WATA UNGUWA:Fita Ta 10
Murmushin da ya auri fuskarsa muddin yana cikin gidan ya yi sannan ya ce "Wannan Sawu na biyar kenan na ɗebo, to uzurin fita ne ya kama ni da gaggawa shi ne na ke son ki sammun na yi wanka in ba damuwa Ranki ya daɗe." Yar dariya ta yi "To to to, na gane jeka abinka Allah ya ma Albarka." Ya amsa da Amin sannan ya shige banɗaki a gaggauce ya yi wanka, tare da canza kaya ya fice daga gidan.
WATA UNGUWA:Fita Ta 10
page 10
BABI NA GOMA
Tun kan su ƙarasa Dagarman ta ɗaga waya ta kira gayenta, sai dai yau ma kamar kullum bai ɗaga ba.
A gaggauce ta tura masa saƙo kamar haka "Masoyi ina hanya gani nan zuwa, na kasa juran rashinka a kusa da ni."
Lokacin da sakon ya shiga wayar Ja'afar yana gidan iyayensa dake unguwar Bashal. Hannunsa ɗaya na riƙe da bokitin roba Babba, ya ɗebo ruwa daga famfon unguwar.
Ya zo dai-dai ƙofar gidansu kenan sakon ya shigo, cikin hanzari ya ɗauko wayarsa don ganin ko saƙon da yake ta dakon jira ne.
"Ai kuwa shi ne." Ya faɗa tare da saka ihu kaɗan ya ce "Yes! Yau akwai shagali kenan bari in yi sauri."
Tun kafin ya shiga gidan ya kira Abokinsa Duddoo da suke hayar ɗakin a tare ya ce "Don Allah guy gyara mana ɗaki, ka saka turare gani nan zuwa yanzu."
Ta samu ke nan?" Cewar Duddoo
Yar dariya ya yi sannan ya ce "Kawai ka gyara mun Babyna na hanya so nake na riga ta ƙarasowa."
"Ba dai Mahee ba?." cewar Duddoo cikin mamaki.
Dariya sosai Ja'afar ya yi ya ce "An gaya ma ni wasa ne? Ai kai dai yau akwai part........"
Kasa ƙarasa zancen ya yi don ganin tahowar Abbansa daga wajen.
Da sauri ya datse wayar tare da ɗurkusawa "Abba ina wuni?."
"Lafiya lau Jafaru, ruwa ka debowa Umman taka ne?" Ya Amsa da murmushi a fuskarsa.
A kullum yana ƙara godiya ga Allah da ya azurta shi da ɗa mai hankali da nutsuwa, wanda kullum ba ya da burin da ya wuce ya faranta masu rai.
"Eh Abba." Ya faɗa a taƙaice sannan ya ɗauki bokitin ya shige ciki a hanzarce.
"Wai har ka dawo ne Jafaru?" Cewar mahaifiyarsa dake zaune tsakar gidan ta ga shigowarsa.
"Eh Umma na dawo." Ya faɗa yayin da yake zuba ruwan a bokitin wanka.
"Ya kuma na ga kana juye ruwan ne, ba ni ka samowa ba?" Ta faɗa da mamaki.
Murmushin da ya auri fuskarsa muddin yana cikin gidan ya yi sannan ya ce "Wannan Sawu na biyar kenan na ɗebo, to uzurin fita ne ya kama ni da gaggawa shi ne na ke son ki sammun na yi wanka in ba damuwa Ranki ya daɗe."
Yar dariya ta yi "To to to, na gane jeka abinka Allah ya ma Albarka."
Ya amsa da Amin sannan ya shige banɗaki a gaggauce ya yi wanka, tare da canza kaya ya fice daga gidan.
Ita kuwa Mahee ko da ta ƙaraso dai-dai adireshin da ya bata sai ta ja ta yi turus, tana ƙarewa gidan kallo.
Kafin ta gama tantance ko adireshin da ta zo dai-dai ne, ta ga wani matashi ya fito daga gidan ya na shan taba sigari yayin da wasu saurayi da budurwa suka zo suka shige hannunsu na sarƙe da juna.
Shanye mamakin da ya zo mata ta yi tare da ɗauko wayarta ta kuma kiran Ja'afar, sai dai wannan karon ma bai ɗaga ba. Hakan yasa ta shiga zullumi da tashin hankali fiye da farko.
'Tabbas fushin da Ja'afar yake da ni ya yi tsanani tun da har na zo ya kasa ɗaga kirana.' ta faɗa a ranta.
Tana nan tsaye tana tufka da warwara, ta saƙa wancan zaren ta kunce wannan. Sai ga kiransa ya shigo wayar, sosai ta yi mamaki ta so ta ja aji sai dai a wannan karon ba zata iya ba, domin ba ita kaɗai ba hatta wayarta ta yi kewar kiran Ja'afar. Bata san lokacin da ta kai hannu ta danna malatsin karɓar wayar ba.
"Kin ƙaraso ne?" Ya watso mata tambayar da yanayin fushi-fushi.
Cikin ɓarin baki ta ce "Ina ƙofar gidan da ka kwatanta mun tun ɗazu."
Wani irin tsananin murna ne ya kama shi don ganin haƙarsa ta kusa cimma ruwa, saura kaɗan ya buga ihu har ɗan tsalle ya yi saboda murna sannan ya ce "ki ƙara haƙuri kaɗan Babyna gani nan ina ƙarasowa zuwa gare ki muradına." Ya faɗa cikin murna duk da bai so bayyanar da hakan ba.
Can bayan kamar mintuna Goma ta hango shi tafe akan Babur ɗin haya. Daga nesa kaɗan mai Babur ɗin ya sauke shi.
Cikin tafiyarsa ta ƙasaita yake nufo ta ya sha ado cikin ƙananun kaya, t-shirt ja da wando dark blue ɗamamme, ya taje sumar kansa ya yi kyau abunsa sai ƙamshi yake zubawa.
"Sannu da zuwa sarauniyar kyawawa ta duniya." Ya faɗa yayin da ya ƙaraso dab da ita.
Ƙamshin fitinannen turarensa ne ya daki hancinta, ta ja dogon numfashi ta sauke domin tabbas ƙamshin turaren yayi mata daɗi.
Matsawa ta yi kaɗan tare da kawar da kai gefe ta ce "Yawwa Babyna, amma ba zan ɓoye maka ba a'iya jiya kaɗai ka yiwa zuciyata babban rauni, da ace ban ganka ba a yau tabbas komai zai iya faruwa da ni."
Ƙayataccen murmushi ya jefe ta da shi sannan ya ce "Ai shi ke nan Babyn komai ya wuce yanzu tunda gani mu ƙarasa daga ciki ko?"
"Ina jin kunyar su Umma ne, da mu yi zancenmu a nan ina son komawa da wuri." Ta faɗa.
Kallon sakarai Ja'afar ya mata a ransa ya ce 'Wannan wace iriyar Sakara ce da take tunanin zan kawo ta gidan iyayena? A dai yanda na ke ƙaunar iyayena ba na jin zan iya barin kyandiri ɗaya da zai haska masu ko ni asalin waye a yanzu, domin bana son damuwarsu.'
A zahiri kuwa cewa ya yi "Haba Babyn kada ki saka na fara tunanin ko ba kya ƙaunata ne mu je ciki mana."
Ba don ta so ba ta bi bayansa zuwa ciki zuciyarta na tsananta bugawa.
Tun farkon shigar su take ƙarewa gidan kallo tana son tantance abunda ke shirin faruwa.
Bin ko'ina take da kallo, gida ne Babba ga ɗakuna nan jere riras kamar dai gidan haya, idanunta suka hango mata wasu tarin 'yanmata da samari zaune a kan tabarma suna buga lido sai shewa suke ana tafa hannu.
Sai wasu tsirarun 'yanmata dake ta yawo da shigar tsiraici a jikinsu.
Saurin runtse idonta ta yi, nan take fargaba da tsoro suka yi dirar mikiya a zuciyarta. Ji ta yi kamar ta ja da baya ta falla da gudu, sai kuma ta dake.
Haƙiƙa wannan gidan bai yi kama da keɓaɓɓen gida na ma'aurata ko kamilan mutane ba. Ko da gidan haya ne tabbas wannan sai dai ya ci sunan gidan 'yan'bariki.
A kiɗime ta kalli Ja'afar yayin da yake ƙoƙarin kunna kai cikin ɗaya daga cikin ɗakunan da ke gabansa.
"Baby.... Me muka zo yi a nan? Ni fa na ruɗe na kasa gane komai." Ta faɗa murya na rawa.
Haɗe girar sama da ƙasa ya yi ya ce "Saida ki zan yi, da Alama katon kankin nan zai yi kuɗi."
Ganin yanayin fushi ya dira a fuskarsa cikin ƙanƙanin lokaci, ya sa ta haɗiyi wani yawu mukut ta ce "Yi haƙuri don Allah ba haka nake nufi ba, ka fahimce ni."
Dubanta ya yi har yanzu dai bai sake fuskar ba ya ce "Habah! Ai ni kin ban mamaki Babyn dama can ba ki yarda da masoyinki ba? Ke kin san ko wani na ga zai cuce ki bana bari ba bare har ni da kaina."
Ya faɗa cikin daɗin baki.
Wani sashe na zuciyarta na gaya mata kada ta yarda da shi domin maza ba su da tabbas, yayin da wani sashe na zuciyarta ya ƙaryata sashe na farko tare da ƙarfafa mata gwuiwa akan ta bi bayansa.
Da ya tabbatar ya yi nasarar ɗorar da ita kan yaudararsa sai ya shige ciki. Cikin ɗar-ɗar ta bi bayansa.
*Rashin sani ya fi dare duhu*
Tabbas ƙaddara ba a iya kauce mata, kuma ko wacce ƙaddara da mafarinta, da Mahee ta san irin tarin ƙalubalai da fitinar da zata afka mata bayan shiga wannan ɗakin tabbas da ta gujewa duk wata hanyar da za ta sada ta da wannan ƙaddarar.
Bayan kamar awa biyu Maheerah ta fito daga Napep tana rangaji kamar za ta kifa da ƙasa.
Allah ya sa lokacin duhun Magriba ya fara sauka kuma mafi yawan mutanen unguwar suna masallaci a lokacin. Hakan ya bata damar shigewa gidansu ba tare da kowa ya ganta ba.
Ko sallama bata yi ba ta faɗa gidan tana layi irin na 'yanmaye sai haɗa hanya take, a haka ta samu ta faɗa ɗakinta tare da zubewa kan katifar ta fara sharar barci cikin wani irin yanayi da bata taɓa samun kanta a ciki ba.........
Ko da Umman ta idar da sallah sai ta fito waje tana mamakin ya aka yi har yanzu Maheerah bata dawo ba? Tana cike da fargabar kada Malam Isah ya dawo gidan ya tarar ba ta nan ta shiga uku, domin tana sane da cewa kanta laifin zai sauka, don haka ta koma ciki ta ɗauko wayarta ta komo waje tana ƙwalawa 'yar tata kira.
Ga mamakinta sai ta ji ƙarar wayar a cikin ɗaki don haka ta nufi can. Tana zuwa ta tarar Mahee na barci ko hijabin jikinta bata cire ba.
"Ikon Allah! Ni Indo yau Ina ganin abu, yaushe wannan ta dawo? Ko sallamarta ban ji ba." Ta faɗa tare da kama haɓa.
Nan ta shiga bubbuga jikin Maheen tana faɗar "Mahee ki tashi ki yi sallah, daga dawowa sai barci.?"
"Mahee!! Wai wannan barcin lafiya ne?" Ta kuma faɗa yayin da take girgiza jikinta a karo na barkatai amma ko gezau ba ta yi ba balle ta saka ran za ta tashi.....