Babban Buri:Fita Ta Goma
BABBAN BURI!
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.
بسم الله الرحمن الرحيم
FITOWA TA GOMA
~~~~Sai da na gama hutun da nake yi sannan na miƙe na shige uwar ɗakinsa , na harhaɗa komai a muhallinsa sannan na share ɗakin fes na dawo Parlour, shima fes na sharesa, sannan na fesa turaren ɗakin dana gani a ajiye.
Sai da na gama ƙarewa ɗakunan kallo gwanin sha'awa, ji na keyi kamar nawa ne, sai da na rufe idanuwana lokacin da wannan tunanin yazo min , sannan na fice daga ɗakin.
A tare na tarar dasu a Parlour shi da Hajiya Inna , ita tana zaune a ƙasa tana gyaran farce shi kuwa yana saman kujera yana aikin sarrafa na'ura mai ƙwaƙwalwa wato computer, kallo ɗaya nayi masa na ɗauke idanuwana a kansa na mayar a kan Hajiya Inna wacce ita ma take kallona kan ta ce "harkin kammala Hadeejatu?."
"Da "eh na amsa mata iname zama a gefenta nasa hannu na amshi rezar dake hannunta na ci gaba da ɗebe mata a kaifar.
Kallon ƙasa ƙasa yake aika mata, yana me yaba hankalin yarinyar haka kawai shi dai yarinyar ke burgesa.
Ƙarar shigowar mssg ce da yaji ya sanya shi saurin ɗauke kansa a kanta ya mayar a kan wayarsa.
Mamaki ne ya bayyana a saman fuskarsa ganin abinda saƙon ya ƙunsa.
Ɗaga kafaɗa ya yi alamun ko oho sannan ya ajiye wayar gefe ya na meci gaba da sarrafa computers sa.
Ina ƙarƙarewa Hajiya Inna yankan akaifar nayi mata sallama na koma kitchin muka ɗaura abincin rana.
Muna tsaka da abincinne Safiya ta shigo kitchin ɗin karo na farko dana fara ganin ƴaƴan gidan a kitchin kenan tun farkon zuwana gidan.
Kallonmu ta keyi a hankaɗe kan ta tsaida idanuwanta a kaina ta ce "ke zonan!"
Fito da ido waje na yi na ce "ni" "a'a ni nake nufi!, ta faɗa tana me nuna kanta.
Ajiye robar dake hannuna na yi nabi bayanta iname rarraba idanuwana domin ganin ina ta nufa dani?.
Sashen ƴan matan gidan ta nufa dani ina tafe ina addu'ar Allah ya fitar dani daga sharrinta, domin kuwa na tabbata ba alkheree bane ya sanyata kirana ba.
Ɗakinta dake na biyu a cikin jerin ɗakunan ta nuna min sannan ta ce "oya shiga ki sharemin ɗakinnan ki haɗa da banɗaki ki gyara min".
Ɗakin na shige ba tare dana ce da'ita komai ba.
Wannan ne karo na farko dana taɓa shiga ɗakin , tsayawa turus na yi ganin yadda ɗakin yake a hargitse ba zaka taɓa yadda ana rayuwa a cikinsa ba.
Tufafine a yashe ko ina , ga ledodin kayan ciye ciyenan yashe bila adadin, ɗakin na ƙara ɗaga idanuwana ina kallonsa , ko ina ka kalla ba tsari sai tsami dake faman tashi kamar ɗakin kutare.
Ba tare dana taɓa komai daga ɗakin ba na shiga banɗaki domin can ya kamata na fara gyarawa kan ɗakin.
Saurin dawowa baya nayi lokacin dana shiga banɗakin domin kuwa wani zarnin fitsari ne ya yi man barka da zuwa , bugu da ƙari ko ina baki ƙirin kamar wanda ba a taɓa wanke wa ba.
Shahada na yi na sanya kaina a ciki sannan na kwance ɗan kwalin kaina na kulle hancina sannan na fara gyara toilet ɗin.
Cikin ƙanƙanin lokaci na kammala sai gashi ya yi fes dashi kamar mutum ya lashe.
Parlour na dawo shima na hau tattara mata kayan dake yashe a ƙasa na zuba su a basket dake ajiye bayan ganmu bakomai a cikinsa.
Shima haka na gyarasa, wa'iyazu billah, dauɗar dana fitar ita kanta idan mutum ya ganta saiya rammawa duk inda aka fitar da'ita.
Kallon ɗakin na tsayayi gwanin sha'awa, lokacin dana kammala komai na feshe shi da turaren ɗaki, ba zaka taɓa cewa shine a hargitse ɗazu ba.
Bayan na kammala na fito daga cikin ɗakin ban ganta ba hakan be damar dani ba kuma na kama hanyar zuwa kitchin domin koma wa aikina.
Ina gaf da shiga party ɗin naga wata mota ta shigo farfajiyar gidan, ɗan rage saurin tafiyar dana keyi na yi domin ganewa idanuwa su waye a ciki.
Zaro idanuwa na yi ganin turawannan dana gani na ranar dasu Shalelen Hajiya Inna suka dawo daga wajen karatu suna fitowa daga cikin motar su biyar reras dasu kamannin su ɗaya , haka tsawon su ɗaya idan ka gansu zaka yi tsammanin ƴan biyar ne.
Ganin suna dunfaro gunda nake ya sanya ni saurin ƙarasa wa na shige cikin kitchin iname mamakin wai ina suka shiga ne haka, tun ranar ban koma sanya su a idanuwana ba.
Kallona Yahanazu ta yi sannan ta ce "lafiyarki kuwa?".
Ƙasa na yi da muryata sannan na ce "ke turawannan na ranar na gani yanzu sun shigo cikin gidannan yanzu."
"Haba dan Allah?", ta faɗa tana me leƙa tagar kitchin ɗin.
"Sosai kuwa, kema kina nufin tun ranar baki sake ganinsu ba?".
Gyaɗamin kai ta yi sannan tace "inajin tun ranar da suka dawo basu zauna ba, sai da daddare nake jin motsin shigowarsu amman ban taɓa ganinsu ba tun daga ranar."
"Haka muka kammala abinda muke yi a cikin kitchin ɗin Yahanazu ta nufi ɗakinsu.
Da yake anan suke kwana su saɓanin nida Mama taƙi yadda da hakan, ni kuwa na nufi sashen Hajiya Inna.
"Mommy ni har yanzu naji shuru anya aikin bokannan naci kuwa? Kar dai ace kinyi hasarar kuɗin kine dake da daddy."
Kallonta Haj Umma ta yi sannan ta ce "Waime kika ci na baka na zuba ne Safara'u?, nafa gaya maki yadda bokannan ya gayamin ya ce abune me wuya dole sai anshagaltar dashi ibadarsa kan a samu nasarar yin aiki a kansa, dan haka ko kwantar da hankalinki aure ne tsakanin ke da Haidar ba makawa matuƙar ina numfashi a duniyarnar".
"Allah ni mommy abinne ya ɗauremin kai har yanzu idan muka haɗu da Yayah Haidar ko gaidashi muka yi baya amsawa saima wani kallo da yake wurgo mana".
"Sha kurumin ki ƴata na yi maki alkawarin wannan Haidar naki ne ke kaɗai ba wata bayan ko."
{Hhhhhhh ni kuwa DOCTOR nace uhummmm bara dai na yi shuru karnayi ɗumin kuɗi}.
Na tafi shiga sashen Hajiya Inna na tsinkayo muryar ta daga gefe na "naga gyaran ɗaki kinyi ƙoƙari sosai", cewar Safiya kenan.
Ba tare dana juya na ga wacece ke maganar ba domin kuwa na sheda wacece na yi shigewata iname tsinewa ƙazanta da ƙazami. { Taufar ƙazamai kunji me Dijah ta ce hwa}.
★★★★★★
Ɗakin cike ya ke da ayarin su, su 31 , kama daga kan Alh Bello har zuwa kan Alh Usman dake ƙarami a cikinsu.
Bayan an buɗe taro da addu'a kana Alh Sunusi ya ce "Haidar wannan shine zama na biyu da muka zartas a kanka , so wannan zaman ya banbanta dana farkon wannan umurni ne daga gurinmu haɗi da kuma sanarwa zuwa a gareka".
"Na farko mun zaɓa ma mata ba kowa bace face ɗaya daga cikin ƴaƴanmu kuma ƴar uwa a gareka wato Safiya."
"Na biyu muna me sanar dakai mun tsayar da ranar aure a ƙarshen watannan na 5 idan Allah ya kaimu."
Ɗago da kansa ya yi sannan ya ce "Woww wannan haɗin ya yi kuwa, sai dai iname ƙara tabbar maku da cewa ba wacce zanyi zaman aure da'ita daga cikin ƴaƴanku, idan kuwa kuka ɗaura auren zan baku key ɗin gida kusa ta a ciki amman iname gaya maku da babbar murya cewa duk abinda ya biyo baya kar wanda ya yi kuka dani daga cikin ku....
Za mu cigaba a gobe......
ƳAR MUTAN BUBARE CE
Maryamah