MAMAYA:Labarin Soyayya Tsakanin Mutum Da Aljan, Fita Ta Takwas 

MAMAYA:Labarin Soyayya Tsakanin Mutum Da Aljan, Fita Ta Takwas 

MAMAYA:

 

 *Shafi na Takwas*

 

 

 

Bilkisu ta dubi Shema'u cikin hawaye tace, "Ban san abin da nayima Mal Aminu ba ya tsananeni bai son ganina cikin makarantar Islamiyyar nan ,,

 

Shema'u ta goge hawayenta ta dubi Bilkisun tace ,

"Gaskiya yakamata ki faɗi a gidanku a ɗauki mataki kansa domin abin nasa yayi yawa,,

 

Gaba ɗaya ƴan ajin sun natsu suna jin abin da ya faru cikin haushin lamarin.

 

"Maganar gaskiya idan ke bazaki magana to mu zamu je muyi gun Malam Surajo yasan abin da ke faruwa dan akwai cutarwa a lamarin gaskiya ,, (inji wasu daga cikin ƴan ajin nasu )

 

 

Haka dai sukaita bata haƙuri suna nuna mata idan ya ƙara to tabbas zasu ɗau mataki kan lamarin ko shakka babu .

 

 

 

 

Tun da ta doso gidan nasu taji hankalinta ya tashi , tana ji a jikinta akwai wani babban lamari dake faruwa cikin gidan nasu , fatanta Allah yasa ta iske alheri .

 

Tsabar yanda take jin faɗuwar gaban yasa ta manta da yin addu'ar da tasaba yi duk sanda zata shiga gida ,kai tsaye ta faɗa cikin gidan hankalinta a tashe .

 

 

Babu kowa gidan kasancewar ƙannenta idan suka tafi tun safe sai yamma ƙwarai suke dawowa makarantarsu a haɗe take da boko da islamiyya.

 

Har ta nufi ɗakinsu sai ta jiyo kamar alamar motsin Innarsu a ɗakinta, ga alama aiki take mai ɗan yawa dan  daga gun tana jiyo ƙarai saukewa da ajewa daga nan inda take .

 

Kai tsaye ɗakin Innar tasu ta nufa dan ganin aikin da take yi haka cikin ɗakin.

 

Nan ma cikin rashin sa'a ta faɗa ɗakin Innar tasu babu sallama .

 

 

Saurin ja da baya tayo domin ganin babu Innarsu a ɗakin sai wata mata mai mummunar fuska amma kuma fara ce tas da ita irin farin nan da ake kira zabaya , ba abin da matar keyi sai wani zagaye ɗauke da jan kasko tana furta wasu ƙananan maganganu da mabanbanta yaruka .

 

Ido huɗu su kayi da matar wanda hakan yasa kan Bilkisu muguwar sarawa ta ɗora hannunta kan goshinta , bakinta ya kasa furta ko da kalma guda .

 

 

Cike da dariyar samun nasara matar ta wangame wawasheshen bakinta ta bushe da dariyar ƙeta .

 

 

"Bilkisu kinyi kuskuren haɗuwa da Ni a wannan ranar , domin yau babu abin da zai hanani ɗaukarma yaya malam fansar abin da kikai masa ,,

 

 

Ga alama ita Bilkisu ta rasa tunaninta na wucin gadi, dan ida zamewa tayi a gun cikin sigar barci mai nauyi ya kwasheta .

 

 

Cikin ƙanƙanin lokaci wasu halittu suka bayyana cikin ɗakin kowanne da kalai halittarsa da irin kalan jikinsa .

 

 

Gaba ɗayan su suka zagaye Bilkisun suna ƙare mata kallo, zuwa can suka dubi junansu suka kwashe da dariya mai karfi da firgitarwa ainun.

 

"Ya kamata mu ɗauketa mu kaita fadar Yaya Malam dan ya yanke mata hukunci ko ya huta da azabtar da ruhinsa da yake duk bayan mako ,, (Furucin matar da Bilkisun ta iske a ɗakin kenan ga sauran halittun da suka bayyana daga baya )

 

Ɗaya daga ciki yace "Allah bazamu kai ta gunshi ba domin yace kashe ta zai yi , Ni kuma ina farin ciki idan bata tsoro tare da masifaffiyar Gyatumarta ,,

 

Sai wasu daga ciki suka amince da kar a kaita ɗin a barta suita shan nishaɗi da ita da Huraira kawai zaifi .

 

Wasu kuma suka ce ai sai an kaita ba fashi tun da yau tazo hannu jiran mi zasu tsaya ?

 

Cike da ɓacin rai ta farin tace, "Kun san dai Yaya Malam tsab zai hukunta mu kan lamarin nan dai ko ?

 

 

Sadda kansu ƙasa sukai su dukan , domin sun san ba karya tayi ba Yaya Malam bai da kirki bai da haƙuri musanman da abin ya shafi Bilkisun to zai iya komi ga kowaye ma.

Sai dai wasu daga basu aminta da maganar tafiyar da ita ba , dan ba karya suna jin daɗin yanda suke firgita masifaffiyar Gyatumarta Huraira duk sanda suka so , dan irinsu daɗin wasane dasu ga resu, tunda ba damu da addu'a ba kwata-kwata ,(su kuma Aljanu na jin daɗin leƙema duk wanda bai damu da addininsa yanda ya kamata ba Allah ya tsaremu)

 

 

Haka sukai ta jayayya tsakaninsu har na tsawon wasu daƙikai lokuta .

 

 

Malamtsakaninsu ya shigo gidansa bakinsa ɗauke da sallama, ganin gidan kamar ba kowa ya nufi ɗakin Huraira dan ganin ko barci take .

 

Da sallama ya yaye labulen ɗakin sai dai ba Huraira ba alamar ta sai Bilkisu dake kwance ƙasa tana sheƙa barci ko kayan makarantar bata cireba .

 

 

Ahankali ya fara tadinta "Bilkisu ɗiyar albarka, ke Bilkisu ɗiyar albarka maza ki tashi ba kyau barcin yamma kinji ,,

 

 

Mafarki take gata cikin wasu halittu marassa kyan gani, haƙoran su tamkar girman turamen dakan mata , kowane yana da alshe sama da talatin a bakinsa, cikin idanuwan su wani koren hayaƙi ne ke fitowa, sai faɗa suke ya junansu wasu na yunƙurin taba jikinta wasu na hana waɗancan taba jikinta , sai wata

Kabceciyar mata wadda gaba ɗaya ba'a ganin fuskarta saboda wani katon kullutun abune kan fuskar yayi tsawo kamar irin shantu ɗin nan .

 

Sai kumbura take ga alama ranta a ɓace yake dan hayaƙi ne ke fita daga jikinta mai kalar ja ,tamkar zafin wuta haka hucinsa yake idan ya tunkaro inda kake.

 

Babu yanda bataiba dan karanta addu'a amma bakinta yayi mata nauyi bata iya ɗaga koda halshenta .

 

 

"Bilkisun albarka karanto min suratul junnu ,,

 

Muryai Baban su ce taji yana bata umarni sai kawai ta samu kanta da fara rero karatun Alkur'ani mai girma.

 

Abin da yasa halittun yin girgiza suka ɓace kenan bat.

 

 

Malam.ganin kamar batajin daɗin barcin sai ya samu kansa da tadata .

 

 

A firgice ta farka tamkar wadda taga  gagarumin abin tsoro .

 

Kallonta Mal Ahmad yayi yana nazarin wani abu .

 

 

"Anya kuwa Bilkisu kinyi addu'a kafin ki kwanta barcin nan ?

Ko da yake koda kinyi addu'ar ma babu kyau barcin yamma yana kawo ciwo da damuwa ,,

 

Ita dai ido kawai tabi shi dashi domin kuwa bata da abin cewa .

 

 

Jikinta sanyi ƙalau ta fice daga ɗakin, dan bata da abin cewa kan lamarin baki ɗaya.

Major Nasir zaune cikin tunanin abin da ya hana Bilkisu buɗe sakonsa yake, ya saka mata sabuwar waya a ciki wadda zasu dinga magana cikinta dan har sim ya saka ciki amma ko da yaushe ya kira kashe wayar take abin ya sashi cikin damuwa , kar dai ace  Innar tasu ta bata da tabude tabbas zai koma ya dauki mataki akan Innar.

 

Shiru-shiru ba Inna ba alamarta har aka gama sallar ishsha'i dan haka suka fara tunanin ko lafiya ?

 

 

Ya kamata muji abin da ya faru da Innar tasu gaskiya .

 

 

Nagode da addu'ar ku gareni sosai .

 

 *Taku Haupha!!!!