DUHU DA HASKE: Fita Ta 26
su haɗa ido da manal, ya rame sosai ya fita hayyacinshi ya zama miskili, a kullum sai zuciyarshi ta karye fiye da a irga, idanunshi ne suke kara girma tsaban raman da yake sai fari da yake kara yi, yauma kamar kullum ya shiga kitchen ya dafawa ammi indomie shi dama baya cin komai saide yasha ruwan zafi kawai, tunanin Imran da ameesha da fahad yana neman fasa mishi zuciya, musamman ameesha daya mata wulaƙanci cewar itace ta zubar da cikin jikin manal, bai san da wani ido zai fara kallon ameesha ba, kunya yakeji ya kalleta suyi ido huɗu, wannan tunanin yafi komai tsaya mishi a rai, ɗaukan plate ɗin dake cike da indomie yayi
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 26*
~Da kyar ya iya komawa ciki tareda luggage ɗin yana kallonta, cikin wani irin murya yace "ina mama?"
tana dariya tace "kana expecting na faɗa maka inda take? to ai plan nawa baiyi ba kenan manal umar maidawa tanada wayo tasan kuma takunta, abdool ko kanaso ko bakaso saika zauna dani"
zama yayi a wajen ya ɗaura kanshi a jikin luggage ɗin wani irin ɗan marayan kuka ya fashe dashi ganin ta nuna ammi da bindiga tace "kaga itace shaida to itama zan kasheta sabida kada tazo bakinta ya fara magana"
kuka yake sosai kamar zai shiɗe, a hankali ta aje bindigan taje inda yake zaune ta shafa kanshi tana hawaye tace "ka gafarceni soyayyanka yasa kayi haka abdool, kayi hakuri ka daina kuka"
cikin kuka ya tureta daga jikinshi, kallon ammi yayi wacce ta bashi tausayi da gudu yaje ya rungumeta, itama kuka takeyi mara sauti ta kankameshi kam, yasan idan ya kashe manal to mama ba zata dawo ba hasalima kashe mama zasuyi suce shine ya kashe ta kuma tabbas ameesha zata yadda domin da sunanshi aka siyi bindigan, kanshi ya kifa a cinyar mama yana kuka kamar karamin yaron da uwarshi ta mutu, ammi bubbuga bayanshi take a hankali, manal cikin sanyin jiki kamar wacce babu jini a jikinta ta tashi tana tafiya rike da bindigan duk fuskanta ya ɓaci da jini ga wani hawaye da takeyi, a gefe ta zauna tayi shiru ta haɗa kai da gwiwa itama tana kuka, abdool tun mutuwan umma rabonshi da irin wannan kukan, gashi yau yayi fiyeda yadda yayi a mutuwan umma, tsaban kukan har wani ciwon kai me tsananin ya kamashi atake zazzaɓi ya rufeshi, jikinshi ya fara ɓari, manal ganin haka tazo da gudu tana rikeshi, cikin zafin zazzaɓin ya hankaɗata saida ta bugu da bango a karo na biyu kanta ya kara fashewa, dafa kan tayi tace "ashh kaina"
rungume ammi yayi a wajen bacci ya ɗaukeshi, ammi tayi shiru tana kallonshi gashi dare yayi itama manal kanta a jikin bangon tayi shiru tana hawaye, saida baccinshi yayi nisa sosai tazo da kyar ta zameshi daga jikin ammi ta jashi zuwa cikin ɗakinsu ta kwantar dashi akan gadon, kwanciya tayi a bayanshi ta kankameshi tayi shiru, tana jin zafin da jikinshi yayi, a hankali tace "kayi hakuri Abdool nasan ban kyauta maka ba, amma ya zanyi? ya zanyi? da kai kawai nake samun nutsuwa, idan baka tare dani kullum cikin rashin dariya da rashin jin daɗi nake, idan baka tare dani rayuwata shiru saida ka shigo ka canjamin rayuwa shine zaka fita ka barni? a lokacin da nake murnan na samu sauki zamuyi rayuwa kamar kowa? no no no Abdool idan kaga na rabu da kai saide idan mutuwa kuma na rantse".
Ameesha jikinta a sanyaye har suka karasa gida, shiya rike mata jakanta da wayarta suka shiga ciki, a falo taga momy zaune da hijabi a jikinta, da sauri ta karasa kawai ta kwanta tareda ɗaura kanta a kafar momy, shiru momy tayi tana kallon yadda jikinta yayi datti, zata tambayi yazeed taga ya tafi ɗakinshi, Imran daya shigo yayi kyau cikin kayan ball yace "Anty meesha bakida lafiya ne?"
a hankali tace "ina lafiya"
yace "to ya naganki cikin damuwa?"
ɗago kai tayi tana murmushi tace "ba komai ina nan lafiya lau babu wani damuwa"
zama yayi a gefenta yace "gaskiya ban yadda ba"
cikin tsiwa tace "karka yadda ɗin"
dariya yayi yace "yawwa haka na saba ganinki haka nakeso na ganki kuma"
tsaki taja tana wurginshi da karamin throwpillow, kaucewa yayi yana dariya.
washe gari yana tashi daga baccin yaji jikinshi da nauyi, a hankali ya buɗe ido yana kallonta, tana kwance a kashi tana bacci bata wanke fuskata ba, a hankali komai ya fara dawo mishi, cikin wani irin zafin nama ya tureta ta faɗi ƙasa akan tile karan azaba tayi "wayyooo kafata"
a fusace ya ɗau belt ya fara dukanta yana huce duk wani haushin da yayi bacci dashi, ko gezau batayi ba hasalima rufe ido tayi tana hawaye masu ɗumi, saida ya gaji da dukanta sannan ya durkusa a inda take zaune ya rungumeta ya fashe da kuka yace "manal why? meyasa?"
kuka yake sosai, a hankali take bubbuga bayanshi tana shafa suman kanshi, zamewa yayi kamar wanda aka tsikara da allura yace "zan zauna dake amma ki sani babu ni babu ke ko magana babu tsakanin ni dake duk inda nake idan kika zauna wallahi saina miki illa"
shiru tayi tana ganinshi yaja kayanshi daya shirya jiya duk ya kai ɗakin ammi, yayi wanka acan yayi salla sannan ya hau gadon ammi dake ta kallonshi idonta a kumbure da alama tasha kuka sosai, jan blanket yayi ya rufa har kanshi, manal da kyar ta tashi ta shiga toilet, kayan jikinta ta cire sannan ta kalli kanta a madubi gaba ɗaya ta zama mahaukaciya bayanta ta kalla yadda shatin dukan da yayi mata yayi jajur, kallon fuskanta tayi goshinta da bakinta sun kumbura ga kanta dake azaban ciwo, da kyar ta haɗa ruwan zafi sosai tayi wanka tana kukan zafin da takeji, da haka ta gama wankan ta ɗaura towel ta fito, ko mai bata shafa ba ta ɗau dogon riga me taushi tasa hayewa gadon tayi jikinta yana rawan ɗari ta fara baccin wahala da mugun zazzaɓi.
a haka suka fara rayuwa kullum yana ɗakin ammi yana kula da ita amma baya yadda ko a hanya su haɗa ido da manal, ya rame sosai ya fita hayyacinshi ya zama miskili, a kullum sai zuciyarshi ta karye fiye da a irga, idanunshi ne suke kara girma tsaban raman da yake sai fari da yake kara yi, yauma kamar kullum ya shiga kitchen ya dafawa ammi indomie shi dama baya cin komai saide yasha ruwan zafi kawai, tunanin Imran da ameesha da fahad yana neman fasa mishi zuciya, musamman ameesha daya mata wulaƙanci cewar itace ta zubar da cikin jikin manal, bai san da wani ido zai fara kallon ameesha ba, kunya yakeji ya kalleta suyi ido huɗu, wannan tunanin yafi komai tsaya mishi a rai, ɗaukan plate ɗin dake cike da indomie yayi a hankali ya juya zai tafi, singlet a jikinshi fari da wando dogo, itama yanzu kenan fitowanta daga ɗaki zata shiga kitchen ɗin, sanye take da riga da wando baƙi mara nauyi ta rame ta kara zama fara sosai fuskanta yayi fayau, murmushi tayi mishi da suka haɗa ido, bai kara kallonta ba ya wuce zai tafi tace "good morning my abdool"
shiru yayi ya tafi, a hankali ta jingina da jikin kofan kitchen ɗin ta harɗe hannu a kirji tana kallonshi da kyawawan idanunta, a hankali ta lumshesu ta kuma buɗewa tana kallon bayanshi, yadda yake tafiya ma kaɗai abin kallo ne, bale gashinshi da kuma kyaun da yake dashi, komai nashi abun birgewa a hankali tace "ko a haka muke zaune har karshen rayuwarmu ba zan damu ba my abdool matukar ba zaka rabu dani ba kuma ba zaka koma wajen wata ba, i love you so much my abdool"
taɓe baki tayi sannan ta shiga ciki ta fara shirya breakfast nata da nashi, koda ta gama akan plate tasa ta kai mishi duk da baya ci amma bata fasa kai mishi kullum, fita tayi da nata taje ta fara ci, kallon abincin yayi sannan ya kalli ammi yace "ammi kema kinaso mu bar gidannan ko?"
gyaɗa kai tayi alaman eh, yace "to ammi zamu bar gidannan ki zauna cikin shiri zan saceki mu gudu"
tayi murmushin daya nuna taji daɗi, gama bata abincin yayi sannan ya tashi yace "ki huta bari ina zuwa"
fita yayi daga ɗakin abin mamaki ya nufi ɗakinsu da manal wanda ya jima baije ba tun ranan da abin ya faru, sai yaga ɗakin ya zama mishi sabo, a hankali ya tura kofan ya shiga, tana kwance akan gado tana turawa ƴan company ɗinta sabbin sample na zane sannan tace musu zata fara zuwa bada jimawa ba suci gaba da aiki kamar tana nan, shigowa yayi ta ɗago da sauri tana kallonshi, gani tayi yayi mata murmushi yazo dab inda take ya kwanta a gefenta, da sauri zata tashi ya fizgota ta dawo kusa dashi, rungumeta yayi yana cusa kanshi a kirjinta yace "naso na daure amma kin san bana iya jurewa inada karfin sha'*wa, please koda ba zamuyi magana ba ki barni nayi ko kaɗan ne"
murmushi tayi tana kallonshi yadda yake cusa kanshi a kirjinta itama tayi missing nashi sosai ba kaɗan ba, wannan touches ɗin da dirty talks nashi tafi missing, a hankali ta fara shafa kanshi tace "my abdool koda kasheni nayi na dawo ba zan taɓa hanaka jikina ba"
rufe bakinta yayi da nashi cikin wani irin missing ya fara mata passionate kiss, itama ta rike kanshi tana mayar mishi, a hankali yake bin duk jikinta yana shafawa har ya sauke hanunshi akan b*east nata, ajiyan zuciya ta sauke shima haka, saida ya mantar dasu inda suke shi kanshi da kyar yake iya control na kanshi, a hankali yake kallon fuskanta data rufe ido tana tauna lips nata cikin enjoying abinda yake yi da ita, murmushi yayi shima ya lumshe ido, a ranan sun wuni tare bai kyaleta ba a ɗakin ya kwana tare da ita daga salla sai salla ke rabasu, cikin jin daɗi take bacci, a hankali ya zame jikinshi daga nata yasa jallabiya ya fara duba duk inda yasan tana iya ɓoye abu, da kyar ya samo bindiga ya ɗauke sannan ya ɗauke wayarta ya buɗe kofan a hankali ya fita, ɗakin ammi yaje tana bacci daga zaunen domin bai kwantar da ita ba, ɗan bubbugata yayi cikin kasa da murya yace "ammi tashi"
a hankali ta buɗe ido tana kallonshi, murmushi yayi mata sannan ya nuna mata bindigan da kuma wayar manal yace "mu gudu tana bacci"
wani murmushi ne ya suɓuce akan fatar bakin ammi, ya nannaɗe hanun jallabiyan ya ɗagata sama ya fita da ita, cikin sanɗa yake gudu da ita, ya buɗe kofa zai fita baba megadi ya tsayar dashi, da sauri yace "babu lokacin magana"
baba megadi yace "idan ka tafi kun barni anan wa zai kula dani? tun Alhaji yana raye nake tare dasu da hajiya su suke kula dani, matata da ɗana sun mutu a haɗarin jirgin sama, hakan yasa na tafi na bar garina sabida bazan iya zama a cikin garin ba, na sallamar da duk dukiyan da Allah ya bani masu yawan gaske, nazo nan garin domin na daina tuna matata da ɗana, hajiya da alhaji sune suka kula dani basu taɓa wulaƙantani ba, me zaisa yanzu na zauna basa nan?"
Abdool duk da yana cikin sauri yace "kenan barin garinka kayi sabida ka manta komai?"
gyaɗa kai yayi yace "abdool da kasan wanene ni a garinmu nafi karfin nayi gadi a wannan gidan, kuma koda yau naje garinmu da kai zaka tabbatar da abinda nake faɗa, abdool kuɗin da nake dashi ko Alhajin wannan gidan bai kai yayi gadi a gidana bama bale ya zauna"
baki buɗe abdool yace "to yanzu baba ya zama dole na gudu da ita sabida manal"
yace "na sani kuma nasan halin da take ciki, amma idan babu damuwa idan kanaga ba zan taƙura maka ba ka barni na biku"
a hankali yace "to"
zai fita baba yace "zan buɗe gate na tura mota zuwa waje sai munyi nisa mu shiga mu tada motan"
da sauri yace "to baba"
baba megadi cikin ɗingishinshi yaje ya fara tura motan saida yayi nisa da gidan kafin abdool yasa ammi ciki shima ya shiga baba ma ya shiga ya tada motan cikin rashin sanin ina zasu fara zuwa, gidansu na da ya tuna a hankali yake driving cikin mugun mutuwan jiki ya shiga unguwan har zuwa gidansu na da, gani yayi da mutane a ciki, ya juya zai koma ya tuna da gidansu ameesha, a hankali yaja motan zuwa gidansu ameesha, babu kowa ya shiga yana dubawa, kamar zaiyi kuka ya dawo ya ɗaga ammi ya shigar da ita ciki, gadon Anty da ɗakin ameesha da komai da komai har yau suna nan saide sunyi kura sosai, an jima ba'a taɓa ba, saida ya goge kuran sannan ya kwantar da ammi, fita yayi falo ya samu baba ya zauna kusa dashi, idonshi cike da hawaye yace "baba ya zanyi babu komai a hanuna sannan naji fahad yace an saida gidannan"
baba yasan fahad domin ameesha ta bashi duk labarin a lokacin da tazo wajenshi neman taimako akan mamanta da aka sace, baba yace "ba komai Allah yana tare da kai nima a baya na shiga jarabawa dayawa, asalin ɗan garin Adamawa ne ni, kuɗin da nake dashi har yau bana tunanin koda kwata na rabarwa mutane, tunda naga kana cikin wani hali zanje na ɗauko kuɗaɗena daga yola gobe zanzo dashi nan saimu siye wannan gidan mu zauna a ciki"
yace "na gode baba"
baba ne ya kwanta yace "ba zakayi bacci bane?"
kunyan cewa zaiyi wanka yake, kawai yace "a'a zan koma ɗakin fahad acan zan kwana"
baba yace "to shikenan Allah ya tashemu lafiya"
yace "ameen"
tashi yayi ya shiga ɗakinsu fahad, kallon ko ina yake harda gadon ameesha dana fahad ɗin yana tuna tun daga yarantarsu har zuwa ranan da suka rasu, share hawaye yayi ya shiga toilet Allah ya taimaka ruwan yana aiki nan take yayi wanka domin wankan ya zama mishi dole, fitowa yayi ya shimfiɗa sallaya ya hau salla, da kyar ya idar bacci ya ɗaukeshi akan sallayan,
washe gari baba yace zai tafi yola zuwa yamma zai dawo, abdool ne ya kaishi har tasha yana mishi fatan dawowa lafiya, kafin ya dawo gidan saida ya tsaya ya siyi abinci yazo gida ya dafawa ammi sannan yaje ya tasheta daga bacci, alama tayi mishi da salla, yace "kiyi hakuri ammi ban tuna nazo da wuri ba"
shigar da ita ciki yayi ya mata alwala sannan yazo ya ajeta akan wheelchair ɗin tayi salla, abincin ya fara bata, taki karɓa sabida taga kuka yake, share hawayen yayi yace "kici ammi idan kinaso hankalina ya kwanta"
a hankali ta karɓa ta fara ci, sai can dare baba ya dawo, da makudan kuɗaɗe a cikin jaka ya ɗanka a hanun Abdul, a gaban ammi ya fara basu labarinshi, abdool yayi shiru sannan yace "Allah yaji kansu yasa sun huta"
baba yana share hawaye yace "ameen"
abdool yace "ina neman wani alfarma a wajenka"
"ka faɗa koma menene na amince"
abdool ya kalli ammi dake gyangyaɗi yace "inaso ka auri ammi sabida ka rinƙa kula da ita sabida ni namiji ne ba zaiyi na rinƙa yimata duk wani kulawa ba, amma idan kai mijinta ne na tabbata zaka kula da ita"
da sauri baba ya kalleshi yace "abdool itafa..."
abdool yace "ka amince?"
shiru baba, yayi, yace "ka amince?"
baba yace "to idan na amince itafa?"
yace "ka amince?"
a hankali yace "saina tambayi ƴata"
da mamaki baba yace "wace ƴarka?"
yace "Ameesha"
idanu a waje man yace "ameesha kuma? yaushe ka santa?"
labarin duk abinda ya faru baba ya bashi har kulan da ameesha take yi da ammi a lokacin da suka tafi libya, shiru Abdool yayi hawaye yana sauka a idonshi, cikin rawan murya yace "ka tambayeta idan ta amince"
wayanshi ya ɗauka ya kira numbern ameesha, kira ɗaya tace "hello baba ya akayi?"
wayar a handsfree yace "ƴata kina lafiya?"
tace "lafiya ƙalau baba na daina zuwa tunda su manal suka dawo ina fatan ammi tana lafiya sannan dan Allah ka rinka shiga kana dubata nasan kanada tausayi da amana"
yace "dama akwai maganan da nakeso muyi dake"
da sauri tace "to baba ina jinka"
yace "kin yadda na auri hajiya salma? wato ammi?"
da sauri tace "a,a baba banason rayuwarka ta shiga haɗari manal zata iya saka cikin matsala"
a hankali ya fara bata labarin ɗauke ammi da sukayi daga gidan, har zuwa gidansu da sukayi a yanzu haka suna ciki, shiru tayi tace "yanzu kana tare da ita?"
yace "eh"
da mamakin abdool yaji tace "a gidanmu na da?"
yace "eh"
tace "na yadda da auren amma ka tsaya yanzu zanzo"
kafin yayi magana ta katse wayan.
murmushi Abdool yayi jin bata kira sunanshi bama ya kalli ammi, hanunta ya rike yana hawaye yace "kinsha wahala sosai a hanun ƴar da kika haifa, amma ba komai Allah yana tare dake, kin yadda zaki auri baba?"
a hankali ta gyaɗa kai alaman ta yadda murmushi yayi, ya tashi yace "bari nayi magana da makota sabida ance su suka siyi gidannan idan zasu siyar mana saimu siye"
baba yace "me zai hana muje tare?"
tare suka fita sukayi sallama wani babban mutum ya fito da alama an canja mutanen gidan domin basu abdool ya sani ba, bayan sun gaisa ya kawo mishi zancen su waye masu gidan?
mutumin yace "Allah sarki yayana ne ya siya gidan amma kafin su kauro Allah ya mishi rasuwa yanzu ma gidan yana kasuwa munaso mu siyar mu siyawa marayu abincin da zai jima musu sosai harma suyi karatu a ciki"
Abdool yayi murmushi yace "zamu siya"
kuɗin gidan ta faɗa musu, baba yace abdool ya bada, ya shiga ciki ya ɗauko kuɗin mutumin ya basu takaddu tareda yi musu godiya domin basuyi mishi tayin wulaƙanci ba, Abdool yace "idan babu damuwa zanso ka taramun mutane kamar biyar za'a ɗaura aurene yanzu"
mutumin yace "to babu damuwa zamu iya shiga idan na kirasu domin makota ne?"
abdool yace "eh zaku iya"
tare da baba sukaje asibiti aka yiwa baba gwajin jini, dama ammi kam koda yaushe ana gwada jininta domin ciwon da take fama dashi.
cikin sauri take sa mayafi ta ɗau rakalmi a hanu da gudu ta fita daga ɗakinsu Imran ya riketa ganin tana gudu yace "wait mana anty meesha ina zakije da gudu haka?"
tace "gidanmu na da"
da mugun mamaki yace "meke faruwa?"
murmushi tayi tace "baba megadi zai auri ammi ya saceta sun gudu sun bar gidansu abdool, dama kullum ina tsara yadda zan ɗauketa daga gidancan Imran matar innocent ce sosai tana cikin damuwa"
yace "amma kin samu taɓin hankali ko? kin san me kikeyi kuwa?"
tace "na sani mana"
yace "maman manal ce fa"
taja hanunshi tace "ba zaka gane bane muje zaka fahimci hankalinta"
fahad yace "zan biku nima inaso na kara ganin gidanmu"
tace "okay muje"
momy tana kallonsu suka fita tare, hanan sukaji karan saukowanta da gudu tace "ku jirani nima yau na gaji da zaman gida duk inda zakuje saina biku"
tare suka fita, motar yazeed ne ya tsaya yanzu a cikin gidan, ganin zasu wuceshi zuzu kamar zasu tashi sama ya sauke glass sannan ya cire glass na idonshi wanda ya kara mishi kyau, cikin muryanshi me bala'in daɗi yace "where are you guy's going?"
ameesha tace "gidanmu nada baba megadi yace zai auri ammi ya saceta daga gidan sun gudu"
Imran yaga yayi murmushi yace "Alhmdllh yanzu hankalinki zai kwanta, ku shigo na kaiku"
shiga sukayi su duka ameesha dashi a gaba su hanan da Imran a baya, momy tana tsaye a stair tana kallonsu sun shaƙu da juna suna son junansu sannan suna rayuwa cikin jin daɗi, murmushi tayi har suka fita, Abba ne ya tsaya kusa da ita yana kallon inda take kallo yace "my love tunda babu yara a gida yau muje ki kula dani"
murmushinta me kyau tayi sannan tace "ai zasu dawo"
yace "ki rage wannan kunyan ko taɓani fa bakyayi idan yarannan suna nan nidai yau please tunda sun fita yau babu hayaniya, ki daina wannan kunyan"
zatayi magana yaja hanunta, dariya take yi sosai, ya zuba mata ido momy duk inda kyau yake taje ta ɗauko kuma ta dawo gata innocent magana ma batayi sosai shiyasa yake kara sonta, duk matan daya aura bai samu ta gari ba duk son abinshi suke sai itace kawai take sanshi da Allah hakan yasa yake yawan mata kyauta akai akai.
Yazeed yace "my meesha yanzu baki jin tsoro?"
tace "tsoron me?"
yayi murmushi kawai yasan ta gane shariya ne kawai, kallonta yayi ta madubi ta murguɗa mishi baki yadda ta saba mishi kullum, bakinta ya rike da hanunshi ya matse da karfi, kara tayi tace "dan Allah ka barni"
yace "shashasha"
tayi dariya tace "ka tuna wancan mutumin kenan na wajen aikina nada?"
dariya sukayi tare, Imran yana kallonsu yana ganin yadda suke shaƙuwa sosai kullum suna tare suna cikin fara'a, a hankali ya rufe ido yana tunawa da ya Abdool, ko ina yake yanzu oho, tunda aka shigo unguwansu jikinsu duk yayi sanyi, hanan tayi shiru tana kallon fahad dake kokarin ɓuya ya share hawaye, a hankali ta janyoshi jikinta tana shafa kanshi tace "kar kayi kuka"
ameesha ta sunkuyar da kai tana maida hawayen da suke shirin zuba, yazeed ya rike hanunta yana matsawa a hankali alaman kada tayi kuka, Imran kam kasa daurewa yayi sai hawaye, hanan ce take share mishi hawayen, duk jikinsu yayi sanyi motan yayi shiru, kofan gidan yayi parking cikinsu babu wanda ya iya fitowa, saida hanan tayi musu wa'azi ta basu hakuri kafin suka fita, a hankali suka shiga ammi ce a falo zaune akan wheelchair tana ganin ameesha ta fara kokarin jan wheelchair taje wajenta, murmushi sosai take mata kana ganinta kasan tana cikin farin cikin ganinsu, ameesha tazo ta zauna a gabanta ta ɗaura hannayenta a cinyan ammi tace "ammi nayi kewarki"
murmushi tayi ta shafa fuskan ameesha, ganin yazeez a tsaye ta rike hanunshi ta durkusar dashi kusa da ita tace "ka gaisheta"
a hankali yace "ina wuni ammi?"
shafa fuskanshi tayi alaman lafiya, duk sukazo gabanta suka zauna, ammi sai murmushi take musu duka tasan sunansu domin ameesha tana nuna mata hotunansu tana basu labarinsu, sallama sukaji baba ne ya fara shigowa yana ganin ameesha yace "ƴata har kinzo?"
da sauri ta tashi taje gabanshi ta durkusa ta gaisheshi, zama yayi suka gaisa da kyau, sannan ya fara basu labarinshi sabida yaji su kamar family ɗinshi, duk suna hawaye har ya gama yace "zan aureta sabida halin da take ciki kun amince?"
Ameesha tace "mun amince baba"
sallama akayi saida kan ameesha ya kusa fashewa jin muryan da ko a bacci ta tashi ba zata taɓa mantawa ba, shigowa yayi ya tsaya a bakin kofan kanshi a kasa tunda ya kallesu sau ɗaya bai kara ɗago kanshi ba, a hankali ameesha ta tashi daga gaban baba ta rike hanun imran dana fahad suka raɓa ta gefenshi zasu fita, baba yace "nine na kiraku ba shi ba Ameesha"
cak ta tsaya bata juyo ba sai wasu zafafan hawaye da take yi, baba yace "na yadda zaku tafi amma kuyi hakuri ku tsaya a ɗaura auren"
a hankali ta juyo hanunta a cikin nasu taje ta zauna suma suka zauna a kusa da ita duk cikinsu ba wanda ya yadda ya kara kallon Abdool, wasu maza suka shigo su biyar dattijai suka zazzauna, goro da cingum ɗin da suka dawo dashi aka rarraba sannan baba ya mika dubu ɗari biyu a matsayin sadaki a wajen aka ɗaura auren akayi fatiha, mazan suka fita bayan sun gaggaisa sun gabatar da kansu a matsayin makota, baba yayi godiya suka tafi, Ameesha tace "ammi congratulations Allah yasa iya jarabawanki kenan inada tabbacin baba zai rinka kula dake, baba kaima congratulations ka samu mata me hakuri na tabbata zata kula da kai idan tayi lafiya sannan na baka amananta"
hanun Imran dana fahad ta rike tace "muje"
tashi sukayi harda yazeed da hanan wacce jikinta a mace suka fita tare, tafiya sukeyi babu wanda ya kara juyowa, daidai zasu fita yace "Imran fahad"
cak suka tsaya banda Ameesha data cigaba da tafiya tana jan hanunsu, muryanshi yana rawa sosai ya kira sunansu, cikin hawaye yazo gabansu ya durkusa kasa ya haɗa hannu biyu ya sunkuyar da kai yace "dan Allah...dan Allah..."
ya kasa magana sai wani irin kuka da yake yi, ganin zasu tafi ya ɗaura kanshi akan kafafunsu yana kuka sosai, ameesha tace "ku muje dare nayi"
gani tayi sun kasa tafiya, taja hanunsu da karfi cikin tsawa tace "muje nace"
tafiya suka fara, da rarrafe abdool yaje ya rike kafafunsu banda na ameesha wacce take huci, kasa tafiya sukayi suna jinshi yana kuka sosai, sakin hanunsu tayi tace "okay ba komai sai ku zauna dashi"
hanunta tasa a cikin na yazeed tace "muje"
shima rike hanunta yayi gam, akan idon abdool yana ganinsu suka fita tare harda hanan dake juyowa tana kallonshi cikin tausayi, shiga motan sukayi bata saki hanun yazeed ba, ɗago kai tayi taga Imran da fahad sun durkusa kasa sun haɗa kai da abdool suna wani irin kuka kamar yau suka rasa iyayensu, ɗauke kai tayi tace "muje ya yazeed"
a hankali yace "meesha a karaye kuke fa ku duka..."
gani yayi ta zauna kan cinyarshi ta kunna motan da mugun gudu ta bar kofan, karaf akan idon abdool lokacin data zauna akan cinyar yazeed.
_Jiddah Ce...._
managarciya