HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita ta 45

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita ta 45

HAƊIN ALLAH

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 


          Page 45

 
 *Alhamdulillah! Mun gama exam lafiya sai fatan mu ga kyakkyawan sakamako, sai ku daure ku ta ya mu da addu'ar dacewa da sakamo mai kyau jama'a.*


Wayar sai ƙara take amma Mustapha ba alamar zai ɗaga kiran, saboda yasan wadda ke kiran bata da haƙuri komai zata iya aikata wa kan Jiddah. Kira na biyu ya sake shigowa cikin wayar dole ya ɗaga kiran murya ƙasa -ƙasa ya yi sallama yana jiran ya ji me zata ce mai, amma ya sadaƙar da cewa ƙarya ta ƙare mai Yau tabbas bai faɗa tashin hankali ba yanzu ne zai faɗa tashin hankali.

Alawiyya  "Assalamu alaikum Malam Mustapha kana lafiya? Ya karfin jikin? Ai jiya na zo Jiddah ke gayamin baka lafiya kana asibiti to zan je Kaduna a lokacin shi yasa ban zo ba, yanzu na kira lambarta bata ɗauka ba shi ne nayi tunanin ko tana gida kai kuma kana asibitin ne?" 

Wata ajiyar zuciya ya saki ta jin daɗi da kunyar Jiddah watau ita ta ko'ina  sai ta nuna wa mutane shi ɗin mutumin kirki ne mai adalci ne kenan? Yasan ko shakka babu ta je ta iske ka a hargitse ne don haka tai wannan dabarar... Alawiyya jin ya yi shiru tace, "Ko Malam Mustapha bai kan layin ne?" Dole ya yi gyaran murya ya ce, "Wallahi ina kai, ana yi min wannan ne. Jiki da sauƙi alhamdulillah yanzu haka ma ta ɗan fita ne ta siyo wani abu amma yanzu nasan za ta dawo."

Alawiyya tai dariya tace, "Jiddah na masifar sonka Mustapha ko ince Prince don Allah kar ka ci amanar ta ko ka zama marar adalci a gare ta don Allah. Baka ga yadda na iske ta ci kuka ta gode wa Allah ba ranar duk ta yi zuru-zuru kamar ita ce bata lafiyar ba kai ba." 
Tamkar ya nutse a gun haka ya ji amma ya zai yi komai ya faru shi ne ya ja. Da kyar ya samu ya rabu da Alawiyya a wayar duk zufa ta gama wanke shi tsab.
Tabbas ya zama raggo marar cika alƙawari tun da ba haka suka tsara rayuwarsu ba Jiddah amma sun afka ciki sanadin Hafsat.

Dr. Ne ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Kana iya shiga don ta farka yanzu haka."
Daram! Gabansa ya faɗi da wane ido zai kalle ta shi kam? Amma dai haka ya ja ƙafa ya shige ɗakin da take kwance jiki sanyi ƙalau.
Tun da ya turo ƙofar ta lumshe idonta akan idonsa don haka kai tsaye ya isa bakin gadon ya kama hannunta ya riƙe ya sunkuya cikin sanyin murya ya ce, "Princess don Allah ki yi haƙuri don Allah ki gafarta min duk abin da nayi maki koma miye. Nasan ba kyau tashin-tashina kuma ba halinki bane hakan don haka ki manta baya mu tari gaba kawai don Allah."

A hankali ta runtse hannunsa sosai a cikin hannunta hawaye sun kasa tsayawa daga idanunta sai kawai ya kwanto jikinta ya saki kuka mai sauti yana furta, "Don Allah princess ki yafe min kada ki bari tarin laifina ya shiga tsakanina da kyakkyawar ƙaunar da kike nuna min don Allah Princess... Kuka ya hana shi idawa sam ita kam ta yi lamo tana jin saukar kukansa ji take kamar ta lallashe shi amma sai ta dake saboda tana son daga wannan lokacin ya zama na ƙarshe da wata zata sake shiga tsakaninsu ko ta halin ƙaƙa ne.

Jin tayi shiru bata ce komai ba ta kuma rufe idonta sai kuka take yasa hankalinsa sake tashi sosai, don yasan ba abin da Jiddah ke kasa jurewa irin kukansa amma a Yau ga shi yana yi a jikinta tayi shiru sai rera nata kukan take yi kamar ma bata san Allah Ya yi ruwansa ba a gun  ba sai hankalinsa ya sake tashi sosai.

Jiddah ta kama hannunsa sosai tace, "Ina son don Allah ka yi haƙuri ka sallame tun da abin ya zama haka... Mustapha ya zabura kamar zai tashi sai kuma ya dubi fuskarta ya ce, "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un!!! Wace irin magana ce wannan kike yi Princess? Me nayi maki kike son ganin bayana ne? Wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba Jiddah duk yadda za ai kuwa. Ki tausaya min ki yafe min ki daina wannan maganar don Allah Princess wallahi daga yanzu komai ya wuce ba zan sake yi ma ki abin da baki so ba don Allah."

Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba haka bata tanka mai ba, hakan yasa ya ƙara ruɗewa sosai da sosai saboda rasa Jiddah tamkar rasa rayuwarsa ce baki ɗaya.
Dr. Ya zo ya iske su a haka, ya sallame ta ya sake jaddada ta cire damuwa a cikin zuciyarta ta daina ɗora wa kanta tashin hankali idan ba haka ba zata rasa rabin jikinta, ya ƙara da cewa ta tabbatar ta gujewa duk abin da zai sa ta a cikin damuwa.

Wannan ma bayani ne daya ƙara tada ma Mustapha da hankali sai yake jin kamar ma Dr. Shawarar ta bar gidansa yake bata kawai. Don haka sai kawai ya tashi ya kama hannunta suka fice daga room ɗin.

Ko a mota bata ce mai komai ba shi ne kawai ke ta surutunsa ita kam ta kame a mota ta yi shiru abunta.

Su na isa gidan ta fice bata ce komai ba ta buɗe gidan ta afka tai sauri ta shige ɗakinta kai tsaye ta fara haɗa kayanta alamar zata tafi ne.

Tsaye ya yi hankalinsa ya kai ƙarshen tashi saboda yadda ya ga ko alamar murmushi babu akan fuskarta zuwa yanzu ta daina kukanma haɗa kayanta kawai take yi ba ji ba gani.
Tana gamawa ta ɗauki jakarta zata raɓa shi ta wuce ya janyo ta ya rungume ya fashe da kuka sosai ya kasa cewa komai gare ta ma.

Jiddah ta shiga kicaniyar ƙwace jikinta daga gare shi amma ta kasa don haka a ɗan fusace tace, "Ka rabu da Ni na tafi na barka ka huta tun da na zame maka jidali a rayuwarka... Rufe mata baki ya yi da nashi bakin dole ta yi shiru ta koma mutsu-mutsu kawai na son ƙwacewa.

Mustapha ya ga dai da gaske Jiddah so take ta barshi sai ya sake ta ya tsugunna a gabanta ya ce, "Don darajar Allah da Manzonsa ki yi haƙuri kar ki barni...Jiddah ta sake kauda kanta gefe guda tace, "Ka taimaka ka barni na tafi saboda ban san na zame maka matsala daga zuwana gidanka."

Da gaske fa hankalin Mustapha ya tashi sosai don haka ya cigaba da lallashinta ta ko'ina dole ta saduda ta koma ɗakinta ta haye bisa gado ta yi lamo.
Biyo ta ya yi har cikin ɗakin jikinsa ya yi sanyi ƙalau ya zauna gefen gadon ya kama hannunta ya ce, "Princess wallahi ba za ki taɓa zama matsala a gareni ba sai dai na yadda Ni na zama a gareki, saboda ke mace ce ta gari wadda kowane namiji ke buƙatar samu a matsayin matarsa. Shin na sameki mai zai sa nayi sake? Wannan ma kuskurena ne kuma na gyarama insha Allah ba zan gyara ba."
Tai ajiyar zuciya ta dube shi sosai tace kamar bata son yin maganar, "Prince ka sani duk son da nake maka ba zan ɗauki matsatsi da takura ko zaman ɓacin rai ba a gidanka. Zan iya haƙura da aurenka ko da hakan zai ban matsala, saboda na gama auren baƙin ciki na gama zaman takaicin ɗa namiji a gidan aurena."
Kamar ƙadangare haka yake ɗaga mata kansa, wani lokacin ma har da cewa "Haka ne." 
Duk da ya yi mata alƙawarin ba zai sake yi mata abin da ranta bai so ba hakan baisa Jiddah ta saki ranta ba sai wani shan ƙamshi take shi kuma sai lallaɓata yake kamar ƙwai.

Zuwa dare Jiddah ta manta komai ta saki ranta suka koma kamar washegarin aurensu.

Hafsat ta dinga kiran Mustapha amma ya ƙi amsa kiran ƙarshe ya tura mata saƙon cewa idan ta ga dama ta koma ɗakinta idan bata gani ba kuma tai ta zama gidansu.

Wannan abu ya sake tunzura Hafsat da mahaifiyarta don haka suka yanke shawarar kai Mustapha kotu ya sake ta bata iya zaman kishi da Jiddah.

Maryam ma ba daga baya ba sai dai ita tafi Hafsat sauƙi don iyakarta masifa kuma kan mijinta take sauke abin ta bata damu ba tai Mai duk kalar rashin mutuncin da ya yi mata daɗi amma bata ko maganar Jiddah da wani sai fa Mustapha takan yawaita ce mai Allah zai saka mata abin da yake mata saboda matarsa. 

Cikin sati biyu Jiddah ta goge tayi shar da ita komai ya ji yadda ake so zamanta da Mustapha ba a cewa komai sai hamdala domin hatta yawan fita bai yinta duk ranar girkinta sai dai idan ba gidanta yake ba.

Tsakaninta da dangin mijinta abin sai godiyar Allah komai yana tafiya yadda ya kamata haka surukarta ta sonta sosai da sosai itama tana bakin ƙoƙarinta don kyautata masu.

Kwatsam Mustapha ya amshi takardar sammaci daga kotu daga gun Hafsat cike da ɓacin rai ya isa gidansu ya nuna wa iyayensa suka ce matarsa ce shi yake zaune da ita don haka duk abin da ya yi daidai ne.

Hakan yasa bai sake cewa komai ba sai ranar zaman kotun ya aika mata da takardar sakinta ya ce ta je wani gidan shi da ita duk mai cutar wani Allah Ya saka mai.

Sai zaman gidan ya sake sauyawa ba laifi ba kamar farko ba abubuwa da dama su na faruwa na farin ciki ba laifi duk da cewar Maryam idan kishin ya motsa takan shafe ranakun aikinta tana zabga ma maigidan nata masifa amma yana komawa gidan Jiddah shike nan farin ciki ya same shi hatta mutane ma sun shaida idan yana gidan Jiddah yafi sakewa da alamar hutu da kwanciyar hankali a tattare da shi.

A hakan Jiddah ta tsiro kiran yaran Maryam tana yi ma su kitso da ƙunshi idan za su tafi ta basu turaren wuta ko humra mai daɗi tace su kaiwa Mamarsu tun bata amsa har dai ta fara amsa ba gode bare na gode amma Jiddah ko a jikinta bata fasa ba, duk da yaran na gaya mata irin masifa da bala'in da take duk lokacin da ta aika mata da kyautar.

Ranar da suka fara haɗuwa a gidan wani sunan ƴan'uwan Prince ɗin kamar Maryam tai bindiga don tsabar kishin yadda ta ga Jiddah tayi shar da ita. Ga wani ƙamshi na musamman da take fitarwa wanda ba shakka ba na turare bane ba. Sai taji duk ta tsani kanta da kanta tai ta kallon jikinta tana kallon jikin Jiddah ta ga ba a ma haɗawa sam. A kasan ranta ta hango turaren da humrar da Jiddah ke bata tabbas zata fara amfani da su indai zatai irin ƙamshin Jiddar. Kasa haƙura tai ta koma gidanta ta gyara ɗakinta ta zuba turaren wutar ta shige toilet tai wanka ta fito ta saka kayanta ta shafa humrar sai ta ji ƙamshin kamarma yafi na jikin Jiddah.

Hankalin Alawiyya ya kwanta ganin Jiddah bata cikin damuwa ko da yaushe tana cikin farin ciki ga duk inda zata je Prince ke mata rakiya.

Ranar wata Asabar Jiddah na kwance jikin Mustapha ba sallama ba komai sai ganin Hafsat su kai har cikin falo kamar an jeho ta tai ma ɗakin kallon wulaƙanci sannan ta koma kan Mustapha ta dinga zaginsa ta uwa ta uba.
Ba wanda yasan ya akai kawai jin saukar mari Hafsat tai a kumatunta Jiddah na hucin ɓacin rai ta nuna ta da yatsa tace, "Wace irin dabba ce ke wadda bata san ciwon kanta ba balle tasan na wani? To bari ki ji me zan gaya maki babu wata jaka kidahumar ƙaramar kilakin da zata isko mijina har cikin gidana ta ci mai mutunci na kyale ta ba, don haka tun kafin nayi waya ofis ɗinmu ki bar gidan nan , don idan kika sake kafin su zo ma sauya maki kamanni."

A zaton Hafsat zata ci wani abu jikin Jiddah don haka ta nufeta zata rama marinta ai kuwa Jiddah ta dinga jibgarta sai da ta sauya mata kamanni sannan ta watsata waje ta rufe gidanta.

Mustapha daɗi kamar ya kashe shi matarsa ta ƙwatar mai ƴanci, sai ya ji shi wasai kamar ba zagi ya sha gun tsohuwar matarsa ba.

Jiddah na dawowa ta shige jikinsa suka ci gaba da zuba ƙaunarsu kamar ba abin da ya faru.


Hafsat kuwa kai tsaye gidan Maryam ta wuce kamar wata mahaukaciyar gaske.


Taku a kullum Haupha.