Babban Buri:Fita Ta Ashirin Da Shidda

Zuwa lokacin A'isha itama ta yi aure tana goyon ɗan ta na miji Abubakar sadiq haka kuma tana aikita a asibitin kwararru dake nan Sokoto. Umar ma a lokacin yana Babbar jami'ar Usmanu Danfodiyo. Ahmad kuwa lokacin yake rubuta jarabawar kammala sikandare ta hukumar Neco. Ƴan matan dake gidanmu a ƙalla sun kwai sha biyar suma gaba ɗayan su Baba da Ya Haidar duk sun haɗa su sun aurar da su. Arziki sai ƙara bunƙasa yake yi agurin mijina da mahaifina, a wannan shekarar ma muke saran sauke farali dani da A'isha da Mama da Hajiya Inna.

Babban Buri:Fita Ta Ashirin Da Shidda
BABBAN BURI
Fitar Karshe
 
 
 
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
 
 
 
 
Kyakkyawar gaisuwa zuwa ga:
 
 
ANTY HAUWA MAMAN USWAD.
 
HUSSAIN 80K.
 
HUSSAIN ABU SAMEER.
 
MUHAMMAD KAREEM.
 
NAZIFI YARIMA.
 
 
YUSUF NUHU.
 
FATEEMA SUNUSI RABI'U UMMU AFFAN.
 
AISHA IDREES ABDULLAHI SHATU.
 
AND ALL MY FANS.
 
 
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {,SHATU}.
 
 
 
 
 
 
 
FITOWA TA ASHIRIN DA SHIDA
 
 
 
~A haka muka ci gaba da rayuwarmu cikin kwanciyar hankali kuma ina rainon ɗan ƙaramin cikina.
 
Watan mu goma sha ɗaya da aure na haifo 'ya mace mai kama da Ya Haidar sak da ita, gida na koma dan yin wanka kamar yadda al'adarmu ta Sakkwatawa take, ranar sunan
yarinya ta ci sunan Hajiya Inna wato {MARYAMAH} uwarta A'isha ke kiranta da {Islam}.
Sosai a ka sha shalin bikin suna inda muka samu kyatuttuka na musamman daga sassa daban daban.
 
Watan Islam ɗaya, lokacin  duk bamu koma ba muka sha shagalin bikin Safiya da Safara'u a rana ɗaya a ka kaisu.
 
Lokacin da muka yi arba'in idan kaga Islam ba zaka taɓa yadda ƴar 40dys ba ce domin kuwa ta yi ɓul ɓul da'ita gwanin sha'awa.
 
Sai da na yi arba'in biyu na zaga dangi ko ina, kana muka koma.
 
Duk da ayukkan dake gaban Ya Haidar hakan bai hana mu samun kulawa a wajensa ba, sosai muke samun lokacinsa da, haka muke rayuwarmu cikin kwanciyar hankali da son junanmu.
 
*Bayan shekaru biyar.*
 
Zuwa lokacin idan ka ganni na zama big Madam ɗin nan, yayin da nake goyan ɗana na biyu wato Irfan wanda ya ci sunan margayiya Baban Ya Haidar.
 
Zuwa lokacin A'isha itama ta yi aure tana goyon ɗan ta na miji Abubakar sadiq haka kuma tana aikita a asibitin kwararru dake nan Sokoto.
 
Umar ma a lokacin yana Babbar jami'ar Usmanu Danfodiyo.
 
Ahmad kuwa lokacin yake rubuta jarabawar kammala sikandare ta hukumar Neco.
 
Ƴan matan dake gidanmu a ƙalla sun kwai sha biyar suma gaba ɗayan su Baba da Ya Haidar duk sun haɗa su sun aurar da su.
 
Arziki sai ƙara bunƙasa yake yi agurin mijina da mahaifina, a wannan shekarar ma muke saran sauke farali dani da A'isha da Mama da Hajiya Inna.
 
Zaune nake a babban Parlour Islam ce zaune a gefena  tana home work, yayinda Irfan ya ke rungume a jikina yana shan mama, jin mutum kawai na yi a jikina yana ƙara shigewa jikina, hannayena nasa duka biyu iname ƙara rungume su a cikin jikina, itama Islam tana ganin hakan ta yi wurgi da book ɗin da take home work dashi kana ta yi azamar zuwa ta shige cikin jina.
 
Kallon mijina na yi sannan na ce "bani da  *BABBAN BURI* yanzu a duniyar nan sai na gamawa da duniya lafiya, domin kuwa duk abinda nake nema na same shi a duniyar nan".
 
Shammata ta yayi ya yi azamar haɗe bakina da na......
 
 
 
 
 
TAMMAT BI HAMDALLAH.
 
 
Laifin daɗi ƙarewa!.
 
Duka duka anan na kawo ƙarshen wannan littafin, kurakurran da na yi a cikin sa Ubangiji Allah Ya yafe min.
 
 
Na sa daukar da wannan littafin zuwa ga uwar ɗakina a harkar rubutu wato AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}, Rabbu Ya sadaki da dukkanin alkheereensa.
 
 
 
Sai mun haɗu a sabon Littafina  mai suna..........
 
 
 
DOCTOR MARYAMAH na yi wa kowa fartan alkheree.
 
Lv U all.
 
 
Ga duk wanda zai bayar da shawara muna bukata ya bayar.