HAUSA FILM:MI YA SA DATTAWAN DA SUKE SANA'AR SUKE ƘORAFIN BA SA SAMUN KOMAI

HAUSA FILM:MI YA SA DATTAWAN DA SUKE SANA'AR SUKE ƘORAFIN BA SA SAMUN KOMAI
Ra'ayin Jamilu Sama'ila Dandana
Nadaɗe inajin Mutane suna zargi, Tare da ƙorafin yadda Dattawan maza da mata  da suke sana'ar wasan kwaikwayon hausa suke kamar kisan ƙadangaren yara (Inda suke nan suke).
Babu shakka akwai takaici, sannan ba kowane mai ƙarfin Zuciya ba ne, zai kasa zargin Cewar; ana yiwa Dattawan cikinsu rashin adalci, Kokuma Ƴan matan suna fakewa da sana'ar suna wata sana'ar, (sana'a cikin sana'a).
Batu na adalci, Kowa yanada gaskiya akan batun, su masu kallo, da Kuma masu shirya finafinan (Producers, director) domin ana biyan Aikin ne a yadda na fahimta, wasu ana la'akari da yawan fitowar su, Wasu kuma ana Duba yadda tauraron su ke haskawa, yadda ana Nuna fuskarsu Film Zai karɓu kaitsaye.
Mafi yawan tsofaffi dake yin Film, da wahala kaga su ne suke jan ragamar Film kacokan, Amma Yan matan zaka samu su ne suke jan ragamar Film baki ɗaya, wanda idan a Film aka yi fitowa, Kamar 50 zaka samesu a samada guda 25, kaga Dole a bambanta Wajen biyan su da wanda zaiyi fitowa Biyar.
Abinda masu Kallo suke suke kallo, yadda zaka ga yarinya idan tanada fuska mai kyau, zaka ga da wuri ta samu kudi,mota, waya Mai tsada. Shima abin dubawa ne, Amma Maganar gaskiya, wasu suna yin Wasu harkokin bayan Film, Wanda masu sana'ar basuda ikon hanasu, amma wasu suna yin tallace tallace ne suke samun kudin.
Abinda Yakamata Anan shine; su masu shirya finafinai su ringa la'akari da nauyin dake Bisa tsofaffin, su ringa yimusu  biya, yadda Zasu ringa biyawa kansu buƙatu nayau da kullum. Su daina la'akari da yawan fitowa, da kuma yadda suke haskawa a lokacin.
Amma maganar gaskiya akwia gyara kwarai dagaske, domin anayin wasu abuwa na rashin kyautawa musamman su yanmatan. Manyan su ringa tsawatar musu, ta Hanyar shaidawa iyayensu haƙiƙanin abinda suke samu, idan anga bakon abu su binciki ya'yan su.