Gamsuwa Da Aikin Mabera Ya Sanya Abdullahi Hassan Yiwa Tambuwal Addu’a
Tsohon shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa jigo a jam'iyar PDP a Sakkwato Honarabul Abdullahi Hassan ya bayyana gamsuwarsa ga aikin magudanar ruwa da gwanatin Aminu Waziri Tambuwal ta samar a unguwar Mabera a birnin Sakkwato.
Honarabul Abdullahi ya yi addu'a ga Tambuwal da duk wadan da suka taimaka aikin magudanar ruwa a unguwar Mabera ya kammala a tsanake.
"Na shiga Mabera naga aiki Allah Ya biya Mai Girma Gwamna da duk mai hannu a cikin wannan aiki," a cewar Abdullahi Hassan.
'Yan siyasa ba su cika yabon aikin dan uwansu ya aiwatar ba ko ana jam'iya daya sabanin halayyarsa, Honarabul bai dade da sake komawa jam'iyar PDP ba kuma ya fadi aiyukkan cigaba ne da Tambuwal ya samar ya sanya shi dawowa a yi tafiyar da shi a kafa gwamnati a 2023.
managarciya