daɗin gaske idan ta maidata addininta. Tasan dai ba wanda yasan asalinta balle idan Baban Jiddah ya zo a kai shi can ko a kwatanta mai ya je ya amso ɗiyarsa.
 
Shiru-shiru har lokacin dawowarsu makaranta ya yi amma basu dawo ba, tun abin bai dameta ba har ta fara masifa da bala'i, ƙarshe dai ta zari makulli ta datse gidan ta bisu makarantar. Tana zuwa ta iske har kowa ya watse bata jira komai ba ta wuce gidansu Alawiyya don suna biyawa wai ko Inna Kande ta dawo su gani. Canma basu iske kowa ba, ta koma gida zuciyarta na saƙe-saƙe kala-kala na inda yaran suka tafi, tabbas yau sai ta ci Uban-Uwarsu la'ada waje kuma sai ta azabtar da su iyakar azabtarwa.
 
Sai dai ganin basu dawo ba kuma sai a lokacin hankalinta ya kai kan jakarta inda take aje kuɗaɗe kuma ta diba bata ga takalman data amshe nasu ba, sai ta fasa ihu ta kama zage-zage tana sun gudu da kuɗaɗe ita sai an biya ta. Nan da nan gidan ya cike da mutane, da dama sun yaba ma abin da yaran sukai mata domin kowa ya kwana ya tashi a layin yasan yadda take bautar da su da azabtar da su ba kamar Jiddah. Ta kwasa ta nufi shagon da ƴan garinsu Baban Jiddah yake ta gaya mai amma ba kowa sun tafi bukin Sule har an zuba sabbin fuska shagon ba wanda ta sani ma cikinsu.
 
Kamar mahaukaciya haka ta koma sai ihu take da zabure-zabure kamar kamun mayya. Ƙarshe ta fasa tafiya ranar ta ƙara kwana biyu ko zasu dawo tunda ba wanda suka sani kamar yadda ƙawarta ta gaya mata duk inda su ka je zasu dawo mata tunda ba su iya riƙe kansu sun ƙanƙanta da yawa. Daga gefen zuciyarta kuma tana tunanin me zata gayama Baban Jiddah idan ya zo? Me yasa ta gayama Jiddah zata koma garinsu da ita ne ma wai? Akan me tai wautar cewa zata bar Alawiyya a nan? Tabbas laifinta ne amma zata nemo duk inda suke a cikin Lagos ta ida cika burinta kan Jiddah ko shakka babu kuma sai sun biya ta kuɗaɗenta tas da suka sace.
 
Abu kamar wasa Iyami taita neman su Jiddah amma basu ba labarinsu ko mai kama da su bata gani ba, sai lamarin ya sake tada mata da hankali domin dai ta riga ta tsara komai yadda ya kamata har ta kira fastocin garinsu ta gaya masu zata kawo ƙaruwa a cikin addininsu saboda murna har kyautar manyan kuɗaɗe aka turo mata kuma aka dakatar da mijinta daga ƙarin auren da ya yi niyyar yi. To yanzu me zata ce ma su idan ta je? Anya kuwa Jiddah tasan talalar tsiyar da tai mata? Gaskiyar magana ba zata amince ba da rashin cikar burinta ba don haka wajibi ne ta shiga ta fita ta nemo duk inda take... "Ana magana a waje." Cewar wani ƙaramin yaro yana kallon Iyami da fuskar mamakin ganin tana kuka.
Kamar karta fice amma data tuna da neman Jiddah take sai ta fice tana share hawayenta.
 
Tsaye suke su biyu gudan ya juya bayansa, gudanne ya tsira ma ƙofar fitowa daga gidan idanu, fuska ba alamar fara'a balle dariya. "Ku ne kuna nema na ?" Cewar Iyami kenan cikin muryar damuwa. Gudan na juyowa ta dafe ƙirjinta ta fara kiran "Jesus !  Sak fuskar Alawiyya don dai kawai ya fita duhu kaɗan amma kana ganinsa kasan yana da kyakkyawar alaƙar jini da Alawiyya... 'Iyami manyan gari kina gida ashe?" Cewar Baban Jiddah daga sauka daga mashin da ƙaruwar jakar tsarabarsa a hannu ya nufi gun mazan nan biyu ya basu hannu suka gaisa don ya gane musulmai ne.
 
Cikin Iyami ya bada "Ƙuuuuu! Ga Baban Jiddah ga Baban Alawiyya ga dukkan alama shi ne mahaifin Alawiyya ko bai faɗa mata ba asalin kamar su da Alawiyya ta bayyana dangantakar dake tsakaninsu.
 
Ƙawarta ce ta iso gun da gudunta tace, "Iyami kin ga yaran kuwa?"
 
Mazan suka dubu juna su uku suka maida dubansu ga Iyami dake tsaye kamar ace ƙat ta ruga.
 
 
To jama'a ko ya kenan? Da gaske Baban Alawiyya ne ?
Ya Baban Jiddah zai yi idan ya ji ƴarsa ta  ɓace?
 
Ku biyo Haupha dan jin yadda zata kasance.