KUSANCI: Fita Ta Farko

KUSANCI: Fita Ta Farko


KUSANCI: Fita Ta Farko

NA

HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM 
(Mrs Aliyu mayere)
          

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
           
       ........  Page 1

            SHIMFIDA

     Kaduna 
Unguwar sarki
Karfe 2 na dare


       Cike da tashin hankali gami da gajiya da masifa da bala'in da sajeeda ke zuba masa,wanda tunda ta fara ba ta huta ba, cikin matsanancin fita hayyaci take, domin ji take kamar duk duniya a Lokacin idan aka bincika ba za'a sami macen da ta fita shiga tashin hankali da damuwa ba, domin Bakil ya zo mata da maganar da ba ta taɓa zaton jinta daga gare shi ba a wannan lokacin da ta gama dammarar zama da shi ita kaɗai ba tare da ta raba shi da ko wace mace ba a duniya.

Bakil ya dubeta idanunsa jajir da alamar ya kai bango, ma'ana sajeeda ta fara tuke shi, cikin wata dishasshiyar yace " Duk abinda zaki fada, da kuma duk irin rashin kunyar da zakiyi min, basu zasu sa na fasa abinda na yi niyya ba,don haka ki cigaba kiyi ta yi, tunda idanunki sun rufe kin kasa gane baƙi da fari, kamar yadda ki ka manta ni waye a gare ki, tun karfe tara kike yin duk abinda kika ga dama". Ya numfasa cike da takaici sosai,
    Ya daga kai ya dubi agogon dake makale a bangon falon , sannan ya dawo da kallonsa kan sajeeda wacce gaba daya ta fita hayyacinta saboda bala'i sannan yace "Har zuwa yanzu karfe biyu da minti biyar na dare ba ki gaji ba, ba ki huta ba, ina son ki sani duk abinda Allah ya ƙaddara babu wani mahaluki da ya isa ya hana,  garama ki yi hakuri kisa ma kan ki dangana".
    Sajeeda ta aje wani nannauyan ajiyar zuciya sannan tace cikin dishasshiyar Muryar da ta fara galabaita da fita.
   "Yaya Bakil, idan kana tunanin zan saduda na rungume hannayena na sa maka ido, ka kashe min rayuwata to ka yi kuskure, domin kara aure a gareka tamkar kashe min rayuwata ne,".
   Ta kara daga murya tace "Baka isa ka wulakantani ba, kwata kwata yaushe muka yi auren , shekara huɗu kacal amma don tozarci da son ganin iyakata gami da butulci shine zaka ce zakayi min kishiya, kamata duk izzata ace yau ni ce zan zauna da wata mace a matsayin kishiya a ƙarƙashin inuwar aurenka, wannan ai abin kunya ne a gare ni, don kuwa sam a cikin lissafi na da tsarina babu zama da kishiya "

    Bakil ya yi mata wani irin kallo ,ya na matuƙar mamakin irin kalaman da ke fita daga bakinta, tamkar ba sajeedar da ya sani ba, mai gudun fushinsa da son faranta ransa, yau magana ɗaya tasa ta canja ta juya ta dakko wani hali da bai taɓa sanin ta na da shi ba.
Yace "kuskurenki na farko kenan da ki ka ɗauka daga ke babu wata, sanin kuma halin kishinki yasa tun farko ban sanar da ke komai ba, a game da maganar ƙarin aurena, don kamar yadda na yi tsammani hakance take faruwa, ki na da son Kai sajeeda, da kuma tun farko kinsan wacece Jawaheer a cikin rayuwata da ba ki wahalar da kan ki wajen azabtar da ruhinki da wannan mugun kishin ba".
   Cikin tsananin tashin hankali Jawaheer ta zube gabansa tana kuka sosai me karfi tana cewa "shin me na yi maka , ta ina na kuskuroka da zaka min wannan mummunan sakayyar, bayan soyayyata da na baka, ban haɗa sonka da komai ba, kasan yadda nake jin kishinka a cikin zuciyata?, ka ji yadda bargona ke tafasa?, ka ji yadda zuciyata ke zafi?, tunda nake a duniya ban taɓa jin tashin hankali da damuwa ba irin na wannan daren, me yasa zaka min haka?"
   Bakil ya girgiza kai gami da kallonta sosai, ya dade baiga mahaukacin kishi irin na sajeeda ba, gaba daya cikin kankanin lokaci duk ta susuce ta fita hayyacinta sai kace ance karshen rayuwarta ya zo. Zahiri mugun kishi masifa ne, ya na jin tausayinta a cikin ransa, amma hakan bazai canja komai ba.

     Ya miƙa hannu zai tabata ta ture hannunsa da sauri ta na yi masa wani irin tsanannen kallo cikin shakakkiyar muryar da ta gaji da kuka tace 

"kada ka tabani"
  Ya saki ajiyar zuciya, sosai yake ƙoƙarin danne zuciyarsa tare da son yi mata uzuri.yace "sajeeda babu ta inda kika kuskuro ni, illa iyaka ina son na auri jawaheer  saboda Allah ya jarabce ni da kaunar ta, babu abinda ki ka sani a game da tarayyata da Jawaheer, sanin halinki yasa tun farko na boye miki koma,i yauma naga ya dace na daina boye miki komai ne saboda aski ya zo gaban goshi, tabbas aurena da Jawaheer babu fashi, domin mahaifinta gobe yake buƙatar ganina, ina kuna da tabbacin maganar auren mu ce tasa ya kira ni, domin wannan shi ne lokacin da ya dibar min, to meye amfanin na ci-gaba da boye miki abinda komai daren dadewa dole sai kin sani,domin ba ni da wani zabi da ya wuce na aureta......?
  " Ka aureta ni kuma ka kashe ni ko? Na sani kana sonta ba sai ka fada ba, ni kuma ba ka sona baka kaunata shi yasa kake kwadayin ka rushe min rayuwata , ka dora min bakincikin da babu ranar gogewarsa, don haka zan cigaba da yaki da kai da ita har sai na ga bayan kudurinku,"
  Yayi mata wani galabaitaccen kallo yace "Ban yi Miki alkawarin da ga ke ba zan kara aure ba, don haka babu wanda ya isa ya takura min na fasa aure domin kuwa rayuwata ce kuma dole a barni na yi yadda na ga dama da ita".
     Ta dube shi a fusace ido na zubar hawaye tace"To shikenan,  mu zuba ni da kai, kuma ina tabbatar maka da cewa kai da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali har a bada a gidan nan".
     Sosai ya gaji da wannan sa'insa ɗin da suke yi, ya kuma tabbatar a bak'ar zuciya irin ta sajeeda zata iya kaiwa har safe ta na  wannan jarabar, ba tare da ta gaji ba 
   Hakan yasa ya mike ba tare da ya kara cewa uffan ba ya nufi dakinsa.
   Da saurin gaske ta mike da ga durkuson da ta yi, ta sha gabansa, cikin masifar tace "ina zaka? Babu inda zaka tafi yadda ba zan iya bacci ba kaima ba ka isa ka runtsa ba".
   A fusace ya nunata da hannunsa yace "ki kauce ki ba ni waje, ni ba shashasha bane da zaki sani a gaba da masifa da bala'i akan abinda kika san ba zai yuwu ba, don haka na gaji ki matsa ki ba ni waje".
   Ta ƙara babbake hanya cike da rashin kunya take faɗin "bazan matsa ba sai dai ka bi ta kaina".
   Sajeeda ta gama kaishi bango , don haka cikin matuƙar fusata yasa hannu ya ture ta da karfi sai da ta fadi ƙasa hannunta ya bugu da tiles din falon.
   Bakil bai saurari irin ihu da bakaken maganganun da take gaya masa ba. Kamar ta sha kwaya ya yi shigewarsa daki, lokaci daya ya murza makullin kofar ya rufe.
     Hakan yasa duk yadda sajeeda ta so da ta bude kofar hakan ya faskara, ba ta damu da irin zafin da hannunta yake ba, domin zafin da take ji acikin zuciyarta ya wuce duk yadda ake tsammani, ta yi ta buge bugen kofar harta gaji, Bakil yana zaune a gefen gadonsa duk yadda za'a fasalta yadda yake jin zafin abinda sajeeda take yi ba za'a gane ba.
     Gaba ɗaya ji yayi son da yake mata yana kokarin ficewa a ransa, yasan sajeeda ba ta da hakuri ta na kuma da shegen kishi amma bai san abin nata ya kai irin wannan matsayin ba.
   Shin tana tsammanin wannan faɗa da tashin hankalin da take yi , shi zaisa ya janye daga kudurinsa na auran jawaheer.
   Lalle idan hakane kuwa tayi babban kuskure domin duk duniya baya jin akwai abinda zai hana masa auren jawaheer idan ba Allah ba. Ya kuma sani idan tsananin addu'a nasa Allah ya baka abinda ka ke so, to tabbas yasan Allah zai mallaka masa Jawaheer, domin bai san iya lokacin da ya ɗauka ya na addu'ar Allah ya ba shi Jawaheer a matsayin abokiyar rayuwarsa.
    Domin tun da yake a duniya babu wata halitta da yake so sama da son da yake ma jawaheer.
  Babu abinda sajeeda ta sani a game da soyayyar da yake ma Jawaheer domin ko shi baisan wane irin so yake yi mata ba.
    Sajeeda tayi kuka a wannan daren tamkar idanunta zasu tsiyaye, tuni jikinta ya dauki zafi, kan tiles din falon ta kwanta tamkar matacciya , duk wani sassa na jikinta radadi yake yi mata, a tsarin rayuwarta babu zama da kishiya shin ta yaya zata bari Bakil ya yi mata kishiya, kishiyar ma ta wulakanci, shekara huɗu kacal da aurensu, ko daɗin auren ma ba ta gama sani ba, domin yanzu ne ta fara jin itama macece, ko haihuwa ba ta yi ba, wannan ai abun kunya ne a gareta ace har ya hango wata yace kuma zai aureta, sannan kiri kiri ko kunyarta baya ji a gabanta yake iya faɗin ya na son Jawaheer, shin wacece wannan Jawaheer din da take son ta tarwatsa mata rayuwa?. Shin Bakil ya manta cewa 
      ba ta haɗa sonsa da komai ba ne, kuma akansa babu abinda ba zata iya ba. ina ma lefin ya bari ta kwashi shekaru ta zuba ya'ya yadda babu wata da zai aura ta iya gogawa da ita.
     Idanunta sun dauki zafi , babu wani abu da zai iya faranta ranta ko cire ta da ga cikin wannan kangin face Bakil yace ya fasa auren nan .
     Yadda sajeeda bata runtsa ba , haka Bakil bai wani runtsa ba, domin ko bacci ya fara kwasar sa kukan sajeeda yakan tashe shi.
   Har akayi kiran sallar asubahi , sannan Bakil ya tashi ya dauro alwalarsa, a gida ya gabatar da raka'atanul fajir. 
     Sannan ya bude kofa ya fito da nufin tafiya masallaci.
   Zaune ya tadda sajeeda a kasa ta zuba tagumi, akaro na farko ya ji tausayinta ya kamashi domin dai tayi nisan da bata jin kira, kishi ya rufe mata ido tana neman ta yi fito na fito da Ubangiji.
   Bata ko dubi inda yake ba, shine ya dakata a gabanta yana kallonta, tamkar babu abinda ya faru tsakaninsu a daren jiya.
   Yace "An kira sallah, ki tashi kije kiyi sallah".
  Bata tanka ba, shima kuma bai jira tankawar ta ta ba yasa kai ya fice zuwa Masallaci wanda baida nisa da gidansa.
   Ko da aka idar da Sallah, baiyi tunanin komawa gida ba, kasancewar asabar ce babu aiki, kuma baya son komawa gidan saboda gudun tashin hankalin sajeeda, don ba ya tunanin ta hakura tabbas yasan yana komawa gidan zata dora daga inda ta tsaya.
     Hakan yasa ya yi zamansa a cikin masallacin, ya dakko Kur'ani ya cigaba da karatunsa.
     Ya dade acikin masallacin
Don kowa sai da ya watse ya bar shi aciki. Karfe tara saura ya tashi ya gabatar da sallar walha bayan idarwarsa ya dade ya na addu'a akan bukatunsa masu yawa.
   Kafin ya tashi ya nufi gidansa yana rike da casbaha ya na ja.
   Sosai yake kokarin ya ƙara tusama kansa hakuri da juriya agame da duk wani abu da zai cigaba da shiga tsakaninsa da sajeeda, duk da yasan ta kusa kai shi bango ta kusa Kure dukkan hakurinsa.Ba ya tunanin idan ta cigaba da nuna irin wannan halin agare shi zai iya jura,saboda shi ma mutum ne kamar kowa ya na da zuciya a cikin kirjinsa, ya kuma san mai daɗi yasan mara daɗi, sannan a matsayin ta na wacce take karkashin sa sam bazai iya ɗaukar irin wannan rainin daga gareta ba.

  Har ya isa gida cikin sake sake yake. Gidan a bude yake sai dai babu alamar motsin mutum a ciki.ya yi zaman kusan mintuna biyar a cikin falon amma bai ji duriyar sajeeda ba. Ya so ya jure ya cigaba da zama a falon ba tare da ya san halin da take ciki ba , amma sai ya ji ya kasa samun nutsuwa dole tasa ya tashi ya nufi dakin ta amma bata ciki, ya bude banɗaki nan ma bata , ya cigaba da kiran sunanta amma shiru.
   Ya fito ya shiga kicin nan ma bata ciki,babu kuma alamar an shigo cikin kicin din.
  Da sauri Bakil ya koma falo ya dakko wayarsa ya danna sunan sajeeda hotonta da sunanta na my wife ya fito a allon wayar tasa , sai dai wani abu da ya ƙara dasa damuwa da tashin hankalin Bakil shine irin yadda wayar ta yi ta kuka harta gaji ta katse ba tare da sajeeda ta ɗauka ba.
   Bai hakura ba haka ya cigaba da kiran wayar amma ba'a dauka har ya gaji da kira.
  Ya koma ya zauna yana tambayar kansa, shin ina sajeeda ta shiga?.
    Rashin sanin amsar tambayar, yasa ya ƙara tashi da sauri ya ƙara komawa dakin ta, so ya ke ya samo wata shaida wacce zata nuna masa inda sajeeda ta tafi.
    Kai tsaye wadrof din kayanta ya wuce ya bude yana nazarin cikinta.
   Sosai ya fahimci babu mafi yawa daga cikin kayanta ta kwashesu , ya maida ya rufe gami da kallon jerin akwatinanta, nan ma ya fahimci babu akwati daya hakan ya tabbatar masa da cewa aciki ta zuba kayanta.
   Falo ya dawo ya zauna, yanzu dai ya sami nutsuwa saboda yasan duk inda sajeeda zata je bazai wuce dandume ba.
   Ya lumshe idanunsa, zuciyarsa na saka masa abubuwa da dama, tabbas abinda sajeeda ke so bazai yuwu ba, ko alkawari yayi mata bazai kara aure ba to akan jawaheer tsaf zai warware wannan alkawarin, da kuma sajeeda tasan matsayin da jawaheer take da shi acikin rayuwarsa da bata batama kanta alokaci ba akan dole sai ya fasa aurenta.
    Domin idan bata sani ba, son jawaheer da son aurenta zai iya sawa ya rabu da sajeeda ba tare daya dubi zumuncin dake tsakaninsu ba, domin akan jawaheer ba ma ita ba yana jin zai iya rabuwa da kowa akanta.
   Domin shi yake tare da zuciyarsa a kirjinsa shi kuma yasan irin tsananin soyayyar jawaheer da ta cika cikin zuciyar tasa, shi kansa zai iya bugan kirji yace baisan adadin son da yake mata ba, abu daya dai ya sani numfashin sa yana tattare da kasancewarsa da jawaheer ne.
   Har cikin zuciyarsa baya son ya nuna ma sajeeda yana son jawaheer fiye da yadda yake sonta, saboda baya son ta ji babu dad'i , amma tabbas yasan an kawo gabar da zata san hakan.
   Bakil ya dade zaune yana tunani ya saka wannan ya kwance wannan, daga bisani ya tattara komai ya aje ya tashi ya shiga wanka.da kansa ya haɗa coffee ya sha bayan fitowarsa da ga wankan.
   Domin idan da sabo ya saba hadama kansa breakfast domin tun da suka fara takun saka da sajeeda,wato tunda ya fara gaya mata ya na son ƙara aure, ta sakar masa ragamar kula da kansa, shi yake yi ma kansa komai a gidan, tamkar ba shi da mata, bazai iya cewa ga rana ta karshe da sajeeda ta bashi abinci da hannunta ba. Daren da ya gabata shi ne daren da ya tsaya ya gaya mata gaskiyar da gaske fa auren zai ƙara ba wani boye boye, shi ne ta karasa haukacewa gaba ɗaya.

    Yau itace ranar da Alh Nuraddeen  canji ,ya bukaci ganin Bakil ,duk bugun agogo sai ya duba saboda ya ga karfe nawa ne, domin karfe biyu ya ke son su hadu.
    Karfe daya da minti biyar ya dawo daga masallaci sallar azahar, daga nan ya shiga shirin amsa kiran mutumin da yake ganin kima da darajar sa matuka , dattijon kirki me dimbin cikar kamala wanda duk arzikin da yake da shi bai sa shi yin dagawa ko kyamatar talaka ba, yana da matukar mutunci wannan yana daya daga cikin dalilin da yasa soyayyar yarsa jawaheer ya  ƙara kama zuciyarsa.
   Ya dade yana jiran zuwan wannan ranar da zai ji kira daga Alh Nuraddeen canji domin dukkan burinsa anan ya tsaya.
   Duk kayan da ya dakko zaisa sai ya ji basu dace da zuwa gidan Alh Nuraddeen canji ba, haka ya dinga sa kaya yana cirewa daga bisani dai ruwan idonsa ya kare akan wani tattausan farin boyel wanda ɗinkin ya dace da boyel ɗin ya kuma yi masa matukar kyau.
     Domin Bakil irin mazan nan ne masu sassanyan kyau, wato irin kyan da akan dade ba'a gano mutum kyakkyawa ba ne sai ka dade kana kallonsa sannan zaka fahimci yana da kyau, ba fari bane wankan tarwada ne, yana da tsayi sannan yana da cikar jiki, ba ramamme ba ne.
   Dan sajensa ya kara kawata kyawun fuskarsa.ya murza bakar hula akansa, haka zalika ƙafarsa bakin takalmi ne me kyau, tsintsiyar hannunsa tana daure da wani kyakkyawan agogo me matukar daukar hankali.
   Jikinsa na fitar da wani daddadan kamshi da dama tuni ya gama bin jikinsa, domin ko bai fesa turare ba a jikinsa kamshin na nan makale a fatar jikinsa. Ya fito tsaf cikin shigar kamala. Sai da ya gama kulle ko'ina a gidan sannan ya shiga motarsa ya fito da ita waje sannan ya fito ya kulle get din da kwado, sannan ya ja motarsa a hankali cikin nishadi da farinciki tamkar babu wata damuwa a tare da shi.
    Ya nufi unguwar malali, In da gidan Alh Nuraddeen canji yake, zuciyarsa har wani bugawa take saboda zakuwa da kosawa ya isa gidan, da dukkan farincikinsa yake cikinsa.

KUSANCI LITTAFIN KUƊI NE N1K NE KU BIYA TA KAN WANNAN ACCT ƊIN 2083086009 HABIBA ABUBAKAR IMAM.
UBA BANK.
KO TUNTUƁAR WAƊANAN LAMBOBIN KAMAR HAKA.
08033484021, 09069067488.

   Ku dakace ni
       Daga alkalamin 
Yar gidan imam.