HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 42

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 42
HAƊIN ALLAH
   Labari da rubutawa
       
  
Dr. Faisal ya sake jin karaya a zuciyarsa yadda sam yanzu Alawiyya bata ɗauki abin da muhimmanci ba. Ko da yake yasan yadda take daman bata da sauƙi ya yi mamakin yadda ma ta daure ta nuna mai bata fahimci komai ba tun farkon lamarin har kuma ya dinga sauka kan layi tana biye da shi ba alamar rashin fahimta yasan da gaske take a lokacin daya samu sa'ar auren Jiddah da ya gama hayewa amma yanzu don baƙin buƙulu bai samu Jiddah ba ita kuma tana gara shi tamkar wata garaya ko waina a tanda.
Baffa ne ya shigo ya iske shi zaune ya haɗa kai da gwiwa suka gaisa ya wuce ba tare da ya tanka kan abin da ya kawo shi gidan ba.
Yana cikin yanayin ne Baffan ya sake fitowa har ya sauya kaya zuwa marassa nauyi ya zauna ya kira sunansa ya ce, "Faisal daman ina son ganinka kiranka ne kawai ban yi ba. To masha Allah tunda ga ka ai shike nan. Daman abin da nake so da kai shi ne ka fita sabgar Jiddah domin ba aurenka zatai ba, da kanta ta tabbatar min da cewa karatu za tai don haka kar da ka sake kiranta da sunan soyayya na yanke alaƙar hakan a tsakaninku."
Zufa ta yanko mai ta ko'ina yana jin tashin hankali nayi mai sallama. Kenan ba mai iya daidaita tsakaninsa da matarsa kowa ya kawo ido ya saka masu duk abin da take ba mai iya yi mata magana ta daina? Gaskiya ba ai mai adalci ba sam.
Baffa ya tashi ya shige ɗaki yana yi mai Allah Ya kiyaye hanya idan ya tafi zai kwanta ne shi.
Alawiyya ta dubi Jiddah sosai tace, "Me yasa naga duk kin damu ne daga wannan abin? Ko dai kina jinsa ne a zuciyarki daga zuwansa?"
Jiddah tai ajiyar zuciya tace, "Wallahi ban san ya akai ba kawai naji gabana na faɗuwa haka kawai sai nake hango fuskar Prince cikin damuwa."
Wayarta tai haske sai ga pic ɗinta da Prince suna murmushi wani sansanyar kiɗan India na fitowa.
Kasa ɗaga kiran tai, sai da Alawiyya ta ɗaga kiran ta miƙa mata wayar sannan ta amsa cikin sanyin murya ta ambaci sunansa.
Shima kamar haɗin baki ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi Princess tun ɗazun gabana ke faɗuwa duk na rasa me ke damuna ban jin farin ciki ban jin daɗi don haka na kira ki ko naji farin ciki domin nasan ko kuka nake idan naji muryarki sai dariyar farin ciki ta maye gurbin kukan."
Bakinta ya yi mata nauyi ta kasa ko da furta kalma guda.
"Princess ko dai na zo ne? Wallahi baki ji yadda nake ji ba, ina cikin matuƙar damuwa kuma ban san miye dalilinta ba sam."
"Ba sai ka zo ba, ka yawaita karanta innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, zaka ji ka daidaita Prince." Tana furucin ne yayin da hawaye ke zubowa daga fuskarta.
"To amma Princess ji nake tamkar ke ma kina cikin damuwar ai, don Allah me ke faruwa da ke ne? Tabbas akwai abin da akai wanda ba zai mana daɗi ba don Allah miye ya faru ne?" Magana yake da muryarsa kamar ta mai kukan shima.
Cikin dakewa tace, "Ba abin da ya faru Prince, ba kana gun aiki ba? Don Allah ka dage kai aikinka ban da wasa da ja masu hankali don Allah na san halinka fa." Tana jin sautin ajiyar zuciyarsa irin hankalinsa ya fara kwanciya ɗin nan  ya ce mata, "To ki yi min." 
Dariya tai, Prince akwai rigima duk lokacin da su kai waya idan bata ce mai Love You ba ya ce mata love you too ba sai ya yi mata tsogumi ya ce ta ƙi yi mai, tsabar abu har kiss yake cewa sai ta hura mai ta wayar ya ji haka suke ko da yaushe idan suka gama waya sai sun yi ma juna.
Yau kau bata jin zata iya ce mai hakan balle har ta hura mai wani kiss.
"Ni, Ni, Ni, dai ki yi min nace." Da muryar shagwaɓa ya furta hakan.
Dole ba don tana jin son yi ba tai mai, don dai kawai su rabu lafiya.
Alawiyya ta miƙe ta fice daga ɗakin saboda yadda mijinta ke ta kiranta.
Duk da ya fara bata tausai sai ta share tai kamar bata ma ga yadda ya yi tsugunne ba ga damuwa fal a ransa ta samu waje ta kame ta watsa mai ido alamar tana jinsa.
Komai ya kwance mai ya rasa ta ina zai keɓo ta don haka ya tashi da sauri ya rungume ta ya fashe da kuka yana cewa, "Bai kamata ba don kowa ya ƙyale Ni kema ace kin ƙyale Ni ba matata, saboda ke ce farin cikina haka ke ce natsuwata don Allah ki daina azabtar da Ni da wannan mummunan hukuncin naki wanda zai iya nakasar da zuciyata." Kuka yake sosai yana ƙara shigar da ita cikin jikinsa.
Lub tai a jikinsa tana jin yadda yake zuba mata kalaman soyayya masu daɗi da sanyaya zuciya wanda rabon da ya furta mata kalma guda ta soyayya har ta manta.
Sai da ta tabbatar da cewar ya yi laushi sosai sannan ita ma ta rungume shi jikinta tana cewa cikin sanyin murya, "Haba mijina abin tunƙahon rayuwata, mai dasa min natsuwa da kauda min tashin hankali, me yasa ka zaɓi raba tsakanina da wadda ban da kamar a faɗin duniyar nan? Me yasa ka manta yadda na mutu kan ƙaunarka nake biye da sonka lungu da saƙo ne don kawai na tabbatar da cewa nayi kane-kane na hana idanunka da zuciyarka hangen wata ɗiya mace bayan Ni? Don Allah ka daina razana zuciyata ta hanyar nuna kulawar soyayya ga wata mace bayan Ni mijina."
Yana kwance jikinta tana wasa da sumar kansa ya ce, "Nayi maki alƙawarin ba zan sake tada maki hankali ba haka ba zan sake kallon Jiddah da kallon soyayya ba har abada insha Allah zan ɗauke ta tamkar wadda kuka fito Uwa ɗaya Uba ɗaya insha Allah."
Sai ga su sun baje suna ta fira kamar ba su ba, har ta tashi ta shige ɗakin da take ta haɗa mai ruwan wanka ta ja shi suka shige don ya yi wanka ya samu natsuwa.
Jiddah kuwa tana gama waya da Prince sai tai murmushi domin ta lura duk lokacin da waninsu ke cikin damuwa sai gudan ya ji a jikinsa shima ya kasance a damuwar. Ba zata manta ba wata rana da wani ya biyo ta ya dame ta har dai ta gaji ta tsaya kasancewar tana tafiya ne a ƙasa. Sun gaisa sama-sama ya gabatar mata da kansa da sunansa Jameel da sana'arsa ta saida zinari da azurfa a nan Kadunar yana da mata guda da yara biyu mace da namiji. Ba yadda bai ba ta shiga motarsa ya kaita gida ta ƙi don haka ya amshi lambarta da alƙawarin zai kira ta tai mai kwatancen gidansu don da gaske yake ya ga mata shi a karo na biyu rayuwarsa bayan matarsa ta gida.
Suna rabuwa da Jameel wayar Prince ta shigo wayarta tana ɗagawa ya ce mata, "Princess gabana ke ta faɗuwa sosai ina jin kamar wani abu ne zai faru da ke ko Ni marar daɗi don haka na kira ki naji ko kina lafiya?"
Kamar ta bayyana mai abin da ke faruwa sai kuma ta share tace ba komai ya dinga Salati kawai daman haka ne wani lokacin ana jin irin hakan.
Haka ma akwai lokacin da ta sake haɗuwa da wani Abdul shi ma suna rabuwa ya kira ta hankali tashe yana gaya mata yadda yake jin damuwa da faɗuwar gaba na addabarsa.
Hawwa'u (Iyami) ta shigo ɗakin tace "Ɗiyata ana kiranki bakin gate in ji maigadi yanzu."
Sai da tai jim, domin dai tasan ba wanda su kai zai ganta a Yau koma tace yanzu amma sai ta share tunanin tace, "To ace mai ina zuwa ya shigo da shi cikin harabar gidan a ba shi ruwa kafin na fita."
Hawwa'u (Iyami) ta fice tana murmushin yadda kowace rana sai Jiddah ta samu ɗaukaka daga ko'ina kamar ba ita ce ta sha baƙar wahala ba a rayuwarta ba, ko da yake Malam ya gaya mata daman haka rayuwar take idan ka sha wahala da fari ka zo daga baya ka sha daɗi, to ita dai yanzu daɗin ne take sha har ya so yafi na Alawiyya ma, tunda ita a sake take ga maza nan birjik kowane so yake ya samu shiga gunta don haka sai banko alheri suke mata ta ko'ina tamkar babu talauci a duniyar ma baki ɗaya idan akai mata wata kyautar, don ma ta kasance ƴar halak tana matuƙar kula da danginta da mahaifiyarta bakin gwargwado.
Yana zaune sai waige-waige yake tamkar ace arr ya ruga. Kallo guda za kai mai ka tabbatar da cewa duniya tai mai juyin taliyar Hausa da taji wuta. Ya jeme ya rame ya fice hayyacinsa kayansa duk sun yage da ganinsa yasan inda talauci ke kwana yake tashi ko ace ma shi ne talaucin don basu da mara ba.
Sauke kansa ƙasa ya yi lokacin da aka sauke mai ruwa mai sanyi da lemu tare da kayan tsotse-tsotse aka ce tace ya fara sha kafin ta fito yanzu.
Ke duniya ina za ki damu ne? Yanzu nan Jiddah ke rayuwa a wannan gidan mai kama da aljannar duniya? Yanzu nan Jiddah ce a jikin jaridu da gidajen rediyo ake magana kanta?" Shi ne tunanin da baƙon ke yi yana kallon kayan gabansa hawaye na zubowa daga idonsa.
Cike da natsuwa ta nufi inda tasa a sauke baƙon nata, ko a ranta bata kawo komai ba har ta isa inda yake ta ja kujera tai sallama ta zauna.
A firgice ya ɗago kansa ya kalleta sai kuma ya miƙe tsaye sai kuma ya tsugunna ya kama ƙafarta yana cewa, "Don Allah ki taimaka min kar da ki tuna baya ki taimaka ki yi min abin da Ni na kasa yi maki watau halacci ki ceci rayuwata daga ƙangin data afka don darajar Allah Jiddah."
Bata gane shi ba, ga dai shi kamar ta so tasan fuskar amma ta kasa tuna inda tasan fuskar don haka ta janje ƙafarta tace, "Bawan Allah tashi ka zauna ka gaya min waye kai. Wane halacci ne zan maka?"
Sadda kansa ƙasa ya yi ya ce, "Tabbas nasan daman ba za ki iya gane Ni ba a yanayin da kika ganni yanzu ba Jiddah, amma hakan duk ya faru ne saboda sakayyarki da ke bibiyar rayuwata ta hanyar mallakar wata hatsabibiyar da ke ce ya kamata ki zauna inda take."
Sai kanta ya ɗaure ta rasa inda zancen sa ya nufa baki ɗaya ma, don haka tace mai, "Kai haƙuri na kasa gane inda maganarka ta nufa idan ba damuwa kai tsaye mu je kan abin da ya kawo ka guna domin ina sauri ne fita zan."
Ya jima yana kallonta kafin ya nuna kansa da yatsa ya ce, "Ni ne Abubakar wanda mu kai karatu a makaranta guda wanda ya zuba maki yarda da aminci tare da soyayyarsa ya guje ki ya auri wata ya barki ba tare da duba tarin alherin da ki kai mai ba a tarenku ba."
Da sauri ta kalle shi ta nanata sunan, "ABUBAKAR! 
Kansa ya ɗaga mata alamar amsawa ko nuna cewar e shi ne fa.
Kanta ta sadda sai kuma ta ɗago fuska cike da murmushi tace, "Don Allah kai haƙuri Abbakar da kasa gane ka da nayi. Ban san yadda akai ba na kasa gane ka ba."
Hawayen takaici suka zubo mai ya dube ta ya dubi jikinsa ya ce, "Dole ki kasa gane Ni Jiddah saboda yadda na koma ai."
Ta ɗauki robar ruwa mai sanyi ta sha ta dube shi tace, "Abbakar ina aikinka da nasan kana yi? Ina matarka da yaranka domin nasan lokacin da akai ta posting ɗin hoton yaronka a facebook da Media duk da lokacin ban fara chat ba. Ko da yake shi ne abin da yasa na ƙara tsanar waya a rayuwata ma baki ɗaya a lokacin."
Ya goge hawayen fuskarsa ya ce, "Jiddah don Allah ki yi haƙuri na zo ne na baki haƙuri kuma na nemi alfarma gunki don Allah ki tsaya min a shari'ar da za ai da Ni wadda ban aikata komai ba illa son zuciya da zafin kishi ne kawai suka sa matata tai min sharrin da yasa na rasa komai nawa komai ya ƙare kuma na kasa samun nasara kuma an ƙi yanke min hukuncin daya kamata an barni sai yawo ake da ni gari-gari da sunan shari'a."
Jiddah ta gyara zaman tabaran fuskarta sosai tace, "Ban labarin asalin abin da ya faru da kai yadda zan samu damar taimaka maka to."
Abubakar cike da tausayin kansa ya fara bata labarin abin da ya faru gare shi.
               SHEKARUN BAYA
"Lokacin da na ga A'isha na kuma samu labarin Babanta mai kuɗi ne kuma ɗan siyasa mai ci yanzu, sai naji cewar irinta ya kamata na aura wadda zan samu wani abu daga gare ta ba irin ki ba wadda ke ma kanta komai ba, ga yaranki waɗanda ban san ma me kike nufi da su ba idan mu kai aure da su za ki zo min gida ko'ina za ki kai su? Duk lokacin dana tuno ki sai naji nayi tsaki kawai ina jin cewar sam bamu dace da ke ba tunda baki da ko sisi Ni kuma a lokacin da uwar kuɗina sai nake ganin da A'isha kawai na dace tunda Babanta na da kuɗi.
Ban sha wahalar samun soyayya gunta ba saboda yadda nayi fice gun iya kalaman soyayya da iya tsara mace. Hatta Babanta ban samu matsala da shi ba, sai ga mahaifiyarta wadda sai da nayi da gaske sannan ta amince da aurena da ƴarta domin ta raina abin da nake samu a wata na aikina.
Babban abin da na fara samu na ribar neman auren A'isha shi ne motar da Babanta ya ban kyauta, sannan kuma ya maida Ni na hannun damansa a kowane harka nashi.
Cikin lokaci kaɗan ya taimaka min na gama gidana wanda ke ce kika tsara yadda kike son ginin ya kasance. Ba a ɗauki lokaci ba aka saka ranar aurenmu da A'isha wata shida masu zuwa.
Tabbas nayi farin ciki da saka ranarmu da akai, duk da wani lokacin kina ban tausayi yadda kike tsaye kaina komai kina yi min, duk abin da kika siya makaranta sai kin saimin, duk sarin kayan da ki kai akwai nawa ciki bayan ban taɓa sakin jiki nayi maki wata kyauta ta bajinta ba, sai dai kece mai min kyauta kike min gata baki kuma jin komai haka baki taɓa nuna jin haushin yadda ake ma abokanki kyautuka ba amma ke ko da wasa ban taɓa ko saka maki katin wayar daya kai darajar ɗari biyar ba.
Don kar ki gane komai yasa na gaya maki ban da waya amma sai kika ban taki wayar, haka zalika na dinga yi maki ƙarya don kawai baki ganina saboda a lokacin ina cikin hidimar bikina ne da A'isha.
Bayan anyi auren ne na zo gareki da zummar na cigaba da yaudararki har na gama karatuna na tsere daga rayuwarki ashe kin gane nayi aure ki kai min magana kuma kika nuna min ɓacin ranki har ki ka ce min duk wanda ya cuci wani Allah Ya saka mai.
Naso ƙwarai mu shirya kika ƙi baki ɗaya kika tsane Ni kika fita sabgar kowane namiji amma ban ji komai ba sai naga ma a lokacin ai ke kika sani kawai don haka na cigaba da kula da matata na bar ko tuna mai sunanki, idan an kira ma sai nayi dogon nazari nake gane inda na taɓa sanin mai irin sunan.
Lafiya lau muke rayuwa da matata, har ta samu ciki wanda nayi murna kamar me, duk da cewar ina azabtuwa da abubuwa da dama daga matar tawa, irinsu raini bata ganin girma na sam ban isa idan zata fita ba ta tambayeni ba, idan nayi mata magana sai tace tana da kuɗin mota don haka tsayawa tambayar me zatai min? Daga ƙarshe ma ta koyi mota duk inda zata motata take ɗauka kawai ta fice ban isa nace mata don me ba? A haka ta samu ciki na sha baƙar wahala domin daina komai tai na gidan tace ita cikinta ba zai wahala ba, don haka nike komai na gidan wanki, girki, da wanke-wanke duk nike mata su.
Bayan suna da kwana biyu sai ga wata yarinya an kawo mata daga gidansu wai ita ce zata dinga mata reno da sauran aikin gida ita kam bata iyawa. Abin ya ɓata min rai sosai domin na lura duk bayan lokaci sai A'isha ta fito da sabon salon iskanci wanda ban isa nace ga nawa ra'ayina ba kan nata. 
Komai na gidan Aminatu ke yinsa kasancewar yarinyar na da natsuwa da hankali sosai take da tsabta yasa naji daɗi wani wajen na zuwanta gidan.
Babu ruwan A'isha haka take barin yarinyar da yaron ta fice sabgarta don yanzu ita ma ta zama ƴar siyasa don haka bata zama gida ko da yaushe tana waje idan ta dawo gidanma tare da jama'arta take dawowa maza da mata. A takaice dai bata da lokacina ko na Yarona sai na hidimar siyasar da take yanzu nayi mata magana tai min rashin mutunci ta tafi gidansu na ɗauka idan naje iyayenta zasu yi mata faɗa bayan na gama karanta masu zaman da nake da ita sai naga sun goyi bayanta har suna iƙrarin jin zafi nake mata so nake na ga tana zaune kamar yadda nake zaune ina jiran wasu ƴan canji daga gwamnati wanda ba abin da za su yi mata ga iyali ta fara tarawa. Haka dai naita basu haƙuri amma duk da haka sai da ta shafe sati uku bata dawo ba sai dai nike zarya kullum ina ƙara bata haƙuri da iyayenta.
Sai da ƙyar na samu ta dawo, amma fa da sabon salo ta dawo na raini da wulaƙanci, gadara da nuna min isa ko shan waye haka zata ci min mutunci ba ruwanta da mijinta ne Ni.  Yawo kuwa sai tai sati bata nan kuma yarinyar nan take barma yaronta haka bata gayamin zata yi tafiya sai dai idan ban ganta ba na kira wayarta sai ta gayamin ai bata gari ne lafiya nake nemanta? Abin na matuƙar damuna ko da yaushe na dawo daga aiki Aminatu mai aiki nake iskewa ta haɗa min abinci tai ma yaro wanka komai na gidan a hannunta yake. Sannu a hankali sai na fara jin cewa gwara na auri yarinyar tunda ta saba da kula min da gida haka ta iya rainon Yarona tamkar ita ce ta haife shi. Ban ɓoye mata ba, amma sai Aminatu tace min a'a tana tsoron Hajiya A'isha nayi haƙuri, Ni kuma sai na kasa haƙuri domin a lokacin sai A'isha tai wata bata ma ƙasar tana wata ƙasar hidimar ta. Kin san namiji da naci kan abin da yake ganin zai ba shi mafita don haka na dage gun cusa ma Aminatu soyayyata har kuwa nai nasarar saka mata soyayyata a cikin zuciyarta ta amince zata aureni amma ba gidan zata zauna ba zan ware mata gida daban. Na amince domin gaskiya na gaji da baƙar wahalar da nake da sunan ina da aure kuma, kai tsaye naje gun iyayen Aminatu da farko basu amince ba sai daga baya sannan suka amince aka tsaida maganar aure wata huɗu, matsalar da aka samu ita ce, sai na dawo da Aminatu gidana ta ci gaba da zama, ban san wa ya gayama A'isha maganar aurena da Aminatu ba sai gata a fujajan ta dawo ta kama yarinya da duka da ƙyar na ƙwace ta, na tabbatar mata da cewar aurena da Aminatu babu fashi sai dai duk abin da zata yi ta je tayi na gaji da iskancin da take min.
 Mun yi sati guda ana wannan bala'i kwatsam! Rannan sai jin ihun Aminatu nayi ina zuwa na iske A'isha ta caka mata wuƙa a ciki , tsabar ruɗewa tasa na fisge wuƙar daga cikin Aminatu sai kawai jin ƴan sanda nayi a baya na suna cewa "Kar ka matsa daga inda kake ."  A kotu ne naji daga bakin Lauyar A'isha wai ta shigar da Ni ƙara na nayi wa mai aikinta ciki kuma na kashe ta. Nasha baƙar wahala gun shari'ar domin ta ɗauki babbar lauya wadda kowa yasan ta haka sauran Lauyoyi ke shayin buga shari'a da ita watau Barista Alawiyya Bello Gareji, sai da komai nawa ya ƙare amma har yanzu ba a gama shari'ar ba, don Allah ki taimake Ni Jiddah domin naga hotonku ke da Barista Alawiyya ki yi min ƙoƙari ki fahimtar da ita cewar alhakin ki ke ya kama Ni ban kashe kowa ba."
Tun da ya fara bata labarin kanta ke ƙasa har ya gama. Lallai yana cikin matsala ko bai faɗa ba jikinsa ya bayyana, kuma insha Allah zatai ƙoƙarin ƙwatar mai haƙƙinsa.
Ta kalle shi tai murmushi tace, "Kar ka damu a wane gari kuke shari'ar ne? Yaushe za ku koma kotun ne?"
Cike da farin ciki ya sanar da ita a Kano suke shari'ar Yau saura sati guda su koma Kotun. Tai mai alƙawarin zata taimaka mai, ko waya bai da ita sai ta zare sim card ɗinta ta ba shi ɗaya daga wayoyinta tace ya riƙe zata aiko mai da sabon sim card yanzu idan ta shiga gida don su dinga waya tana jin abubuwan dake faruwa kafin zuwan ranar . Nan ta bar shi yana kallonta irin kallon nadama da mamakin yadda ta koma kamar ba ita ba.
Bata jima ba sai ga wata ƴar aiki ta kawo mai saƙon cikin baƙar leda ba ƙaramin mamaki ya bayyana a kan fuskar Abubakar ba ganin iyayen kuɗi a cikin ledar tare da sim card ɗin sai wata ƴar takarda da ta rubuta.
"Ka je ka samu kaya masu kyau, kuma ka kula da kanka kafin na shigo Kano ɗin."
Tana komawa ta iske miss call ɗin Prince dana Yusuf Matashi sai ta fara bin kiran Prince domin yana cikin ranta daman, tana son ta dawo ta kira shi ta ji ko ya tafi inda ya ce mata an tura shi aiki. Kiran farko ya ɗaga kiran har da ajiyar zuciya.
"Haba Princess anya kuwa kina jin yadda nake ji kuwa?" Ƴar dariya tai tace, "Ai Prince na fi ka ma jin abin da kake nufi kana ji indai ana so da ƙaunarka ne."
"Haba Princess ban ga alama ba, don ko da yaushe Ni ke cikin tararrabin kar ki kuɓuce min."
"La,la,la, Prince haka ma zaka ce yanzu? Duk yadda sonka ya yi min kamun kazar Kuku kace min wai ban kai ka ba? Ni fa na ɗauka ma son da nake maka ya ninninka wanda kake min domin Ni duk abin da nake kana cikin raina."
"To ai Princess ban ce baki sona ba, kawai dai na ce nawa yafi naki yawa son."
Tasan ko za su shekara ba zai amince da cewar tafi shi son ba don haka ta aje maganar ta je wata.
"Yawwa Prince, zan shigo Kano nan da kwana shida insha Allah kan wata shari'a da zan yi."
Tana jiyo saukar numfashinsa, ya ce cikin farin ciki, "Ban mu kashe Princess, har kin sakani cikin nishaɗi da jin daɗi, duk da ban gari amma zan koma kafin ranar dama na tsara daga nan gun ki nayo kawai na kwashi ƙauna, na ganki naga kyakkyawar fuskarki nai tozali da kwalliyarki mai ɗimauta Ni."
Itama cikin farin cikin tace mai, "Ai baka kaini farin ciki ba kan hakan, domin ina son naga na tasa ka a gaba ina ta kallonka ina kallon dogon hancinka, ina kallon fararen idanunka, kana halakar da Ni da murmushinka mai ƙara jefa min ƙaunarka a sassan jikina."
Duk lokacin da Jiddah ke buɗe baki tana gaya mai irin kalaman nan sai ya dinga jin tamkar ya buɗe ido ya ganshi a bayyanar jama'a ana mai Allah sa alheri an ɗaura masu aure.
Yana son soyayya, Jiddah ta iya soyayya, yana son kulawa Jiddah ta iya ba shi kulawa, yana son shagwaɓa Jiddah ta ƙware da iya shagwaɓa don haka duk bayan sakan yake mutuwa yana dawowa kan soyayyarta.
"Prince shi ne za kai banza da Ni ka ƙyale Ni ina ta yi maka magana?"
Cike da shagwaɓa take maganar, abin dake ƙara zuzutar da shi kenan idan yana jinta.
Shima cikin nashi salon shagwaɓar ya ce mata, "Afuwan Princess ina can ina tunaninki ne shi yasa kin san ko da muna tare a waya indai ba gani ga ki ba sam ban daina tunaninki."
Farin ciki ya sake mamaye zuciyarta don haka ta sake gyara kwanciyarta cike da nishaɗi tace, "Ni kuma ko da yaushe addu'a nake, fata nake so nake Allah Ya ƙara ɗaukaka min kai, Ya ƙara maka buɗi Ya baka duk abin da kake nema Yasa ka gama lafiya Prince, ƙarshe Ya azurta Ni da samun damar zama mata a gareka."
Baki ɗaya sai ya dinga jin wani barcin nishaɗi nason kwashe shi, Jiddah na matuƙar saka shi a farin ciki da nishaɗi, tasan duk kalaman da yake so tasan duk abin da yake buƙata wanda zai saka shi a farin ciki.
Tana ganin kiran Yusuf Matashi tun da suka fara wayar amma bata jin zata iya amsa mai ko tace ma Prince ɗin ana kiranta zata ɗaga kiran,sai ma ta dinga jin haushi.
Alawiyya ta shigo cikin shirinta da gani tafiya zatai, ta dubi yadda Jiddah ta saki baki cike da fara'a tana waya tana ta keta dariya sai taji ba zata iya datse mata wayar ba, don da gani tana sakata cikin farin ciki ko da jin yadda take dariyar.
Ta gefe guda kuma ji take inama ace ita ce ke da halayen Jiddah gun soyayya? Ina ma ace yadda Jiddah ke zuba soyayya da Prince ɗinta haka ita ma take zubawa da Babansu Anam? Tabbas tana son gwada abubuwa da yawa da Jiddah ke yi ma Prince amma sai taji sam bata iya yadda take yi.
Ganin Jiddah bata iya daina wayar ga shi tafiya za su yi sai ta dafa kafaɗarta tace, "Princess ta Prince za mu wuce mu domin ina da shari'ar da nake yi nan da sati guda."
Jiddah tace ma Prince ɗinta "Don Allah ka cigaba da zabga tunanina kafin nayi sallama da Sahibata za su tafi gida yanzu."
Yar dariyar daɗi kashe Ni ya yi ya ce mata, "Ko baki ce ba, ko da yaushe cikin tunaninki nake da kewarki ga begenki dake ɗawainiya da ni ba dare ba rana balle safiya. Ki sallame ta ina jiranki Princess baki da damuwa."
Jiddah ta dubi Alawiyya ta kwashe da dariya bayan ta kashe wayar tace, "Ya naganki da shirin tafiya har komai ya daidaita kenan?" 
Alawiyya ta ɓata fuska tace, "Ban san iskanci miye na dariya kuma?"
Jiddah ta kasa daina dariyarta tace, "Ni fa ba cewa nayi ba ya zo biko ya samu nasara kenan ba, cewa nayi har za ku koma anyi daidaito?" 
Alawiyya tsab ta fahimci Jiddah so take ta yi mata shegantaka don haka sai ta juya tai ficewarta ba tare da tace mata komai ba.
Da sauri Jiddah ta diro daga kan gadon ta bi bayan ta tana bata haƙuri.
Har sun fice suna ta fara'a tai sauri ta buɗe wa Alawiyya ƙofar motar tace, "Ranki ya daɗe Allah Ya tsare Ya kiyaye hanya, sauka lafiya mata ga Dr. Uwa ga su Afnah."
Duk sun fahimci tsiya take masu, don haka sukai tsit kawai suka wuce, sai da ya tada motar ya leƙo ya ce mata, "Mu zamu wuce, a gaida mana da Yarima idan ya kira."
Da gudu Jiddah ta koma tana dariya, suma suna dariyar suka wuce.
Yusuf Matashi shi ne sunan dake karaɗe kunnuwanta bayan ta ɗaga kiran, sai dai tayi mamakin jin cewar yana ƙofar gida yana jiranta.
Kamar ba zata fita ba, sai kuma ta zari gyalenta ta fice tana jin faɗuwar gaba sosai.
Tun daga nesa ta hango su Afnah na wasa suna tsalle suna ihu irin abin nayi masu daɗi ɗin nan.
Ta ɗauka Baba maigadi ne ke wasa da su, sai da ta fita fili sannan ta hango shi, ya biye masu sai tsere suke a harabar gidan, su ruga bayan waccan motar su koma bayan waccan motar suna ta dariya.
Ta jima tsaye tana kallonsu kafin ta ida isa inda suke, suna hango ta kuwa suka rugo inda take suna dariya.
Shi kuma ya yi tsaye yana kallonsu cikin farin ciki fal a kan fuskarsa.
Yaran ta tura cikin gida ita kuma ta nufi inda take ganawa da baƙin ta, saboda bata taɓa shigar da baƙon ta cikin gidan ba sai dai a harabar gidan, Prince ne kawai yake shiga cikin gidan.
A hankali ta isa inda yake zaune yana kallonta, yana sakin murmushi, ji yake tamkar ya ruga ya rungume ta don ta yi bala'in birgeshi, bai tsammaci da gaske ta taɓa aure ba, sai da yaran ke faɗa mai ita ce Mamansu sannan ya lura da suna kwasar kama da juna.
Cikin siririyar murya tai mai sallama ta ja kujera ta zauna, ta sadda kanta ƙasa domin shi ne karon farko da ta fara haɗuwa da shi.
Kallonta yake yana son fahimtar wane yanayi take amma sam taƙi ba shi wannan damar, ta sadda kanta ƙasa ya kasa ganin ko idanunta sai bakinta kawai yake kallo wanda ya sha man baki da gani zai taushi.
Cikin natsuwa take gaida shi wanda sai ya ji tamkar a fili muryarta tafi cikin waya daɗi da zaƙi. 
Ganin tai shiru daga gaisuwa ya gyara zamansa yana kallonta ya ce, "Jiddah naga kamar ba ki yi murna da zuwana ba, don Allah kada ki sa naji a raina ban samu karɓuwa ba daga gareki ba, bayan na gama bin dangi da abokaina na bayyana masu ke a matsayin abokiyar rayuwata."
Ajiyar zuciya tai, shi kam fes da shi gwanin sha'awa, amma sam kalamansa basu birgeta, ita a kalaman da ake faɗa indai na soyayya ne to na bakin Prince ne kawai ke birgeta sune kawai ke saka ta nishaɗi, amma darga ba bakinsa ba duk wanda zai gaya mata kalaman ƙauna  ranta ɓaci yake sam bata jin ko daɗi suna yi mata, yanzu ta ji ta gundura da zama kusa da mutum indai ya fara yi mata maganar soyayya yanzu ta ji ta tsani magana da mutum.
Don haka ta tsuke fuska tai shiru bata ce mai komai ba sai shi kaɗai ke zuba kamar Kanyar da babu daɗi.
A nashi ɓangaren ma mamakin kansa yake da kansa wai Yau shi ne a gaban mace yake ta magana ko  kallo ga alama bai isheta ba, ya fahimci baki ɗaya ta takura da zamansa a gun don haka ta kasa ko furta mai kalma guda irin wadda yake furta mata.
Maimakon ya ji haushi ko ya ji cewar bata kyauta mai ba, sai ya sake ji har a ƙasan zuciyarsa cewa ya yi mata, yanzu ne aurenshi ya zo, domin yanzu ne ya samu irin macen da yake ta lalube shekara da shekaru bai samu ba.
Yana son macen da tasan kanta, tasan martabar ta da ajinta mai tsare gida ko da yaushe, sannan wadda bata son abin duniya bai dame ta ba sam, tun da ya ganta yake bibiyarta don kawai ya fahimci halayenta, ya sha mamakin gaske lokacin daya tattara jawabai kanta, bai sake mamaki ba sai Yau da ya zo ya iske kyawawan yaranta suka tabbatar mai da cewa ita ɗin mahaifiyarsu ce, ko a jikinta ba a gane cewar ta taɓa aure, lallai ya yi masifar samun dacen matar aure mai matuƙar tsada da wahala a wannan ƙarnin da ake ciki.
Jiddah kuwa ganin ya tasa ta gaba sai wasu surutai yake waɗanda ba abin da suke saka ta sai ciwon kai ta dube shi ta ɗan muskuta tace, "Ranka ya daɗe naga saƙon ka na yi matuƙar farin ciki, ina addu'ar Allah Ya saka maka da alheri Ya baka abin da kake nema."
Murmushi ya yi, ko shakka babu ya ji daɗin addu'ar da tai mai, hakan ma wata alama ce ta bayyana cewar ya samu Mar'atussaliha.
Yana dubanta kamar kar ta daina magana saboda yadda muryarta ke saka shi nishaɗi. Da ƙyar ya samu ya ce mata, "Kar da ki samu damuwa Special komai nawa naki ne, don haka ba godiya a tsakaninmu."
Jin ya ambace ta da suna Special sai da ta ja tsaki a cikin zuciyarta, sai ta ji sunan ba wani daɗi haka zalika bai ma bada wata ma'ana ta azo a gani ba.
"Special ina so don Allah ki taimake Ni kar da ki barni, idan kika barni tabbas kin ida kashe bishiyar da ta fara bushewa daman samuwarki ce tasa ta fara yabanya."
Kanta na a ƙasa ko kallonsa bata iya yi, saboda Prince ne kawai take iya jure kallo ko da za su kwana su yini ba zata ji ta gaji ba, haka zalika ana yawan cewa idan aka cika kallon mutum ana ganin muninsa to ita dai duk lokacin da take kallon Prince ƙara mata kyau yake sosai ta ji yana bala'in birgeta har bata iya ɗauke ido daga kallonsa, mafi yawan lokuta ba san lokacin da take tambayarsa ba shin yasan yana da kyau kuwa? Tabbas da gaske take yana matuƙar yi mata kyau na gasken-gaske.
Ganin ya jefa ta a tunani yasa ya miƙe tsaye yana kallon fuskarta ya ce, "To Special Ni zan wuce ina fatan zan ji kyakkyawan labari daga zuciyarki ta hanyar bakinki ko rubutunki?"
Sai taji wasai da ya tashi zai tafi har ta saki murmushin jin daɗin tafiyarsa, wanda shi kuma sai ya ɗauka na abin da ya ce ne yasa ta murmushin wanda hakan na nufin zai ji abin kirki kenan.
Tana kallonsa ya isa gun motarsa, da hanzari wani ya taso ya buɗe mai gidan baya ya shige sai kuma ta ga mutumin ya fito da akwati biyu ya nufi inda take.
Kamar ta shige cikin gidan haka taji, don ta tsani kyautar soyayya indai bata Prince ɗinta bace ba.
Kamar ya sani sai taga ya wuce ta ya nufi cikin gidan kai tsaye da kayan, don haka sai ta bishi baya kawai.
Yana kallonta yana kallon yadda ta ɓata rai ganin an fito da kayan, sai abin ya sashi murmushi, da gani ta ƙware a shagwaɓa yarinyar.
Ƙofar ɗakinta ta nuna mai ya aje mata, ya juya, ita ma ta shige ɗakinta ko kallon kayan ba tai ba, wanka tai kai tsaye ta fito ta saka doguwar riga marar nauyi ta janyo wayarta don ta ga ko Prince ya kira ta ko ya turo mata saƙo.
Ilai kuwa kira goma sha biyar na shi sai kira biyu na Alawiyya sai kira ɗaya na Mama kira biyu na Maryam ƙawarta ta Kano maƙwabciyar Prince ko tace ƙawa ga matar Prince. Tai mamakin kiran Maryam don sun jima ba su yi waya ba, amma sai ta fara kiran Prince don kiransa duk yafi na sauran yawa.
Yana ɗauka kamar ya fashe da kuka ya ce, "Haba Princess don Allah ki dinga jin tausayina mana, don Allah ki daina azabtar da Ni haka nan wallahi ji nake tamkar na mutu idan na kira ki baki ɗauka ba sai na ji tamkar wani ne ya zo ki ka je kika manta da Ni."
Murmushi tai, don ta saba yanzu duk lokacin da wani ya kira ta a waya ko ya tsaida ta ya yi mata maganar yana sonta sai Prince ya yi mata ƙorafi ya ce mata ya ji alamar wani na sonta.
Don haka sai ta share tace mai, "No Prince wallahi ba haka bane ba, ina can gun Alawiyya zata tafi gida,muna bankwana shi ne fa sai yanzu suka tafi na dawo cikin gida na shigo ɗaki na iske miss call ɗin."
Tana jin ajiyar zuciyarsa alamar ya samu kwanciyar hankali jin kalamanta, don haka sai ya ce, "Kwantar da Ni kawai za ki yi Princess ai nasan daman ba za ki taɓa bari na kama ki da laifi ba, amma ke kin iya kama mutane da laifi."
Cikin dariyar samun nasara kanshi tace, "Amma dai Prince kasan cewa kafin na kwantar da kai, ai kai ka jima da halakar da Ni ko?"
Shima cikin shagwaɓar ya ce, "Princess shike nan naji amma dai ki sani nafi ki kulawa da ƙaunar nan tamu, don nasan da za a fiddo su duka a auna to tabbas tawa sai ta fi taki yawa nesa ba kusa ba."
Har tana diddira ƙafa gun magana alamar shagwaɓar tai nisa tace, "Ni... Ni... Ni...ba zan yadda da wannan maganar ba, ta ya ma za ai kace wai ka fini bayan ko da yaushe nice mai magana kan baka min waya akan lokaci baka turamin saƙo a kan lokaci to shi ne za ka ce wani taka ta tafi tawa yawa?"
Cike da nishaɗi yake sauraren muryarta ji yake tamkar ya fito da ita daga wayar tsabar son ganinta da yake, muryarta na saukar ma shi da kasala jin barcin nishaɗi yake duk lokacin da take mai irin wannan shagwaɓar.
Anya kuwa akwai mazan da su kai dacen da ya yi ma samun mata kamar Jiddah? Gata da natsuwa gata da hankali sannan tasan abin da take,  mafi yawan lokuta ita ke ba shi shawara idan wani abu ya faru haka zalika tana matuƙar son cigabansa ko da yaushe tunaninta idan kai kaza kai kaza Prince za a ƙaru don Allah ka jaraba yi man.
Duk ɓacin ran da yake fuskanta mantawa yake yanzu daya tuna da yana da yana da Jiddah sai ya ji komai za ai mai ba komai ya manta ma sam.
Haka yanzu ya kawo idanu ya zubama matansa duk abin da suke bai tanka masu ko kallo basu ishe shi ba, shi dai yasan yana fita duk wani haƙƙinsu don haka duk abin da suke yanzu bai ɓata mai rai, ko ranshi ya ɓaci ma yana kiranta a waya sai ta saka shi cikin farin ciki don haka shi yanzu ta auren su kawai yake bata haukan da suke zuba mai ba a cikin gida.
Duk yana sane da yadda suke zuwa suna mai ƙarya gun mutane suna zubar mai da mutunci duk yana sane amma yasan dai cewa Allah shi ne shaida kan abin da ke faruwa a gidansa don haka duk masu zaginsa da masu cewa bai riƙon aure duk ya barsu da Allah , saboda shi ne kawai wanda zai saka mai kan ƙananan maganganun da ake binshi da su, duk da yasan hada laifin matan nasa amma ai mutane ya kamata su yi mai adalci su dinga tunawa da cewa duk macen da take zaune gidan mijinta kuma tana iƙirarin yana zaluntar ta ƙarya take tunda ba ɗaure ta ya yi ba, haka zalika ai babu yadda za ai ace namiji ne kawai mai laifi ban da mace a zaman aure.
Jin ya tafi duniyar tunanin da tasan ba makawa na iyalanshi ne yasa ta sauya firar zuwa ta tsokana tace, "Yawwa Prince ba jiya kaban labarin yarinyar da tace tana sonka ba? To har zuwa yanzu ban gama tsinewa idanunta albarka ba da suka hango mata kai, don da ace zan ganta ba shakka sai naji dalilin da yasa take sonka ana zaman lafiya kawai."  Magana take ba alamar wasa da jin muryar yasan bata fara'a take maganar sai ya ji ya ruɗe baki ɗaya don haka ya sake gyara kwanciyarsa bai damu da Hafsat dake tsaye kansa ba tana ta jan tsaki ba, tana cewa wane dare ne Jemage bai gani ba." 
Cikin lallashinta ya ce, "Princess don Allah ki manta da wancan shirmen yarinyar na rantse maki da Allah ban bari ma an jima ba a nan gun nace mata ta nemi daidai da ita ba bai niba."
Ta wani zaburo cikin wayar tace, "Na shiga uku ni Jiddah an fasa aurena ! Yanzu don Allah har wannan muryar taka sai da taji bayan ta gama kallemin kai sai kuma ka bata tukuicin muryarka?" Sai ta fashe da kukan shagwaɓa.
Zaune ya tashi a ruɗe yana cewa, "Dakata Princess, dakata, kin san dai ba zan maki ƙarya ba ko? To billahizzali ban yi mata magana cikin sakin fuska ba, to wai Ni da nake da kamar ki ke zan da wata mace kuma Princess?" 
Ai sai Hafsat ta ɗora hannu bisa kai, kome ta tuna kuma sai ta sauke hannun daga kanta ta fice tana maganar da ba shakka yasan zagin Jiddah take bai mamaki ma idan har da shi ta haɗa ta zagen.
Jin abin da ya ce yasa Jiddah fashewa da dariyar farin ciki, sai shima ya samu kansa da sakin dariyar ya ce, "Oh ! Watau har kin ji daɗi nace ban gane mata idan ba ke na gani ba ko?"
Cike da farin ciki tace, "Sosai kuwa don tsabar daɗi har ɗora ƙafa ɗaya nayi kan ɗaya ma yanzu haka Prince."
Ya ƙyalƙyale da dariyar jin daɗin abin da tace ya ce cikin zolaya, "Yanzu nan ke murna kike ba ce wa za ki min ba, a'a Prince ai duk ɗaya ne Ni da su ba komai ka yi yadda kaga dama kai da kowa ce ma."
Yana jin ta sauke wani gauron numfashi sannan tace, "Nabi su da gudu su duka matan da kake magana kan su to." Ko bai tambaya ba yasan harara take yayin da take maganar don yasan halin ƴan kayansa tsab. 
"Ki ka bisu da gudu har ina kenan Princess?" Cike da takaici tace mai, "Na bisu da gudu har ƙofar gidanka nace." Ya ce "A'uzubillahi ya za ki ainufin biyo matan mutane da gudu ainufin har ƙofar gidana Princess?"
Sai kawai ta kama cewa, "Hello. Hello. Hello." Wai ita bata ma jin me yake cewa.
Dariya yake har yana riƙe cikinsa, Princess da kishi sai addu'a kawai, ita duk wata ɓaraka bata sonta indai ta shafe shi.
Tana jin shi yana dariya abin da take so kenan don haka ita ma sai ta cigaba da taya shi dariyar su duka suka shiga yin dariyar.
Wannan na ɗaya daga abin da yasa duk yadda ranshi yake a ɓace yake saurin kiranta domin yasan ba su gama wayar ba tare da tasa shi ya manta ɓacin ranshi ba ya ji shi a cikin farin ciki ba kamar dai yanzu.
Ta ɗan saurara da dariyar tace mai, "Prince ɗazun muke magana da Alawiyya zamu shiga wani zubin adashe duk wata dubu ɗari me zai hana kaima ka shiga cikin adashen nasan kuɗin sun yi maka rana?"
Ya daina dariyar shima jin tai magana mai ma'ana ya ce, "Kuma kinga wallahi dana ji daɗin hakan amma fa sai idan ta ƙarshe za a ban saboda ban san ɗaukar wuri." Baka da matsala sai Ni da kai mu zama na biyun ƙarshe da ƙarshe kenan."
Sun jima suna wayar wadda daman haka take duk lokacin da za su yi waya sai su ɓannata katin dubu biyar ba tare da sun ankara ba.  Sai da katin ya ƙare su kai bankwana mai tsayawa kowa a rai a tsakaninsu watau ya ce mata, "Sai anjima love you." Ya ja kalmar You ɗin sosai itama sai tace mai, "Love You too. Sai sui ma juna kiss kowa ya kashe kiran, yabi wayar da kallon farin ciki.
Sai tana cikin yanayin farin cikin ne taga saƙonshi kamar haka.
"Princess nace wai da ace babu waya ya za mu samu kanmu a ciki kenan? Ni dai ko awa nayi ban ji muryarki ba zaucewa nake na shiga cikin tararrabin rayuwa ke fa?"
Tai murmushi bayan ta gama karantawa ta maida mai da amsar.
"Prince don Allah daina jawo mana abin da ba alheri bane, kasan Allah? Duk wani motsi nawa sai na kunna recording ɗin wayarmu na saurari muryarka naji daɗi, haka zalika duk lokacin da sakan zai buga ban jin daɗi idan ba tare da kiran wayarka ya buga ba. Prince kai ɗin na asalin daban ne a rayuwata, addu'a nake dai na ga ranar da zan ƙwamushe ka a kirani da matarka a kira ka da mijina."
Sai da ya harba ƙafa don farin cikin amsar data ba shi, don haka ya maida mata da amsar.
"A ranar za a ga yadda za mu dinga shiga muna fita cikin shigar alfarma tare da nuna tsantsar godiya ga Allah ta hanyar buɗe duk wasu ƙofofin alheri dake manne da mu Princess.
Allah ban san ya zan kasance ba, amma dai nasan idan acan Jalingo za a ɗaura maki aure to zan bi ki ne tun ranar da za ki tafi har a ɗaura auren mu taho tare, saboda ba zan iya nesa dake ba, sai dai ƴan ɗaurin auren su biyo NI daga baya amma ba zan iya haƙurin kina can ina nan ba Princess saboda ance idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi to haka ne kam na yadda saboda yadda nake ƙara jin sonki a raina tamkar zai lahanta Ni, gaskiya Princess ki gode wa Allah don ya saka min ƙaunarki sosai a zuciya da ruhina."
Lamo tai kan gado tana zuba mai shagwaɓa shi kuma yana biye mata yana bata haƙuri ta daina kuka yana tare da ita kowane lokaci.
Ita kam idan akwai abin da ke birgeta shi ne ta dinga shagwaɓa ana bata haƙuri ana lallashinta abin na matuƙar tsumata taji tafi kowa farin ciki haka zalika tafi kowace mace dace da samun mai kulawa da ita.
Ta sake narkewa sosai tace, "Prince kasan wani abu kuwa?" 
Ya ce cikin kulawa da natsuwar gaske, "Princess sai kin faɗa zan sani dai."
Ta ɗan yi jim sannan tai ajiyar zuciya tace, "Wallahi na rasa yadda akai nake masifar sonka sosai nake jin ƙaunarka tana yawo a cikin gaɓɓan jikina ban iya kwashe tsawon yini guda ba tare da naji muryarka ba mai sakani nishaɗi da walwala ba, ana yawan cewa soyayya da mai mata jidali ne amma Ni kam mantawa nake da kana da mata, ko da yaushe kai ne kawai a gabana kai ne muradina kaine abin tunawa ta don haka ta kai nake bata matanka ba. Ta ja ajiyar zuciya tace "Wallahi Prince ban jin akwai wata barazana ko maganar da za ai kanka wadda zata saka naji cewar ba zan iya aurenka ba, domin so ne nake maka daga asalin cikin zuciyata ya fito zuwa cikin sassan jikina har ya tumbatsa ya bayyanawa halshena shi kuma ya yi jagora zuwa ga fuskata har jama'a suka shaida cewa lallai Jiddah na son Mustapha so bana wasa ba, so irin wanda idanuwa ke rufewa kunnuwa su toshe ba ji ba gani sai zallar ƙaunarka kawai nake iya ji da gani haka zalika nake iya ganewa."
Sai kawai taji shi yana cewa, "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah na gode maka daka azurtani da samun wannan kyakkyawar mace natsattsiya son kowa hassada ga wanda bai samu ba.
Don Allah Princess mu cigaba da ƙaunar juna, mu zama haka har abada kar da mu ba wasu mutane damar raba mu ko shiga tsakaninmu domin nasan hakan duk mai sauƙi ne saboda nasan ina da tarin maƙiya na ɓoye dana bayyane waɗanda ban isa na hana su aikata abin da suke yi ba a kaina. Princess ba wai don ki soni ba zan faɗa maki ne kawai don ki sani ina cikin wani hali wanda Allah ne kawai shaidata kan komai ke faruwa a cikin gidana, don haka ina so ko anyi maki maganata don Allah ki dasa adalci kafin ki yanke min hukunci, saboda nasan cewa yanzu duk wata hanya da za a bi don aga an rabani dake ita za a bi, za a gaya maki abubuwa da dama masu nauyi kaina wanda za ki ji cewar ban kamata na zama miji gareki ba, amma ina so ki sani Ni nake sonki kuma nake burin aurenki don haka nayi maki alƙawarin zan zauna dake da zuciya guda kuma zan yi duk wani ƙoƙarin ganin kin rayu cikin aminci da farin ciki har mutane su yi mamakin abubuwan da ake faɗa kaina nasan a kanki ne za a gane cewar ba laifina bane ba Princess laifin matan da nake aure ne don Allah Princess ki yi min wannan alfarmar... Kuka ya ci ƙarfinsa ya kasa ida maganar da yake yi.
Jikinta ya yi sanyi sosai, tabbas mutane na ba shi laifi kan damuwar gidansa mafi yawan mutane cewa suke shi ne mai babbar matsalar bai da mutunci haka zalika bai ganin matansa da gashi duk ya raina su ga shi da masifar faɗa ga disgin masifa tare da buyagin tsiya , wasu ma cewa su ke har dukan mace yake da zaginta, duk ta ji labarin ne zuwan da tai suka fara soyayya ake gaya mata hakan, jikinta kan sanyi taji zuciyarta na rawa kan shi da farko amma daga baya data jima tare da shi kuma ta fahimci wasu abubuwan daga ƙawarta maƙwabciyar Prince ɗin wadda ƙawa ce ga matarsa Maryam, ita kanta Bilkisu tana gaya mata cewar bai da laifi yana da kirki kuma tsaye yake kan gidansa babu rashin ci haka babu rashin sha balle sutura asalima bai da ƙaramar ci ma don ɗan gayu ne shi ko da yaushe cikin son rayuwar hutu yake kawai halin matan ne sai a hankali kuma sai su dinga tsine mai don kawai ace suna da haƙuri shi ne bai da kirki bata san miye amfanin hakan ba kuma da suke.
Jin ya kasa daina kukan ta sausauta murya sosai tace mai, "Haba Prince kamance da cewa kowane mutum yana tare da kalar tashi ƙaddarar ne? Ko ka manta da cewa mutane ba su ne za suyi maka hisabi ba idan anje lahira? Don Allah ka daina damuwa ka natsu ka kwantar da hankalinka insha Allah ba za kai nadamar aurena ba kamar yadda nima ba zan nadamar aurenka ba insha Allah.  Wallahi a da ne nake jin ɗar kan aurenka amma yanzu na shirya zan iya aurenka ko da kuwa da gaske ake maka kana tare da waɗancan halayen insha Allah zan ƙoƙari naga na sauya ka zuwa magidanci mai adalci da tausayi ga iyalinsa.
Wallahi Prince ina tausan kaina amma kaima ina matuƙar tausanka sosai hakan yasa ko da yaushe nake ƙara sonka nake ƙara jin na ƙagara na aureka saboda gaskiya tai halinta a fahimci cewar fahimtar baibai akai ma baka da wani laifi a rayuwar gidanka.
Amma duk da haka ina so na ƙara shaida maka cewar na yadda da kai na amince da kai nasan cewar ba zaka taɓa juya min baya ba balle ka aikata min ko da rabin abin da ake kiran halinka ne Prince. Ina kuma baka shawara suma matan naka ka sake samo hanyar da zaka daidaita tsakaninka da su ku zauna lafiya kai da su saboda zaman lafiya shi ne ke ƙarawa maigida yalwar arziƙi Prince." 
Ajiyar zuciya yai ko bai faɗa ba tasan ya samu sauƙin abin da yake ji a ƙasan ransa, sai ta kauda maganar tace, "Prince kasan kuwa idan ka tashi ba da sadakina ko nawa zan ce ka ban?" 
Kamar tana gabansa haka ya girgiza mata kai sai kuma ya amsa mata da a'a Princess nawa zan ba da ne?"
Ta kwashe da dariya sosai tace "Kasan dai ai ba wani sauƙi zan maka ba, saboda kasan zan yi matuƙar tsada ta ban mamaki wadda sai kowa ya yi Allah san barka ance lallai Jiddah tayi wuta."
Ya fashe da dariya ya ce, "Too ashe kice na tashi tsaye na nemi kuɗi auren mace mai kyau daman sai mai kuɗi." 
Ta murmusa don daman burinta ta sashi ya manta baƙin cikin da yake ci kuma ga alama ta ɗauki hanyar don hata ta sake ce mai, "Prince Ni fa gaskiya sai naga kamar ka fini kyau don haka ba zan amince ba da gayun da kake ko ranar auren ban yadda kai kwalliya ba kar da ace angon ya fi amaryar kyau ma." Ta idasa maganar da alamar shagwaɓa a muryarta.
Ji ya yi komai ya yaye mai tamkar ba abin da ke damunsa ya dinga dariya yana jin nishaɗi yana jin yadda ta dage tana lissafin kuɗaɗen da ko a gwamnati sai an yi wata ba a nemo inda suke ba tana cewa a hakan ma duk don saboda so da ƙauna tare da wani munafin tausanshi ne yasa ta lissafa kuɗaɗen kaɗan amma ba don haka ba tsab zata lissafa manyan kuɗaɗe masu tsoka saboda ta ci su ai.
Shi dai ya samu abin yi don haka ya dinga zolayarta yana dariya har da dafe cikinsa tsabar farin cikin halin da yake ciki.
Maryam ce ta banko ƙofar ta shigo ɗakin ta ɗauka da Hafsat yake nishaɗi don sun ɗauke ta sakarya ranar aikinta  za su shige ɗaki suna wata banzar shewa ? Sai dai ganinsa manne da waya a kunne ya wani lumshe idonsa sai dariya yake ta fahimci cewar da Jiddah yake wayar sai ta samu kanta da fisge wayar ta jefar gefe guda ta ci ɗamara tana huci tana kallonsa burinta yai magana ta ƙare mai tanadi tsab, sai dai yana ganinta ya tashi ya ɗauki wayarsa yai mata kallo guda yabar ɗakin.
Sai kawai ta zauna ta ci-gaba da zubar da ruwan tujara da zagi tana cewa zata ga inda za ai auren nan sai dai inbata nan, amma babu mai kawo mata karuwa cikin gida.
Yana fita ya ga kiran bai katse ba, Jiddah kuwa ba abin da bata ji ba na maganar Maryam ɗin sai kawai ta saka dariya tace "Gaskiya na taya ka murna matanka na sonka budurwarka na sonka so na gaskiya mai matuƙar girma."
Sai kawai ya ji ya washe daman tunanin me zai ce mata yake don haka jin maganarta yasa ya samu sauƙi ya ji komai ya wuce ma sai kawai suka cigaba da hirarsu gwanin sha'awa ya zauna ƙofar gidan yana wasa da tsinke suna zuba soyayya abin da ruhi da jikinsa ke so kenan a rayuwarsa.
Sai da katin wayarsu baki ɗaya ya ƙare daga shi har ita sannan suka haƙura ba don ransu ya so ba.
Ranar da zata tafi Kano tun da safe ta shirya ba da  yara zata tafi ba saboda karatunsu don haka su kai bankwana ta ɗauki hanya zuciyarta cike da nishaɗi a hankali take tuƙin har ta isa gida kamar yadda ya shaida mata kuwa yana zaune yana jiranta ya ci gayu sai ƙamshi ke tashi na turarensa mai saukar mata da nishaɗi.
Da hanzari ya buɗe mata mota yana cewa, "Oyoyo Princess sannu da zuwa." Tamkar su rungume juna haka suke ji su duka amma ba dama don haka sai kawai suka zuba ma juna ido kowa fuska fal farin ciki.
Sun jima a hakan sannan ta rufe motar ya ja mata akwatinta suka shiga gidan tamkar wasu sabbin amare satin farko da aure.
Hajjo ta kalle su ta kauda kai, don tana jin maganganu marassa daɗi dake kai kawo daga cikin gidan Mustapha ɗin wanda ita ba zata jure su ba sam.
Har ɗaki ya kai mata kayanta ya fito suka gaisa da Hajjo fuskarsa cike da farin cikin ganin masoyiyarsa ta zo.
Hajjo ta taɓe baki tace, "Kai gafara can tun da Jiddah tabar garin nan ban sake ganinka ba sai Yau data dawo to ban maraba da kai Ni."
Ya sha kansa yana sunne kai ya ce, "Afuwan Hajjo wallahi ban zaune nima yanzu haka Yau na iso garin afuwa nake nema dai bamu haka dake ai."
Shiru tai don maganar da matarsa ta saki a cikin ɗakinta jiya ba ƙaramin shiga kunnenta tayi ba duk da ba da ita suke maganar ba amma dai ai taji. Tana jin Maryam na cema Bilkisu Yau kwana biyu kenan yaranta basu lafiya amma tayi mai maganar duniya ya ƙi kai su asibiti ko ya bada kuɗi ta kaisu ita kanta bata lafiya amma ba tasu yake ba, idan ta matsa da magana kuma ya dinga masifa yana turaja shi bai san haka, to ina zata bari Jiddah ta kai kanta gidansa ? Sai ta ƙara tsuke fuska tai banza da shi kawai ta tashi ta shige ɗakinta tana cema Jiddah ga kayan abinci can idan zata ci ta ɗiba.
Tana shiga ya langaɓar da kansa abin tausai ya ce, "Princess me nayi ma Hajjo take fushi da Ni kuma? Allah Yasa ba hanani aurenki zatai ba Princess." 
Ita kanta sai da gabanta ya faɗi jin abin da ya ce, kuma ta lura da sauyin Hajjon Yau itama wanda bata san ko na miye ba, amma dai zata ji ko na miye tunda suna tare ai.
Sai ta kwantar mai da hankali sosai tace mai zatai magana da ita karya damu Hajjo nada fahimta kuma ai da tana son shi yanzu ma dole akwai dalilinta na yin hakan.
Shi dai cike da sanyin jiki yabar gidan yana jin damuwa fal a ransa na sauyin Hajjon.
Yana shiga cikin gidan ya iske su suna halin nasu ko kallo basu ishe shi ba ya wuce su kowacce na zagin ƴar'uwarta kan yara shi dai ba tasu yake ba abin da ke ranshi yafi ƙarfin faɗan nasu ya samu ya kwanta yana jin sautin bugawar zuciyarsa. Kasa jurewa ya yi ya kira wayar Princess ɗin don ya ji abin da ke faruwa wanda yasa Hajjo sauya mai fuska.
Jiddah ta ɗauka tasan cewa daman yana can cikin damuwa don haka ta fara da cewa, "Zaka iya faɗa min gaskiyar magana idan na tambaye ka Prince?"
Kamar tana gabansa haka ya girgiza mata kai sai kuma ya ce, "Wallahi zan faɗa maki koma miye Princess in dai na sani wallahi tambaye ni."
Ta ja ajiyar zuciya tace mai, "Prince yaranka su waye basu lafiya ne yanzu haka?" 
Ya yi jim sai kuma ya ce, "Lafiyarsu lau amma dai jiya na saima Hanan maganin zazzaɓi dake damunta."
Tace to, "Maganar gaskiya jama'a ne suka tabbatar ma da Hajjo cewar yaranka basu lafiya kuma matarka ma bata lafiya amma kace kai ba tasu kake ba."
Ya yi ajiyar zuciya irin ta takaici ya ce, "Princess wallahi ba haka bane ba, na sai mata magani kuma a cikin matan ba wadda tace min bata lafiya duk suna ta harkar gabansu."
Hajjo dake gefe guda tana ji ta sauke ajiyar zuciya don dama ta ɗauka da gaske ne duk da tasan yana da tausai ba komai take yadda ba idan aka ce ya yi ba.
Jiddah tace, "Na gane Prince na kuma fahimci inda maganar ta dosa, anyi amfani da Hajjo ne matsayinta na wadda nake da kusanci da ita aka ɓata ka gunta saboda taji tsoro tace ba zan aure ka ba. To ba komai ai Ni zan zauna da kai ba wata ba don haka ka kwantar da hankalinka kai dai ka zama mai tsare gaskiyarka ka zama mai adalci ka kiyaye duk wasu haƙƙi nasu dake kanka zaka zauna lafiya."
Godiya ya yi mata ya ce "Insha Allah Princess za ki same Ni mai kwatanta adalci mai yin duk abin da ya kamata na kuma bar ko waye ya yi min wannan sharrin da Allah."
Hajjo ta saki ranta don ta gamsu da maganar Jiddah sai yanzu ma ta fahimci daman saƙo ne aka naɗo har cikin gidanta aka bata saboda kawai a rusa auren to Allah Ya kyauta.
Ta jima tana kwantar mai da hankali sai da taji ya fara dariya sannan sukai sallama ta kira lambar Abubakar dake ta kiranta tana waya.
"Ranki ya daɗe kin iso ne?" Cewarsa.
"E na iso yanzu haka na gama shiryawa zan fito anjima zuwa can kotun da za ai shari'ar don gabatar da kaina."
Godiya yake yana ƙarawa cikin alamar kuka ita dai ta kashe wayar kawai don tare za su fita da Prince sai taga dacewar ta shiga gidan ƙawarta Bilkisu su gaisa an daɗe basu haɗu ba.
Tana shiga ta iske ta zaune su ka gaisa kamar yadda suka saba, sai Bilkisu ta kalli Jiddah tace, "Kin ban mamaki ƙawata ban taɓa tunanin za ki yi min haka ba sai ga shi kin yi min."
Jiddah ta dube ta da kallon rashin fahimta tace, "Bilkisu ban gane ba me kike nufi da hakan?"
Tai dariya tace, "Yanzu ace kina soyayya da maƙwabcina amma ko da wasa baki taɓa gayamin ba?"
Bilkisu tai murmushi don ta fahimci inda maganar ta nufa yanzu don haka sai tace cikin murmushinta "Au don zan soyayya sai kuma na gaya maki ashe? Na ɗauka kin bari ai sai anyi bikin ban kawo maki kayan auren ba sai ki yi min mitar nayi aure ban gayyace ki ba."
Ko da taji amsar Jiddah sai ta wayance tace, "Abin ne yaban mamaki Jiddah da Mustapha na soyayya wai."
Jiddah tai dariya tace, "Bamu dace da juna bane ko yafi ƙarfina Bilkisu?"
Tana yaƙe tace, "Kai haba Ni na isa nace haka? Ai nasan idan ke baki ce kin fi ƙarfinsa ba shi ba za a ce yafi ƙarfin ki ba."
Jiddah ta sake duban fuskar wayarta tana kallon hotonsu ita da Prince ɗin tace, "Kin san shi aure HAƊIN ALLAH ne don haka Ni da shi HAƊIN ALLAH ne kawai ko Ni ba zan ce maki ga rana ko lokacin da na kamu da sonshi ba."
Sai ta yamutsa fuska tace, "Amma dai kin yi dace don kun dace sosai ya huta da baƙar ƙazanta da rashin godiyar matansa ma ai."
Jiddah ta murmusa tace, "Wannan kuma daban kowa kansa ya sani Ni ban san komai ba sai soyayyata da shi kawai mantawa nake da wasu matansa ko wani hali na gidansa." Ta miƙe ta gyara gyalenta tace "Zan tafi akwai inda zan je dama shigowa nayi mu gaisa kwana biyu ba a haɗu ba." 
Tana maganar tana tafiya don haka bata  damu da kiran da Bilkisun ke yi mata ba kawai tafiya take abinta tana murmushi.
Yana zaune ya sauya kaya sai ƙamshin nan nashi yake ya cika ko'ina da ƙamshi suka dubi juna suka saki murmushi.
"Wow! Prince kaga yadda kai kyau kuwa?" Tai maganar tana kallonsa ta riƙe bakinta.
Sai ya yi murmushi ya ce, "Ban yadda ba Princess domin ke ce kikai kyau har ma naji kishi ya kamani kada ki wuce wani ya ganki ya ji yana sonki."
Sai gardama ta kaure a tsakaninsu kowa na cewa kowa yafi shi kyau har suka ɗauki lokaci mai tsawo suna gardamar har Bilkisu ta fito ta kalle su ta shige gidan Mustapha ɗin ba a jima ba sai ga yaran gidan suna leƙowa ɗaya bayan ɗaya.
Ganin haka yasa Jiddah cewa su tafi time na ƙurewa don za su je yawon soyayya daga can.
Suna tafiya suna firar duniya suna ta nishaɗi gwanin daɗi, har suka isa inda za su.
Ba ƙaramin mamaki mutanen gun su kai ba ganin Barista Hawwa'u Bishir (Dawa)ce zata kara da Barista Alawiyya Bello Gareji ba , nan da nan sai ga ƴan jarida sun rufe su wai ya take ganin wannan shari'ar zata kaya a tsakaninsu kuwa, ko sun manta su ɗin Aminan juna ne wasu ma cewa suke gidansu guda amma zasu yi shari'a tare matsayin kowa da wanda yake karewa?" Dariya tai tace, "Ku dai ku zuba ido ku sha mamaki amma tabbas gobe zamu bayyana don karawa."
Daga can suka wuce wajen shaƙatawa suka dinga yawo kawai cikin gari haka kawai sai wajen goman dare suka koma gida.
Da uwar siyayyarsa da ya yi mata, tana kula komai ya sai mata zai siyi wani daban, taji daɗin hakan don tasan na gidansa ne ya siya ko bai faɗa mata ba.
Ko da suka dawo sun jima suna fira sannan su kai bankwana tana jaddada mai ya dinga cin abinci don ta gaji da ganinsa a rame ko da yaushe sai baƙi yake alamar bai da natsuwa da kwanciyar hankali.
Washegari tunda safe ta kira Alawiyya tace ta zo ta ɗauke ta idan zata Kotun.
Haka kuwa akai sai ga Alawiyya cikin shirinta itama daman ta shirya suka ɗauki hanyar Kotun suna ma juna dariyar kowa zai nasara?
Suna isa suka iske Kotun cike da mutane kowa ya zo don ganin wannan Shari'a ta Aminan juna kuma abokan juna sannan ƴan'uwan juna.
Nan da nan ƴan jarida su ka yi masu caaa! Kowa da abin da yake son ji daga bakinsu amma su kai tsit sai murmushi kawai da suke saki.
Abubakar ganinsu tare sai da gabansa ya faɗi ya tabbatar da cewa ya yi wauta na zuwa gun wadda ya yaudara ya yi ma butulci neman taimako. Bai san cewa bakinsu guda ba ai da bai je ba sam, amma ya miƙa komai ga Allah shi ne kawai zai bayyana gaskiyar lamari, sannan ko da ace an yanke mai hukuncin kisa ba zai damu sosai ba tunda Jiddah ta yafe mai kuma yasan yabar baya.
                Kotu
Bayan Alƙali ya zauna kotu ta natsu aka sake koro bayanin laifin Abubakar aka tambaye shi ko yana da Lauya? Sai Barista Hawwa'u Bishir (Dawa) ta miƙe tsaye ta gabatar da kanta a matsayinta na wadda ke kare wanda ake tuhuma.
Barista Alawiyya Bello Gareji ta miƙe tsaye ta gabatar da kanta a matsayin Lauyar wadda aka kashe.
Shi kanshi Alƙalin ya jima yana nazarinsu musamman Barista Jiddah domin kowane Alƙali yasan yadda ta gurfanar da babban Alƙali ƙara kotun Allah Ya Isa ta ci galaba kansa wanda yanzu haka yake tsare.
Yasan Barista Alawiyya Bello Gareji kuma farin sani, wadda bata amsar shari'a ta faɗi tunda take shari'a bata taɓa faɗuwa ba.
Mutane kuma sun yi zugum don ganin yadda shari'ar zata kwashe .
Ƴan jaridu, masu gidan talabijin duk sun hallara don samun abin yayaɗawa.
Barista Alawiyya ce ta dubi Abubakar tace, "Kotu na son ka takaita mata wahala ta hanyar bayyana gaskiyar yadda kai ka kashe ƴar aikin matarka Aminatu saboda kai mata ciki baka son asirinka ya tonu."
Abubakar ya sadda kansa ƙasa yana jin wani ɗaci na damunsa a duk lokacin da akai mai wannan tambayar ji yake inama ace shima ya mutu ya huta da wannan baƙar rayuwar da yake yi?"
Barista Alawiyya"Taya kotu na tambayarka amma kai kunnen uwar shegu da ita?"
Barista Jiddah "Saboda shi ma yana cikin neman nashi haƙƙin ne da aka tauye kuma yana son wannan kotun tai mai adalci wajen nema mai nashi haƙƙin a cikin wannan shari'ar da ake tabkawa mai cike da son kai da nuna izza da taƙamar dukiya."
Cikin Alƙali ya juya, kar dai Barista Hawwa'u tasan ƴan kuɗin da A'isha ta maka mai ne yasa take sakar mai magana cikin hikima?"
Barista Alawiyya "Ya kamata Lauya tasan inda take ba wajen ka-ce-na-ce bane ba gurine mai girma inda ake ladabtar da wanda ya kamata."
Barista Jiddah "Tabbas na gamsu da wannan zance amma ina son Lauya ta sani ban sauka daga hurumin wannan shari'ar ba sai ma ƙara komawa da nayi cikinta tsundum, don haka ina neman kotu taban damar tambayar A'isha matar Abubakar wanda ake tuhuma."
Alƙali, "Kotu ta baki dama za ki iya tambayarta, idan tana kusa sai ta matso."
Barista Jiddah, "Na gode."
A'isha jin an ambaci sunanta sai da cikinta ya katsa domin duk shari'ar da ake bata taɓa tsayawa gaban kanta ba don amsa tambaya saboda bata iyawa wannan na cikin abin da ta gayama Alƙalin ta ba shi kuɗi na musamman wanda zai hana ta fita cikin mutane ko da an kira ta, amma ji yanda yai mirsisi ya ce ta bayyana.
Haka nan dai ta fita tana cika tana batsewa zuwa inda ake nemanta. 
Aka gabato da Alkur'ani mai girma aka ce tai rantsuwa zata faɗi gaskiyar duk tambayar da akai mata.
Tai shiru ta kasa yin rantsuwar sai kawai Barista Jiddah tace a ƙyale ta tambaya ce kawai zatai mata ba shaida ce ba ai.
Barista Jiddah ta matsa kusa da A'isha dake tsaye ta ci uban ado har da su ƙunshi ga kitson gashin doshi fal a kanta tace mata, "Ya kike da wadda aka kashe ne?"
A'isha cikin yamutsa fuska, "Ƴar aikina ce man."
Barista Jiddah, "Shi kuma wanda kike ƙara waye a gunki?"
A'isha cikin nuna gazawa da maganar Barista Jiddah tace, "Mijina ne shi."
Barista Jiddah, "A gabanki ya kashe ta ko sai bayan ya kashe ta kika iske gawarta?"
A'isha tai shiru kamar bata ji me aka ce ba.
Barista Jiddah, "Na fahimce ki ga alama baki wajen bayan ya kashe ta ne kika je gun kenan?"
Barista Alawiyya, "Ya mai girma Alƙali bai kamata ba Lauya ta dinga jefa mata magana ba a baki wannan babu shi a tsarin shari'a."
Alƙali cikin yamutsawar ciki ya dube su duka yaga yadda Barista Jiddah ke wani sakin murmushi sai ya ce a ɗan dake "Barista ki dinga gyara kalamanki kina bakin aiki ne nan."
Barista Alawiyya, "Na gode."
Barista Jiddah, "Insha Allah zan kiyaye amma ya mai girma mai Shari'a ina son ne naji da bakinta domin ance waƙa daga bakin mai ita tafi daɗi."
Alƙali, "Kotu ta baki dama za ki iya cigaba daga inda kika tsaya."
Barista Jiddah ta kalli A'isha dake ta son Alƙalin ta kalli inda take ya ƙi tace mata, "Kince ma kotu ciki ya yi mata don haka ya kashe ta, to ina shaidar Likita daya bada na akwai cikin Abubakar a jikin Aminatu? Sannan cikin wata nawa ne? Kuma ke da kike matarsa kuma matar gida kina ina har mai aikinki ta samu damar yin lalata da mijinki har ciki ya shiga jikinta?"
Sai kotu ta ɗauki ƙananan maganganun domin wannan ma abin duba ne abin tambaya ne kuma.
A'isha cikin masifa tace, "Dalla Malama dakata! Nawa aka biyaki ne da za ki ritsani da wasu banzayen tambayoyi naki marassa kan gado?"
Barista Jiddah cikin murmushinta tace, "Suma na lura baki da amsar su, to ina son ki gaya min watan baya kina a wace ƙasar kuma dawa kika je ƙasar me ki kai a can? Sai tambayar ƙarshe shin wa kika bari da mijinki a gidanki matsayinki na matar aure ki kai tafiya har ta tsawon watanni, shin da sanin mijinki da kuma amincewarsa kika tafi?"
Ba A'isha ba hatta iyayenta sai da zufa ta yanko masu jin tambayoyin Lauyar masu kama da tonon asiri a bainar jama'a.
A'isha cikin ruɗewa tace, "Ni ba inda naje kuma ban je ko'ina da wani ba Allah."
Barista Jiddah ta dube ta tai murmushi tace, "A watanni uku da suka shige kinje Amurka ke da shugaban majalisar dattawa kuma ba harkar siyasa bace ta kaiku kin je ne a matsayin yarinyarsa wadda duk inda yake kina tare da shi.
Sannan ba Abubakar bane ya kashe Aminatu ba ke ce kika kashe ta saboda kin dawo kin samu labarin zai aureta don haka kika kashe ta kika liƙa mai laifin kisan saboda kina taƙamar kina da dukiya iyayenki ma nada dukiya.
Sannan ta wani ɓangaren ma kina harka da manyan dilan ƙwayoyi wanda ke ce ke fitar da ƙwayar ta hanyar fitar da kike da shugaban majalisar dattawa .
Ta gefe guda kuma kin zubar da cikin Abubakar sau uku saboda yana takura maki wajen tafiyar da harkokinki.
Ina da waɗannan hujjojin a rubuce da kuma a cikin wannan faifan mai ɗauke da sautin muryarki da duk wasu abubuwan da kika aikata ciki har lokacin da ki kai kisan kuwa." Ta miƙawa Alƙali ɗan abin shi kuma ya bada aka kunna.
Sai ga muryar A'isha na gayama mahaifiyarta ta kashe Aminatu saboda zata auri Abubakar ita kuma tace tai maza ta kira ƴan sanda tace shi ne ya kashe ta bayan ta tabbatar da ya riƙe wuƙar da tai kisan da ita don sawun hannunta ya fice nashi ya zauna.
Sai kuma aka kunna na kallon inda take amsar ƙwayoyin tana zubawa a jaka da inda take kwance jikinsa a cikin jirgi tamkar wani mijinta.
Sai kuma aka hasko lokacin data take cakawa Aminatu wuƙar shi kuma ya shiga jin ihun Aminatun sai ta fisge wuƙar daga cikin Aminatu ta jefa mai shi kuma ya ɗauka ya riƙe yana tallafe da Aminatun har ƴan sanda suka shigo suka amshe wuƙar suka tafi da shi kamar gawa.
Sai kotu ta ɗauki kabbara don an jima ana wannan shari'ar taƙi ci taƙi cinyewa sai ɗaga ta ake kamar wani bukin da ake son rushewa.
Sai Aisha ta kama zage-zage tana tsinewa Abubakar da Barista Jiddah.
Alƙali ya wanke Abubakar ya ba da damar kama A'isha da mahaifiyarta wadda ta taimaka mata gun ɓoye laifinta ta ɗora shi kan mijinta.
Nan take kuma aka ba damar kawo mutanen da A'isha ke harkar ƙwayoyi da su, hatta shi kanshi ɗan majalisar sai da aka ce a kamo shi an yanke mai hukuncin kisa ta hanyar jefewa, saboda ya yi tayayya da matar aure.
Kotu ta tashi ana ta ƙara yabawa Barista Jiddah.
Bayan sun dawo gida Abubakar ya zo ya sake bata haƙuri yana kuka yana ƙarawa. Alawiyya ce ta dube shi ba fara'a tace, "Kasan da cewa tun a binciken farko na gane ba kaine ka kashe yarinyar ba? Nayi ta jan shari'ar ne don kawai na rama wa Jiddah abin da kai mata, amma har ga Allah na tsara wannan shi ne zaman ƙarshe da za ai da kai, daman so nake ka talauce ka shiga gararin rayuwa yadda ka jefa ta cikin ƙunci kaima ka shiga cikinsa ka ji yadda taji kuma dama so nake ka rasa kuɗin da kake taƙama ka samu wanda saboda su ne ka gujeta."
Kowa ya kalle ta, sai ta miƙe tsaye tace, "Jiddah sai dai ki yi haƙuri amma sai Yau nasa aka saki Baba da Deeni ba tare da ko sisi sun mallaka ba sai tarin nadama da nemanki ido rufe don su nemi gafararki, sai dai ban basu wannan damar ba, baki ɗayansu motar Jalingo nasa aka sasu domin na cika burina da nayi cewar duk wanda ya taɓa saka ki kuka sai na sa shi mafiyin wanda ya saka ki. Ƙawarki ce dai Safiya lokacin da nake nemanta ban same ta sai bayan data fara amsar tukuicin abin da tayi na ganta a garin nan ne a sabon gari gidan karuwai da yarinyarta guda wadda ita kawai ta mallaka a duniya kuma abin takaici yarinyar bata sunna bace ba, sannan ta haɗu da lalurin ɓacin jiki wanda hakan yasa masu bin ta duk suka gujeta komai ya ƙare mata ga wasu irin abubuwa da suke ta ƙara bayyana a jikinta ba kyan gani duk kuɗin data samu a harkar sun ƙare kuma bata warke ba don haka ta koma saida goro shima ba mai siya daga ƙarshe dai bara ta koma yi yarinyarta kuwa duk da ƙanƙantar ta maza sun fara buɗe mata ido wanda ita ce ke sana'ar uwar tana ci da uwar haka nan a wahale ko gun kwana mai kyau ba su da shi haka suke kara zube a zauren gidan karuwan."
Jiddah ta fashe da kuka jin abin da Alawiyyar tace mata, tabbas zata je da kanta ta ceci rayuwar yarinyar ko da ita ne Safiya ta tsira.
Haka ita ta jima da yafe ma duk wanda ya cuce ta ranta fari tas ne kan kowa yanzu haka.
Alawiyya ta dubi Jiddah tace, "Amma ina kika samo hujjar da kika bada a kotu kan A'isha?"
Jiddah tai murmushi tace, "Yau kwana huɗu kenan muna chat da Matashi sai naga ya yi status ɗin wani pic wanda ya ɗauki hankalina har nayi mai magana nace suwaye a jikin hoton daya ɗora a status ɗinsa? Shi ne yake gayamin abokinsa ne ke birthday party, to a jikin hotunan mata biyu ne rak don haka sai na sake tambayarsa matan fa suma duk abokanka ne Matashi? Sai ya ce min a'a ɗaya yarinyar abokinsa mai birthday ɗin ce gudar kuwa abokin wani ne daga abokan ya zo da ita gun bai san ta ba sai a hoton don bai je gun ba.
Sai zuciyata ta dinga hasko min fuskar matar Abubakar duk da sau uku zance na taɓa ganin hotonta amma don kauda kokonto sai na kira Abubakar nace ya turomin hoton matarsa, shi ne ya turomin a take na gane ita ce a jikin wancan hoton na abokin Matashi don haka sai na sake tambayarsa yana da kyakkyawar alaƙa da wanda ya zo da ita ne gun? Ya yi dariya ya ce ga alama dai tana cikin komarki don haka zan nemo maki labari kanta sosai amma dai ina fatan ba wani case bane mai girma ba kanta? Nai dariya nace ko kaɗan kawai sunanta dana abokin nake son ji ya wadatar ma da Ni.
Ba a jima ba ya kira Ni ya ce min sunan ta A'isha shi kuma Abdul abokin kasuwancinta ne amma ban san wane kasuwanci bane suke. Nayi mai godiya na aje waya sai ga saƙon number Abdul ya turomin kamar yasan abin da nake tunani kenan.
Ban ɓata lokaci ba na ɗauki lambar na saka a layina na aiki na kira shi ta jima tana ƙara bai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka yana tambayar waye.  Na gyara muryata sosai nace mai ƙawar A'isha ce na kira ne na gaya mai gaskiya kanta idan ba damuwa. Ya yi jim sai kuma ya ce ina jinki amma ke ya sunanki? Ban ɓoye mai sunana ba nace Jiddah sunana  , ya ce min "Ina jinki to meke faruwa ne?" 
Nace ko kasan da cewar ta kashe ƴar aikinta ta ɗora wa mijinta laifin kuma yanzu haka tana shirin fallasa alaƙarka da ita a kotu saboda wani ɓoyayyen dalili nata? 
Ya yi wani uban ashar ya ce, "Ƙarya take wallahi bari na kira Oganmu ki turomin account ɗinki zan saka maki na kati na gode sosai da taimako."
To sai na dasa alamar tambaya a gun, me yasa ya ruɗe don nace Aisha zata tona alaƙarsu? Waye Ogansu da zai kira? Me yasa ya ce zai min kyautar kuɗi don na taimake su? 
Nan da nan sai ƙwalwata ta fara nazari tana saƙawa tana tacewa sai kawai na ɗora su a mazaunin masu laifi su duka don haka yanzu ina tare da masu laifi uku ne ɗaya nasan laifinta kisan kai ne, su kuma biyun ne ban da tabbas kan nasu laifin amma ina da tabbacin masu laifi ne.
Don haka sai na kira A'isha a waya nace mata, "Ina magana da A'isha matar Abubakar ce? Sai ban amsa da e ita ce lafiya nake nemanta? Ina na samu lambarta ? Nace mata na kira ki ne daga  cibiyar bincike ta ƙasa bisa jagorancin abokin harƙaklarki guda dana kama mai suna Abdul M Adam ina fatan kin san sunan koma ince mai sunan? Ta ja gwauran numfashi tace min tabbas tasan sunan tana jina. Na cigaba da ce mata, ki kwantar da hankalinki ba kece abar harina ba kamar yadda ba Abdul bane abin harinmu ba, idan kikai min yadda Abdul ya yi min tabbas ba zan sake kiranki ba, haka ba zan bari sunanki ya fita a jerin sunayen abokan cinikayyar ki ba. A'isha ina jiranki ki yi min bayanin irin harƙallar da kika san kuna yi sai ki ban sunan mutum guda cikin manyan dilolinku tare da bayani kaɗan to Ni kuma zan cire ki a list ɗin waɗanda za a kama.
Cikin ikon Allah tai min bayanin ƙwayoyi ne suke safara amma ita iyakarta fitar masu da ita ƙasashen waje kawai saboda tana tare da babban mutum mai madafan iko wanda jirgin kansa garesa daga shi sai ita ke tafiya cikin jirgin sai mai tuƙin jirgin don haka suke amfani da damar suna bata ƙwayar tana kaiwa duk ƙasar da suka je ita da ɗan majalisar.
Ta ban sunan dilansu da ƙarin bayanin inda take zuwa tana amsar ƙwayar duk na naɗe a wayata.
Bayan mun gama wayar na shirya kai tsaye na isa inda tai min kwatance na yi sa'a ba kowa gun sai masu gadi su biyu ban sha wahala ba gun shiga saboda guda ya sanni sosai ta silar wata shari'a da nayi mai kan wani yaro da aka sace mai nabi mai haƙƙinsa don haka cikin natsuwa suka buɗe min ko'ina na shiga nayi bincike na samo sunayen duk masu hannu a cikin lamarin.
Sannan a cikin ofishin dai naga hoton A'isha da shi ɗan majalisar na ɗauki hoton na tafi da shi kai tsaye gidan shi na shaƙatawa yana ciki kuwa na iske shi na zauna na fito da hoton A'isha da sauran gan ɗin su na ƴan kwangilar ƙwaya na fara da kora mai bayanin laifinsu da ƙara mai da cewar shi ne babban mai laifi wanda ke taimakawa ana fitar da ƙwayar daga ƙasar nan zuwa ƙasashen waje don haka sunansa ne a farko kafin nasu, sannan na nuna mai hoton A'isha da Abubakar da hoton yaronsu na gaya mai yana bin matar aure matsayinsa na babban  ɗan siyasa a ƙasar nan wanda idan wannan maganar ta fita zai rasa abubuwa da dama, irinsu siyasarsa, mutuncinsa, ba mamaki har da iyalansa ma. Hakan yasa ya ruɗe yake ce min wallahi bai sani ba, ya ɗauka bata da aure sai a satin nan ne yake ganin abin da ke faruwa tana Shari'a da mijinta wai ya kashe mata ƴar aikinta bayan ya yi mata ciki, to da yake kin san mu ƴan siyasa bamu da yadda tun haɗuwarmu bada jimawa ba na sai mata wata sarƙar zinari mai tsadar gaske na saka mata Camera a cikinta na saka mata nace kada ta sake ta cire ta sai zan sake mata wata, tunawa da hakan yasa na kunna Camerar don ganin meke faruwa a nan ne naga wannan abin da ya tada min hankali watau kisan da tai ma ƴar aikinta da kiran da taima mahaifiyarta. Ya ban ɗaukar na kalla, na riƙe na yi mai godiya nace sai mun haɗu a kotu, duk da ya so na cire shi a lamarin nace ba zai yiyu ba saboda ya jima cikin manyan siyasar dake gurɓata ƙasar nan.
To kin ji yadda akai na samu shaidun dana gabatar a wajen Alƙali Yau."
Abubakar ya sake yin godiya ya tafi cike da jin nauyin abin da yai ma Jiddah a baya Yau ga shi ita ce ta cece shi ta ƙwatar mai haƙƙinsa a lokacin da kowa ya ƙyale shi ya juya mai baya.
Prince ya dubi Princess ɗinsa ya ce, "Zan je gun Baba mu yi maganar zuwa kai kuɗin aurenmu don wallahi na gaji da wannan ja min ran da kike ko da yaushe so nake na ganki kusa da Ni ga Ni gaki."
Alawiyya ta goya mai baya tace zata kira Baffa ta gaya mai yanzu kuwa gwara ayi hidimar a wuce gun haka nan.
Da dare Jiddah ta gayama Hajjo ita ma ta kira Maman Jiddah ta gaya mata, tai ta addu'a tana ƙarawa domin ta gane yaron da akace yana son Jiddah tabbas bai da kwaramniya da gani yana da hankali yasan me yake yi kuma don ba laifi yafi Deeni shekaru.
Alawiyya ma ta kira Baffa ya ce sai ya ji daga bakin Jiddah sannan zai yadda don ba auren dole zai mata ba kuma ya zatai da karatun da take yi? 
Ya kira ta ya tambayeta ta amsa mai da cewa Mustapha ya amince ta cigaba da karatunta ba zai dakatar da ita ba ko bayan sun yi aure hakan yasa Baffan jin daɗi ya amince kuma sai dai ya ce ya tura can Jalingo shima zai je can su haɗu da yayyen mahaifinta su amshi kuɗin auren.
Ba haka ta so ba, so tai shi ya amsa ya zama waliyinta kawai a ƙyale su tunda ba wanda yasan da zaman ta a duniyar daga su har mahaifin nata amma tunda ya ce haka sai ta amince sai dai umarnin ƙarshe ne ya sosa mata rai da ya ce ta shirya ita da Alawiyya suje Jalingo ta gaida iyayenta kafin ai auren don ba lokaci za a saka ba mai tsawo.
Ba yadda zatai haka ta amsa da to duk ba daɗi a ƙasan zuciyarta.
Ta shaidawa Prince da Hajjo da Alawiyya yadda su kai da Baffa su duka sun goyi bayan hakan don haka ita kaɗai ce abin baima daɗi ba suka saka ranar tafiya Jalingo nan da kwanaki biyar.
Sai kuma wata sabuwar fitina ta fita na yadda mata da dama ke sallama har gida suna gaya mata cewar karda ta sake ta auri Mustapha yadda take haka idan ta aure shi ta ci baya kuma sai tayi nadama tayi danasanin aurensa kowace mace tana kafa mata hujja da tarin auren da yayi a baya da yadda yanzu gidansa yake ba zaman lafiya wai bai kula da mata kashe mace yake komin diri da kyanta idan ya aureta ƙaryar daga waje ne kawai tana shiga gidan ta zama sorry.
Ita kuma duk lokacin da aka kawo mata zugarshi sai taji ya bata tausai amma dai Hausawa na cewa ana tauna tsakuwa ko dan aya taji tsoro sai ta kira shi a waya taita fushi tana cewa ta gaji da surutun mutane kada fa ace da gaske ne.
Bawan Allah zai ta lallashinta yana rantse mata kan idan ya ci amanarta Allah ya saka mata kawai hassada ce ake mai don zai aure ta.
Ni da Bilkisu ƙawata sai komai ya lalace domin na fahimci munafuka ce tana son samun magana daga bakina don ta gayama matarsa Maryam sai kawai na rufe ta na fice daga sabgarta amma sai ta dinga biyoni har gidan Hajjo tana son bugar cikina don taji yadda muke ciki da Prince, Ni kuma sai na ƙi gaya mata komai sai ta koma yi min bincike a waya tana duba saƙonni da hotunan da mukai da shi, hakan yasa na fito na gaya mata cewar mun ɓata da Mustapha yanzu har na fitar da wanda zan aura a Kaduna buɗar bakinta sai cewa tai, ai wallahi daman nasan kin fi ƙarfinsa yo me za ki yi da Mustapha Allah na tuba? Ai ba ajinki bane ba ya je ya ji da kansa ma da hayaniyar gidansa ina shi ina ke ban da neman magana? Ai daman nasan yaudararsa kawai kike don ki yagi abin da kika yaga ki kama gabanki don bai da wayau kashe ma mata kuɗi kawai yake suna mai wayau don ba mai iya aurenshi ta kawo kanta gidanshi duk masifa da ƙazanta ta kashe ta."
Tun da naji haka daga bakin Bilkisu sai nayi mata dogon layi mai kyau na saka ta ciki kawai na rufe.
A farko tana gaba wajen cemin nayi dacen miji domin bai da matsala har cewa tai yafi mijinta kula kawai mata ne bai dace ba amma mutum ne har da ƙari Yau kuma ga abin da tace min saboda ta haɗe kai da matarsa bata son na shiga gidansa da sunan aure.
Sai na sauya mata ko a fuska na daina ko doguwar magana da ita kawai na kame kaina na daina bata ko wayata duk da cewar tana tambayata .
Sai kuma suka tsiri turo min yara su gani ko Mustapha na gidan Hajjo sai ina zaune naga yara na leƙe duk na tarkata su na watsar kawai nasa a raina aurene dai nice mai yinsa don haka zan auri Mustapha ko da ace munanan halayen da ake ambata yana da su to tabbas ina da tabbacin zan iya sauya shi indai da gaske yana sona nima ina sonsa to sauya shi ba wani abin ku zo ku gani bane ba. Tunda nayi rayuwa da Deeni wane namiji ne ban iya rayuwa da shi? Ban ganshi ba zan iya rayuwa da kowane irin namiji a yanzu Ni.
                    JALINGO
Tafiya mai daɗi a gunsu Alawiyya da Prince Ni kam murna ɗaya nake zan je na ga Mamana ban da wannan ba wata murna da nake sai kawai kallon titi, lura da hakan da sukai ma yasa sai fira su ke su kaɗai basu saka Ni don hankalina ba kansu yake ba ya koma a can shekarun baya na koma tunano rayuwar da nayi a baya mai cike da ƙalubale kala-kala ko ince iri-iri a cikin garin Jalingon.
Har muka isa fuskata ba walwala gidan Mamana muka fara sauka da yake tasan da zuwanmu ta shirya mana abinci mai rai da lafiya naji daɗin yadda na ganta cikin aminci da natsuwa bata tare da damuwa ko takaici hakan yasa na sake sakin fuskata na ji daɗi ya ziyarci zuciyata baki ɗaya har ma na ware ana ta fira da ni kamar ba nice mai haɗe ran nan ba sam ba fara'a kan fuskata ba.
Daga nan gidajen dangin Mamata muka je suka ga wanda zan aura sunata addu'a suna nuna jin daɗin su kan auren da zan yi kuma ga alama duk sun yaba da zaɓin nawa.
Sai daga ƙarshe muka nufi gidan Babana tun daga nesa naga gidan duk ya sauya kamar ba shi ba, haka mu kai fakin muka sauka.
Yana zaune yana jan casbaha a hannunsa duk ya rame ya koma kamar ba shi ba, ga alama ma bai da wadatar lafiya, a hankali muka isa inda yake muka gaida shi amma abin takaici abin mamaki Alawiyya kawai ya gane ya zabura yana roƙonta ta kaishi inda zai ga Jiddah don Allah.
Kaina na ƙasa ina kukan takaici aka nuna mai Ni matsayin ɗiyarsa wadda ya manta da ita wadda bai sonta wadda bai damu da ita ba ita ce gabanshi tsugunne bai gane ta ba.
Ya kama Ni ya riƙe yana kuka yana neman afuwata sai kuma tari ya taso mai kamar zai sume hakan yasa zargina ya tabbata bai da lafiya ganin mutane sun fara taruwa yasa muka shiga cikin gidan baki ɗaya.
Komai na yadda yake yadda na sanshi yadda na barshi sai dai tsufa kawai da gidan ya yi na rashin fenti .
Mutanen gidan suma kowa na nan sai ƙara manyan ta da sukai ba kunya ba tsoron Allah haka suka dinga ihun murnar zuwan Jiddah gidan nasu.
Lokaci kaɗan kowa ya hallara don haka Mustapha ya gaida kowa ya gabatar da kansa matsayin wanda ke neman auren Jiddah ba musu kowa ya amince to daman wane musu za su yi tunda ba wanda ke ci da ita ko shayar da ita balle ya damu da halin da take ciki ko a baya balle yanzu?
Washe gari Baffa ya zo da tarin mutanensa inda dangin Mustapha suka iso suma da zummar kawo kuɗin neman aure sai dai labarin ya sha bamban inda nan take aka ce a bada kuɗin sadaki dana jin magana da komai a ɗaura auren.
Cikin ikon Allah mutane suka shaida ɗaurin auren Hawwa'u da Mustapha akan sadaki naira dubi hamsin cif.
Nan da nan bakin ango ya kasa rufuwa ya dinga kiran abokai da ƴan'uwa yana gaya masu an ɗaura mai aure da Jiddah yanzu haka a Jalingo.
Cikin murna ya kira matarsa Maryam ya gaya mata an ɗaura aurensa da Jiddah tai ta ruwan masifa da bala'in nan za a zo a iske su a tai a barsu dai.
Washegari aka dunguma baki ɗaya har da Baban Jiddah sai Kano don ganin inda za a aje Jiddah.
Gida mai kyan gaske kuwa aka kai kayan Jiddah wanda tsayawa bayyana su abin kamar ƙauyanci ne, saitin kaya biyu masu kyan gaske ƴan yayi Baffa ya yi ma Jiddah da kujerunta masu kyau komai ya ji a gidan sai fatan zaman lafiya ga masu gidan kawai.
An tsaida lokaci Jiddah zata tare gidanta bayan sati biyu cif wanda hakan sam bai ma ango daɗi ba ji yake tamkar an ce sai bayan shekara biyu Jiddah zata tare a gidan nashi.
Jiddah kuwa ta ji daɗin hakan don ba shirin da tai, don haka cikin lokaci suka fara kimtsawa ita da Alawiyya, ba a bar Iyami (Jiddah) a baya ba itama ta tashi tsaye ta shiga kimtsa Jiddah ta ko'ina Jiddah amsar kayan gyaran jiki take hakan yasa duk lokacin da suka haɗu da Prince sai ta yi da gaske suke rabuwa sai ya bi ya narke ya koma abin tausayi ya ce bata jin tausansa ta daina sonsa ƙorafi kala-kala kuma wai sati biyun taƙi yi ma shi ina zai sa kansa?
Duk inda Jiddah ta saka ƙafa Mustapha na biye da ita, haka duk inda zai je tana tare da shi hakan yasa Hajjo ta ƙagara su tare gidansu ma a huta da nacin da Mustapha ke yi duk da yadda matansa ke ruwan masifa da aiken baƙaƙen maganganu abin bai mata daɗi amma ta lura ita uwar gayyar ko a jikinta harkar gabanta kawai take ba ruwanta da ƙananan lamurran da ake yi kanta da mijin nata.
            Bayan sati biyu
Tunda safe ya kira Alawiyya a waya yana tambayarta yanzu za a zo ɗaukar amarya ko ko sai da rana?" Abin dariya ya ba Alawiyya ta dubi agogo taga ƙarfe bakwai na safe amma yake kiran yanzu za a zo ɗaukar amarya, lallai Mustapha abin nashi azimun ne don haka sai tace ka kira Hajjo ka ji man ai sune masu bada amaryar.
Jiddah na gefen Alawiyya ta dubeta suka fashe da dariya suka tafa , Alawiyya tace "Ke nifa ban ga laifinsa ba taya ina da mata kamar ke ace kina can ina can? Tab ai kawai ya yi magana akai mai matarsa kowa ya huta shima ya huta kema tsohuwar munafuka ki huta. Yawwa wai ya akai kika gayama Yusuf Matashi za ki aure har naga ya aiko maki da saƙon Allah Yasa alheri da kyautar girma Jiddah?"
Jiddah tai murmushi tace, "Ranar da muka fito kotu kan case ɗin Abubakar a ranar ya turomin da hotonsa da wata yarinya ya ce min ita ce zaɓin da mahaifiyarsa tai mai ta kuma yi rantsuwa cewar ba zai auri Lauya ba ƴar wuta ba ya kai mata cikin zuri'a ba. Hakan yasa yake ban haƙuri don Allah na yafe masa amma don Allah kar da mu yanke zumunci nayi murmushi nace abin ya yi min daɗi don haka bayan kwana biyu na tura mai hotona da Prince nace mai ga wanda zan aura ɗan'uwana ne. Shike nan yanzu haka maganar da nake maki suna matuƙar mutunci da Prince nima ina gaisawa da matarsa Hanan sunce ma yau za su zo gun tare wa ta insha Allah."
"Kai Jiddah tabbas kina da sa'a a rayuwarki duk yadda abu ya dunƙule maki sai kinga inda haske ya fito ya warware maki shi." Cewar Alawiyya kenan tana murmushi.
Da yamma aka ɗauki amarya sai gidan mijinta kuma Prince ɗinta.
Mahaifinta ya jima yana mata nasiha haka ma su Baffa sun yi mata nasiha sosai ta zauna gidanta lafiya da abokan zamanta kar da ta zama silar damuwa ga mijinta.
Bayan kowa ya watse ne Alawiyya ta dubi Mustapha tace, "A al'adarmu bayan an kawo amarya an watse Ni zan sake ɗaukar amarya na kaita gidana tayi sati biyu sannan na dawo da ita ɗakinta."
Ya zabura ya miƙe tsaye sai kuma ya zauna ya ce, "Amma da Ni za ki tafi ko? Don Wallahi Yau ba zan iya rayuwa ba sai naga matata cikin ɗakina."
Jiddah sai dariya take tana ɓoyewa don tasan zolaya ce kawai take mai.
Sai da Mustapha ya haukace ya fara rantse-rantsen sai dai a tafi da shi sannan Alawiyya ta kwashe da dariya tace, "Kuɗin sayen baki kawai zaka ban na wuce mijina  nacan na jirana ."
Sai lokacin ya sauke ajiyar zuciya ya fito da kuɗi masu dama ya bata ya buɗe mata ƙofar fita ya ce, "Ranki ya daɗe mu tashi lafiya sai Allah Ya kaimu."
Wannan karon dole dariyar Jiddah ta bayyana ta miƙe ta raka Alawiyya har wajen motarsu Faisal na ciki na jiranta.
Bayan sun tafi ne sun dawo cikin ɗaki cikin hanzari Jiddah ta faɗa toilet ta haɗa ruwan wanka ta zuba kayan ƙamshi ta kira Prince tace ya yi wanka ya samu sauƙin gajiya.
Yana shiga ta koma ɗaki da zummar fito mai da kayan da zai saka marassa nauyi sai wayarta ta hau ƙara ta ɗauka Alawiyya ce ta sake kira tai mata sharhi sai kuma taji saɓanin hakan don bata duba lambar ba daman.
"Sannu amarya, ina maki barka da zuwa gidan tashin hankali da rashin kwanciyar hankali tattare da gurɓacewar rayuwa! Ba dai kin shiga gidan Mustapha ba? To ki sani kin kawo kanki a gidan matsala don ko shi maigidan bai isa ya aiwatar da abin da yake so ba haka bai isa ya saka ba balle ya hana ba. Ina jajanta maki zuwa cikin gidan Mustapha Jiddah za ki gane kurenki za ki nadama da danasani saboda za mu gwabza kishin bal-bal dake a cikin gidan nan zamu fitar dake ko ta halin ƙaƙanikayi saboda mune kawai zamu iya rayuwa a gidan Mustapha.
Ba yana tunanin ya auri wayayyar mace ba wadda zata mantar da shi baƙin cikin gidansa ba? To ina so ki sani ke baki isa haifar masa da ko da rabin farin ciki ba indai ina raye."
Kit ta kashe wayar tabar Jiddah da waya riƙe a hannu tana murmushi madadin ɓata fuska.
Cikin fara'a ta adana lambar wayar ta saka sunan mai lambar tana jin ta samu matakin farko na samun abin da take nema a gidan Prince.
Kamar yadda matarsa tai alwashin sai ta wargaza mata aure sai ta saka ta cikin kishin bal-bal ta raba ta da jin daɗin aure to itama tai alƙawarin sai ta gyara gidan Prince sai ta maida mai gida tamkar gidan lumana da farin ciki haka zalika sai ta gyara mai duk wata matsala ta gidansa ta ɗinke mai duk wata waraka da take bayyane cikin gidan nashi sai an wayi gari ana cewa gidan Mustapha gwanin ban sha'awa sai an dinga kwatancen matan Mustapha da mata masu saka mijinsu farin ciki da walwala insha Allah sai samunsa ya sake yawaita ya ƙara cigaba a rayuwarsa fiye da baya.
Wannan shi ne alƙawarin da Jiddah taima kanta na gyara gidan Mustapha a daren farkonta.
To jama'a sai mu bi page na gaba don jin wane irin kishi ne na bal-bal da za a kwabsa tsakanin matan Mustapha da Jiddah?
Shin Mustapha zai zama mai cika ma Jiddah alƙawarin daya ɗaukar mata na share mata hawayenta na shekara da shekaru?
Shin da gaske Mustapha ne mai matsala ko matansa ne masu matsala?
Ta wace hanya Jiddah zata bi don warware duk wani baƙin hali da ta samu ga Mustapha?
Ku biyo Haupha ✍️