Na fara ganin nasarar shiga harkar fim -- Amina A. Shehu

Na fara ganin nasarar shiga harkar fim -- Amina A. Shehu

Amina A. Shehu, sabuwar jarumar fim a masana'antar Kannywood wacce ta sha alwashin samun nasara a burin da ta ke so ta cimma game da shigowar ta wannan masana’anta nan ba da jimawa ba.

A cewar ta, a yanzu har ta fara ganin hasken cikar burin nata.

Tun da farko, a tattaunawar ta da mujallar Fim, jarumar ta bayyana cewa ita haifaffiyar garin Zariya ce, inda a nan ta yi makarantar firamare, sai kuma ta yi sakandare a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Daga nan ta dawo Kano domin ta shiga harkar fim gadan-gadan.

Amina ƴar kimanin shekara 23, ta ce, “A lokacin da zan shiga fim sai na zo Kano, da man akwai gidan ‘yan’uwa na a nan, don haka sai na dawo gidan da zama to da haka na samu na shiga harkar fim ɗin.”

Ta ƙara da cewa, “A shekarar 2018 na shiga harkar fim, kuma daga lokacin zuwa yanzu na yi finafinai da dama.

Amma dai waɗanda zan iya tuna sunan su akwai ‘Gidan Danja’, ‘Gidan Mato’ ‘Wata Makauniya’, da sauran su.”