DUHU DA HASKE: Fita Ta Bakwai
DUHU DA HASKE: Fita Ta Bakwai
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 7*
https://chat.whatsapp.com/CGf8vl2tuAo75eBYR6Yl7h
~Da sassafe ta tashi da kanta ta shiga kitchen tana girki, bata iya komai ba sai indomie data jiƙa ta zuba a cikin plate ta rufe ta kai dining, juice ta juye na gora a cikin cup guda biyu kala ɗaya, saida tasa shaida a jikin cup ɗin ta yadda zata gane nata da wuri, ciro maganin da aka bata tayi ta zuba a cikin juice ɗin, juyawa tayi saida ya narke ta fito dashi a hanu tana murmushi, a kusa da abincin ta aje ta juya zuwa ɗakin ammi fuskanta fal murmushi, knocking tayi kana ta shigo, ammi na zaune abakin gado tasa hanu a cikinta tana shafawa yayinda idanunta suke kan hoton dady, ganin bata san ma ta shigo ba ta tafa hanu kamar karamar yarinya ta maida face nata tace "Ammiiii"
a firgice ammi ta ɓoye hoton karkashin pillow tayi saurin share hawaye tace "manal"
takawa take tana yi kamar me rawa har ta isa inda take, faɗawa kan gadon tayi ta kwanta tana kallon pop na ɗakin, kafafunta a kasan gadon tace "ammi tun ɗazu nake jiranki na gama breakfast"
murmushi tayi cikin innocent face nata tace "to manal muje dama yunwa nake ji"
tashi tayi ta rike hanunta suka fito, kallonta take tana kallon cikin daya fara nuna kanshi, akan kujera ta zaunar da ita kana ta matso da abincin gabanta tace "eat"
kallo tayi da ganin indomie kasan bai dahu ba, tace "to manal"
ci ta fara itama manal ta zauna suna ci tare, ammi zata ɗau goran ruwa tayi saurin tura mata cup na juice, ɗauka tayi tasha, suna haɗa ido manal tayi mata murmushi itama ta mayar mata, da haka har suka gaba cin abincin, saida ta tabbatar ta shanye juice ɗin duka kafin itama ta shanye nata, tashi tayi tana tafiya tana cewa "yau zan tafi aiki ina fatan ba zaki zauna kina kuka a gida ba"
tace "ba zanyi kuka ba"
tace "okay"
ɗakinta ta shiga, kayan jikinta ta cire sannan ta ɗaura towel ta kwance gashinta domin zata wanke, zata shiga toilet ta dawo da baya tana kallon kanta a madubi, murmushi ta yiwa kanta tace "nice manal"
shiga tayi ta fara wanka da tsadaddun sabulanta da shower gel, gashinta ta zuba shampoo me kamshi wanda dady ya dawo mata dashi daga kasar paris, yana kamshi sosai kuma yana maida gashi baki ƙirin da laushi, ta jima tana wankan kafin ta fito ta ɗaura towel a kirji santala santalan cinyoyinta farare tas suka bayyana domin karami ne towel ɗin, ɗayan pink towel ɗin kuma karami ta ɗaura a kanta tana tsane ruwan, wajen mirror, gaban mirror cike fam da kayan mayuka da turaruka, zama tayi ta ɗauko dryer ɗinta da dady ya siya mata shima a paris, busar da kanta tayi sannan ta fara shafa mayuka, saida ta ɗau lokaci a wajen kafin ta tashi ta buɗe wardrobe, kayanta a jere suna kamshi zaɓo wani yadin larabawa tayi yana sheƙi ammi ta siya mata a makka, dogon riga fited gown ne baƙi ya zauna a jikinta ya fitar da duk wani shape nata, yanada ado sosai a jikin domin sheƙi yake yana walƙi, takalmi me tsini tasa baƙi ta yafa karamin mayafi akan gashinta da tayi parking, kallon fuskanta tayi idan ma batayi kwalliya ba tafi kyau, fesa turaren tayi sannan ta buɗe drower tana kallon tulin gilasanta, ɗauko babban cikinsu tayi half face tasa a idonta, jakanta baƙi kiran gucci ta rike a hanu ta ɗau makullin mota tana tafiya tana karkaɗa makullin tana hura fito da ɗan karamin bakinta, wani irin smiling da yake kara mata kyau ta yiwa ammi ganin tana kwance tana kallo, itama ammi murmushi tayi sannan ta ɗaga hanu tayi mata alaman kinyi kyau, tace "ammi na tafi"
tace "saikin dawo Allah ya tsaremin ke"
tace "ameen"
tafiya take tana fito har ta isa wajen motarta, shiga tayi cikin natsuwa take driving, me gadi yace "fuska kullum babu dariya kamar me ɗaukan rai"
tana shiga company tayi parking, makullin motar a hanu tana kaɗawa tana fito duk wanda ta gani yana durkusawa ya gaisheta hanu kawai take ɗaga musu idan taga dama tana cigaba da fito harta shiga ciki, duk suka daina aiki da computer ɗin gabansu suka tashi daga zaunen da suke suna mika mata gaisuwa, tsayawa tayi tana karewa kowa kallo a cikinsu, gani tayi kujeran mutum ɗaya babu kowa, sunan dake jikin kujeran ta kalla tace "ina rahma husain?"
sukace "bata zo ba"
jijjiga kai tayi tace "meyasa?"
a takaice take yin magana bata yadda magana yayi mata tsayi, wani daga cikinsu wanda aka rubuta kamal a jikin kujeranshi yace "babanta baida lafiya"
tace "shiyasa bata zo ba?"
duk suka kalli juna jin abinda ta faɗa, tace "shiyasa bata zo ba"
a hankali yace "eh"
tace "okay"
zuwa tayi wajen kujeran ta cire daga cikin masu zama a wajen, waje ta fitar da kujeran sannan ta ɗauke laptop ɗinta bata yiwa kowa magana ba ta wuce office nata.
wayan office aka kira tana ɗauka akace "muna magana da c.e.o ɗin companyn m.u.m ne?"
tace "eh kuna magana da manal umar maidawa"
daga ɗayan ɓangaren akace "munga zanen da akayi daga company ɗinki sannan mun fitar da sabbin kaya irinshi, munaso mu haɗa hannu da company ɗinki zamu baki contract ɗin zana mana sabbin kayan da zamu fitar a sabon shekara"
tana juyi akan kujera a takaice tace "kamar guda nawa?"
yace "munaso kamar kala dubu biyar"
shiru tayi tana nazari sai kuma tace "okay zaku iya zuwa ku aje kuɗinku aiki zai kammala bada jimawa ba"
yace "akwai account number ɗinku na m.u.m a wajena zansa naira biliyan goma idan an gama aiki zan cika Biliyan uku sabida daga china aka bada order kuma kasashe da dama suna jiran sabon kayan da za'a fitar"
cikin kakkausan murya tace "idan kasa biliyan goma sha uku duka a account zaka samu aiki idan kuma ka rage koda naira biyar ne a ciki ba zanyi aikin ba"
zata kashe wayan yace "tsaya zansa duka"
tace "okay"
tana zaune taji karan message alaman kuɗin ya shigo account ɗin m.u.m murmushi tayi ta tashi daga zaunen ta fita zuwa waje, suna ganinta suka tashi, goya hanu tayi a baya tana zagayesu ta fara magana "an bamu aikin zane guda dubu biyar kuma kunsan ba karamin aiki bane, inason kara girmar da company ɗin m.u.m fashion designing ta yadda daga ƙasashen waje kawai zamu rinƙa karɓan aiki, to amma hakan na zai faru ba domin naga baku da kwarewan da nakeso a zane, wannan dalilin yasa dole mu nemi kwararre wanda ya kware wajen zana zane hakan zaisa mu kara samun mutane dayawa susa hannun jari da company ɗinmu, mu rinƙa karɓan manya manyan contract daga manyan kasashen duniya, kunga wannan?"
takadda ta nuna musu na neman kwararren me zane, tace "photocopy ɗinshi zakuyi kamar guda ɗari ku manna a kowane bango da kuka san zai janyo hankalin mutane, sannan a social media kowa yayi posting cewar company ɗin m.u.m fashion designing suna neman ƙwararren me zane, a yadda na kware a zane ba lalle a samu wanda ya kaini ba, nasan nice kaɗai a nigeria nake iya zana duk abinda naga dama kuma ya fito fes, hakan yasa kowa yakeson ganin manal tayi mishi zane, nasan ba za'a samu wanda ya kaini ba amma may be a samu wanda ya kware ina fatan kun fahimceni?"
a tare sukace "yes madam"
tace "okay a fara yanzu yanzu"
duk suka buɗe laptop daga tsayen sun kai su goma sha biyu suka fara posting a social media ta yadda zai tafi viral, farko a account ɗin m.u.m suka fara posting kafin sukayi da sauran personal account nasu, me photocopy kuma yana gefe yana copy ɗin saida yayi guda ɗari ya raba musu suka fita domin mannawa, manal wayarta aka kira ta amsa "ammi"
cikin jin ciwo tace "manal an kirani a waya akan dadynki sunce sunason yin meeting da matarshi ko kuma ƴarshi domin akwai kuɗin daya zuba hanun jari suna so su mayar kishi"
tace "okay aina za'ayi meeting?"
tace "zan tura miki address"
tace "okay ammi"
tana kashe wayan ta turo mata address, kallo tayi sannan taje wajen mota ta shiga, ammi ta kirata tace "sunce suna jiranki na basu number ɗinki da kinje kin kirasu zasu ganeki"
tace "okay"
fita tayi tana driving a hankali tana duba address ɗin, tayi tafiya da ɗan nisa kafin ta isa wajen, kamar company ne domin yanada girma sosai gashi da kyau kamar a turai, fita tayi ta rufe mota tana taunan cingum tana tafiya harta isa ciki, me gadi zaiyi magana ta nuna mishi ID card nata na m.u.m yana gani ya bata hanya, shiga tayi har zuwa wajen data tabbatar anan ne ake taro domin taga alaman takalman mutane na mata a bakin kofa, bata cire takalminta ba tayi knocking suka amsa mata da "yes"
shiga tayi duk suka kalleta suna zaune akan kujera sunsa manyan kaya da ganinsu masu kuɗi ne kuma masu muƙami, akan kujera itama ta zauna sannan ta cire glass na idonta ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya ta zuba hannayenta akan table na gabanta tace "gani"
duk suka kalli juna kafin ɗaya daga cikinsu da alama shine babba yace "kece manal?"
tace "umar maidawa nice"
ya jijjiga kai yace "okay"
takaddu ya tura gabanta yace "wannan takaddun Alhaji umar yayi sign kafin ya mutu, makudan kuɗaɗe ya zuba hannun jari saide ya mutu kafin ayi harkallan, ina fatan zaki bamu goyon baya kiyi sign sabida kada a dakatar da abinda ya fara"
murmushi tayi sannan tace "nawa ya zuba a ciki?"
mutumin yace "biliyan 20"
murmushi tayi tace "ba zanyi sign ba saida sharaɗi guda biyu"
kallon juna sukayi sannan suka ce "menene sharaɗin"
tace "sharaɗin farko shine ku tabbatar koda ciwon kai ba zai samu naira biyar a cikin kuɗinnan ba, idan abu ya samu kuɗinnan manal umar maidawa ba zata bar kowa a cikinku ya zauna lafiya ba"
shiru sukayi, tasa glass nata ta tashi daga zaunen tace "sharaɗi na biyu shine ba zanyi sign ba har sai kowa ya nuna min abinda ya mallaka wanda ya kai naira biliyan ɗaya ta yadda koda abu ya samu kuɗin inada right ɗin da zan nuna abin a matsayin jingina"
duk suka kalleta, murmushi tayi musu ta juya zata tafi, sukace "dakata"
tsayawa tayi tana murmushi tace "kun amince?"
duk sukace "eh"
zuwa tayi duk suka nuna mata kadaran da suke dashi a waya da address ɗinsu da kuma numbern wayarsu dana ƴaƴansu manya, murmushi tayi ta janyo takaddun tayi sign sannan ta mika musu, tafiya tayi, har ta fita sai kuma ta dawo, wayarta ta buɗe ta fara nuna musu video daga lokacin data shigo har lokacin da zata fita duk abinda sukayi tayi video basu sani ba, murmushin gefen baki tayi kana tace "bani kaɗai keda wannan video ba a yanzu harna turawa mutane biyu wanda nasan koda wani abu ya sameni zasu baza video a lungu da sako har sai an gano menene dalilin faruwan na barku lafiya"
fita tayi ta shiga motarta cikin kwarewa a tuƙi ta har wajen, shiru sukayi babu wanda ya kara magana, ɗaya daga cikinsu yace "Alhaji lawal wannan yarinyar ta fimu taurin kai"
wanda aka kira da Alhaji lawal ya share zufa yace "Innalillahi ashe duk taurin kanka akwai wanda ya fita kuma duk wayonka akwai wanda ya fika, wallahi na gama sawa a raina tana gama yin sign zamu sa a gama da ita mu raba kuɗin a tsakaninmu"
ɗayan yace "kut akwai aiki wato sunanta mukeji yau mukaga asalin wacece manal, ni dama cewa nayi idan mun raba kuɗin saina lallaɓa na aure kyakkyawar matar Alhaji umar daya bari ashe da sauran aiki"
ɗayan da yayi shiru sukace "Alhaji sani kayi shiru fa bakace komai ba"
yace "ta gogemin hadda ne, saifa mun san takun mu domin babu tsoro a idonta kuma babu shaƙƙa"
duk sukace "tabbas hakane akwai dakakken zuciya a wajen".
Ameesha parking na mashin nata tayi bata cire hulan tukin daga kanta ba ta fara tafiya a hankali zuwa cikin gidansu man, hanunta rike da wayarta ta buɗe kofan a hankali ta shiga, ɗaga hulan tayi, kyakkyawan fuskanta ya bayyana amma babu walwala kamar yadda ta saba, da alama yau akwai abinda yake damunta, kamar kullum riga ne da wando a jikinta wandon a buɗe sosai rigan kuma ya kamata kaɗan pink wandon fari, cikin sanyin murya tace "umma ina wuni"
umma da mamaki tace "lafiya ameesha"
wucewa tayi ɗakin man tayi sallama a hankali ta shiga, yana zaune a kasa yana zane, ɗauke kai tayi cikin jin haushin zanen da yake yi kullum gashi zanen bai taimaka musu da komai ba, kallonta yayi har ta karaso ta zauna a bakin gado kafafunta kusa dashi tayi shiru tayi tagumi, yana cigaba da zanen hotonta da nashi yace "meya samu princess ɗina yau?"
tsaki taja kaɗan sannan ta ɗauke hoton daga gabanshi ta nuna hoton tace "mutane suna samun cigaba a kullum cikin rayuwarsu, mu saide abu ya koma baya bama samun cigaba, kullum ina cemaka muje mu nemi aiki koda kai ka samu babu damuwa amma kaki saide ka zauna kayi ta zana hoton da babu amfaninshi, bana bacci kullum ina searching a social media ta yadda zaka samu aiki amma bamu samu ba"
tashi tayi ta ciro hotonsu dake kasan gadonshi ya zana da wanda aka ɗaukesu tun suna yara da wanda suke tareda su abba da kuma su umma sai wanda suka rungume juna suna dariya ita dashi, zanen yafi yawa akan asalin hoto, tace "kullum sai kayi wannan zanen kwarewanka a zane bai kawo mana komai ba"
tana magana tana hawaye, ya zuba mata ido ko kyaftawa babu, ta ɗago manyan idanunta sexy tace "ko dai zamu bar garinnan ne man?"
gyara zama yayi yana kallonta ya lumshe mata kyawawan idanunshi yace "meesha kin san matsala dake?"
shiru tayi yace "gaggawa"
magana zatayi yace "shiiiii a kullum kin manta kina min addu'a Allah ya bani aikin yi? to meyasa ba zakisa a ranki watarana Allah zai bamu aiki ba?"
a hankali tace "to ai..."
rufe mata baki yayi da hanunshi, kallonshi take shima yana kallonta yace "please nasan kin gaji, amma mu kara hakuri muci gaba da addu'a, ba gashi duk da babu aiki bamu bar kannemu suna zama ba karatu ba? kinga fahad ya gama primary ya shiga jss 1 shi kuma Imran zai gama secondary nan bada jimawa ba"
tace "to idan ya gama karin karatu....."
yace "karki damu da wannan zamu saki aiki kafin hakan ya faru"
shiru tayi ta ɗaura kanta a gwiwa tana kallonshi yana zanen yana murmushi, saida yayi nisa ya ɗago kai ya kalleta, murmushi yayi mata tace "kanada kyau"
fentin da yake zanen dashi ya lakata mata a karan hancinta yace "kin fini kyau"
turo baki tayi tace "shine zaka shafamin fenti?"
yace "sorry baby"
tace "tashi ka rakani"
yana kan zanen yace "ina?"
tace "zanje kasuwa"
yace "siyan me?"
tace "pant Anti ta bani kuɗi na siyo"
murmushi kawai yayi a ranshi yace "ta riga ta saba faɗamin tun muna yara ba zata iya dainawa ba hasalima bata ɗauki hakan wani abu ba"
a fili kuma yace "bari na gama"
saida ya gama zanen ya nuna mata, dariya tayi ta karɓa tana kallo tace "Ameesha da Abdulrahman"
yace "munyi kyau?"
tace "yes amma nice zan tafi da wannan hoton"
taɓe baki yayi yace "normal"
ɗauka tayi ya tashi ya wanke hanunshi suka fita tare, akan mashi suka tafi kamar ko yaushe itace take driving, har sukaje kasuwa ta siyo sannan ta juya kan mashin zasu tafi gida yace "no rakani gidan abokina bilal"
tace "okay"
juya mashin tayi suna tafiya suna hira har suka isa gidansu bilal, tare suka fito dashi tace "tunda kuka gama school baku haɗu ba sai yau"
yace "yes"
sallama yayi bilal ya amsa tareda cewa "ina zuwa"
jim kaɗan ya fito masha Allah yanada kyau amma baƙi ne irin me glowing ɗinnan, yana ganinsu yace "su waye wannan?"
Abdul yace "mu ne"
yace "mu shiga ciki"
hanu Abdul ya mika mishi suka gaisa yace "kana nan?"
yace "ina nan ka shareni"
kallon ameesha yayi wacce bata rabo da murmushi yace "hi ameesha"
hanu ta mika mishi alaman su gaisa, da sauri man ya rike hanunta ya hana gaisuwan, murmushi bilal yayi yace "mu shiga ciki mana"
Abdul yace "no ba zamu shiga ba dama nace kawai nazo na dubaka mun jima bamu haɗu ba"
yace "gaskiya kun kyauta Allah ya bar zumunci nima rasa number ɗinka nayi ai da kullum ina kai muku ziyara"
numbern shi ya bashi yace "muna jiranka"
sunyi hira kaɗan kafin yace "hajiya ameesha ki gaida gida sosai"
tace "to insha Allah"
har suka hau mashin bilal yace "wai har yanzu baka daina hawa baya idan zaku fita ba? mace ke janka a mashin?"
taɓe baki yayi yace "ba itace taki ba"
dariya ameesha tayi taja mashin ɗin tace "bye"
har sukayi nisa yana ɗaga musu hanu, a rayuwa bai taɓa ganin amintattu irin ameesha da Abdul ba yace "Allah ya barku tare"
wajen gyaran motarshi sukaje akace musu mota ya gyaru, amma sai sun cika kuɗin gyara kafin a basu, kallanshi tayi kamar zatayi kuka tace "wannan motan naka shine ya kara talautamu ka siyar kawai mu cinye kuɗin tunda muna tafiya a mashin ɗina"
girgiza kai yayi shima kamar zaiyi kukan yace "no inason motata ai kema kina hutawa idan tana gyare"
ɓata rai tayi tace "sai muga inda zamu samu kuɗi mu ɗauka"
yace "eh dai a barmin abuna"
hawa mashin ɗin yayi suka tafi gida, a fusace ta juya bayan ta ajeshi a kofa ta tafi, shima a fusace ya shiga gida, tana shiga gida tayi wurgi da hulan tuƙin sannan ta wuce zata shiga ɗaki taji fahad yana cewa "to daka Anty ai da ya Abdul sukayi faɗa shiyasa take fushi kuma anjima kaɗan zaki ga sun shirya"
cikin fusata tace "ba zan shirya dashi ba wannan karon na daina mishi magana"
shiga ciki tayi ta kwanta akan gado ta ɓata rai, meyasa ba zai yadda su saida motan daya gama talautasu ba?
tana fushin har dare basu ga juna ba, ta taƙura sosai kamar yadda shima man yake a taƙure sai juyi yake a gado ya kasa samun nutsuwa, ya saba suna waya da dare har suyi bacci amma yau tunda suka dawo bata kara zuwa ba shima kuma baije ba, Imran dake shirin bacci yace "ya man ba zaka iya fushi da Ameesha bafa gara kawai ka kirata"
cikin tsawa yace "kamin shiru zanga me kiranta"
taɓe baki Imran yayi ya saba ganin haka kuma da kansu suke kara shiryawa ya ɗale gado yaja bargo ya rufe har kanshi ya fara bacci, ameesha tana kwance akan gado cikin rigan baccinta ta rufu da blanket sai juye juye take tana kallon wayarta ko zai kira, shiru taga bai kira ba, fahad dake kwance yana rubuta home work nashi yace "Anty meesha ki kirashi kawai nasan ba zaki iya fushi dashi ba"
cikin tsawa tace "kamin shiru zanga me kiranshi yau koya kira zanga me ɗauka"
ɓata rai tayi, har ya gama home work yaja bargo kamar me bacci ya rufe ido, lekawa tayi tana son ganin ko yayi bacci ganin idonshi a rufe ta ɗauka wayan a hankali zata latsa mishi call, shima man leka fuskan Imran yayi ganin yayi bacci ya danna mata call, gani tayi ya rigata kira da sauri ta ɗauka ta kara a kunne, cikin kasa da murya tace "hello?"
shima kasa yayi da murya yace "na kasa bacci"
tace "nima haka"
yace "kiyi hakuri"
itama tace "kayi hakuri kaima bazan iya fushi da kai ba"
shima yace "nima bazan iya ba"
hira suka fara tace "bye good night"
shima yace "good night"
kashe wayan tayi cikin sanɗa ta tashi tasa a caji komawa tayi ta kwanta tana hamdala da fahad bai tashi ba, tana kwanciya yace "ai dama na gaya miki"
waro ido tayi alaman meyasa yaji, sai kuma taja tsaki ta shareshi ta kwanta.
leka Imran yayi ganin yana bacci yace "alhmdllh bai jini ba"
Imran yace "na jika tsaf"
ɓata rai yayi kamar bai taɓa dariya ba, Imran a ranshi yace "cin maganin banza"
washe gari meesha tana tashi da gajeren wandon baccin dake jikinta ta shiga toilet tayi brush kasancewar bata salla yasa batayi alwala ba kawai wanka tayi ta fita, wandon da man ya siya musu kala ɗaya tasa kamar na ƴan ball tasa riga me dogon hanu tayi parking gashinta sannan ta ɗale gadonta zata koma bacci wani abu yace ta hau online, facebook ta hau ta fara searching masu neman ma'aikata, tsaki taja harta gaji zata sauka can taga anyi tagging wata daga cikin friend ɗinta a wani post, bi tayi taga wani post ne, gani tayi an rubuta M.U.M designing company is currently for an exceptionally talented artist to join our design team"
tsalle ta daka akan gadon ta fara tsalle, kallon address ɗin tayi sannan tayi screenshot, numbern wayarsu ta ɗauka atake ta kira, ɗauka akayi "kina magana dame kula da harkokin m.u.m fashion designing dame zamu taimaka miki?"
da sauri tace "naji kuna neman ƙwararren me zane?"
da sauri yace "kwarai kuwa muna nema kuma muna maraba dake idan kin kware"
hawaye taji na farin ciki ya cika mata ido tace "yaushe zaku fara interview?"
yace "yau zamu fara zuwa gobe zamu rufe"
tace "to na gode sosai"
rigan sanyi kawai ta ɗaura akan kayan jikinta ta ɗau makullin mashin da gudu ta fita kamar zata faɗi kasa, Anty tace "ina zajije?"
tana gudu tana sa hulan mashin tace "Man zai samu aiki yau"
fita tayi daga gidan kamar zata kife akan mashin ɗin harta isa gidansu, wurgar da mashin ɗin tayi da mugun karfi take bubbuga kofan gidansu, umma tazo ta buɗe tasan ameesha ce da wannan bugun kawai ta juya ta koma gida, rungumeta ameesha tayi ta baya tana tsalle tace "man zai samu aiki umma"
cikin kwaɓa fuska da gajiyan maganan aikin tace "to Allah yasa"
sakinta tayi ta ruga da gudu zuwa ɗakinsu, knocking take yi da karfi suna bacci su duka da Imran, cikin bacci Imran yayi tsaki yace "wallahi ameesha zata kashemu lokacin mu baiyi ba"
yana buɗe kofan ta rungumeshi kam tana juyi dashi, cikin mamaki yace "meya faru?"
tace "man zai samu aiki yau"
sakinshi tayi yaja tsaki a ranshi sabida yasan rashin sa'ansu a fili kuma yayi murmushi yace "to Allah dai yasa"
kallon man wanda yake bacci peacefully tayi, da gudu ta faɗa kanshi buɗe ido yayi da sauri yana kallonta, dariya take yi cikin farin ciki tana rungumeshi kamar zata shiga jikinshi, cikin baccin da ba isheshi ba ya motsa karamin bakinshi yace "what?"
kiss yaji tayi mishi a baki abinda bata taɓa yimishi ba saide a gefen kumatu ko kuma a goshi, Imran ya rufe ido, zamewa tayi cikin murna tace "yau zaka samu aiki"
runtse ido yayi jin yauma maganan aiki ne kamar kullum, tashi yayi yana sauketa yace "sauka"
sauka tayi amma bata zame kafafunta daga jikinshi ba tana kusa dashi sosai ta buɗe wayarta ta nuna mishi, wani irin smiling yayi ganin da gaske ne, rungumeta yayi ya ɗagata sama yana juyi da ita a cikin ɗakin, dariya takeyi, ajeta yayi a kasa yace "thank god"
umma dake tsaye a bakin kofa tace "wai kunje kun samu aikin ne kuke wannan murnan?"
ameesha tace "no amma zai samu sabida nasan ya kware"
man ya shiga toilet da sauri yayi wanka ya fito, ameesha ce ta ɗauko rigan yana shafa mai tana sa mishi, Imran yace "to Allah yasa a samu wannan aikin ko zamu fara baccin safe cikin nutsuwa"
yana gama shiri suka rike hanu atare suka fita, akan mashin nata suka tafi ta fara gudun da bata taɓa yi dasu ba sabida kada suyi late, sunyi sa'a suna zuwa mutane sun gama taruwa amma basu fara Interview ba, gefe taje zatayi parking mashin shi kuma Man ya fara tafiya a hankali yana jiran ta iso, ji yayi an kusa bigeshi da mota da ihu ameesha ta dafa kirji tareda waro manyan idanunta tace "maaaaan!!!!"
rufe ido tayi shima ya rufe ido, da kyar ta tsayar da motan bata bigeshi ba, parking tayi a hankali tasa kafanta dake sanye da high hill red, fitowa tayi tana fito kamar kullum tana taku cikin isa da gadara, jan dogon riga ne a jikinta yana da tsayi yana sharan kasa bayan gaban kuma guntu tasa mayafi akan gashinta daya bayyana har hips nata, Ameesha bakinta a buɗe tana kallonta dan ba karamin kyau tayi ba gashi tana tafiya cike da class, a gaban man ta tsaya tana cigaba da yin fito ta kalleshi from head to toe sannan ta buɗe baki kamar batason magana tace "kai makaho ne ko kurma?"
shiru yayi yana kallon cikin idonta kamar yadda itama take kallon nashi, tace "useless ka rinƙa kallon hanya idan kana tafiya kada watarana na bigeka"
wucewa tayi tana fito tana tafiya kamar ɗawisu, shima fito yayi sau ɗaya, juyowa tayi tana kallonshi, signal yayi mata sannan ya fara karkaɗa makullinta dake hanunshi, da mamaki ta kalleshi "ya akayi makullinta yaje hanunshi?"
zuwa yayi gabanta ya tsaya yana kallon cikin idonta yace "ke makauniya ce ko kurma?"
matsawa tayi baya ganin yadda yake kallonta, wurga mata makullin yayi a sama, cafkewa tayi yace "ki rinƙa kula da kanki idan kina tafiya domin kada watarana nayi miki sata"
a fusace ta juya bata mishi magana ba ta shiga ciki kamar zata tashi sama tsaban ɓacin rai, duk suna ganinta suka tashi, sai a lokacin Ameesha tayi hamdala tace "ya Allah har raina ya tsinke"
zuwa tayi ta rikeshi tace "ka rinƙa kula raina ya tsinke wallahi"
yana rike da ita yana fito shima suka shiga ciki, aka kujeran da taga an bawa mutane suka zauna, hanunta a cikin nashi suna jiran layi yazo kansu, manal zaune take akan kujera tana kallon duk waɗanda suke wajen a cikin computer dake gabanta, idonta akansu ameesha wacce suke rike da hanun juna, komawa baya tayi da kujeranta tana kallon duk masu shigowa, duk cikinsu bataga wanda ya kware ba, Ameesha ta gaji sosai domin suna jimawa kafin su fito, ga ciwon cikin da takeji yana damunta sabida tana period, ɗaura kanta tayi a kafaɗanshi ta fara bacci a hankali yace "ko dai zamu tafi naga kamar baki da lafiya"
tace "ina lafiya bacci kawai nake ji"
yace "to yi bacci kafin azo kanmu"
bacci ta fara a hankali yayi shiru yana jin numfashinta a jikinshi, a hankali ya rike hanunta sosai dake cikin nashi, sun kara jimawa sosai kafin akace su shigo, tashinta yayi da sauri ta buɗe ido yace "muje an kiramu"
kallon time tayi a agogon hanunta tace "mun jima sosai"
hanunta ya rike zasu shiga, manal dake juyi akan kujera tana kallonsu har ya tsaya yana gyarawa ameesha hulan rigan sanyinta zasu shiga tace "kuce an tashi sai gobe kuma"
hanu yasa akan handle ɗin akace "an tashi sai gobe kuma"
ranshi ne yayi mugun ɓaci zaiyi magana ameesha ta rike mishi hanu tareda girgiza mishi kai alaman yayi hakuri, shiru yayi taja hanunshi suka tafi, basuyi magana ba har suka isa gida, rai ɓace ya wuce ɗaki umma tana ganin yanayin ameesha tace "to yauma haka"
Imran kam ɗauke kai yayi baima yi magana ba, ɗakin ta shiga ya kwanta akan gado ya juya baya, zama tayi a kasa ta ɗaura kanta a gefenshi tayi shiru, a hankali ya juyo ya shafa gefen fuskanta yace "karki damu na miki alkawari gobe zamu koma"
murmushi yaga tayi wanda yake burin ganin tana yinshi a kullum tace "ka tabbata?"
yace "eh"
ya faɗi haka ne dan yasan da kyar yau tayi bacci zataga kamar ya fasa zuwa tasan halinshi, tashi tayi tace "to shikenan bari naje nasha magani cikina na ciwo"
zai rakata tace "no koma ka kwanta ka huta"
yace "bye"
fita tayi ya lumshe ido, ameesha itace rabin rayuwarshi.
washe gari tana jin ciwon ciki amma ta daure tazo tana hon a kofan gidan tana kiranshi kamar yadda ta saba "MAAAAAAAAN"
gani tayi ya fito rataye da jakan takaddun a bayanshi da sauri yazo ya hau mashin ɗin suka tafi, tace "good morning"
yace "morning princess ya jikin?"
tace "da sauki"
yace "har kin kai fahad school?"
tace "yes gashi har na dawo kanata baccinka"
yace "gaskiya meesha ina ganin kokarinki bakya bacci kullum ɗawainiya kede sai kinga kowa yayi successful hankalinki yake kwanciya"
tayi murmushi kawai, Allah yasa basuyi late ba, suna shiga suka zauna akan kujera ta jarɓi jakan takaddun ta rungume, karan takalminta sukaji kowa ya tashi daga zaunen da yake itama ameesha ganin kowa ya tashi ta tashi, lokacin manal ta shigo tana waina makulli a hanunta, idonta ya sauka kan man wanda yake gyangyaɗi baima san ta shigo ba, cikin tsoro ameesha ganin ta zubawa man ido ta fara janshi alaman ya tashi, buɗe ido yayi yace "me kina jana?"
idonshi ya sauka kan manal wacce take aika mishi mugun kallo tana huci, ameesha tace "tashi"
a hankali ya tashi, wucewa tayi bata amsa gaisuwan kowa ba, saida ta wuce suka zauna, akan kujera ta zauna tana tuna wani irin abu zatayi mishi yaji zafin da taji lokacin data ganshi a zaune? ta nuna mishi ita ɗin wacece?"
kallonsu take ta cikin laptop ɗin har ta fara kiran interview, saida akazo kansu sannan tace an tashi sai gobe, cikin fusata ya dunƙule hanu zai buɗe kofan ameesha ta fara janshi, da kyar ta lallaɓashi suka fita, gani yayi tana hawaye yaji jikinshi yayi sanyi, yace "kar kiyi kuka gobe zamu dawo kinji?"
gyaɗa kai tayi, dama tayi kukan ne sabida tasan dole zai karaya bayason ganin tana kuka.
*Jiddah Ce...*
08144818849
managarciya