Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 13
Ciwon ciki sai gaba, yake na rasa Uwa mahaifiyata, ba zato ba tsammani naji wani irin kashi ya taho min, cikin dauriyar gaske na nufi waje da nufin ko tsakar gida nayi shi gobe na kwashe, don ban iya zuwa har toilet ɗin kashin. Sai kuma wata dabarar ta zo mun na saƙa hannu gefen kujera na ɗauko baƙar leda na rarrafa na fita waje. Sai kuma tsugunnin ya gagara, dana tsugunna da zummar yin kashin sai naji wani uban nishi ya taho min, sai na daina yunƙurin kashin. Ina haka naji surutun mutane, ashe gidansu ya je ya taho da kishiyoyin Mamarsa. Ɗaki ya shige ko sannu bai min ba, su ne suka kama ni muka shiga ɗaki suna jera min sannu wata kan wata. Shiru-shiru ba haihuwa ba alamar ta sai ɗan karen shan wahalar da nake, ganin hakan yasa ɗaya daga cikinsu tace gaskiya a samo mota a kaini asibiti tunda abin ya ƙi hannu. Shi dai Deeni yana cikin ƙuryar ɗaki bai ce min sannu ba ko sau ɗaya, ganin suna ta maganar ya fito ya samo motar kaini asibiti ya ƙi guda daga cikinsu ta leƙa ɗakin. Salati ta kamayi tana tafa hannuwa tana cewa, "Yau ni Asabe naga ikon Allah! Matarka na halin naƙuda kai kuma ka kama kanata barci? Kai Deeni me ke damunka ne haka kamar dai wanda bai da tausayi?" Ni dai abin da ya ishe ni ya ishe ni don haka nace masu, "Don Allah ku kama ni mu tai asibitin haka nan a ƙasa indai zan haihu na daina jin ciwon nan don Allah." Dukkansu sai suka tasa ni gaba suna jera min sannu amma Deeni yana ta barci ya ƙi fitowa ya samo motar da za a kaini asibiti. Ganin dai abin da gaske yasa guda ta fice zuwa gidan maƙwabcinmu ta buga, cikin ikon Allah yana gari tun da aiki yake zuwa wani gari ba ko da yaushe yake kwana gida ba. Ya fito ta nemi alfarmar ya taimaka ya kaini asibiti haihuwa tayi gardama, cikin azama ya fito da motar yana ta addu'ar Allah Ya raba lafiya.
Deeni na cikin ɗaki muka nufi asibiti bai leƙo ba balle ya ji wane asibiti za a kaini .
Ina jinsu a mota suna ta faɗan halin Deeni bai da kyau mutum kamar bai da zuciya a jikinsa, ace matarka na a wannan yanayin amma kai ko a jikinka? Ni kam addu'a nake yanzu Allah Yasa ajalina ne ya zo ta haka kowa ma ya huta nima na huta da ƙangin da nake ciki kawai.
Muna zuwa aka rubuta abubuwan da ake buƙata aka ce a nemo da sauri, amma ga alama cikinsu babu mai ko sisi ko da yake ko akwai ma ai basu ne ke da alhakin badawa ba, don haka su ka amshi takardar su kai shiru kowacce ta kasa cewa komai. Sai maƙwabcinmu ne ya amsa ya tafi ya siyo ya kawo yace ba a samu guda uku ba ciki ance ana samunsu a nan cikin asibitin don haka su amso can, ya yi min fatan alheri Ya tafi yana jaddada Allah Yasa a rabu lafiya. To su kuma ko ɗauka su kai ya je can ya biya kuɗin guda ukun kamar yadda ya biya sauran magungunan da alluran daya kawo ? Sai suka je kawai suka amso su ka bada zuwa lokacin an kai ni can cikin ɗakin masu haihuwa, na fara fita hayyacina sai make-make nake tamkar zance ga garinku.
Likitan ne ya kira wanda suka kawo ta yace "Jininta ya yi matuƙar hawa, don haka ba zata iya haihuwa ba, ga shi abin da ke cikin nata ƙoƙarin fitowa. Yanzu sai dai ai mata aiki kawai a fito da abin da ke cikin, idan ba haka ba za a iya rasa ta a rasa abin da ke cikin cikinta."
Su duka suka ɗauki Salati suna jinjina maganar, "To yanzu Likita ya za ai kenan?" Cewar guda daga cikinsu.
"Muna buƙatar mijinta ya saka hannu ko wani na kusa da ita sosai sai a shigar da ita ɗakin aikin gaggawa a fito da babyn."
"To Likita ai mijinta na gida, yanzu haka mu kishiyoyin Mamarsa ne, ya kira mu yace zata haihu a gida, to ganin tana ta wahala ne yasa muka kawo ta nan shi bai zo bama."
Cike da mamaki Likitan ya maimaita kalmar mijinta na gida. Wata nurse ce ta fito da sauri tana kiran "Doctor ta haihu yanzun." Bai saurari komai ba ya wuce gun ta don yaga a yanayin da take ciki.
Iyakar tausayi yarinyar ta ba shi tausai gata ƙarama ga ciwon hawan jini ya yi mata kamun gaske. Yaro namiji ne ta haifa ya dudduba ta ya taimaka mata da allurai ya tabbatar da bata cikin hatsari sannan ya fice, ya bar nurse na gyara ta da babyn.
Bayan an kammala komai ne aka miƙa masu yaron ni dai ban iya tuna komai, kawai dai gani kwance kaina na mugun ciwo jikina ba ƙarfi ko kaɗan.
Ɗakin hutu aka kaini don ƙara tabbatar da yanayin jikina, domin Likitan yace hawan jini gare ni, kuma irin wanda ke yin ƙasa ne ba sama ba, yace yafi haɗari irinsa sosai, dole sai na dinga kiyaye abubuwa da yawa don kare lafiyata.
Wata nurse ta leƙo tace a bada kuɗin allurai guda uku da suka amso gunsu kafin na haihu. Nan fa su kai shiru, da ƙyar guda tace " Sai mijinta ya zo zai bada yana hanya."
Shiru-shiru ba Deeni ba labarin Deeni har nayi awa biyu da haihuwa su kuma ba kuɗin da za su biya na allurar, don haka ban san ya akai ba naga sun tashi sun ce min "Jiddah bari mu je can gida mu gaya masu, har Deenin ma sai a gaya mai." Suka goya yaron suka tafi suka bar ni kwance yunwa na damuna bakina kamar ya ƙafe don ƙishirwa.
Tunda suka tafi basu dawo ba haka ba wanda ya zo ga nurse ɗin nan bata da mutunci sai masifa take kar a gudun masu da kuɗi,abin duk ya taru ya yi min yawa.
Na haihu ko fuskar yaron ban gani ba, ga yunwa, ga ƙishirwa, sannan an barni kan gadon asibiti da bashin da ban san ko nawa bane ba.
Mutane nata shigowa gaida marassa lafiya nan wata ƙawar Mamana ta ganni kwance ta iso gadona tana min ya jiki ta tambayeni yadda akai.
Na gaya mata sun je da abin da aka haifa gida tun ɗazun basu dawo ba su nake jira mu tafi tare.
Nurse ɗin nan ce ta dawo tana ta masifar duk abin da nake tana kallona ba zan gudar masu da kuɗi ba.
Kawar Mama ce ta dube ta tace, "Ke kam baiwar Allah kuɗin har nawa ne da kike ta wannan masifar? Kuma ita miye nata a ciki ba kawo ta akai ba?"
Nurse ta taɓe bakinta tace, "Ai dole nayi masifa Naira ɗari tara ne da talatin kuɗin, kin ga kau ba nayi shiru ba a wuce da su ba." Zaninta ta kwance ta fito da Naira dubu ta bata, "Ga shi ban canji, Allah Ya sawwaƙe." Ta amsa tana "Amin dai."
Waje ta fita ta siyomin taliya da ruwa, na kuwa cinye ta tas, sai naji ciwon kan ya rage har ina iya tashi. Ganin hakan yasa tace "Daurewa za ki yi mu isa can gidansu mijin naki Jiddah? Sai na kai ki na je na sanarwa da Innarki halin da ake ciki." Na ji daɗi, domin zaman asibitin ya ishe ni sosai.
A ƙasa muka tafi gidan, domin babu masu mota, Ni kuma ban iya hawa mashin saboda ciwon kaina ga marata na juyawa lokaci zuwa lokaci. Da muka isa gidan har an ma yaro wanka an goye shi , suna ta hidimar su kamar ba a bar kowa asibiti ba watau ni Jiddah uwar yaron.
Suna ganinmu sukai ta irin abin nan na jin kunya, nan da nan aka ɗora ruwan wanka aka zubomin tuwo.
Ita kuma ta wuce don isar ma Mamata sauƙon haihuwar.
Sai da nayi wanka na fito na gyara jikina don ma naga ban zubar da jini sosai, ko da yake mi na ci wanda zai sa na samu jini mai yawa a jikina? Babbar Yayarsu ce ta goya yaron muka tafi gida har zuwa lokacin ban saka Deeni a cikin idanuna ba. Muna zuwa muka iske gidan a buɗe, ga wuta na ci alamar girki Deeni ke yi, yadda na bi shi da kallo haka ya bini da kallo yaron kawai ya amsa ba tare da yace komai ba.
Ni dai kwanciya nai ma, don na gaji sosai kamar an mun dukan tsiya haka nake jin baki ɗaya jikina.
Sallamar dangin mahaifiyata naji sun shigo da yawansu suna ta fara'a da jera min sannu ba iyaka. Bokiti ne riƙe a hannun ƙanwar Mamarmu cike da kunun kanwa sai ƙamshi yake. Ko ba ace daga Mama ba nasan ita ce ta damo min shi.
Ai kuwa naji daɗin kunun sosai, domin na lura tunda na haihu motsi kaɗan sai in ji cikina babu komai yunwa na neman zautani. Duk abin nan sai lokacin Yayar Deeni ta amso yaron a hannunsa ta kai masu, shi kuma ya fito ba kunya ba komai ya juye taliyar da ya dafa ya koma ɗaki, sai su ne ma suka dinga gaida shi suna yi ma shi barka an samu ƙaruwa. Yana gama cin abincinsa ya fito ya bar gidan ba tare da ko kalma guda ta shiga tsakanina da shi ba balle ya sammun taliyar daya dafa.
Ƙanwar Mamarmu ta kira ni cikin ɗaki daga ni sai ita tace, "Innarki tace a tambayeki kuna da kayan abinci? Kuma akwai kuɗi gunki? Kina da kayan da yaron zai sa?" Kaina ƙasa nace "Babu komai gidan Inna."
Nan tabar ni ta fice ina jin lokacin da take ce ma sauran zata je ta dawo.
Bata jima ba ta dawo da kayan abinci masu dama ba laifi ta kawo kuɗi Naira dubu uku taban tace ki riƙe kafin suna ki dinga yin cefane da sauran abubuwa da ake buƙata." Kasa magana nayi saboda tsabar jin daɗin kayan abincin nan, domin na lura Deeni bai sauko ba, babu ruwansa da haihuwar da akai cigaba da halinsa zai ko a gaban mutane .
Matan unguwa suka cika gidan, Allah Ya rufamin asiri kayan abincin da aka kawo min daga gun Mama aka ɗebo shinkafa aka gyara aka dafa, nan da nan aka auni gero aka niƙo shi aka ɗora ruwan damun kunu. Dare nayi kowa ya watse aka barni da Yayar mahaifiyata ta zauna min kamar yadda ake yi a al'ada haihuwar farko ana kai tsohuwar da zatai zaman ɗaki har na tsawon kwana bakwai, idan mai jego bata koma gida wankan jego ba kenan.
Muna zaune muna ta fira Deeni ya shigo an ci sa'a ya yi sallama Yau, ya shige ɗaki mun ɗauka kayansa zai ɗauka ya fice tunda yaga Inna kuma yasan nan zata kwana tunda har goman dare ta gota. Ai sai kawai mu ka jiyo tashin waƙa na tashi daga cikin ɗakin alamar ya kwanta ma shi.
Bata ce komai ba, tace na samo mata zani ta kwana nan falon, ganin rashin kunyar Deeni tai yawa yasa nima na shimfiɗa zanin gado muka kwana nan duk da ta dage sai na je ɗaki na kwana na ƙi. Haka mu kai ta kwana falo Deeni na kwana ɗaki yana kunna waƙa kullum har barci ya ɗauke shi sai ya farka ya kashe. Da safe kuma idan ba ita ce ta fara gaida shi ba sam bai gaidata.
Nasha zuwa gidajen barka cikin unguwarmu naga an kawo ma mai jego naman ƙan baki, har mu ƴan zaman barka mu ci, amma ni ko kan kifi Deeni bai siyo ya kawo min ba, ko da yake abincin ma bai badawa sai dai da rana ya aiko yaro ya amsar mai abinci da kunu kullum haka yake. Inna tai ta faɗa ni dai ban cewa komai, sai idan abin ya dameni na shige kewaye naci kukana na fito.
Har ga Allah so nake na ci abu mai daɗi amma ban da yadda zan yi, kuɗin da aka kawo min ma sun ƙare Yau daren suna tun da safe da ƙyar suka isa mu kai kalaci.
Ranar daren suna mutane su ka cika gidan suna jiran a fito masu da kayan miya da garin tuwo su rage aiki kamar dai yadda ake yi kowane gidan daren suna amma babu alamar Deeni zai kawo ko ruwan sha a gidan balle kayan abincin suna.
Har zuwa lokacin babu mutun guda da ya zo daga dangin mahaifina kuma a gari guda muke da su amma ba wanda ya zo min barka. Ko da yake shi kanshi Babana ance min yana garin amma bai zo ba, don haka ban ga laifin danginsa ba da basu zo ba.
Tunda na shiga wankan yamma na shige cikin robar wankan na fashe da kuka ina addu'ar Allah Ya fitar da ni daga wannan kunyar da Deeni ke neman saka Ni. Gida cike da mutane amma babu abin da za su yi aikin abincin gobe na suna. Wannan wane irin bala'i ne haka? Sai da Inna tayi da gaske ta fito dani daga kewayen Yau dai ita kanta ina lura da yadda take kallona tana share hawayenta a ɓoye.
Muna zaune mun yi zugudum naji sallamar Safiya, tun da na haihu bata zo ba, ko da yake ba mamaki sai Yau ta dawo daga unguwar da ta je. Muka gaisa ta ɗauki jariri tana ta yaba kyan shi, anan ne ma naji sunan yaron daga bakinta Deeni ya gaya mata sunansa Al'ameen, nace Allah Ya raya min shi a raina.
Bayan ta fice Binta ta shigo da Naira dubu taban tace, "In ji mijinta yace na ɗauki ɗari biyar naba Deeni ɗari biyar."
Ba ƙaramin daɗin kuɗin nan naji ba wallahi kamar an saka ni aljannah haka naji.
Muna a haka ya shigo na je na same shi yana ta cika yana batsewa na gaya mai an bamu kuɗi amma don Allah ya amsa ya siyo min kayan miya da su domin Inna tace daga can gida za a kawo min garin da za ai tuwo da fate gobe.
Wani banzan kallo ya bini da shi yace, "Dilla ban kuɗina, kuma ki sani sai kin ban kuɗin mashin sannan zan je siyo maki kayan miyar idan ba haka ba sai dai ki nemi wani ba dai Ni ba. Kuma da da ki yi abin arziƙi ma da kin bar min ɗari biyar ɗinki domin nasan ke gobe cikin kuɗi kike."
Baki buɗe nake kallon shi na rasa abin cewa.
Ikon Allah! Ku dai biyo Haupha don jin shin zata ba shi kuɗin ya haɗa duka ne koko zata hana shi?
Daga taku a kullum Haupha!!!