BABBAN BURI
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUƘARWA GA A'ISHA IDREES ABDULLAHI.
بسم الله الرحمن الرحيم
FITOWA TA SHA TARA
~~~A can waje kuwa gaba ɗaya hankalin su Alh Bello ya tashi domin kuwa duk inda ALIYU ya shiga ya dawo gida bazai taɓa ɓace masu ba.
Sosai suka shiga zarar idanuwa idan wannan ya kalli wannan can wannan ya kalli wannan, har al'ummar dake zaune a gurin suka fara tambayar "lafiya kuwa?", amsar ɗaya ce "bakomai".
Miƙewa Alh Bello ya yi yana meyi wa Alh Murtala magana ƙasa ƙasa, shima miƙewa ya yi suka koma gefen da bakowa har rigen rigen magana su keyi "Yaya kamar ALIYU ne ya dawo ko?", faɗan Alh Murtala tana me tsare Alh Bello da idanuwa.
"Ba kama bace Murtala shi ɗin ne ya dawo", ya faɗa yana me sharce zufa.
"Ya hakan ta kasance Yaya?".
"Taya zan sani Murtala."
"To kasan tabbas bayyanar ALIYU ba alkheree bace a garemu ba ko?, domin kuwa lokacin tonon asirin mune ya yi hakan kuwa babban ƙalu bale ne a garemu", cewar Alh Murtala kenan da yake ta faman zarar idanuwa.
"Tau yanzu dai bamu da abinyi face mu zubawa sarautar Allah idanuwa, kai kanka kasan bana cikin kwanciyar hankali tsakanin jiya zuwa yau, yau kuma saiga wata matsalar ta ɓullo".
Haka suka yi shiru kowa da tunanin dake yi masa yawo a cikin ransa.
Sunjima tsaye kana suka koma suka zauna akaci gaba da amsar gaisuwa.
Suma su Baba lokacin ne Hajiya Inna ke gaya masu matar Alh Bello ce Allah ya yi wa rasuwa, fitowa sukayi suka yi masa gaisuwa suka koma domin kuwa Malam ya ce "shi a yau zai koma gida dashi da Gwaggwo , amaryar da yayi bayan rasuwar mahaifiyar Mama.
Ƙarfe 4pm kuwa Shalelen Hajiya Inna yasa Baban Gida direba ya mayar dasu gida haɗi da sha tara na arziƙi.
Mukam anan aka barmu gidan mahaifinmu munzo kenan.
Cikin raina na ce "rayuwa kenan".
Da daddare wuraren bayan isha'i muna zaune muna fira wacce taƙi ci taƙi ƙarewa naji wayata ta yi tsuwa alamar shigowar saƙo , da sauri na duba domin kuwa na tabbata Ya Haidar ne tunda dama bayanan zaune tun kamin ayi magariba rabona dashi.
_"Dear plx ki ɗan fito waje akwai maganar da nake son mu yi."_
Na jima zaune a gurin sannan na sulale na yi waje daman firar ta fara gundurata.
A can wurin shaƙatawar gidan na tsinkayo shi ya zubawa ƙofar sashen idanuwa yana ganin na fito ya sauke ajiyar zuciya haɗi da lumshe mayatattun idanuwansa.
Cike da takun ɗaukar hankali wanda ni kaina bansan lokacin dana iya saba na isa gurin , tunkan na kawo ya gyaramin kujerar da zauna a kai, ina isa gurin bakina ɗauke da sallama , amsawa ya yi yana faman lumshe idanuwa sai naji tsikar jikina ta tashi lokaci ɗaya na yi azamar ɗauke idanuwana a kansa na ɗanja kujerar sannan na zauna akai bakina ɗauke da bisimillah.
Kallona yaci gaba dayi wanda hakan ni kuwa yayi masifar kashemin jiki na rasa dalilin hakan.
Sai da ya tabbatar ya gama kashemin jiki da rikitattun idanuwansa sannan cikin muryar ƙasa ƙasa ya ce "I LOVE YOU" jin kalmar na yi tun daga ƙafafuwana har tsakiyar kaina, sai na yi kamar banji me ya ce ba na ce "me kace?," "I LOVE YOU KHADEEJAH nace ko laifine?".
Hannuna nasa na rufe idanuwana cike dajin kunyarsa domin kuwa koda wasa ban taɓa tsammanin jin kalmar a bakinsa ba.
"Zan cire maki kunyar very soon domin kuwa bazan bari ta yaudare ni ba".
Da gudu na miƙe na yi sashen Hajiya Inna, a bakin ƙofar shiga na tsaya na huta sannan na shige cikin part ɗin.
Haka muka raba daren yau muna waya da Ya Haidar cike da tsantsar soyayya, har nake mamaki ashe dama soyayya ba koyonta a keyi ba?, na tabbata kuwa domin kuwa.
Da kyar muka haƙura muka kwanta cike da begen juna.
Gari na waye na shige kitchin ni da A'isha muka shirya lafiyayyen break fast me rai da motsi, kana na faɗa toilet na sullo wanka na fito na shafa mai sai gani yau da zama yin kwalliya.
Duk da ba wata kwalliya na yi ba, sai gashi lokaci ɗaya na fito fess dani, haka na wanke su Umar suma fes kana muka fito muka fara break.
Duk da a gaban iyayenmu muke hakan be hanamu aikawa da junanmu kallon love ba, amman ko wannen mu cikin taku yake yi sa.
Muna kammalawa na gyara wurin kana na koma kitchin domin na wanke kwanu kan da muka ci abinci dasu.
Ina tsaka da wanke wanke naji mutum a bayana da sauri na juyo inga waye sai dai nasarar da idanuwana suka samu ta faɗawa cikin idanuwan Yayana ya sanya ni sakin lallausan murmushi wanda ya ƙara ƙawata fuskata har yasanya gefen kuma tuna ɗan lotsawa.
Jin hannunsa kawai na yi a cikin rabin, na yi maza naja da baya da baya, domin kuwa wannan ne karo na farko dana ji hannun na miji a jikina.
Harara na wurga masa sannan na ce "meye haka ka keyi Ya Haidar?".
"Afuwa ƴar kyakkyawata Allah ban san lokacin da hakan ta kasance ba, amman ai duk kece da kika yi murmushin daya kusa tafiya dani."
Kallonsa na yi sannan na ce "so plx Ya Haidar kar hakan ta sake kasance wa , na fison muyi komai cikin tsari".
"Insha Allahu ba zata sake kasance wa ba hakan, kiyi haƙuri kinji?".
"Bakomai ya wuce", na basa amsa iname juya masa baya na ci gaba da aikina.
Don karya sake gigin taɓamin jiki ya sanya na yi masa haka, domin kuwa da zaran na sake masa yadda nake ganinsa zai wuce gona da iri ne gani dama yadda nake, ko kallona a kayi sai..... Inada taɓamin jiki.
Bayan na kammala abinda na keyi ne da rana na samu na leƙa babban kitchin domin inason mu gaisa dasu Yahanazu.
Ai kuwa na isko su a kitchin suna ta faman dafa abincin masu zuwa gaisuwa , sa hannuna na yi muna yi nake sanar dasu ai mun dawo nan gidan da zama domin kuwa Hajiya Inna kaka tace itace ta haifi Baba na, sunyimin murna sa'annan daga ƙarshe na koma sashen Hajiya Inna.
Miƙomin key ɗin part ɗaya na gidan ta yi ta ce "muje ni da A'isha mu gyarawa Mama sashen ta ganta a takure.
Haka muka amshi keyn muka je na buɗe sashen kamar yadda na sauran matan gidan yake haka ko wannan ya ke, Parlour ne babba sai kuma dakuna a gefensa guda uku ko wanne da uwar ɗaki a ciki sannan da ban daki.
Kasancewar akwai komai a ciki ya sanya mu kakkaɓe ƙura sannan muka wanke na wanke wa muka fesa turaren ɗaki sannan muka kulle sashen muka dawo na Hajiya Inna.
Ƙarfe 4pm a kayi addu'ar kwana uku na Hajiya Umma sai muce Rabbu ya jiƙan magabatanmu.
4:30pm Ya Haidar ya shigo ya ce muzo ya kaimu super market mu siyo a bubuwan buƙata.
Nida A'isha muka shirya muka fice a tare.
Kai tsaye kuwa ya kaimu gurin sayar da kayyaki kala kala ba abinda babu a gurin.
Nan ya hau kwasarmana kaya kala kala masu yawan gaske sai da nace dashi "halan shago zai buɗe"?.
A haka ya biya kuɗi aka loda mana kayan a mota muka kama hanya zuwa gida , mai makon naga ya ɗauki hanyar zuwa gida sai naga ya kauce hanya, bance dashi komai har yayi parking ya fita , kasancewar bansan unguwanni da yawa ba ban gane a ina muke ba, amman tabbas na kula da gurin sayar da wayoyi ne nan......
ƳAR MUTAN BUBARE CE