WATA UNGUWA: Fita Ta 19
Sosai maganganun Baba akan mahaifiyarta suka daki zuciyarta ko kaɗan bata ji daɗi ba, duk da ta samu labarin ƙuruciyar mahaifiyar tasu bata yi kyau ba, amma koma menene uwa uwa ce, sai dai ba bakin mayar da martani, don haka ta raɓa shi zata wuce a tsorace yayin da shi kuma ya kawo mata mangara ta kauce da gudu ta ƙarasa cikin gida.
BABI NA SHA TARA
_MAI RABON SHAN DUKA BAYA JIN KWAƁO...._
"Yarinya dama kin haƙura da wannan zancen don kuwa wannan yaron ya miki nisa." Haliru ya faɗa
Sofi ta yi murmushi "Me yasa kace haka ɗan'uwa?"
"Saboda zuciyarsa a kulle take kirif, ma'ana dai wata ta miki shigar sauri ta riga ki kafa tutarta a birnin zuciyarsa."
Wani murmushin ta sake jifarsa da shi kana ta ce "Ba daga nan take ba, na tabbatar da cewa zan iya rikito da tutar tata ƙasa har ma na yi galaba a kanta, shi kenan dai Nagode."
Daga haka ta juya ta bar gun tare da kama hanyar gida. Tana tafe tana murmushi ita kaɗai ƙwaƙwalwarta na hasko mata yanayin zaman soyayyar da zasu yi da tauraron zuciyarta.
Bata yi aune ba ta ji an dafa kafaɗarta ana faɗar "Shegiyar gari, daga ina kuma haka?"
Waigowa ta yi ta kai dubanta ga mai maganar ta wadata fuskarta da murmushi "Ka ga _dakalin majina a hauka a zame ka hau mutum ka zauna daidai._ _Duddoo ƙanin iblis idan baya kusa kai ne ɗan aikensa._"
Ya yi dariya sosai "Zancenki dutse 'yar hannu, amma fa yanzu na fara laushi."
Ita ma dariyar ta sheƙe da ita kana ta ce "_Kowa ya tuba don wuya ba lada,_ yanzu dai me ka zo yi a unguwarmu?"
"Wallahi na zo duba wani abokin Babanmu ne ba shi da lafiya, a nan layin yake so har ma na fito zan juya gida ne yanzu."
"Nima dai gida zani yanzu, sai mun jame wurin Partyn Billy Lukency." Ta daga masa hannu sannan ta juya.
"Ok bye." Yana daga mata hannu.
Kowa ya kama hanyarsa.
*****
A ƙofar gida ta tarar da Baba, yana hangota ya haɗe girar sama da ƙasa.
Jikinta ne ya hau ɓari kamar an kaɗa mazari ƙafafunta suka shiga harɗewa jin take kamar ace mata ƙyat ta ruga. Amma ta kwana da sanin cewa _Bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne_ dalili kenan da yasa ta matsa bakinta na motsi.
"Baba Barka da hutawa."
Ya zuba mata harara da ta saka yan cikinta suka hautsine.
"Daga gidan uban wa kike da ranar nan." Ya ƙara tamke fuska.
"Am! Baba, dama-dama na je...." ta kasa ƙarasa zancen.
"Dama kin je gidan ubanwa ne? Ko dai daga wurin yawon karuwancin naki kika dawo? Ko da yake komai kuka yi _baku yas ba kan gado kuka ɗauko_ mahaifiyarku nan ba yawon ta zubar ɗin da bata yi ba har Kajara take zuwa can ne kuwa ƙarshen matattarar 'yan tasha, ba yadda mahaifiyata bata yi da ni ba na ƙi ji dama' yan magana sun ce _kowa yaƙi ji ba ya ƙi gani ba._ haka nan mai rabon shan duka ba ya jin kwaɓo sai ya sha._
Sosai maganganun Baba akan mahaifiyarta suka daki zuciyarta ko kaɗan bata ji daɗi ba, duk da ta samu labarin ƙuruciyar mahaifiyar tasu bata yi kyau ba, amma koma menene uwa uwa ce, sai dai ba bakin mayar da martani, don haka ta raɓa shi zata wuce a tsorace yayin da shi kuma ya kawo mata mangara ta kauce da gudu ta ƙarasa cikin gida.
Hanee ta fito daga banɗaki kenan suka yi arangama,goshinsu ya haɗu da juna ƙum.
"Ahh!" Suka saka ƙara a tare.
Cikin raɗaɗin gumuwar Hanee ta ce "Wai me yasa kika tsane ni har haka ne Sofi?."
"Ki yi haƙuri Hanee wallahi Baba ne ya koro ni, kinsan masifarsa dai." Ta faɗa a kiɗime tana waiwayen bayanta.
********"****
ALLURA TA TONO GARMA.
Bayan wata biyu Hanee ta fara laulayin da aka rasa gane kanta, kullum da zazzaɓi mai zafi take kwana ga yawan amaye-amaye, duk abin da ta saka a cikinta ba ya tsayawa sai ta haras da shi take samun salama, ba yadda mahaifiyarta bata yi da ita akan su je asibiti ba amma fafur ta ƙi, domin tana jin tsoron kada garin bincike _Allura ta tono garma._
Sai faman shan saƙa-saƙai da ganyayen itace take tamkar 'yar mai ganye, amma duk na banza.
Ko da Baba ya ga ciwon ya ƙi ci ya ƙi cinyewa sai ya matsanta akan cewa sai an je asibiti.
Ganin tana munƙi-munƙin zuwa ya ji a ran shi cewa tana ɓoye wani abin ne don haka watarana ya tasa keyarsu a gaba ita da mahaifiyarsu suka je asibitin gwamnati.
Gwajin farko aka tabbatar masu da cewa tana ɗauke da juna biyu ne.
_Tashin hankali gobarar gemu_
Jin wannan labarin ya saka Hanee ta ɗora hannu akai ta saka ihu.
"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Na shiga uku ni jikar mutum huɗu." Ina ta faɗa tana ɗora hannu a kai tsabar firgici.
Baba Mudi kuwa tun kafin, Hanee ta rufe bakinta ya samu nasarar gwabje mata baki da iya ƙarfinsa har sai da Haƙorinta ɗaya ya fara gyangyaɗi yana fitar da jini sosai. Sai kururuwa take yi.
Likitan da ya ga haka sai ya shiga rarrashin Baba Mudi har ya samu ya kore su daga office ɗin gudun kada su tara masa jama'a.
Tun a cikin harabar asibitin baba yake dukan Hanifah da iya ƙarfinsa yana bambamin bala'i "Shegiya karuwa, matsiyaciya wacce ta yi gadon gantali a gun uwarta, ni zaki zubarwa da mutunci a gari? Cikin shege a gidana?"
Ya ci gaba da dukanta, Inna ta matso ta shiga tsakani ita ma ya kai mata mangara a kumatu, dole ta kauce ba shiri.
"Habah Mudi, wannan wane irin tonon asiri ne kake mana? Don Allah ka yi haƙuri, komai zaka faɗa ko ka aikata ka bari sai mun je gida tukunna." Cikin Muryar kuka Inna ke ba shi haƙuri amma bai saurare ta ba.
Wasu tsirarun mutane daga cikin waɗanda ke tsaye a gun suka matso suna ba shi baki, wani dattijo ya ce "Ka yi haƙuri bawan Allah, idan rai ya ɓaci bai kamata hankali ya gushe ba."
"Ka san me ta yi ne?" Ya faɗa a kufule yana kallon tsohon, sai huci yake tamkar kumurci.
"Koma me ta yi ai ka yi mata uzuri ku je gida, kuma ban da abinka ai _ice tun yana ɗanye ake tanƙwarashi_
_Da ƙyar da sidin goshi_ suka ƙwace ta a hannu Baba Mudi suka tare masu Napep ita da Inna suka shiga, shi kuma ya hawo mashin ɗin hanya.
**********
"Ina take matsiyaciyar, ƙaramar karuwa? Yau ko ni Ko ke a gidan nan." Da wannan furucin ya shigo a maimakon sallama.
Jin sautin muryarsa ya ƙara kiɗimar da Hanee har ta ji ta yi nadamar dawowa gidan.
"Shi kenan na shigangaɗi, yau na san sai nafi gyaɗa markaɗuwa ka cuce ni......."
Wane tasku Hanifah zata fuskanta a rayuwarta bayan faruwar wannan mummunar ƙaddarar?
Shin Alhaji Saminu zai saurare ta?
Ku biyo ni don jin ƙarashen labarin.
Ummu Inteesar ce
managarciya