INA HUJJAR TAKE: LABARI MAI SOSA ZUCIYA, FITA TA 11
Page 11
Lantai ta dubi ɗan aiken ta taɓe bakinta ta ce, "Shi da kansa mai garin ne yace ban da Lantai Inna Kande kawai yake buƙatar gani ?
Ɗan aiken ya ɗaga kansa alamar haka ne, ta kuwa kalli Inna Kande ta ce, "Ki je abinki Inna Kande tunda ke kaɗai yake son gani, ni kuma da nake son ganinsa da kaina zan iske shi."
Inna Kande ta dage bata zuwa da farko sai da Lantai tai mata raɗa sannan ta miƙe ta ɗauki gyalenta ta bi ɗan aiken suka nufi gidan mai gari.
Lantai ta shige ɗaki da gudu tana kwasar dariyar abin da akai jiya gidan mai gari.
Tasan dai bai isa fara zama ba sai dai yayi tsaye kamar bafade yau don tasan yanzu wajen yayi tsami.
Inna Kande suna zuwa suka iske ƙofar gidan mai gari cike da mutane domin dai labari ya buɗe ƙauyen na abin da ya faru.
Mai gari na tsaye sai cika yake yana batsewa yana jiran yaga da fitsararriyar yarinyar za'a zo koko ? Tabbas idan da ita aka zo sai ya fara korar mutanen wajen kafin ya faɗi musabbin kiran Kanden.
Sai kuwa ya ga Kande ita kaɗai ba marar kunyar yarinyar tare da ita.
Inna Kande ta Samu waje ta zauna ta miƙa gaisuwa.
Mai gari ya dubi mutanen wajen rai ɓace yace, "A yau ni mai gari ina son kowa da kowa ya shaida cewa na kori Kande daga wannan garin ita da ƴar banzar jikarta Lantai."
Daman kowa yasan abin da zai ce kenan , abin kuwa yayi ma mutane da dama daɗi agun domin dai Lantai fitina ce a ƙauyen.
Nan kowa ya bada goyon baya ana ta ƙara kuranta mai gari shi kam sai cin magani yake yana hararar Inna Kande don har zuwa yanzu Allah kaɗai yasan yadda yake ji don azaba.
Inna Kande ta miƙe jikinta sanyi ƙalau tana tunanin inda za su koma kuma tunda kowa yasan idan mai gari ya kori mutum ya koru a ƙauyen nasu.
Tana zuwa gida ta iske Lantai da littafin jarumin nata sai karatu take tana halin nata watau kuka ita kam har bata son Lantai ta fara karanta littafin nan don yini take kuka tana kiran sunayen mutanen cikin littafin tamkar suna gabanta tai ta surutu.
Inna Kande ta dubi Lantai ta ja uban tsaki ta ce, "Burinki ai ya cika tunda kin sa mai gari ya koremu daga ƙauyen nan ai Lantai."
Lantai fa karatu take tana ta kuka tana ƙarawa.
Sai da Inna Kande ta fisge littafin sannan ta zabura tana cewa, "Yi haƙuri Inna Kande har kin dawo ?
Inna Kande ta jefar da littafin kafin ya kai ƙasa Lantai ta cafke shi tana ajiyar zuciya ta dubi Inna Kande hankali tashe ta ce, "Na rantse da Allah Inna Kande da littafin nan ya samu matsala gara ƙauyen nan ambaliyar ruwa ta cinye shi ko kuma ace ...
Bakinta Inna Kande ta buge cike da ƙarin takaicin da ta bata ta ce, "Sakaryar banza sai ki tashi ki haɗa kan kayanki yau mai gari ya koremu daga ƙasar sa ai ."
Lantai dai ta dafe bakinta tana kallon Inna Kande cike da haushin buge mata baki da tayi.
Kamar gaske Lantai ta haɗa iyayen kayansu masu dama ta ɗauka bisa kai kamar mahaukaciya Inna Kande ta ɗauki wasu suka fice Inna Kande na mitar duk inda suka koma tasan Lantai ce zata sa a koresu ai.
Lantai kuwa gidan mai gari ta nufa kai tsaye sai nishi take don kayan ba ƙarya akwai nauyi.
Inna Kande ta bita a zatonta haƙuri Lantai zata je taba mai garin ba mamaki ya haƙura ya barsu su zauna don yanzu haka sai dai su je can Mahuta su zauna gun danginta kafin Hafizu ya zo daga Maraya asan yadda za ai.
Suna zuwa kuwa mai gari ya ƙara tumbatsa a zatonsa haƙuri Lantai ta zo ba shi.
Lantai kuwa tana zuwa gaban mai gari ta jefar da kayan sai da ƙasa ta cika idanun na kusa da ita harda mai garin ta buga tsalle ta haye saman kujerar mai garin ta kwaɗa kiran sunan Inna Kande da ƙarfin gaske tana cewa.
"Inna Kande don Allah zo ki ɗora min kayan nan a bisa kaina."
Inna Kande ta wuce ta kama kaya da ƙyar ta ɗora mata su ta bita da ido don bata san abin da take nufi da hakan ba.
Lantai ta dubi jama'a ta dubi mai gari ta buɗe baki sosai yadda kowa zai ji ta ce, "Mai gari kace wai mu bar maka ƙasarka ?
Mai gari ya ƙara haɗe rai yace, "Tabbas ni mai gari na baku umarnin ku bar min ƙasata yanzu ba sai anjima ba."
Lantai ta sake cewa "Jama'a kuna dai jin me mai gari yace ko ? Yace mu bar masa ƙasarsa ko ?
Jama'a akai tsit don kowa yasan Lantai shakiyyar gaske ce yanzu ta ja ma mutum bala'i ba ruwanta.
Ta dubi mai gari cike da gamsuwa da abin da zata ce masa ta ce, "To mun ji mun amince za mu bar maka ƙasarka amma ka naɗe taka mu zauna akan ta mai kowa mai komi wato Ubangiji.
Daman ni na rantse da Allah na gaji da ƙasarka don babu wani cigaba cikinta sai ci baya.
Don haka ka naɗe abarka mu za mu zauna kanta Ubangiji sai ta fi albarka ma."
Sai mutane suka fara kallon mai gari suna sunne kai ƙasa.
Lantai ta fasa ihu tana cewa, "Don Allah mai garinsu ka naɗe ƙasarka ko na sauka kan ta Ubangiji ni."
Sai mai gari ya fara haɗe miyau mukut don bai taɓa tunanin wannan yarinyar zata ce masa haka ba.
Yayi ta kallon mutane yana son ko Allah zai sa wani ya tsawatar mata don sai kuka take tana ihu ita jiransa take ya naɗe ƙasarsa ta sauka kan ta Ubangiji.
Mutane kuwa sai abin ya basu dariya yanzu don mai gari sai zufa yake yana ƙarawa duk ya muzanta.
Lantai ta kalli mai gari ta ce, "Wai mai gari ko dai baka iya naɗe ƙasarka ne sai jira nake amma ba alamar zaka naɗe ɗin."
Mai gari ya dubeta cike da tashin hankali yace, "Lantai wai ke wace irin yarinya ce marar kunya ? Ina kika taɓa jin an naɗe ƙasa ne a rayuwarki ?
Lantai ta dubi mai gari cikin muryar kuka ta ce, "Tunda ka ce taka ce ai sai ka ɗauke abinka mu dai ko mun samu mu zauna kan sabuwar ƙasa."
Wasa-wasa mai gari yayi juyin duniyar nan da Lantai tabar maganar ya naɗe ƙasa amma kamar yana ƙara tunzura ta.
Mutane har sun fara cewa to mai garin ya ɗauke ƙasar mana tunda haka ne ?
Mai gari daya fahimci idan ya sake sai Lantai ta cire duk wata kima tashi a idon mutanen ƙauyen sai ya nemi da yasa mu ya lallasheta su bar gun tunda sauran darajarsa a idanun mutane .
Ya dubi Lantai yace, "Lantai ki sauko ki koma gidanku ni daman wallahi wasa nake maku ba inda za ku ai an riga an saba da ku."
Lantai ta dube shi da ido ɗaya ta ce, "Ni dai ka naɗe taka mu sauko don Allah na gaji sosai akan taka ƙasar."
Mai gari ya dubi Liman yana so ya saka baki tunda unguwar su Lantai yake.
Liman kuwa ya fahimta don haka ya dubi Inna Kande yace, "Kande ki kama jikarki ku koma gida mai gari zai aiko maku da kayan abinci dana cefane."
Mai gari ya dubi Liman da sauri cikin ransa yana cewa ko ubanwa yace yayi mata kyautar ?
Lantai ta sake fashewa da kuka ta ce, "Ni fa ba zan sauko ba sai mai gari yaba Inna Kande haƙurin zagin da yayi mata ɗazun."
Mai gari ya kalli Inna Kande dake tsaye duk ta gaji saboda uban kayan da aka ɗora mata akai yasan kuwa duk aikin Lantai ne yace, "Kande don Allah ki min aikin gafara komi ya wuce daman rashin sani ne ya sa komi ya faru ."
Daga ƙarshe sai da kowa na gun ya saka baki sannan Lantai ta haƙura ta sauko daga kan kujerar mai garin ta washe bakinta ta ce, "Mun gode da kyauta mai gari amma don Allah idan azumi ya zo ka daina shanye sikarin da ake kawowa daga Maraya da gero muna so muma ai ."
Mai gari dai so yake yarinyar tabar wajen don haka komi ta ce sai yace an gama jikar Kande.
Cike da fara'a ta dubi tsaffin dake zaune gun ta fito da littafinta ta dube su ta ce, "Zan dinga koya maku karatu ta hanyar karanta maku labarin baya wanda wani haziƙin marubuci jarumi kuma ya dage ya rubuta wanda akwai darasin rayuwa sosai a cikinsa mai suna INA DA HUJJA nasan kun san daga jin sunan labarin akwai abubuwa cikinsa na ƙaruwa .
Don haka zamu dinga zama safe da dare ina karanta maku duk ranar asabar da Lahadi saboda makarantar da nake zuwa .
Duk wanda bai zo ba kuma sai na yi maganinsa Allah."
Ba wanda yayi ko tari suna ta kallon ikon Allah wai yarinya ƙarama da shegen kicihi da neman suna tare da neman ayi .
Lantai kuwa tana ganin littafin bata san lokacin data fara karanto littafin ba cikin farin ciki .
Ɗaya bayan ɗaya suka watse ba tare data ankara ba sai da Inna Kande ta taɓota sannan ta ɗago kanta taga babu kowa hatta mai garin daga ita sai Inna Kande a wajen.
Ta kuwa ji haushi ta matse littafinta ta kwasa da gudu Inna Kande na kiranta ko ta waigo kai tsaye ta nufi ƙauyensu Barbushe tana kuka .
Barbushe yau bai fita farauta ba domin haka kawai yake jin bai jin daɗi zuciyarsa na masa zafi sai bankar taba yake da wiwi yana doka tsaki.
Innarsa tai maganar duniyar nan amma bai kulata ba domin ko buɗe bakinsa bai iya yi don azabar ɓacin rai idanunsa tamkar garwashin wuta don tsabar jan da yayi.
Su kansu yaran nasa yau kowa a tsorace yake domin duk ranar da Barbushe yake haka tabbas sai ya zubar da jini yake samun sauƙi.
Kawai jin kukanta sukai tamkar wadda uwarta ta mutu gabanta ta ratso ta bayan gidan tana waige kamar wadda aka biyo.
Barbushe na zaune yana ta bankar wiwi ya ji kukanta da hanzari ya fito su kai karo ta faɗa jikinsa ta fashe da sabon kuka kamar zata siƙe.
Wani irin uban ihu ya saki wanda sai da tsoro yasa Lantai kusan sumewa tayi luf a jikinsa .
"Na rantse da wanda raina yake a hannunsa a yau babu babba babu yaro ba sani ba sabo duk ɗan jarfar bura'uban daya taɓa min Nuratu sai na zubar da jininsa ya kwarara a doron ƙasa."
Nan take yaran suka ɗauko kayan faɗan su , suka zagaye shi suna jiran umarni.
Lantai jin abin da yace yasa ta saki murmushi ta cigaba da sauke ajiyar zuciya kamar gaske.
Tambayarta yake waye ya taɓa ta a duk faɗin duniyar nan ?
To ko me Lantai zata ce ?
Haupha
managarciya