Matasa Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Neman Shugaban PDP Na Kasa Ya Sauka A Abuja

Matasa Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Neman Shugaban PDP Na Kasa Ya Sauka A Abuja

A wannan Laraba ne sakateriyar PDP ta cika makil da jama'a yayin da rikici ya barke a PDP kan tikitin takarar gwamna a jihar Delta a 2023.

Matasan PDP ne suka mamaye sakatariyar jam'iyyar ta kasa suna neman shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus nan take.

 Rahoton Vanguard ya ce, an ga magoya bayan jam’iyyar a karkashin kungiyar Concerned Deltans for  Good  Governance a dandalin Wadata Plaza, domin nuna rashin jin dadinsu.

Sun nuna damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin kin bin umarnin babbar kotun tarayya ta korar Rt. Hon. Sheriff Oborevwori a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna na shekara mai zuwa a Delta.

Idan baku manta ba, umarnin kotu wanda mai shari’a Taiwo Taiwo ya bayar ya bayyana Olorogun David Edevbie a matsayin wanda aka zaba bisa doka kuma dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna mai zuwa.

Haka kuma ta umurci jam’iyyar PDP da ta mika sunan Edevbie zuwa ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), hakazalika INEC ta ba shi cikakken hakki da ya kamace shi a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Akasarin masu zanga-zangar da suka yi dandazo domin neman jam'iyyar ta bi hukuncin mai shari'a Taiwo na dauke da kwalaye da rubuce-rubuce, kamar su: "Ayu ba shi da kimar da zai sa PDP ta kai ga nasara", "Ku yi biyayya ga hukuncin kotun Abuja ta FHC", da dai sauran kalamai na nuna rashin jin dadi.

Da yake yiwa manema labarai jawabi yayin zanga-zangar, shugaban kungiyar, Chris Anthony, ya yi zargi cewa, Ayu zai jagoranci jam’iyyar zuwa ga halaka.