INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciy, Fita Ta 10

Liman na ɗaya daga cikin waɗanda Lantai ta addabi yaransa ko da yaushe sai ta yi sanadiyyar da akai masa daren tuwo gidansa sai kalli mai gari yace, "Ai lafiyarta lau raini ne da tai maka ranka ya daɗe sai ka nuna mata ikon ka zata natsu tasan fada take ba wajen wasa ba."

INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciy, Fita Ta 10

    Page 10

 

 

Mutanen wajen sai kallon-kallo suke domin dai sun san yau akwai bidiri yadda mai gari yake da mugunta haka Lantai take da mugunta duk da tana ƙarama ta fi shi iya ƙeta don ko yaran ƙauyen shakkarta suke yadda bata raga masu ko kaɗan ba ruwanta da girman yaro sai ta ci ɗamara ta dambace da yara sama da biyar idan ta kai niƙan tuwo injin niƙa, mai niƙan duk sanda Lantai ta kai niƙa nata yake yi ko da yana niƙan wani sai ya aje yayi mata idan ba haka ba sai tasan yadda tayi ta lalata injin dan bala'i.

 

Mai gari ya duƙa ya tambayi Liman "Yarinyar nan kuwa ita kaɗai ce ko akwai aljanu bisa kanta Liman ?

Liman na ɗaya daga cikin waɗanda Lantai ta addabi yaransa ko da yaushe sai ta yi sanadiyyar da akai masa daren tuwo gidansa sai kalli mai gari yace, "Ai lafiyarta lau raini ne da tai maka ranka ya daɗe sai ka nuna mata ikon ka zata natsu tasan fada take ba wajen wasa ba."

 

Tuni mai gari kansa ya kumbura ya dubi dogarin dake zane mutane yace "Yi mata bulala goma tasan inda take ."

 

Lantai ta dubi mai gari ta dubi wanda aka ce ya daketa, sai ta sake kwashewa da dariya  abin ta.

 

Aikuwa mutumin ya fusata ya dage iyakar ƙarfinsa ya ɗaga bulalar da niyyar zabga ma Lantai sai dai abin mamaki yana ɗaga bulalar Lantai ta cukuikuye shi ta shige cikin babbar rigarsa.

 

Yana tsula bulalar sai ta kauce ta koma ɓangaren hannunsa na hagu ya kuwa tsulama ɗuwainiyarsa ta dama bulalar sai daya gantsara don azaba.

 

Ya sake kai mata a ɓangaren data koma nan ma ta sake komawa ɗayan ɓangaren ya samu ɗayar ɗuwainiyarsa da bulalar kaɗan ya hana ya fasa ihu don azaba.

 

Shi kam mai gari duk ya ƙule don ya lura Hure sai harararsa take don haka yayi zumbur ya amshi bulalar wai shi zai zane Lantai.

 

Bafaden har saurin ba mai gari bulalar yake don Allah kaɗai yasan yadda yake ji a ɗuwawunsa saboda zafi.

 

Yana ba mai gari bulalar yayi tsaye yana cigaba da zare idanuwa domin dai yasan duk yau bai ga ta zama da ɗuwawunsa ba yadda shegiyar yarinyar tasa ya zane ɗuwawunsa tas.

 

Mai gari kuwa ya amshi bulala Lantai tai wuf ta shige cikin babbar rigarsa daman tafi ta bafaden girma don haka ko ganinta ba a yi.

 

Duk idan ya buga sai ta fasa ihu, abin da yasa mutanen wajen yi masa kirari kenan domin a zatonsu ita yake bugama bulalar.

 

Ihunta kawai take kamar gaske wanda Inna Kande sai hawaye take tana ba da haƙuri ana zane mata jika.

 

Mai gari kuwa baki ɗaya jikinsa ya kacame da azabar zafi ga yarinyar sai jijjigashi take tana ƙara wahal da shi.

Ganin idan ya biyema mutanen gun yarinyar zata kashe shi a banza yasa ya jefar da bulalar yana hargagin "Gobe ma ki sake ƴar jakar Uba ."

 

Amma me ? Lantai taƙi fitowa daga rigarsa sai ƙara ihu take tana wasan kura da shi.

Tun yana daurewa yana yakice ta tana ƙara shige masa har dai bai san lokacin daya ce da ƙarfin gaske ba, "Ke don Ubanki idan ba ida kashe ni za ki ba ki ƙyale ni haka nan na tuba."

 

Sai waje yayi tsit ba mai magana domin dai sai yanzu suka ankara da yadda bugun yake ashe reshe ne ya juye da mujiya domin mai gari duk ya fice hayyacinsa neman kwatar kansa yake da gaske yarinya ta shige tana ta ihu tana wujijjiga shi ga jikin tsufa.

 

Inna Kande data lura Lantai zatai kisan kai ita ta je ta ɓanɓarota daga jikin mai garin.

Ta kuwa fito tsaye tayi wuƙi-wuƙi da ita ba hawaye ko ɗis a idanunta.

 

Mai gari ya ruɗe ya dinga cewa, "Na kore ku daga ƙasata  yau za ku barmin ƙasata, kin ji na gaya maki Kande ?

 

Abin kamar wani zauci don haka kowa ya sunne kansa ƙasa ban da Lantai dake dubansa tana dariya ƙasa-ƙasa kamar wata surukarsa.

 

Mai gari kaɗai yasan abin da yake ji don haka ko ƙara kallon mutanen wajen bai ba balle ya kalli inda Hure take mai kawo ƙara ya shige gidansa hada gudu .

 

Lantai ta kwashe da dariya tana nuna yadda yake yin maganar.

 

Ai sai kowa yayi ta kansa tabbas yarinyar hatsabibiyar gaske tunda taima mai gari haka babu wanda ba zata iya aikatama abin da ya fi nasa ba.

 

Lantai ta isa gaban Hure ta dungure mata kai ta ce, "Yau da kin sake bulala ɗaya ta sauka kaina Allah sai na baki mamaki kuma ki ban kuɗin Malam Muntasir tunda ba bawanki bane kuma ba ɗanki ba balle ki ce ladar haihuwa ya baki."

Hure ganin abin da Lantai taima mai gari yasa ta kwance ɗaurin zanenta ta fito da kuɗin ta ƙirga ta bata tana kyarma.

 

Lantai ta amshi kuɗin taba Inna Kande ta ce, "Nufi gida Inna Kande ni ina nan sai na ida karance wannan littafin a kan kujerar mai gari domin mai littafin yafi mai gari daraja nesa ba kusa ba don haka alfarma ce zan yi ma mai gari in zauna kan tsohuwar kujerarsa in karanta littafin babban mutum kamar jarumi Nasimat Wallahi."

 

Inna Kande ita dai duk da tafi kowa sanin halin Lantai amma batai tsammanin abin Lantai ya kai haka ba.

 

Lantai kuwa ta zauna ta cigaba da karatun littafinta har  duhu ya fara ta aika cikin gidan mai gari tace, "A bada fitilar mai gari."

Da yake yaron mai gari ne ta aika kuma tsoronta yake don tasha naɗa masa kashi yasa ya je ya amso fitilar domin mai gari sashensa ya shige ya cire kayan yayi ta rawar disko shi kaɗai saboda ko zama ya kasa ga alama ɗuwawunsa sun kumbura ma, ko sallar kasa fita yayi , a nan cikin gidan yake ta kai da kawowa ga zazzaɓi daya rufe sa kai tsaye ga ƙasusuwansa dake ciwo ba arziƙi.

 

Cewa yake yana ƙarawa, "Yau naga fitinanniyar yarinya masifaffar gaske ni mai gari guda ina zani da bala'in wannan yarinyar?"

 

Lantai taita karatunta har na tsawon wani lokaci duk wanda ya zo ya ganta sai ya koma baki alaikum don sun tabbatar da yarinyar akwai abin da ta taka take wannan al'amari.

 

Data ga dare yayi sai ta rufe littafin ta haɗa da fitilar ta nufi gida abin ta tana haska fitilar .

 

Musa na gidan Inna Kande Na ba shi labarin abin da Lantai tayi a gidan mai gari sunata dariya sai gata da fitilar mai gari.

 

Musa ya razana yana nuna ta da yatsa "Ke Lantai wai wace irin yarinya ce ke fitilar da duk nan garin ba a yadda wani ya je Maraya ya siyo irinta ba saboda ta mai gari ce ita ce a hannunki ?

 

Lantai ta kwashe da dariya ta ce, "Ai sai dai ya sai wata domin na samu ta karatun littafin Jarumina Nasimat na rantse da Allah ko mutuwa mai gari yayi a yau ta fita cikin gadonsa don naji malamin islamiyyarmu yace komi na mutum idan ya mutu ya zama na gado."

 

Namanta ta janyo ta cigaba da ci ita da Inna Kande Musa ya kakkaɓe kayansa ya fice yana cewa ba zai ci naman mugun mutumin nan ba Barbushe ya zo ya farka masa ciki a banza.

 

   Washe gari sai ga ƴan aike daga gidan mai gari ana neman Inna Kande Amma kada ta kuskura ta je da jikarta Lantai ita kaɗai mai gari ke son gani ban da Lantai.

 

 

To ko Lantai zata je ko bata zuwa ?

Inna Kande ta je ita kaɗai kamar yadda aka ce ko kuwa ?

 

 

Haupha