HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 40

HAƊIN ALLAH:
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 40
Wayar na kan kunnenta hawaye na tsiyayowa daga kan fuskarta, tana son yin magana amma bata iya furta ko da kalma guda, to me zata ce ma wai? Tana jin rishin kukansa a kan kunnenta yana cewa, "Jiddah kin tafi kin bar Ni cike da kewarki, na rasa ya zan yi na rasa me ke min daɗi, don Allah ki dawo gareni Jiddah tun kafin cutar ƙaunarki ta nakasar da rayuwata."
Ba wai kukansa yasa ta kuka ba, a'a kuka take na jin cewar saboda ita wani ke kuka, ashe har akwai wanda zai mata irin wannan soyayyar da zai zubar da hawayensa saboda ita? Ashe har ta kai matsayin da kamar Mustapha mai aji da kyau da taƙama zai zubawar da hawaye saboda sonta? Tabbas wannan abin kuka ne na farin ciki gareta, dole ta gode wa Allah da wannan matsayi da ya kaita wanda bata taɓa tsintar kanta a cikinsa ba.
Mustapha da gaske kuka yake sosai kamar wani ƙaramin yaro, kuka yake har yana jan majina kuma ba don yana son kukan ba kawai ji ya yi kukan ya zo mai da ƙarfin gaske lokacin daya kira ta a waya.
Ba ƙarya son ta yake sosai son da ko a tarihi bai taɓa yi wa wata yarinya irinshi ba. Jiddah ta zama wata katangar saka shi farin ciki a rayuwarsa yanzu gani yake tamkar zai rasa ne nisan da tai mai, yana ji a jikinsa rasa Jiddah wani babban ƙalubale ne a rayuwarsa kuma ba zai taɓa cika burinsa ba samun irin rayuwar da yake fata da mafarkin samu na zaman aure ba.
Ya ja ajiyar zuciya ya ce, "Jiddah don Allah ki taimaka ki amsa min ko da sau ɗaya ne cewa kina so na don Allah! Na rantse da Allah na rasa farin cikina da annurin zuciyata tun da na ganki za ki tafi har zuwa yanzu ban cikin farin ciki Jiddah. Shin Jiddah ko da sau ɗaya baki taɓa jin cewar na cancanci na so ki bane ba ko me? Na san cewa Jiddah mutane da dama ba za su so wannan haɗin ba, amma don Allah ki taimaka ki daɗe kunnuwanki daga duk wasu surutu da za ai maki ki taimake Ni ki so Ni Jiddah don Allah!
Magana yake cikin kuka sosai don wani abin ma bata san me yake cewa ba.
Ita kuma sai kukanta ya tsananta ji take kamar bata kai ba, kamar bata da matsayin kamar bata da ajin da namiji kamar Mustapha zai zauna ya dinga mata kuka ba.
Tabbas Allah abin godiya ne ya zaɓe ta a cikin dubbun mata ya dasa ma maza uku sonta waɗanda ko a mafarki bata taɓa tsammanin hakan ba.
Tabbas bata shirya soyayya ba, idan ma soyayya za tai to ba zai soyayya da Mustapha ba, haka ba zatai soyayya da Dr Faisal ba shi ma Kawu Mansur ba zata iya aurensa ba, a takaice dai su duka babu zaɓin zuciyarta a cikinsu.
Ita tana ta tunani yayin da shi kuma yake ta kuka kamar wani ƙaramin yaro yana ambatar sunanta.
Da ƙyar ta samu ta daina kukan ta gyara muryarta tace, "Ni ban ce ban sonka ba, amma dai ba yanzu zan yi aure ba, saboda yarana nike kula da su don haka ban zaci zan iya aure ba duk don waɗannan shekarun ba."
Mustapha ya ja majina ya ce, "Na yarda da ba yanzu za ki aure ba amma ina son don Allah ki min alƙawarin za ki aure Ni duk lokacin da kika tashi auren don Allah Princess."
Ta rasa ya zatai mai, akan me zai wautar faɗawa mai mata har uku? Gaskiyar magana abin ba zai mata kyau bata san tai aure inda damuwa zata cigaba da bibiyarta tafi son tai aure inda zata zauna cike da farin ciki da aminci. Idan haka ne kuwa to karda ta kai kanta gidan kishiya don haka haɗin nan ba zai yiyu ba gaskiyar magana.
Mustapha jin ta yi shiru ya ce, "Ina son don Allah ki amince min Jiddah nayi maki alƙawarin zan kula da ke zan baki duk wata kulawa zan tabbatar da cewa kina cikin jerin mata masu farin ciki da rayuwar aurensu nayi maki wannan alƙawarin Princess."
Kamar yana gabanta haka take girgiza kanta, akan me zata amince da soyayyar mai mata? Me ta tsinta a rayuwarta da har zata kai kanta cikin mata kawai ta saka kanta a uku da ranta da lafiyarta a lokacin da take da madafan ikon gina rayuwarta da rayuwa mai inganci a inda take so yai mata kuma? Tabbas gidan Mustapha yafi ƙarfinta ba zata iya zaman kishi da matansa ba sai dai ya yi haƙuri. Don haka tace cikin sanyin murya, "Kai haƙuri amma ba zan iya zama cikin matanka ba gaskiya." Ta kashe wayar kafin ma ya sake cewa wani abu.
Mustapha yabi wayar da kallo yana jin zuciyarsa na zafi kamar zata kama da wuta. Me yake son faruwa da shi ne? Me ye aibunsa don kawai bai dacen mata ba sai a ɗauka laifinsa ne ba laifinsu ba? Me yasa Jiddah zata kasa fahimtar shi? Me yasa mutane suke kasa yi mai uzuri ne? Kuka yake sosai yana fyacewa ji yake tamkar ya mutu ma kowa ya huta tun da babu mai masa uzuri babu mai fahimtar sa balle ya fahimci halin da yake ciki. Haka ya jima a yanayin tamkar ba shi ba, duk wata jimammiyar damuwarsa sai da ta dawo masa sabuwa, ya dinga tuna yadda Salim ke kwatanta mai wata rana sai labari to wai yaushe ne zai zama labarin? Yaushe ne ma komai zai wuce a gunshi to? Hawaye yake yana ƙarawa, tabbas Jiddah ita ce maganin matsalarsa idan ya tasa ta zai ƙara shiga cikin matsalar da tafi ta baya ne nesa ba kusa ba.
Amma ba zai ƙasa a gwiwa ba, zai dage iyakar dagewa zai jure iyakar jurewa ba zai gaza ba har sai ya samu cikar burinsa watau auren Jiddah.
Deeni
Yana zaune kamar an dasa shi, yana tuna ranar da abin ya faru ranar da ba zai manta ba, ranar da kunya da nadama tare da takaicin abin da ya aikata suka sa ya kasa ko da ɗaga halshensa balle ya furta ko da kalma guda ce. A hankali ya dinga hasko yadda abin ya faru a idanunsa.
Yana zaune a ɗakin da aka ware mai bayan ya warke daga ciwon damuwar da ya so ya maida shi mahaukacin ƙarfi da yaji sai ga Likitan ya shigo da sallamarsa ya ce, "Yawwa ga wadda tai ma magani ta zo kamar yadda ka buƙata tana son ku gana."
Cike da fara'a ya amsa da cewa "To Likita na gode sosai mu je na ganta."
Suka tashi Likitan na gaba yana bayansa suka fice daga ɗakin zuwa office ɗin Likitan.
Tana zaune fuskarsa ɗauke da tabarau ta ɗora ƙafarta ɗaya kan ɗaya tana duban wasu hotuna dake hannunta. Fuskarta ɗauke take da murmushi ga ƙamshin turaren ta daya kama office ɗin baki ɗaya.
Da sallama suka shiga su duka har Likitan, bayan shigarsu ne Likitan ya nemi ya fice amma sai ta dakatar da shi tace, "No Dr zauna ai komai a gabanka ai ba wani abu bane sabo, abin da aka saba ne dai kawai."
Hakan yasa Likitan zama kan kujerarsa ya gyara tabaran fuskarsa ya yi shiru.
Kujerar dake kallon kujerarta ta nuna mai ya zauna, bayan ya zauna ta dube shi sosai fuska cike da fara'a tace, "Malam Deeni kenan, kana lafiya? Ina fatan ba abin da ke damunka a halin yanzu? Nufina baka da wani ɓoyayyen ciwo a cikin jikinka?"
Cike da jin daɗi ya amsa mata da cewar, "Ai gaskiya jiki alhamdulillah komai ya yi min lafiya ban da wata damuwa ko matsala Hajiya, sai dai ince Allah Ya saka maki da mafi alheri kan abin da kikai min na gode sosai da sosai Hajiya."
Dariya tai irinta manyan nan ta miƙa mai hotunan wajenta, tana cewa, "Ko zaka iya gane min su waye a cikin waɗannan hotunan Malam Deeni?"
Amsar hotunan ya yi yana dubawa, zumbar ya miƙe tsaye yana ƙarewa hotunan kallo yana sake zaro idanuwa alamar mamaki sosai ya ce, "Ina kika samu waɗannan hotunan, ai wannan matata ce, waɗannan kuma yarana ne don Allah suna ina domin nemansu nake na maida matata da yarana guna mu cigaba da zama kamar baya."
Baƙin ciki da takaicin kalaman sa yasa Alawiyya ɗauke shi da mari tana cewa.
"Wannan da kake gani ita ce Jiddah yarinya mai haƙuri da natsuwa mai cike da tsoron Allah macen da bata ɗauki rayuwar duniya da zafi ba, ta zauna da kai duk da bakai ne zaɓin ta ba, tai maka ladabi duk da azabtar da ita da kai, ta zame maka macen rufin asiri duk da tona mata nata asirin da kai, tai maka sutura duk da sace mata nata da kake, ta ci da kai duk da azabtar da ita da yunwa da kai, ƙarshe ta kare maka mutunci duk da watsar mata da nata mutuncin da kai.
Deeni ina son ka sani Jiddah yanzu tafi ƙarfin ka tafi ƙarfin duk wani wanda ya shafe ka don haka kai shirin amsar tukuicin abin da kai mata a yanzu ba sai gaba ba.
Deeni ka sani tun da nake da Jiddah ban taɓa ganin tayi farin ciki ba saboda kai ne wanda ya kamata ka zame mata farin cikin amma sai ka zame mata baƙin ciki wanda hakan yasa take jin tsanar kowane namiji a zuciyarta har ma bata maraba da aure a rayuwarta.
Deeni ka sani ka yi wa kanka asarar mace mai mutunci da kamala mai riƙe sirrinka mai haƙuri da babunka mai farin ciki da samunka mai neman hanyar zamanka mutumin kirki a rayuwarka.
Shin Deeni wane irin tukuici ka samu na bin matan da kake ne? Shin Deeni wane lambar yabo ka samu na wulaƙanta matarka da yaranka da kai?
Ina so ka sani baka wulaƙanta banza ba, domin Jiddah na da Ni zan iya haƙuri idan Ni kai mawa amma ba zan iya haƙuri ba idan ita zakai mawa ba.
Ka sani dole ne na nuna maka cewar Jiddah tafi kowace macen da kake tarayya da ita ƴanci da gaya ta yadda ko mai irin sunanta ka ji sai ka girmama sunan balle ka ganta.
Nasan kana son jin ko Ni wacece ko? To tabbas nasan indai da gaske kai ne Deeni mijin Jiddah ba zaka rasa sanin wacece Alawiyya a gun Jiddah ba wadda su kai rayuwa a Lagos tare ba. Don haka na zo ne don na ɗaukar wa ƙawata kuma ƴar'uwata fansar abin da kai mata wanda ba zan iya yafe maka ba ko da kuwa hakan zai sa na samu ƙarin matsayi ko tarin dukiya Deeni.
Ko da yake kaga yadda Allah Ya maida Jiddah ita da yaranta suna cikin aminci da kiyayewar Ubangiji yadda ya kamata, to bari na yi maka wani albishir ɗin ma, Jiddah yanzu ta zama cikakkiyar Lauya mai zaman kanta wadda ke aiki a cikin babban gari kamar Kaduna, tana baibaye da tarin masoya manyan gaske masu aji da matsayi waɗanda suna iya rasa komai nasu indai za su mallake ta.
Kamar wasa ta taɓa hannunta sai ga wasu majiya ƙarfi sun shigo su kai waje da shi suka saka a bayan mota, tun yana gane tafiya ake har ya daina gane komai saboda yunwa da ƙishirwa da suka dame shi. Ya yi barci yafi sau tari har barcin ya gagare shi yi ma sannan ya ji motar ta tsaya lokacin da ko hannu bai iya ɗagawa.
Sai dai suka ɗauke shi a wulaƙance suka shiga da shi wani babban gini suka watsa wani ɗaki mai tarin mutane duk maza suka juya.
Ashe bisa wani suka jefa shi, suna juyawa ya jefar da shi ya rufe shi da duka yana zaginsa ta Uwa ta Uba, maimakon mutanen ɗakin su raba su ko su shiga tsakaninsu sai ma suka kama kiɗi da robobin dake hannunsu masu kama dana aljamirai.
Sai da mutumin nan ya yi mai lilis sannan ya ƙyale shi ya koma gefe yana ajiyar zuciya.
Tun daga lokacin ya fahimci cewar gidan maza ne aka kai shi, kuma wani babban ƙalubale da yake fuskanta ne yadda yadda kowa yafi wani ƙarfi a ɗakin dukan wanda yafi ƙarfi yake, idan aka basu abinci kafin ya gama ci ake amshewa ai ta mai dariya bai da yadda zai yi.
Babu irin azabar da bai sha a cikin ɗakin saboda duk ɗakin shi ne raggo bai iya faɗa ba cikin tarin ƴan daba aka kai shi masu zaluncin gaske ba tausayi ba imani a ransu ko alama.
Ko yanzu da yake zaune yana wannan tunanin ji yake tamkar ya nutse don kunya da nadamar abubuwan daya aikawa Jiddah ganinta yake tamkar bata isa ba, kallon marar galihu yake mata wadda bata da mai tsaya mata a dukkan lamurranta ashe ba haka bane shi ne babban marar galihun da bai da mai tsaya mai kan komai na rayuwarsa.
Ko da yaushe cikin tunanin yaushe zai bar gun nan yake ya je ya nemi inda Jiddah take ya bata haƙuri, amma bai san lokacin da zai bar wajen ba ga alama dai nan zai mutu ba tare da ya nemi inda yafiyar Jiddah ba. Kuka yake sosai yana ƙarawa cike da jin haushin kansa.
Baban Jiddah
Tun da yake zaune a cikin gidan yarin nan bai taɓa jin kewar yaransa ba sai Yau ga shi ciwo ya yi mai sallama bai lafiya bai da mai kula da shi duk ya kori yaransa bai nuna masu tausayi ba, bai basu kulawa ba haka ya fifita yaran tasha fiye da yaransa.
Har ya manta yaushe rabon daya saka ko da yaro guda ne a idonsa, su duka bai san inda suke ba, ba kamar Jiddah ita ce wadda ko mijinta bai taɓa sani ba balle gidan aurenta.
Jama'a da dama sun sha iske shi su ba shi shawara kan ya nemawa yarinyarsa ƴancinta a gidan mijinta amma yai biris ya nuna ba abin da ya dame shi sam.
Shi a takaice ma ko kalar yaran da ta haifa bai sani ba, hana rantsuwa ranar da ta taɓa zuwa daga asibiti ta iske shi da yaranta ƴan biyu data haifa ya ji tace nan zata zauna ya kore ta tun daga ranar bai sake ganinta ba har Yau.
Mutane suna yawan ba shi shawara kan yarinyar na cikin matsala amma ko a jikinsa ji yake ita ɗin matsala ce damuwa ce a gunsa wadda ba wata ƙaruwa da zata kawo mai sai dai ta nema gareshi tunda ba cikin kuɗi take ba, talaka ne mijinta kuma ba ta ita yake ba ma mijin nata.
Hakan yasa baki ɗaya ya manta da ita a shafin rayuwarsa.
Yau ga shi yana ta ganin inda yara ke da rana, yana ganin yadda yara ke tsayawa kan damuwar iyayensu saboda suma iyayen sun tsaya ma yaran a kan damuwarsu lokacin da suke yara.
Kullum akai masu wa'azi sai ya zubar da hawayen nadamar abin da ya aikata ma yaransa, tabbas ya cutar da yaransa iyakar cuta wadda bai san inda zai gansu ba su yafe mai ba, ko da yake ba mamaki ma baƙar wahala ta kashe mai yaran yanzu. Kuka yake sosai kamar ranshi zai fita.
Wata tsohuwa da duk lokacin da taga Baban Jiddah na zaune yana kuka ko tunani sai taga kamar ta san shi amma ta rasa inda ta san shi, Yau dai kukan da yake ya yi yawa yasa ta ji tausan shi sosai don haka ta matsa a hankali ta isa inda yake ta zauna kusa da shi tana ba shi haƙuri da Hausar da har zuwa yanzu bata gama kame bakinta ba, da jin Hausar ba Bahausa bace ba ita.
Ya kalle ta yana kukan ya ce, "Tsohuwa ki bar Ni nayi kuka don na aikata abin kukan ne wanda ko ke kika ji shi sai kin ce na cigaba da kukana domin Ni kuka ya kama ba kowa ba."
Tsohuwar ita ma ta rasa ido guda da hannu guda tace, "Ni kam a gani na nice ya dace nayi kuka Ni da na rasa ido guda da hannu guda kuma aka kawo nin gidan yari ake ta ajiya ta, ban da kowa a cikin garin nan, Ni da kake gani nan da can baya a nan nake zaune ina sana'ar saida abinci, ba laifi ina samun ciniki yadda ya kamata saboda ba laifi ina gyara abincina yadda ya kamata. A haka ne Allah Ya haɗa Ni da wani bawan Allah wanda ya ɗauki yarinyarsa ya ban amana, na amsar mai yarinya da sunan zan riƙe ta amana amma na kasa cika alƙawarin dana ɗauka na dinga azabtar da yarinyar nan ban duba ga yarintar ta ba, haka na dinga jibga mata aikin wahala ga ban bata abinci ga duka da zagi na safe daban na rana daban, yarinyar nan babu irin wahalar da bata sha ba a guna ba, komai ita ce ke min, hakan bai sa ba na raga mata ba, idan ubanta ya zo na haɗa mata sharri ko ganinsa ban bari tayi, daga ƙarshe nasa a raina zan gudu da ita na kaita garinmu can Jahar Yobe inda zan fitar da ita daga addininsu na maida ta cikin addini na na haɗa ta aure da yaron ƙanina, yin wannan tunanin yasa na dinga cin kuɗin yaron na aika da wasiƙa nace zan kawo wata yarinya ƴar addinin Musulunci zuwa namu addinin. Hakan yasa aka dinga aiko min da manyan kuɗaɗe suna cewa nayi aikin lada, sai dai ina cikin hakan ne wata tsohuwa ta kawo min ajiyar jikarta da alƙawarin zata dawo nan da wani lokaci kaɗan amma bata ba labarinta don haka da naga kuɗin da taban na ajiyar yarinyar sun ƙare sai na ɗauki karan tsana na ɗorawa yarinyar tare da wadda aka ban riƙo ko da yaushe cikin azabtar da su nake ba ji ba gani.
Muna a cikin yanayin ne aka aiko min da cewa mijina zai ƙara aure a can gida don haka na yanke shawarar tattarawa Ni da yarinyar mu tafi mu bar wadda aka ban ajiya nan tunda wadda ta ban ajiyar ta ƙi dawowa, sai dai a daren ranar yaran nan suka haɗe kai suka gudu bayan sun ɗibar min kuɗi masu dama, ina cikin tashin hankalin ne kuma sai ga Baban yarinyar da aka ban ajiya ya zo har da Yayansa, muna tsaye kuma sai ga wanda yaban ajiyar yarinya shima ya zo ganin yarinyarsa, in takaice maka labari rasa madafa yasa na yi ma waɗancan ƙarya shi kuma na saka mai maganin barci a lemu nabi dare na gudu na bar Lagos don daman ba wanda yasan daga inda na zo Lagos ɗin.
Ina komawa gida sai kuma fastocin garinmu suka matsamin da tambayar ina yarinyar da nace zan kawo a maidata addininmu? Nace ta gudu suka ce ƙarya nake basu yadda ba, kawai nayi masu damfara ne na amshe masu kuɗaɗe kuma sai na biya su, daga ƙarshe dai suka ƙwace duk wata kadara ta suka tsiyata Ni sosai kuma suka ce mijina ya ƙara aurensa. Kasancewar ina kishin gaske yasa muka kasa zaman lafiya a gidan mijina ko da yaushe cikin faɗa da dambe muke.
Muna cikin wannan rayuwar ne wata rana mukai faɗa cikin dare da kishiyata ta ci nasarar caka min tsinken kitso a idona guda ta kuma caka min a tsintsiyar hannuna ni kuma na ɗauki wuƙa na daɓa mata a cikinta ta faɗi ba rai Ni kuma na gudu cikin daren. Rashin gata yasa nai ta yawo ƙauyuka ina bara har na tara kuɗin mota na taho Lagos don in cigaba da Bara ta, sai dai lokacin idona ya tsiyaye hannuna ya ruɓe da taimakon wani bawan Allah ne akai min aikin hannun aka yanke shi har ya warke na cigaba da barata ka'in da na'in sai dai kuma ashe dangin kishiyata basu haƙura da nema na ba har nan Lagos suka zo su kai ƙarata shi ne aka kawo Ni nan gidan yarin aka ƙulle Ni a zuwan an min hukuncin ɗaurin rai da rai.
Tunda ta fara magana yake ƙara sautin kukansa, ashe Iyami ce ita ce yaba ajiyar Jiddah tun tana yarinya ashe haka ta azabtar da ita? Ashe haka ta dinga mata horon duka da zagi? Lallai shi ɗin bai dace da zama Uba na gari ba tabbas dole ya ga rayuwa mai cike babban ƙalubale.
Iyami ta kalle shi tana hawaye tace, a kwanakin baya naga Alawiyya a nan gidan da idona amma aka hanani isa inda take, na ganta a babban matsayi na babbar Lauya tana cikin masu tsaron lafiyarta, na so nai mata magana domin nasan duk inda take tana tare da Jiddah yarinyar da aka ban amanarta.
Baban Jiddah ya rushe da kuka sosai ya ce, "Kina nufin ke ce Iyami mai abinci? Kina nufin ke ce naba ɗiyata Jiddah ajiya? To Ni ne mahaifin Jiddah kukan da nake ba na komai bane ba illa na nadamar abin da na aikatawa rayuwar yarana.
Nan Iyami ta zabura ta tsugunna tana ba shi haƙuri cikin matuƙar kuka da nadama, ya ce, "Ki daina ban haƙuri don ban cancanta da aban haƙuri da abin da ya shafi Jiddah ba saboda Ni ne wanda na fara banzatar da ita na nunawa duniya bata da kowa bata da kima a guna sam."
Nan su kai ta kuka suna ƙarawa suna ba kansu laifuka da dama na abin da ya same su.
Baban Jiddah ya dinga addu'ar Allah Ya kawo ƙawar Jiddah da aka ce an ganta a gidan yana son ya nemi alfarmar ta kan ta haɗa shi da Jiddah ko da a waya ne ya bata haƙuri ya nemi yafiyarta ya nemi alfarmar ta nemi ƙannenta ta riƙe su a gunta tunda shi yasan bai da ranar fita a gidan nan duk da bai san me ya yi ba aka kawo shi gidan ba.
Kano
Alawiyya na zaune ta tasa yaranta tana kallonsu tana jin daɗin yadda rayuwarta ta natsu take zaune gidanta cikin farin ciki da natsuwa duk da cewar maigidan na zaune cikin damuwa da tashin hankali na rashin samun amsar soyayyar Jiddah, ita kuma ba damunta ba ne ba abin bai ba ya dame ta kawai dai ta rasa yadda za tai da lamarin ne yadda Kawo Mansur ya dame ta ya takura mata ya hana ta sakat da kiran waya ko da yaushe cikin tambayarta yake ta gayama Jiddah maganar aurenta da zai yi?
Ita kuma a hangenta Jiddah ita ce wadda ya kamata ta zaɓi wanda take son aure a cikinsu.
Tana yawan ganin yadda Mustapha ke cikin damuwa idan ta je gun Hajjo su gaisa, amma ya zatai ban da kau da kai da nuna mai bata san komai ba kan lamarin? A nata hangen da Jiddah zata amince kawai ta ɗauki Babansu Ammar ta aure shi yadda komai nasu zai zama ɗaya su cigaba da zama tamkar yadda suka zauna a Lagos.
Tana son ta je Kadunar don su zauna da Jiddah ta ji ra'ayinta kan duk masu sonta don ta samu kwanciyar hankali da zaman lafiya ita ma.
Dr Faisal ne ya shigo ba wata fara'a ko annuri ya shige ɗakinsa don a ganinsa ita ce bata tausayinasa, ta daina son sa ta daina kula da damuwarsa ita kawai rayuwarta take cike da farin ciki ko oho take da yanayin da yake ciki.
Kan gado ya faɗa ko takalminsa bai cire ba ya lalubo wayarsa ya kira Jiddah.
Jiddah na zaune tana yi wa Afnan kitso kira ya shigo wayarta ta ɗauka ba tare da ko duba mai kiran nata ta yi ba, jin mai magana yasa nan take ta haɗe ranta kamar yana gabanta ta amsa sallamar da ya yi mata a daƙile.
Cike da gajiyawa da yadda take mai yawo da hankali ya ce, "Jiddah wane irin farin ciki kike idan kika ɓata min rai ne? Ke kam baki da tausayi ko kaɗan baki jin tausayin halin da nake akan sonki komi ya dagule min ko gun aikina kasa taɓuka komai nake sai kwanciya da jinyar zuciyata. Shin Jiddah ba za ki damu ba kin kasa taimakon mijin ƙawarki ba wadda ta fifita ki akan kowa nata ba? Haba Jiddah ban cancanci na zamo abin ƙi a gurinki ba ko dan saboda Alawiyya... Cike da tafasar zuciya tace, "Don Allah Baban Ammar ka daina maida Ni yarinya ƙarama haka nan. An gaya maka Jiddah bata san me take yi bane ba ko an gayama Jiddah bata san ciwon kanta ba balle tasan me ake kira da halacci ba tare da karamci bane ba? Don Allah ina son daga yanzu ka cire duk wata alama mai kama da sona daga zuciyarka ka ɗauke Ni tamkar abiyar tagwaicin matarka wadda babu aure tsakanina da kai har har abada. Na gaji! Na gaji! Na gaji! Wannan karon kuka ya ƙwace mata sosai tana maganar.
Alawiyya na tsaye tana jin kome Jiddah da shi kanshi Faisal ɗin ke cewa sai ta rasa a cikinsu wa za ba haƙuri ne? Me ke shirin faruwa da su ne haka? Me yasa hakan ke faruwa ne? Ashe Jiddah ba zata iya rufa ma mijinta asiri ba ko dan darajarta ba? Ashe Jiddah ba mai auren mijinta bace idan taga ya shiga halin da yake ciki kanta bane ba? Ta juya zuciyarta ba daɗi ta koma ɗakinta ta zauna ta ɗauko wayarta ta kira layin Jiddar.
Tana kashe kiran Faisal ta jefar da wayar ta tashi ta bar Afnan zaune ta shige ɗakinta kuka take son yi sosai bata son yarinyar taga hawayenta saboda shegen wayau ne da ita, don haka ta shige ɗaki ta rufe don tai kukanta son ranta.
Shigar ta ɗakin ke da wuya kiran Alawiyya ya shigo wayarta, tai ta kira amma ba a ɗaga ba, don haka ta sa a ranta Jiddah na can na kuka duk yadda akai tun da har ta kasa ɗaga kiran da tai mata, itama sai ta fashe da kukan sosai ta kwanta.
Ya rasa me yasa ya kasa haƙura da yarinyar, duk da yadda take share shi take nuna mai ko'in kula ya kasa cire ta daga zuciyarsa, tunda yake a tarihin rayuwarsa bai taɓa zuwa gun yarinya tace bata son shi ba, amma Yau ga shi Jiddah ta nuna mai bata son shi kan wata hujja da bata da ƙarfi ko inganci. Ya kasa manta ta a rayuwarsa duk daren duniya kwana yake kukan rashin samun soyayyarta, kuka ya zame mai jiki akan soyayyar Jiddah bai jin komai ya rufe ɗakinsa ya dinga darzar kuka yana kallon hotonta.
Duk lokacin da ya kira wayarta ya ji tana waya kuwa ji yake kamar ya je ya iske ta inda take ya amshe wayar ya yiwa ko wane marar mutuncin ne kashedin kiran matarsa, saboda har ga Allah ya ɗaukar wa ransa Jiddah ce matarsa insha Allah. Duk tarin matsalai da yake fuskanta daga gidansa basu damunsa yanzu babbar damuwarsa ita ce Jiddah ita ce kawai matsalarsa yanzu yana samunta ya gama samun matsala ko damuwa a ransa yasan da hakan.
Wayarsa ya jawo ya kira layinta, har ta katse bata ɗauka ba sai a kira na biyu sannan ta ɗaga kiran.
Ajiyar zuciya ya saki a hankali ya kira sunan da yake kiranta da shi wasu lokutan, "Princess ina kika aje wayar ne haka na kira baki ɗauka ba?"
Bata san me yasa ba shi ne kawai wanda bata iya sakin baki tai mai rashin kunya ba duk cikin masu son nata, bata sani ba ko dan yana ɗan'uwan Uncle Salim ɗinta ne oho.
Ya sake yi mata magana domin ya fahimci bai da waccan amsar tambayar tashi, "Princess kina lafiya?'
Da ƙyar ta samu bakinta ya buɗe ta gaida shi tai shiru.
Cikin muryar ban tausayi ya ce, "Don Allah Princess ki yi min adalci akan soyayyar da nake maki mana kada ki zama mai cutar wa a gare Ni da yawa mana."
Shiru bata ce komai ba.
"Don Allah Princess ki daina azabtar da rayuwata haka nan kada ki sa na ida rasa sauran ƙwarin gwiwata saboda ke ce kika sa na fara ji a jikina zan dawo kamar kowa zan rayu kamar kowane magidanci Princess don Allah ki taimaka min mana." Tana jin sautin kukanshi na dukan kunnuwanta.
Idan zata faɗi gaskiya Mustapha shi ne ya iya irin soyayyar da take nema amma ba zatai kasadar amince mai ba ya aure ta ya kaita gidansa ya haɗa ta da tarin matansa ba da su kansu basu ragama kansu ba balle su ɗagawa wanda suke tare ba.
Idan kuma zatai ma kanta adalci na gaske bai kamata ta auri mai mata ba kamata ya yi ta auri wanda bai da mata yadda za ta je tai rayuwarta daidai yadda ta tsara da yadda take mafarkinta.
Shi kuma jin tai banza ta ƙyale shi yasa ya cigaba da kukansa don bai iya cewa komai a lokacin idan ba kukan ba. Har mamakin yadda yake kuka kan mace yake kamar ba shi ba, bai taɓa kawo a rayuwarsa zai zubar wa mace da hawayen rashin samun soyayyarta ba bayan hawayen damuwar da matansa ke sashi ciki da yake ba.
Jiddah jin ya ƙi daina kukan tai gyaran murya tace, "Indai akaina kake kukan ka daina domin ban jin daɗi kuma insha Allah zan amsa maka maganarka sai dai ina jin tsoron yadda zaka rayu da mata har huɗu ne, don haka ne ba zan iya amsa maka ba gaskiya don ba zan iya rayuwa cikin matanka ba."
Ajiyar zuciya ya saki ya ce, "Wallahi ba haka bane ba Princess matana biyu ne ba uku ba yanzu haka don Allah ki amince min ba zan aje ki cikin Matana ba gidanki daban zan aje ki ba za ki zauna da kowa ba wallahi."
Bata san ya akai ba kawai jin bakinta tai ya furta "NA AMINCE TO!
"Kambu! Kana nufin wannan shegiyar yarinyar mai kama da zubin karuwar zaka aura? To wallahi ba zata yiyu ba indai ina cikin gidan nan." Cewar Hafsat dake tsaye kan Mustapha tana girgiza jikinta cike da masifa.
Kawu Mansur kuwa yana ta kiran wayar Jiddah amma tana waya ya kira ta Alawiyya bata ɗauka ba kawai sai ya samu kanshi da jin rashin daɗin hakan, don haka ya kira wayar Yayansa ya tambaye shi idan yana gida zai je yana da magana mai muhimmanci da shi, ya tabbatar mai da yana gidan, don haka ya zuba wanka ya ɗauki kwalliya ya wuce kai tsaye gidansu Jiddah da zummar zuwa neman auren Jiddah.
Tabdijam! Jiddah ta amsa soyayyar Mustapha ga Alawiyya na bayan mijinta ga Kawu Mansur ya shirya tsab don zuwa gun Yayansa neman aurenta a cikinsu ko wa zai dace to?
Taku a kullum Haupha ✍️