MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta Sha Biyu 

MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta Sha Biyu 

*HAUWAU SALISU*

 *Shafi na biyu.*

 

Cikin matuƙar tsoro Bilkisu ta nufi ƙofar ɗakinsu jikinta na karkarwa saboda Allah ya zuba ma ta tsoro na gaske.

 

Hannu ta kai da nufin yaye labulen ɗakin, bakinta ɗauke da bisimillah.

 

Cikin halin tsoron ta buɗe ɗakin ta kunna fuskarta waje da nufin ta ga mai wannan tafiya cikin talatainin daren nan .

 

Daidai lokacin wani ɓakin kare ne tsaye halshensa waje bakinsa na feshin baƙin jini , haƙoransa kafta_kafta a waje yana cin wani jan nama mai kama da naman mutum.

 

Ƙara laiƙawa tayi wannan karon bakinta ɗauke da A'uzubillahi minasshaiɗanirrajim.

Wannan neman tsarin da tayi shine sanadin da karen ya ɓace bat batare da ta ganshiba ,amma still tana jin ƙarai tafiya da takalmi mai tsini nesa kaɗan da ɗakinsu.

Duk da tsoron Bilkisu akwaita da son ganin ƙwab in dai zata ji motsi to burinta ta ga abin da ke motsin,hakan yasata dinga bin inda take jin motsin amma Allah bai bata ikon ganin abin da ke motsinba sam.

 

Ganin bata kula da shiba yasa ya bayyana bayanta cikin mummunar kama , bakinsa wangame baƙaƙen tsutsoci na tittiɗowa daga cikin bakinsa , hannuwansa sun koma hawa biyar kowane hannu akwai  kan mace mai suffar Bilkisu riƙe tana kuka ga hawayen jini na zubowa, jikinsa tamkar na kada duk da dare ne zaka iya hango yanda yake da kaushi ,ga wasu baƙaƙen ƙwari manya dake yawo daɓa_daɓa akan jikinsa.

Gaba ɗaya yayi mata rumfa ta bayanta wanda tana jiyuwa ba abin da zai hana jikinsu haɗuwa.

Kamar a mafarki taji ana kiranta ta bayanta."Bilkisu ,, "Bilkisu,,

Jin muryar tayi bata san mai itaba ,dan haka cikin sauri ta buɗe baki da nufin ansawa taji bakin nata yaƙi furta koda kalma ɗaya ce balle ta samu damar amsa kiran da ake ta kwaɗa mata da karfi cikin sauri kuma.

 

Cikin zuciyarta ta fara karanto addu'ar neman tsari .

 

Ɗuf taji komi ya dakata an daina ambatar sunanta ,da motsi da ƙarai takalma duk sun dauke .

 

Ajiyar zuciya tayi mai sauti ta nufi ɗakinsu da sauri tana jin miya fito da itama wai ?

 

Sai dai me ? Tana zuwa ƙofar dakin da niyyar shiga ta jishi rufe alamar an saka kuba (sakata)  daga cikinsa.

Mamaki ƙarara a fuskarta dan tasan ɗakin daga ita sai ƙannenta waɗanda sun jima da barci , to waye ya rufe dakin bayan fitowar ta ?

 

Cikin wani tsoron ta fara bubbuga kofar ɗakin jikinta ba inda bai rawa ga fuskar idanun malam Aminu (Dan_bahago)take gani tsab a idanunta ,tamkar shine tsaye gabanta.

 

Innarta ta fara jiyo tamkar ana bubbuga kofar ɗaki dan haka ta yunƙura ta fito dan ganin wake bubbuga kofar ɗaki yanzu cikin tsakiyar dare ?

 

Bilkisu da har ta fara gajiya da buga ƙofar ɗakin ta fara zubar da ƙwalla ta ji fitowar Innarsu daga nata ɗakin tana ambatar waye nan ?

 

Cikin damuwa ta buɗe baki da nufin gayama Innarsu abin da ya faru , sai taji ta kasa fadin gaskiyar abin ta ce "Inna daga na fito inyi bowali (fitsari)shinefa sakata ta shige inaga gun jan ɗakin ne da zan fito,,

Innarsu ta fito tana kakkabin abin kasancewar ta mace mai faɗa .

"Badai jawowar hankali kikai ba ta tsiya kikai ƴar nan kinji ,,

 

Ta iso tana mitar batasan sanda Bilkisu zatai hankali ba.

 

Abin mamaki tana tura ɗakin ya buɗe , ai sai ta balbale Bilkisu da faɗan rashin natsuwa yasa ta kasa gane ƙofar buɗe take ma ashe .

 

Ita dai Bilkisu sanin halin faɗan Innarsu yasata shigewa ɗakin bakinta alaikum.

Jiyuwar da Inna zatai taga tamkar wani guntun jan mutum mai jan gemu na ma ta dariya yayi sama .

 

Bata sake magana ba balle ci gaba da faɗan da take ta afka nasu ɗakin tana haki ta samu ta haye gado ta ja bargo ta ƙudundune tai ɗuf.

Sai dai me, tana natsuwa ta fara jin tamkar ba bargone ta lullube dashi ba , tamkar wani gashine wanda ita dai tasan ba da gashin mutum zata kwatanta shiba ,ai kuwa Inna ta wage baki da nufin kwarma ihu ta ji an matse bakin wani ɗan firit din mutum ya kalleta ya tintsire da dariya yace "kina ihu zan tafi dake , faɗanki ya tadamin jinjirai maza ki koma barci ja'ira mini_mini daku sai tujara,,

 

Kadan ya hana numfashin ta ɗaukewar wucin gadi.

 

Bat guntun mutumin ya ɓace .

 

 

Tun da asuba Bilkisu ta tada ƙannenta dan suyi sallar asuba ,jin bata ji motsin Innarsu ba yasata zuwa ta bubbuga mata ƙofa dan Babansu bai nan balle ya tadata karta makara .

 

Inna da tun da guntun mutumin ya ɓace take jinta tamkar mai mafarki kuma ta kasa koda motsin kirki ta jiyo bugun kofar ɗakinta , sai ta samu kanta da tashi firgigit tamkar wadda tai wani mummunan mafarki haka taji jikinta .

 

 

Bilkisu tayi mamakin yanda ta ga Innarsu a firgice tamkar ba itaba , tasan lafiya_lafiya da yanzu ta fara mitar lafiya tai mata tsaye kofar ɗaki ?

Cikin sanyin jiki tace "Innarmu lafiya kike kuwa ?

Kai ta ɗaga mata kawai ta wuce ta , sai taji duk ba daɗi yanda Innarsu ta sauya kamar ba ita ba sam .

 

Haka dai ta samu tai aikin da take kullum sai shirin zuwa makarantar boko ,kasancewar yau monday ita suke fara zuwa karfe biyu su dawo ukku su tafi islamiyya .

 

Babu abin da bataiba amma Innarsu tace ta dakata karta fita sai ta gyara ɗakunan barcinsu sannan ta wuce .

Sanin halin faɗan Innarsu yasa ta gyara ɗakunan ta fito harta makara amma Innarsu tace sai ta share banɗaki (  toilet)Wai wari ya ke yi . Tamkar zatai kuka haka ta share time din ta gama makara ta wuce jiki sanyi ƙalau dan bata gama wartsake dukan jiya ba ga wani Innarsu ta ja ma ta yauma.

 

New day secondary School Funtua itace makarantarsu tana ss one yanzu , tun daga nesa ta hango ƴan makara birjit suna tsince_tsince a filin makarantar ba ƙaramin jin daɗin hakan taiba .

 

Tana isa gun ta ga wani baƙuwar fuska ya sallami ƴan makarai sun tafi class ita kuma ya dakatar da ita ,

Kwatsam taji ya daka ma ta tsawa "why are you coming late ?

Ɗagowa tayi da nufin bashi amsa , take jikinta ya ɗauki kyarma bakinta ya furta Hassibinallahu_wani'mal_wakim,,

Ganin idonsa tayi ya koma tamkar na malam Aminu (Ɗan_bahago)babu ɗigon fari ko kaɗan a idanunsa ,

Tana rufe bakinta daga addu'ar da tayi yasake daka mata tsawa "move away from there Malama,,

 

Kamar jiransa take ta watsa da gudu ,har ta ɗanyi nisa ta jiyo sai taga ita yake kallo yanzu idanunsa fari tas ba ɗigon ɓaki ko daya .

 

Daƙuwa yayi ma ta yace "kin da ke tsira Bilkisu mu haɗu wani karon ,,

 

Kaf babu kalmar da bata je kunnen ta ba duk da tazarai su.

 

 

Kudai biyoni dan jin miye ke bibiyar Bilkisu ?

 

 

Haupha ce!!!