DUHU DA HASKE: Fita ta 38

DUHU DA HASKE: Fita ta 38

DUHU DA HASKE: 


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 38*


                 ~Office sukaje sunyi manyan baƙi zama yayi suna meeting cikin nutsuwa yake magana yana nuna musu yadda zasuyi aikin tare, sun gamsu sosai da bayananshi kuma sun yadda sun sa hannun jari a company ɗinsu, wayanshi ne ya fara ringing ɗauka yayi cikin ladabi yace "ina wuni Abba"
Abba yace "lafiya lau kana inane man?"
yace "ina company"
yace "okay yazeed fa?"
yace "yana gida"
"to dama sako za'a karɓa min zan kirashi"
yace "Abba zan iya zuwa ai na karɓa maka"
Abba yayi saurin cewa "a,a karka katse aikinka ina fatan ba matsala ko?"
yace "ba komai Abba"
"masha Allah, ubangiji yayi maka albarka"
ya amsa da ameen, lumshe ido yayi bayan Abba ya katse wayan wani farin ciki yake ji da nutsuwa a duk lokacin da abba yasa mishi albarka sai yaji kamar an bashi kyautan aljanna, wayan ameesha ya kira tana falo tareda ammi tana tsefe mata kananan kitson dake kanta wanda manal ce tayi mata, ammi tace "ƙafan naki baya ciwo sosai kam?"
tana zaune a gaban ammi tace "a,a baya ciwo"
ammi tace "to masha Allah, zaiyi sauki a hankali"
cikin shagwaɓa tace "ammi tsifan fa yana min zafi"
tsaki ammi taja tace "to bazan daina ba yau idan kinga na saki kanki to saide idan na gama wannan tsifan kina mace amma kina kin tsifa haka"
tace "to ammi ke zakimin kitso?"
tace "idan ban miki kitso ba wa zan yiwa kitso ameesha?"
murmushi tayi hanan dake chatting da ya faruk tace "ni mana ammi"
hararan wasa tayi mata tace "keda kike chat ko magana bakison yi"
aje wayan tayi tace "to na daina"
hira sukeyi gwanin ban sha'awa idan ka shigo zaka rantse itace ta haifesu, Imran ne yayi sallama hanan dake kwance ta kalleshi yayi kyau cikin orange na riga da wando baƙi yasa p-cap yana shiga ya cire p-cap ɗin ya wurgar da jakan bayanshi ya kwanta akan carpet yace "wayyo na gaji"
hanan tace "wai aina ka samo wannan muryan gardawan ne Imran? wallahi daga shigo na zaci wani katon ne ashe ɗan mitsitsi ne zai shigo"
ɓata rai yayi yace "waye mitsitsi?"
ta nunashi "kai"
tashi yayi kamar zai daketa gudu tayi daga wajen ta rike ammi tace "ammi wayyo ki hanashi dan Allah"
ammi tace "keda Imran kamar wasu yara kanana? bakwa zama ku nutsu waje ɗaya sai tsokanan juna?"
wayan ameesha ne yayi kara ta ɗauka tana duba sunan, kunya taji ganin ammi ta kalli sunan man da tayi saving da heartbeat, receive ta taɓa sannan ta kara a kunne tace "hello man"
yace "baby ya kike?"
tace "ina lafiya ya aiki?"
yace "ba daɗi tunda babu ke"
murmushi tayi tace "ammi na min tsifa"
yace "to ƴar ammi ina su hanan?"
jin ihun hanan da Imran ammi tana rabasu yace "sun fara ko?"
murmushi tayi me sauti tace "yaushe zaka dawo?"
yace "me zaki bani idan na dawo"
da sauri tace "ba komai"
yace "akwai komai mana"
a nitse tace "Allah babu"
yace "Allah akwai"
turo baki tayi tace "to me?"
yace "bre...."
katse wayan tayi jin yana nema yayi mata batsa, dariya yayi ya aje wayan, hamdala tayi ganin ammi bata kallonta.

ammi da ameesha ne a kitchen suna girki hanan an kirata duba mara lafiya a makotansu, ameesha tana yiwa ammi surutu tace "to kenan ammi lokacin da kike secondary kece kike ɗaukan number 1?"
ammi tace "eh nice kuma banida kawaye ni kaɗai nake tafiya har na haɗu da mijina na farko wato Alhaji umar maidawa, ya soni sosai munyi soyayya da umar kamar na cinyeshi haka nakeji amma Allah ya rabamu"
ameesha tace "sorry ammi Allah yasa hakan shi yafi alkhairi"
tace "ameen"
tace "ammi?"

"na'am"
tace "wallahi ina sanki sosai"
tace "nima ina sanki ameesha, kuma inason ganin yaranki da man, inason ganin jikokina"
rufe fuska tayi tace "kai ammi"
murmushi tayi wai kunyanta ameesha take ji, suna gama girki ta kai dinning Ammi tace "muje na wanke miki kanki"
tafiya sukayi zuwa ɗaki ammi ta wanke mata kanta sannan ta ɗauko dryer ta fara busar mata kan, mai ta shafa mata me kamshi ta taje mata gashinta ta kame mata da ribbon tace "salla"
salla sukayi kana suka fito domin cin abinci, akan carpet na tsakar ɗakin suka zauna ameesha ta kwaso abincin, Abba yana zaune akan sofa yazeed suka shigo tareda man, Abba yace "ya kuka dawo tare?"
man yace "ya jirani a office muka dawo tare"
Abba yace "okay bani sakon idan kun gama cin abinci inason magana daku ku kirani a ɗakina zanzo ku duka nakeson magana daku"
suka amsa da to, tashi yayi yace "harda fahad da Imran da ameesha da hanan"
sukace "to Abba"
tafiya ɗakinshi yayi su kuma suka zauna kusa da ammi wacce take shirin sa musu abinci, hanan ce tayi sallama ta cire karamin hijabin jikinta tace "na dawo"
Imran yace "waya tambaye ki? ko bamu ganki bane?"
jakan ta na gefe ta kwaɗa mishi tace "nayi magana da kai?"
ammi tace "kafin ku fara ku bari mu gama cin abinci idan kunga dama karku bari idan kun fara har gobe"
abinci tasa musu itada ameesha da hanan a plate ɗaya sai su kowa yasa nashi, man ya zauna kusa da ameesha yana kallonta murguɗa baki tayi suka fara cin abinci da ammi, yazeed yace "ammi kin san yau da naje airport wai sai naji na gaji da driving, kuma fa ina iya driving me tsayi ban gaji ba"
ammi tace "ka fara tsufa shiyasa, gara kayi aure tun wuri kafin ka daina ina driving ɗin"
dariya sukayi mishi yazeed yace "amma ammi a gaban kannena kike cemin na fara tsufa?"
tace "to su kannen naka ba mutane bane? amma anya kai ko budurwa kana da ita?"
ya sosa kai yace "inada ita mana"
tace "ina take nunan hotonta na gani idan da gaske kake"
wayanshi ya buɗe ya nuna mata hoto ameesha ta leka tace "rohi?"
ammi tace "kin santa ne?"
shiru tayi ganin yazeed yana hararanta, tace "a,a sunanta nakeji a wajenshi"
ammi tace "amma wannan ƴar India ce ko?"
yace "eh amma wallahi ammi ina santa idan Abba zai yadda wallahi zan aureta, musulma ce fa, sunanta rayhana shine suke ce mata rohi kuma marainiya ce iyayenta sun mutu"
ammi tace "Allah sarki amma kana ganin abbanku zai yadda?"
yace "ammi duk ku taru dasu man dan Allah ku tayani rokanshi"
ameesha tayi shiru tunda ya zabga mata taja bakinta ta kame, man yace "to shikenan"
saida suka gama cin abinci yazeed yace "Imran yiwa Abba magana tunda mun gama"
tashi yayi cikin respect yace "to"
ɗakin Abba yaje yayi sallama Abba ya amsa yace "kun gama ne?"
yace "eh mun gama"
"to ina zuwa"
tare suka fita ammi tana ganinshi ta tashi tace "to ni zan shiga ciki saikun gama"
zasu tsayar da ita Abba yace su barta dasu kaɗai yake son magana, zama yayi duk suka zauna a kasa yana kan sofa yayi shiru yana kallonsu, man jikinshi yayi sanyi sam baison ganin Abba cikin damuwa, yace "Abba akwai matsala ne?"
girgiza kai yayi yaja numfashi kafin yace "man ban san ta inda zan fara bane"
man yace "Abba kada ka ɓoye mana komai mu ƴaƴanka ne"
yace "haka ne duk duniya banida kamar ku, babu wanda zan zauna nayi shawara dasu kamar ku, kune jinina to amma maganan yamin nauyi"
yazeed yace "Abba wani magana ne wannan?"
yace "dama aure nake so nayi sabida kunga zama haka ba zaiyi ba"
Imran yace "to Abba wa zaka aura? kanada budurwa ne?"
ranƙwashi ameesha tayi mishi tace "shiru mara kunya Abban kake cewa yanada budurwa?"
shiru yayi Abba yayi murmushin manya yace "dama shawaranku nake nema da amincewarku, idan kun yadda amminku nake son na aura"
farin ciki ne ya bayyana akan fuskansu gaba ɗaya, cikin jin daɗi sukace "Abba mun yadda"
murmushi yayi, Imran yace "Abba to kaje ka sanar mata soyayyanka kawai mana"
man yace "wai kai meyasa bakada kunya ne Imran?"

Abba yace "ku kyaleshi ya maidani kakanshi"
dariya sukayi, yace "to ku zakuyi mata maganan idan ta amince saina kira waliyyai suzo a ɗaura auren a ganina hakan shine rufin asiri"
Ameesha da hanan suka tashi da sauri zasu nufi wajen ammi a ɗaki, Abba yace "ku zauna mu gama magana tukun"
zama sukayi yace "na siyawa man da ameesha gida a nan unguwan kusa damu sosai"
hoton gidan ya nuna musu, murmushi ameesha tayi tace "mun gode sosai Abba Allah ya saka da Alkhairi"
yace "ameen"
man yace "Abba mun gode sosai"
Abba yace "babu komai kaima yazeed gidan guda biyu ne ɗaya yana gefe gashi nan"
nuna mishi yayi sak nasu ameesha, yace "Abba na gode"
Abba yace "ba wai ka gode ba mata zaka cire babu lokacin wasa da lokaci, ka cire mata a haɗa ayi bikinku saiku koma gidanku rana ɗaya"
kanshi kasa yace "Abba dama inaso..."
sai kuma yayi shiru, Abba yace "kana son me?"
man yace "Abba cewa yayi yanason wata yarinya amma yana tsoron kada kace baka yadda ba"

"wace yarinya ce? Aina take da zama? kuma yaushe suka haɗu?"
man yace "a India sunanta rayhana ana cemata rohi, sun jima sosai iyayenta sun rasu marainiya ce"
Abba yace "matsalan bamu san ya tarbiyanta yake ba, kada mu kara faɗawa rayuwar da muka shiga a baya kaga abinda manal tayi"
yazeed yace "Abba na jima da ita nasan halinta nasan abinda zata iya da wanda ba zata iya ba, wallahi tana sona kuma duk abinda na faɗa mata tana ji"
Abba yace "to shikenan zaka iya biya mata kuɗin jirgi gobe tazo"
yace "to Abba na gode"
Abba ya kalli Imran cikin wasa yace "mutumina kai kuma fa?"
ya sosa kai yace "nimafa Abba da za'a min aurennan inaso"
dariya Abba yayi yace "kai ai yanzu ma ka fara karatu so nake ka zama engineer, kai kuma fahad so nake ka dage da karatu pilot zaka zama driver ɗin jirgi da yaddan Allah"
cikin jin daɗi sukace "Allah yasa"
Abba tashi yayi yace "to zan koma ciki na huta duk yadda kukayi Ameesha da mamana saiku sanarmin"
sukace "to Abba"
tafiya yayi ciki su kuma suka tafi ɗakin Ammi, Imran da fahad suka tafi waje yin ball sai man da yazeed ne suka rage, yazeed yayi shiru da alama akwai magana a bakinshi, man ya ɗan taɓashi yace "tunanin me kake?"
yayi kalan tausayi ya marairaice fuska yace "man dama inaso na faɗa maka gaskiya"
gira ya ɗaga mishi alaman ina jinka, yace "rayhana tana nan nigeria dama akwai wani gida dana kama mata anan take karatu ma harta gama degree dama ɓoyewa nayi"
da mamaki man ya kalleshi yama kasa magana, shiru yazeed yayi, man yace "kenan ka kama mata gida da jimawa? All this time kana zuwa gidanta to anya zaku iya zaman lafiya bayan kun gama komai a waje?"
yace "wallahi romance kawai muke, wallahi ban taɓa yin s*x ba, kaji na rantse itama ba yadda take ba"
man yayi shiru yana kallonshi, da alama gaskiya yake faɗa dan kamar zaiyi kuka, man yace "to kasan abinda za'ayi?"
ya girgiza kai, 
"zaka kyale su Abba da nufin gobe ka tura mata kuɗin jirgi jibi zata zo, sai kaje ka sameta kace mata kada ta yadda Abba yasan ta zauna anan kaji?"
yace "to bro thank you so much amma ka rakani muje saika ganta"
man yace "yaushe?"
yace "ko yanzu"
kallon agogo yayi yace "9 fa yayi"
yace "yes muje"
tashi sukayi ya ɗau makullin mota suka fita, motarshi suka shiga shi yake driving man ya ɗau goran ruwa yana sha.

Ameesha tana zaune kusa da ammi itada hanan sun rike hannunta sukace "dan Allah ammi ki amince wallahi Abba yana sanki"
murmushi tayi tace "to shikenan tunda kuna so nima na amince farin cikinku shine nawa"
rungumeta sukayi sukace "thank you ammi"
ganin hawaye a idonta ameesha ta share mata tace "banda kuka ammi farin ciki ya kamata muyi sannan mu godewa Allah, duk gwagwarmaya da mukasha a rayuwa gashi Allah ya canja mana da mafi Alkhairi, kinga Allah bai baki haihuwa ba saiya baki mu har shida yanzu yara shida kike dasu ameesha, hanan, Abdulrahman, Imran, yazeed, da kuma fahad, wannan ma wani kyauta ne da Allah ya baki, hanan Allah ya ɗauke mahaifiyarsu sai ya basu ke, ni kuma mamana babana sun mutu sai Allah ya bani ke da Abba, man da Imran sun rasa umma da Abbansu sai gashi Allah ya basu ke da kuma Abba, harma Allah ya kara mana da karin ƴan uwa, kinga duk wani ƙaddara da Allah ya ɗaurawa mutum akwai hikima a cikinshi, ba lalle sai ciki ɗaya kuka fito da mutum zaku zama ƴan uwa ba, Allah yana iya haɗa mutanen da basu san juna ba su zama ƴan uwa, haka Allah ya haɗamu sabida haka mu gode mishi"
ammi tace "to na gode"
ameesha tace "gidanki na kaduna an siyar harma an turamin kuɗin a account jiya, sannan an saida company ɗin m.u.m kamar yadda kikace man yayi kyauta da kuɗin ya rabawa su faruk sauran kuma an kai gidan marayun Abba, wannan matar data yiwa Abba sharri na sameta da kaina a police station amma ta tabbatar mana cewar manal ce tayi musu barazana da kashe musu iyaye idan basuyi abinda ta faɗa ba, ina fatan kada kowa ya fuskanci irin wuyan da mukasha a baya, amma ina fatan kowa ya samu jin daɗin da muke ciki a yanzu"
ammi tace "to shikenan"
hanan tace "to ammi nifa akwai maganan da nakeso nayi amma inajin kunyan Abba"
tace "wani magana?"
tace "dama ni ya faruk nakeso"
ta faɗa tana rufe fuska, dariya sukayi sukace "to ai wannan abu me sauki ne sai a yiwa abbanku magana"

a kofan wani madaidaicin gida suka tsaya yazeed ya kira waya yace "ina kofa fito"
katse wayan yayi, da gudu ta fito cikin riga da wando irin na India ta kame gashinta kitso ɗaya ta zuba a gefen wuyanta, tayi matukar kyau, buɗe kofan tayi kawai ta faɗa jikinshi ta fashe da kuka, shafa bayanta yayi yace "ya isa, ki daina kuka"
cikin hausanta da bai gama fitaba tace "kullum kana tafi ka barni, ni ɗaya a gida bana jin daɗi na gaji da kallo, na gaji da karatu, am missing you"
yace "ya isa ba gashi nazo ba?"
ɗago kanta yayi daga kirjinshi, ta kewaye hanunta ta waist nashi ta rikeshi, kallon fuskanshi take tace "ya naga ka kara kyau? ko dai baka tunanina?"
yace "inayi mana baby"
share mata hawayen yayi ta turo ɗan karamin bakinta tace "to matso nayi maka kiss"
murmushi yayi ya kalli gefenshi da man yake tsaye ya harɗe hanu a kirji yana kallon ikon Allah, shi ya zaci ameesha ce kaɗai da rigima ashe ga ƴar uwarta anan, yace "ga bro ɗina da nake faɗa miki"
da sauri ta sakeshi ganin man ya leko, ta durkusa kasa tace "sannu"
man yace "tashi mana"
tashi tayi cikin jin kunya da alama batasan dashi suka zo ba, tace "ina wuni ya man"
yace "lafiya ƙalau ya kike?"
tace "ina lafiya"
yazeed yace "muje ciki"
shiga sukayi man ya kalli karamin falon me kyau sosai sai kamshi yake, yazeed ya ɗau laptop nata dake kan sofa ya fara dubawa shiga ciki tayi ta fito da plate da drinks dasu snacks akai ta aje a gabansu ta zauna a kasa tayi shiru ta kasa sakewa, man yace "ki saki jikinki fa"
murmushi kawai tayi, yazeed yace "kizo"
kin zuwa tayi sabida tasan zai iya taɓata a gaban man, dariya yayi yace "ba abinda zan miki fa buɗemin laptop nakeso kiyi"
a hankali ta tashi cikin natsuwanta taje inda yake ta tsaya nesa dashi ta juyo da laptop ɗin tace "kullum saina faɗa maka password baka rikewa"
buɗewa tayi sannan ta tura mishi ta koma ta zauna a gefe, man yasha ruwa kawai suka tashi zasu tafi, man ya riga fita, tana ganin ya fita taje wajenshi, akan kafanshi ta zauna cikin shagwaɓanta tace "sai yaushe?"
yace "guess what?"
taɓe baki tayi tareda rau rau da ido alaman no, yace "Abba ya yadda da aurenmu yace ma na tura miki kuɗin jirgi kizo gobe amma zan bari sai jibi muje sai nace kin tsaya shirye shirye ne"
waro manyan idanunta tayi tace "wasa kake min ko?"
yace "no da gaske ne bakiga mun zo tareda bro man ba?"
wani irin kankameshi tayi tana murna, kiss ta fara mishi a gefen wuya da kumatu, rike waist nata yayi wanda yake bala'in tafiya da imaninshi, bata rabo da waist beats shiyasa daya rungumeta yake wasa da waist beats nata, manna bakinshi yayi a nata yayi relax da ita akan kujeran yana sauke ajiyan zuciya a hankali yake kissing nata, man ya duba wayanshi bai gani ba, tsaki yaja tunawa daya bari akan sofan ɗakin, komawa yayi ya tura kofan ya shiga, juya baya yayi sannan yayi gyaran murya, basu jishi ba kawai ya ɗau wayarshi ya fita, a bakin kofa ya tsaya ya fara knocking da karfi, saurin sauka tayi daga kafanshi tana sunkuyar da kai tana murmushi me haɗe da dariya, ajiyan zuciya ya sauke sannan ya tashi daga zaunen yace "ni kikewa dariya ko?"
girgiza kai tayi tana ɗauke kai yana ganinta tana toshe dariya, yana son ganinta a haka kyau take mishi, yace "okay sai gobe"
tace "bye a gaida su Abba da hanan harda ameesha da Imran da fahad"
tace "to duk zasuji"
fita yayi man ya watsa mishi harara, ɓata rai yayi yace "me kana harara na?"
yace "ban sani ba, ai kafi kowa sani"
dariya yayi yace "oho dai gara ni ba kitchen na bita ba"
man yace "Allah ya shiryeka"
"ya shiryemu dai"
cewar yazeed.

Ameesha da hanan sun samu Abba sun sanar mishi cewar ammi ta amince, yayi farin ciki sannan ya kira shaidu da waliyyai suka zo aka ɗaura auren ammi da Abba, yaune yazeed zai kawo rayhana, duk suna zaune suna jiran zuwanta sunyi kyau sosai daga kan ammi har hanan da kuma ameesha, yazeed ne yayi sallama sannan ya shigo itace a bayanshi rike da luggage shi kuma yana rike da jakanta, kanta kasa da alama akwai tsoro a jikinta, ammi cikin sakin fuska tace "sannu da zuwa rayhana"
hugging nata tayi, ameesha ta karɓi luggage ɗin tace "sannu da zuwa Anty rayhana"
tana murmushi tace "yawwa amarya"
hanan ta karɓi jakanta dake hanun yazeed tace "sannu da zuwa Anty rayhana"
tace "yawwa hanan"
cikin jin kunya ta zauna a kusa da ƙafan ammi, Imran jin ana gaisawa ya fito da riga a hanu yana sawa ya kalleta yace "wai wallahi yayuna sun iya zaɓen mata, nima Allah yasa kinada kanwa ki ɗan haɗamu na aure ta"
hanan tace "kaga ba'ason iskanci baƙuwa ce"
zaiyi magana taja hanunshi suka tafi, fahad yazo ya gaisheta, ammi tace "fahad kira Abbanku yazo su gaisa saita shiga ciki ta huta"
yace "to"
ɗakin Abba yaje ya kirashi suka fito tare, Abba sanye da jallabiya cikin dattaku da iya karantan halin ɗan adam ya zauna yana mata sannu da zuwa, gaisheshi tayi cikin sakin fuska ya amsa tareda yimata ya hanya ta amsa, Abba yace "ameesha shiga da ita ciki saita huta tare zaku zauna ko?"
ameesha tace "to Abba"
shiga ciki sukayi Abba yabi bayanta da kallo, sai kuma ya kalli ammi yace "kamar fa batada matsala"
ammi tace "gaskiya nutsuwan a jininta ne ba aroshi tayi ba"
Abba yace "to masha Allah saisu fara shirin biki domin harda auren hanan da faruk za'a haɗa na kirashi jiya yace gobe zai turo manyanshi suzo ayi magana"
ammi tace "Alhmdllh"
Ameesha ta nuna mata bakin gado tace "ki saki jiki ki zauna mu ƴan uwanki ne kinji?"
tace "to"
idonta cike da hawaye bata taɓa zaton zata samu su karɓeta hanu bibbiyu haka ba, ameesha saida hanan ta shiga sa mata ruwan wanka tace "kiyi hakuri da abinda ya faru a ranan can.."
da sauri zace "ba komai ya faɗamin komai karki damu ya wuce bakida laifi"
tace "na gode"
hanan ta fito tace "je kiyi wanka"
cikin jin kunya ta tashi ta shiga toilet ɗin, hanan tazo kunnen ameesha cike da gulma tace "kut kinga gashinta kuwa? ke kinga yadda skin nata yake glowing?"
tureta ameesha tayi tace "ban son gulma"
tace "ai ba gulma bane dan babu abinda zata nuna mana kawai de fatansu dole yayi banban da namu, badan haka ba wannan kyakkyawar antyn tawa matar ya man ta fita kyau"
tayi maganan tana jan karan hancin ameesha, dariya ameesha tayi tace "tsokana da son kai"
man ne ya kirata ta ɗauka tace "yes"
yace "baby ina mota kiyi sanɗa ki fito ki sameni please"
tace "meya faru?"
yace "ke kam kizo"
tace "da darennan?"
yace "wani abu na siya miki zoki karɓa"
tace "okay"
hanan ta kalleta ganin ta tashi kawai zata fita haka tace "ki canja kaya mana kisa night wears dan nasan ba haka kawai yake kiranki ba"
tsaki taja tace "saiki bari ke kisa idan faruk ya kiraki"
dariya tayi, ameesha ta fita, yana mota yana zaune knocking tayi ya buɗe mata ta shiga tace "ya akayi?"
rufe kofan yayi ya kashe wutan motan zatayi magana ya rufe kofan da key ya janyota jikinshi yace "i missed you sosai"
tace "dan Allah ka...."
yace "kada ki haɗani da Allah ki barni please, kafin komawa gidanmu ai yayi nisa ba zan iya hakura ba"
duk yadda taso hanashi saida ya samu satisfaction kafin ya saketa yace "jeki"
ganin ma harda yin fushi bayan ya gama duk abinda yaga dama da ita, tace "nice zanyi fushi ko kai?"
ɓata rai yayi kamar bai taɓa dariya ba yace "fita"
hanu tasa akan handle ɗin tace "dama ai zan fita ba kwana zanyi anan ba"
maidota yayi ya rufe kofan ranshi ɓace yace "ba kwana zakiyi ba ko?"
tace "leave me alone"
ko sauraranta baiyi ba ya ciro waya kawai ya fara danne danne, ta marairaice tace "kayi hakuri ya man ba zan kara ba"
yayi shiru, tace "dan Allah kayi hakuri kaga munada baƙuwa kamata ace ina tare da ita kayi hakuri"
ya kalleta yace "sai kin yiwa mutum laifi kizo kina bashi hakuri kamar marainiya"
murmushi tayi ganin ya buɗe mata kofan, fita tayi ta leƙo tayi mishi gwalo tace "eh ɗin ba kwana zanyi ba"
binta yayi da kallo ganin ta kwasa da gudu, dariya kawai yayi yaja tsaki bata girma sam kullum gani take kamar tana shekara goma, musamman idan tana tare dashi gani take har yanzu basu girma ba.

*Jiddah Ce....